← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 145

Sashe 97

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga cikin wayar mutumin ya ce "Haba Khair, kamar ba musulma ba, baki yadda da ƙaddara ba? Ki bi komai a hankali mana, idan kika dakatar da harkar kasuwanci shikenan a daina juya kuɗaɗen su lalace a haka? Bai kamata a dakatar da kasuwanci ba, a cigaba da harkokin idan ya so sai ayi binciken zuwa ƙarshen shekara idan Allah ya kaimu".

"Na gaji ne, na gaji da irin yadda abubuwa suke gidana a harkokina, akwai wani abu wanda ban sani ba, da nake buƙatar gano shi a nan kusa".

"Kiyi haƙuri ki bi komai a hankali, ki kwantar da hankalinki komai zai tafi daidai insha Allah"

"Shikenan, amma yakamata ko mai kake yi ka zo, ka san ka daÉ—e dai baka zo ba"

"Haka ne, zan zo insha Allah"

"Ok sai an jima" ta ajiye wayar jiki a sanyaye tana tunani.

Sallamar Abdallah ce ta katseta daga dogon tunanin da take yi.

Ta amsa masa ya ƙaraso ya zauna, a ɗaya daga cikin kujerun falon. Ya dubeta ya ce "Lafiya kuwa Ummi?"

Ummi ta É—an girgiza kai ta ce "Abdullah, Ina cikin damuwa a kan harkar kasuwanci na, gaba É—aya na kasa gane kan harkar nan, nayi waya da shi, ya ce mini yana nan zuwa, amma abin yana damuna".

Abdallah ya ce "Kiyi haƙuri tin da yace zai zo da kansa, ki ɗan ƙara haƙuri".

"Shikenan, bari ya zo É—in in ji shawaa da zai yanke, amma zan gaya masa dole a bincika yadda al'amuran nan suke gudana".

Abdallah ya ce "Hakane, Allah ya yi mana jagora".

Ta amsa da "Ameen"

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, kusan satin su Abra biyu a Dubai, al'amarin Adnan babu sassauci, dan ko zata ci Abinci tana amai sai ta ci, ko tana so ko ba ta so. Kuma bai fasa zuwar mata da buƙatarsa ta Aure ba, duk da yadda yanayin jikinta yake.
Abra ita kaɗai ta san irin wahalar da take sha a kan cikin nan, yana tsufa tana cigaba da shan baƙar wahala, wani irin zazzaɓi take wanda ba ta taɓa tunanin akwai irinsa ba, taji kamar ana sassara ƙasusuwanta, ga wani irin azabar raɗaɗi da take ji a ƙasan fatarta abin ba ya misaltuwa.
Ta ƙara wata uwar rama ga duhu tayi sosai, ga gashi yana ta zubewa ta rasa abin da yake mata daɗi, gaba ɗaya ta sake zama wata so silent.
  Satinsu biyu, suka baro Dubai sai dai babban abin da ya yiwa Abra daɗi da bata taɓa zato ba shi ne yadda suka sauka a Kano, wanda rabonta da Kano tun da aka ɗaura mata Aure aka kaita gidan Adnan.
   Taji daɗin ganin Mami, sai dai Mamin ta tsorata da ganin yadda Abra ta koma, amma sai tayi zaton kawai laulayi ne ya mayar da ita haka, ga cikin ya fito Sosai kai kace da ta durƙusa za ta haife shi.
Bayan Adnan ya kaita gida, a Hotel shi yaje ya sauka, ita kuma ya barta a nan gidan.
Ganin gidan ta din ga yi duk ya sauya mata, ta dinga tuna irin rayuwar da tayi a gidan, duk da irin cuzguna mata da Hajiya Na'ima ta din ga yi, amma rayuwar gidan ta fi mata daÉ—i a kan wadda take yi a yanzu.
Sai dai tana tuna cewa ba gidan mahaifinta bane, ita ɗin Tsintacciya ce, sai jikinta ya ƙara yin sanyi, amma duk da haka rayuwarta da Faris ta faɗo mata, rayuwa mai cike da ƙauna da soyayya.
Jiki a sanyaye ta ce "Mami, wai kuna waya da Faris kuwa? Nifa bani da lambarsa duk ina cikin damuwa".

