← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 145

Sashe 4

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"A'a, Wallahi mun je Asibiti uku duk sai ace mana ba gado, a na ƙarshen ne aka ce mana wai yajin aiki likitoci za suyi, shine aka kwatanta mana nan"

"To ai Hajiya sai kun buÉ—e file sannan likita zai ganku"

Ta ce "To nawa ne buÉ—e file É—in?"

"Naira dubu biyar ne, single file"
Turus tai, dan kuɗin hannunta dama dubu bakwai ne, sun ƙarar da biyu a yawon Asibitoci.

Dubu biyar É—in kenan ta rage a hannunta, a sanyaye ta ce "To a buÉ—e mana"

Haka ta biya kuÉ—in nan, aka buÉ—e musu file, bayan an buÉ—e aka ce su biya dubu uku kuÉ—in ganin likita.

Ta kalli Nurse É—in ta ce "Wallahi suke nan a jikina, ki taimaka min baiwar Allah, kar in rasa É—ana, dan Allah ku duba shi"

"Baiwar Allah, ba fa Asibiti na bane, kuma ba Asibitin gwamnati bane, haka ƙa'idar Asibitin take.

Ta koma gefe kawai ta fashe da kuka.

Wani dogon mutum ne fari sol, ya fito daga wani ɗaki jikinsa sanye da farar rigar likitoci, Nurses na biye da shi sun riƙo masa files, ganin mace ta saka ɗa a gaba tana kuka ya sa ya tsaya ya kalleta ya kalli yaron ya ce "Lafiya baiwar Allah, baki san akwai marasa lafiya a kwance ba kika ware murya kina wannan kukan?"

Cikin kukan ta ce "dan Allah likita kai min rai, ka dubamin yaron nan, dubu biyar É—in kenan na biya kuÉ—in buÉ—e file, kuma yanzu ance sai na biya na ganinka dan Allah ka dubamin shi".

Ɗan shiru yai yana kallon ta, daga bisani ya durƙusa ya tattaɓa yaron, ya buɗe idon yaron, sannan ya miƙe tsaye yace "ku biya naira dubu hamsin, kwantar da yaron za'ai ya galabaita sosai"

Daga haka bai kuma cewa komai ba, ya fara tafiya.

Take hawayen idonta suka bushe jin an ambato dubu hamsin, dan basu da ita ba su da dalilinta, dan Mai_ gidanta ɗan acaɓa ne.

Jiki na rawa ta ɗakko 'yar ƙaramar wayar ta mai madannai, ta nemi lambar mijin nata, cikin kuka tai masa bayanin halin da ake ciki.

Yace "ki kwantar da hankalinki, kice su yi masa duk abun da ya dace, zan bada jinginar babur É—ina, in kawo kuÉ—in.

Allah sarki uwa, kamar zata zare haka ta kuma tashi, ta nufi ofishin likitan nan, ta tarar yana duba wani mara lafiya, a hanzarce ta ce "likita dan Allah ka zo a fara bashi magani, babansa yace gashi nan zuwa zai zo ya biya kuÉ—in"

Cike da ƙosawa da ƙufula ya ce "hajiya baki ga mara lafiya nake dubawa bane? Mu nan Asibitin bama haka, ki je idan kun kawo kuɗin a bashi maganin, kar ki sake shigo min office haka ba izini"

Da ƙyar ta iya jan ƙafafuwanta da su kai mata nauyi, ta bar office ɗin, ta koma in da ta kwantar da yaron, sai jijjiga yake, jikinsa rauu da zazzaɓi, bakinsa se zubar da dafara yake, ta samu guri ta zauna ta ɗora yaron a kan ƙirjinta tana jin yadda zuciyar sa ke bugawa, kamar zata fasa ƙirjinsa ta fito. Ta lumshe ido tana zubar da hawaye tana kallon yadda kumfa ke fite a bakin yaron, amma cikin ma'aikatan ba wanda ya kalle su da idon tausayawa.

