Sashe 1
Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
[9/30, 8:55 PM] Abk: *✷ DARE DA DUHU ✷*
_Bright pens ofâœðŸ¾_
Nimcyluv
Ayushercool
Zee kumurya
1......
Saukar ruwan saman, bai hanashi tafiya da sauri a filin Headquarter, dake nan Abuja ba. Cikin izza, taƙama, da taurin zuciya irinta sojoji, yake taka ƙafafuwan nasa, ruwan na sauka da ƙarfi a jikinsa, da ka ganshi kaga ingarman namiji.
Gaba ɗaya sansanin sojojin cike yake, da manya da ƙana nan sojoji. (Part of Nigerian Armed forces headquarters Abuja, Motto (s) victory is from God Alone!".
Gaba ɗaya sojojin dake cikin Headquarter ɗin, basu damu da ruwan dake sauka kamar da bakin ƙwarya ba, wasu na tsaye, wasu na zaune wasu kuma suna abinda ya shafe su, wasu kuma suna in da babu ruwan suna shan Cigarettes (sigari).
Tun yana tafiya da sauri har ya fara daidaita tafiyarsa ,wanda daman hakan al'adar sa ce, duk inda ya gilma cikin Headquarter É—in hannu ake sara masa zuwa sama, alama dai shi É—in Babban mutum ne, matsayi mai girma gareshi a cikin sojojin.
Wani office ya nufa cike da nutsuwa, yana zuwa aka bashi hanya ya shige, yana shiga office ɗin ya ƙame!.. tare da ɗaga hannunsa sama alamar girmamawa da masu ɗamara kewa junansu. Sojan da yake zaune sanye da kaaki, yayi Murmushi cikin sakin fuska yace
"Have a seat.." yai Maganar yana nuna masa kujera.
Kamar ba zai zauna ba, se kuma ya zauna saman Kujera. General Ibrahim A.M ya kalli matashin saurayin dake gabansa kafin yace "Munyi magana da Chief of Army staff, akan Operation da za'a fita, aiki ne mai wahala kuma bama son, Kidnappers É—in su samu information na aikin nan, dan opretion ne me hatsarin gaske, yana da kyau ku kula, bamu da tabbaci kowa zai dawo da rai acikin ku, dan kun san komai dai"
Matashin dai kansa yake a ƙasa, yana sauraren General babu alamar zai magana, ya tattara dukkan nutsuwarsa yana sauraren shugaban nasa.
General Ibrahim ya buÉ—e wani file yana dubawa kafin ya kalli saurayin yace
"Hope you are ready for it, and kayi sallama da iyalanka?" .
Sai a lokacin Matashin saurayin ya ɗaga idanunsa wanda sukai ja sosai ya kalli General Ibrahim, kallon da yake masa yasa General Ibrahim faɗin "Oh, I forgot you just came back from Zamfara yesterday"
Matashin dai bai ce komai ba, da Idanu kawai yake bin General.
General Ibrahim yace "Zaka iya tafiya, jirgi na jiranku a airport, and airforce zasu rigaku zuwa ku kula da kyau akan dukkanin bayanan da zasu baku, da kuma umarnin da zaku samu daga garemu"
Matashin saurayin ya miƙe tsaye yace "ok sir" tare da sake sara masa, sannan ya juya, yana tafiya a hankali har ya fice daga cikin office ɗin General Ibrahim.
Cikin nutsuwa General Ibrahim ya ɗauki Wayarsa tare da danna wasu lambobi, babu jimawa aka ɗauki wayar daya kira, ƙasa ya yi da Murya yace
"Akwai kyakykyawan labari" daga cikin wayar wata shaƙaƙƙiyar murya ta bayyana akace "Mene labarin?"
General Ibrahim ya ce "Chief of Army staff, ya bada umarni ga Sojojin da suke Headquarter na nan Abuja zuwa Naija state, kai tsaye kuma cikin Dajin Zugurma in da kuke tsare da yaran nan, kuma a wannan karon sun samu cikakken ikon yin harbi, umarni ne daga NAC. _Nigerian Army council_"
Mutumin da General Ibrahim ya kira ya yi dariya kafin ya ce. "Ganganci haihuwa da damuna, a tunaninsu zasu Iya ƙwace ƴan matan da mukai kidnapping ne? Bayan gwamnati ta hanamu abinda muka buƙata?"