"Wallahi Abra duk lambobinsa ba sa shiga, ina ta lallaɓa Abbinku ya je ya dubo mini shi".

"Garin yaya lambobinsa ba sa shiga? Ni tun da yaje gidana ban samu na karɓi lambarsa ba".

Cikin mamaki Mami ta ce "What? Me kike nufi yaje gidanki fa ki ka ce?".

"Eh mana Mami, bai gaya miki ya zo ba?".

Shiri mami tayi sannan tace "Yaushe ya je gidan naki?".

"Almost 5 Months ago, wai be zo nan ba?"

Mami ta ce "No ya zo, ban san yaje gidanki ba ne" da haka ta kawar da wannan hirar.

Abra kuwa satar jiki tayi, ta tafi ɗakin Salman, komai yana nan yadda yake, gani take tamkar zata ganshi kamar yadda ta saba, ta kalli katafaren hotonsa da yake ɗakin da wanda suka yi su biyu, a saɓule ta zauna a kan gadonsa, ta fashe da kuka "Please Faris come back to me, i need you my caring brother, am missing you, kalli halin da Yaya ta shiga, mai yasa kayi nisa da Angel ɗin ka, ma one and only caring brother" ta ƙarasa Maganar cikin kuka mai tsuma zuciya.

A hankali ta tashi zaune, ta shiga Gmail ɗin ta, ta fara rubutawa Salman saƙo mai cike da tsantsar nuna kewa, mai matuƙar ratsa rai da girgiza zukata, tana rubutawa tana zubar da hawaye, ta kammala ta ajiye wayar tare da lumshe idanunta.

Meenal ce zaune a kan makeken gadonta, tana kiran layin Usman, tun safe take kiran wayarsa amm yaƙi ɗagawa, ba ta haƙura ba ta cigaba da nacin kira, sai da babu zato ba tsammani taji ya ɗaga bai ko yi mata Sallama ba ya fara faɗa "Wai me kike nema a gurina ne, tun safe kin hanani sukuni kin addabeni da kira meye haka?".

"Haba Usy, ai ka É—aga kaji dalilin kiran ko?".

"Ba zan É—aga ba idan na É—aga me zan miki?".

Cikin shagwaɓa ta ce "Please calm down baby, dan Allah ka fuskance ni".

'malama ki faÉ—i abin da zaki faÉ—a ina da ayuukan yi".

"Amma ai naga yanzu ba lokacin aiki bane".

"Zaki faÉ—a ko sai na kashe wayata?"

Meenal ta marairaice ta ce "Yaushe zaka zo, sai mu yi magana".

"Haba Meenal, ai ni da gidanku har abada, ko har kin manta wulaƙancin da ki ka yi mini?"

"Dan Allah baby ka daina tunawa, sharrin shaiÉ—an ne, Please come to me haba My usy".

Usman ya ce "Ke dakata, ba wata yaudara ko kalaman ƙarya da zaki yaudareni da su in amince da ke".

Kawai ta fashe da kuka "Allah ba kalaman yaudara bane, dan Allah baby ka zo, Wallahi kai nake so".

Usman ya ce "Eh saboda wancan ya gudu ko?"

"Wallahi be gudu ba, kawai dai zuciyata kai take so".

"Kin manta da rashin ɗaga wayata, da wulaƙanci da ki ka dinga yi mini a kan saurayinki ko?".

"Dan Allah ka daina tunawa, kuskure ne ba zan sake ba".

"Shikenan zan yi shawara".