Tana nan a zaune sai ga mijin nata kamar korarrare ya shigo hankali a tashe, ya ƙarasa in da take zaune da yaron yana faɗin "Zainabu, an duba shi kuwa?"

Kasa Magana tai sai sake rushewa da kuka, yace "ki kwantar da hankalinki, na bada jinginar babur ɗina, na karɓo kuɗin a gurin maƙocinmu, a ina za'a biya kuɗin?"

Ta nuna masa reception, in da zai je ya biya, ya je ya biya ya zo ya É—auki yaron, ya rungume shi a jikinsa, da receipt É—in biyan kuÉ—in a hannunsa.

Aka nuna musu ofishin likitan, Ya shiga da yaron a jikinsa, likitan ya kalle shi ya nuna masa gadon da ke cikin Office É—in yace ya kwantar da yaron ya je waje.

Haka ya kwantar da shi ya fice, ya koma in da ya bar matarsa ya dinga rarashinta yana bata baki.

Nurses É—in jira suke suga doctor ya taso ya duba yaron, amma yace "This boy will not survive, da tun zuwansu sun ba da kuÉ—i ne, da maybe mu iya ceto shi, but for now, ba zai surving ba"

"But doctor, da an jarraba dai ko Allah zai sa a ceto shi" wata Nurse tai Maganar cike da tausayawa.

"Will you shut up, zaki koyamin aiki ne?" Yai maganar yana zazzare ido.

Ta ce "No am sorry Sir"

Wata matashiyar budurwa ce, sanye da uniform ta shigo hannunta da file ta kalli likitan ta ce "Doctor, 'yan uwan matar nan da za'aiwa CS a cikinsu duk babu me irin blood group É—inta, Amma an samu mai O negative a cikinsu, wanda zeyi daidai da jinin Alhajin nan da aka rasa samun jinin da za'a saka masa"

Ya ce "ok, yanzu abunda za'ai shine, ku ɗebi 2 pints of blood, a jikin shi mai O negative ɗin, sai kun ɗiba zuwa anjima sai ku ce musu kun sake gwadawa  jinin bai yi ba, su sake samo wasu mutanen, idan ya so a siyarawa da Alhajin jinin, 20thousands each pints, leda biyu 40 thousands kenan"

Tace "ok Sir"

Ya cigaba da sabgar gabansa, yayin da wannan yaro na kan gado ya cigaba da convulsing, ya kai mintuna talatin a haka, daga bisani rai yai halinsa.

Sai da yaron ya rasu, Sannan Ya miƙe ya saka safar hannu, yai parking ɗin gawar, sannan ya fita daga office ɗin, cikin rige rige iyayen yaron suka ƙaraso suna tambayar ya jikinsa, cikin ko in kula doctor GY yace "He's gone, Allah yai masa rasuwa"

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" shi suka dinga maimaitawa, yayin da mahaifiyar yaron ta koma gefe tana zub da hawaye, shikenan guda É—aya yaron, shima gashi ta rasa shi.
Shi kuwa doctor G.Y yai gaba abunsa.

Wasu daga cikin patient suka dinga bata baki, akan tayi tawakalli Allah ya bata wani.

Cikin kuka ta kalli Nurses ɗin tace "Wataƙila da kun taimaka mana, ko da magani ne lokacin da muka zo yana suma, da wata ƙila bai rasu ba"

Wata Nurse tace "ki ji min mata kamar jahila, maza kiyi saɓo kinji, mutane kamar ba musulmai ba ba tawakalli"

Duk dauriya da jarumta irin ta namiji, sai da mahaifin yaron yai kuka, yace "ki dena faɗar haka Zainab, kinga hankalin mutane ya fara dawowa kan ki, ana gaya miki magana, Khalifa lokacinsa ne ya riga ya yi, Allah ya karɓe shi, Allah ya jiƙansa bari in je in samo adaidaita sahu, mu ɗau gawar".

Haka ya fita dan neman adaidaita sahun da zata kai su gida.