General Ibrahim yace "Na kira dai dan in sanar maka da zuwan su, a Kowane lokaci sojojin sama zasu tsinkayi dajin, nine zan tsara komai na Operation É—in tare da jami'anmu na nan Naija state, zan sanar maka da duk wani arrangement na yaÆ™in, kaga kuna da damar da zaku samu galaba a kansu, dan haka se ku shirya zuwansu"Â
Mutumin ya yi dariya yace "Daman ance da ɗan gari akanci gari, mune mutanan banza, kai kuma maci amanar ƙasa"
General Ibrahim ya yi Murmushi yace "To Rayuwar sai da haka, in ba haka ba a banza za ka gama aiki Kai retire amma na abinci ya gagareka, ko a kashe ka a banza gurin kare ƙasar da ta gaza biyawa masu bata tsaro buƙatunsu, dan haka zan tura maka account number, ka bani share ɗina saboda na samu labarin wasu daga iyayen yaran sun baku kuɗi akan ku sakar musu yaransu"
Mutumin yace "Zanci kaza kazanka, a gidan uwar wa zanga pos ko Networkina cikin tsakiyar jeji?"
Ibrahim yace "Haka ne, ka shirya min kuɗina zan san yadda zan in karɓa, dan Ina da buƙatarsu" yana faɗin hakan ya kashe Wayarsa, yana jin akan kuɗi babu abinda ba zai ba.
Tabbas da É—an gari ake cin gari.
Matashin na fitowa daga cikin office ɗin General ya nufi wani waje domin ɗakko jakarsa, tsaye ya yi ganin wata budurwa sanye da kayan sojoji ta nufu inda yake, hakan yasa ya ƙara haɗe ransa sosai. Budurwar mai suna Salima tace
"Haba Captain at least yau kayi min Murmushi, saboda kai nabar Maiduguri nazo Abuja" Wanda aka kira da Captain É—in, ya kalli Salima se kuma ya É—auke kansa, Salima ta haÉ—e rai tace
"Ban san me nayi maka ba, sama da shekaru biyar nake bibiyar ka, tun kafin kayi Aure" Captain ya gyara tsaiwa cikin tsare gira, murya a kaushashe yace "Bana harka da mutunan banza, ba zan mu'amala da karuwa kazar kowa ba" Yawo mai ɗaci Salima ta haɗiye tace "Yanzu har akwai mutumin kirki a cikin sojoji? Gashi nan kullum tara mata kuke, kuma mu matan dan mun nemi maza sai ya zama iftila'i, nifa a yau kace kana so na, zan zama iya taka kai ɗaya ban damu da matan da zakai harka dasu ba, indai zaka biya min tawa buƙatar"
tsaki Captain yaja tare da ratsa wa ta gefenta ya shige.. duk inda ya gilma sai yaga mace da namiji manne da juna tare da sheƙe a yarsu, ko kunya babu..
Sanarwa aka fara yi, wanda ya Sanya Captain É—aukan jakarsa, ya nufi filin wajan, Salima taso hadda ita za'ai posting zuwa Naija state.
Farar safiya ce, A ranar Asabar wanda yayi daidai ga 25 ga watan Mayu, shekara ta dubu biyu da goma sha ɗaya. Jirgin Sojoji ne (Helicopter). Yake shawagi a saman dajin Zugurma na jihar Naija state. Sosai jirgin yake zaga dajin ta sama, sautinsa ya cika ko ina a dajin, ya dinga bada wata irin amsa kuwwa.
Ƙarfe 12 daidai, jirgin su Captain na sojoji ya sauka a filin tashi da saukar jirage na Niger state, cikin ƙanƙanin lokaci suka kammala duk wani shiri da za suyi, suka nufi cikin dajin.
  Tafe suke a cikin manyan motocin yaƙi, ciki har da egwa yayin da wasu suke tafe a ƙasa, suna tafe suna 'yan iface ifacensu na sojoji, kafin samu umarnin cewar su tsaya su yada zango a wani guri, kasancewar sunyi tafiya me nisa, ba tare da jin wani ƙwaƙwaran motsi a dajin ba.