Bayan ya samu adaidaita sahun ya shigo Asibitin, ya koma reception ya tarar da wanda ya biya kuɗin Asibitin a gurinta ya ce "To, baiwar Allah tunda ba'a kwantar da yaron nan ba, Allah ya karɓi abunsa, ko ba duka ba dan Allah ku rago min kuɗin da na biya"

Jinjina kai tayi tace "Ga doctor Bulama can, shine mai Asibitin wanda ya duba É—anka, kaje ka same shi kai masa bayani".

Bai yi ƙasa a gwiwa ba, yabi bayan doctor Bulama, tare da maimaita masa abunda ya gayawa receptionist.

A wulaƙance ya dube shi sannan yace "Ka taɓa ganin wanda ya je ƙiyama ya dawo?"

Ya girgiza Kai yace "A'a"

"To nan Asibitin, no refundable after payment, kuɗi sun riga sun shiga asusun Asibiti, dan haka sai dai ka haƙura".

Kamar zai shige cikin doctor Garba, haka ya duƙa yana cewa "Dan Allah ka taimaka min, Wallahi babur ɗina da nake neman Abinci na bada jingina, na karɓo kuɗin"

A fusace doctor yace "kaga i have something to attend to, ka san ba ka da ƙarfi meyasa ka taho nan?"

"Wallahi an rasa gado ne, kuma akace ma yajin aiki likitoci za su tafi shiyasa, dan Allah ka temaka mana..."

Ai bai tsaya saurar sauran zancen ba, ya wuce a bar shi a gurin, ɗauke da baƙi ciki goma da Ashirin!.

Kantagora Army barrack Naija state, nan ne in da aka kai gawarwakin sojojin da suka rasa ransu, da wanda a kaiwa rauni, kai tsaye aka wuce da su babban Asibitin da ke cikin barikin sojojin.
Duk in da Faruk ya saka ƙafarsa, a nan yarinyar nan take mayar da tata ƙafar, ita kaɗai a cikin zaratan sojojin nan sai binsu take.

Wani Babban soja yai umarni da a kaita cikin yaran da aka kuɓutar, ko itama a samu nata iyayen.

Wani soja ya ce "To ai wannan yarinyar ba tai kama da 'yan Nigeria ba ma, ko ma dai daga maƙotan ƙasashen nan akai kidnapping ɗin ta?"

Faruk ya ce "i have no idea about it, abunda na sani shine ba ta cikin wancan yaran da aka kuɓutar, dan haka ba cikin su Yakamata a haɗata ba, daban za'ai cigiyar iyayenta, abunyi Yanzu shine ko Madam Halima ce a bata ita ta zauna da ita, kan a san abunyi akanta".

Su kai na'am da shawarar da Faruk ya bayar, akan ta zauna a gurin Madam Halima, itama soja ce a cikin tawagar, mijinta ma soja ne suna zaune a nan cikin barrack É—in tare.

Madam Halima ta kalli kyakkyawar fuskar yarinyar, wadda tai duƙun duƙun, 'yar rigar jikinta tai futu futu da datti, ga gashin kanta a hargitse duk datti da ƙasa.

Cike da tausaywa yadda 'yar ƙanƙanuwar yarinyar tai rayuwa a hannun 'yan ta'adda babu kulawa ta ce "ya sunan ki?"

Maimakon ta amsa sai tai ƙuri da ido tana kallon Madam Halima.

"Ya sunan ki na ce?" Madam ta kuma maimaitawa, amma shiru ba tai responding ba.

Faruk ya ce "ina ga fa ba ta Magana, da tunda aka tsinto ta banji tayi Magana ba".

Madam ta ce "Allah sarki, Allah kaÉ—ai ya san halin da iyayenta ke ciki, ai ita ma a Asibitin zamu bar ta a duba lafiyar ta tukunna"

Faruk ya ce. "ok hakan ya yi".

'Yan matan nan ma da aka kuɓutar, duk nan Asibitin cikin barrack aka kawo su, dan binciken lafiyar su, kafin a miƙa su ga iyayensu.
Chapter 4 · 0% Book details