Daga cikin ɗaya daga cikin motocin, Wani matashi ne zaune, a kujerar mazaunin direba, Zame abin kansa yayi a hankali, yana fitowa daga cikin motar, Idanunsa akan wani matashi wanda yake gyara zaman bindigar sa, cikin rashin ko in kula na sojoji ya nemi waje ya zauna. Musulman cikin su na ƙoƙarin yin alwala suyi salla, wasu suna cin Abinci yayin da wasu suka keɓe suna shan sigari.
Captain Denial ya buɗe jajayen idanunsa akan wani soja yace "Ka gama naka aikin, tun da ka kawo mu cikin wannan jejin" ya faɗa cikin harshen turanci. ya shafa kansa yace
"War is not mine"
Captain Denial ya yi Murmushi yace "You go see" ma'ana zaka gani!.
Duk sun sauka daga motar, se wani soja wanda tun da aka sauka cikin dajin bai É—ago kansa ba, balle yayi magana. Daniel ya kalleshi kafin yace
"Captain Khamal" wanda aka kira da Captain Khamal ɗin, ya ɗago kansa a hankali, Baƙi ne shi sosai, irin baƙin nan mai kyau da kuma ɗaukan Idanu, ( _He's dark-skinned yet handsome_ ).
Kana ganinsa kasan bashi da son wasa, zuciyarsa a tsaye take! Tsayyen mutum akan ra'ayinsa, fuskarsa nan tasa a É—aure take koda yaushe. (But Friendly to his family).
"Akwai matsala ne?" Captain ya Girgiza kansa, yana ƙoƙarin sanya rigarsa ta uniform ɗin soja.
Ɗaya sojan ya nisa yace "Wannan yaƙi ne mai hatsari sosai, idan a kai nasara zaka iya samun matsayi mai girma, saboda kana ƙoƙari sosai akan harkar tsaro ka san aiki sosai, akwai yiwuwar ka samu ƙarin matsayi me girma, amma naga kamar baka farin ciki?"
Captain Khamal ya ware manyan idanunsa akan Jamil, cikin rashin damuwa yace
"Ihu zan tayi ke nan? Saboda na fito
yaƙi, za'a ƙaran girma? Ko mene?"
Jamil ya ɗaga kafaɗa tare da watsa hannunsa yace "Kada ka gayan ba daɗi Malam, ƙilan masifa ka haɗawa kanka, rabonka da Matarka watanni wajan biyar kenan, dole ka rasa walwala ga matan nan birjik kawai ka rage zafi, gaba ɗaya duniyar nawa take daga kano sai Abuja fa, amma ka takure kanka kamar wani gunki" Taɓe baki Captain Khamal ya yi yana gyara zaman bindigar sa, ganin yayi masa banza yasa Jamil faɗin "I advise you, as you best friend, not as coulliqe".
Captain yaja tsaki yace
"Ko kaÉ—an, mahaukacin banza ba abunda kake tunani bane"
Jamil ya ware idanunsa yana ƙoƙarin hana kansa dariya, ganin yadda Khamal ya hayyayaƙo masa, amma ya san tastuniyar gizo ba ta wuce ƙoƙi yace "Nine mahaukacin? Wallahi akwai wata yarinya tana zuwa gidana kullum, kawai zan bar baka ita, in mun koma Abuja" tsaki Khamal yaja yana yin waje yana faɗin "Dana aikata zina, gwara na mutu" yana faɗin hakan ya fita daga cikin motar. Jamil yabi bayansa da kallo yana Mamakin ƙarfin imani da haƙuri irin na Khamal, da yawan sojoji suna da hanyar ragewa kansu damuwa, amma banda Khamal da ya kasance me tsantseni.
Captain babban matsayi ne a cikin sojoji. A rank in the military and maritime service, and the highest-ranking company officer. A Captain gets three vertically aligned silver stars on the shoulders. This is the highest rank among the tactical troop organization. Idan ka shige matakin Captain ka fara hawa babban matsayi a Nigerian Army council (NAC).