"A'a dan Allah ba sai kayi ba, Please Baby me, wlh Ina sonka Sosai na yi missing É—in ka".

'hmm Allah yasa da gaske ki ke".

"Wallahi da gaske nake".

"Shikenan zan duba".

"Yawwa Baby ina nan ina jiranka" bayan sun yi sallama tayi ajiyar zuciya ta kalli wayar ta ce "Gara tun wuri in yiwa kai na ƙiyamul laili, in lalaɓo shi ya dawo".

Jin Abra ta zo,  ya sanya su Ammi suka zo, suka cika gidan wanda hakan ba ƙaramin daɗi ya yiwa Abra ba, Mutanen da ba ta da wata alaƙa da su ta jini, amma suna nuna mata soyayya haka, har hawaye ta dinga yi wanda basu san dalili ba, suka din ga yi mata nasiha a zatonsu duk kewarsu ce ta sanya ta haka.
Sai da duk sun lura da irin ramar da tayi, ba wanda yayi Magana sai granny, da ta dinga bin ƙwaƙƙwafi a kan lallai sai ta ji mai ya samu Abra haka dan da alama ba iya laulayi ke damunta ba, amma Abran ta ƙi faɗa.

Kwanan Abra biyu Adnan ya zo ya ce tafiya za suyi, Abra tamkar ta ɗora hannu a ka tayi ihu, gashi tun da ta zo Abbi baya gari basu haɗu ba, ta shiga cikin fargabar komawa cikin uƙubar Adnan, amma ta koma duba abinda ka iya faruwa idan da ta sanar da halin da take ciki, haka nan ba yadda ta iya, ta bishi suka koma Kaduna.

Faris na zaune a aji ana mus lectures, sai dai ya ji bugun zuciyarsa na matuƙar ƙaruwa, ya rasa abin da yake masa daɗi, kuma ya rasa dalilin faruwar hakan, yayi ta maimaita "Hasbunallah wa ni'imal wakil" hakan ya sanya ya ɗan samu sassauci.

Malamin da ke musu lectures na Anatomy yace su yi connecting Wifi a system É—in su, zai tura musu wani abu.

Salman yana Connecting, yaga messages na shigowa ta Gmail É—insa, dan rabonsa da amfani da daya har ya manta.

Ana tsaka da lectures, amma hankalinsa na kan saƙonnin, ya fita ya tafi Gmail ɗin sa, ya ci karo da saƙon Abra. Cikin hanzari ya buɗe ya fara karantawa.
Subhanallah duk da yadda sanyin A.c ke Ratsa ko ina a ajin, amma wani irin gumi ne ya shiga karyo masa, ya kasa gane kan in da saƙon nata ya dosa gaba ɗaya, take jikinsa ya ɗau rawa ya kasa mayar da hankali a kan karatun.
Har aka kammala bai fuskanci komai ba, haka ya koma masaukinsa, ya karanta saƙon nan ya fi sau talatin yana sake jujjuya saƙon a zuciyarsa.
Tuni zuciyarsa ta fara raya masa ya bar abin da yake, ya shirya ya tafi Nigeria ya ga Abra.
"No she's married now" ya faɗa da ƙarfi yana rintse idanunsa.
So yake ya cire Abra daga ransa, ya manta da shafin soyayyarta, dan haka dole ya nesanta kansa da duk wani abu da ya shafe ta.
Kai tsaye ya fara ƙoƙarin goge message ɗin da ta turo masa, amma hannunsa ya hau rawa, ga wasu zafafan hawaye da suka fara sauka a fuskar sa.
Copying É—in message É—in yayi, daga nan ya goge shi gaba É—aya ya dangwarar da system É—in ya zauna yana kuka.

Tafiyar Abra da kwanaki uku Abbi ya dawo gari, sai dai haryanzu tsawon wannan lokaci ya ƙi sakin jiki da Mami su koma kamar da.
Ta same shi a part É—insa, ta kai masa Abinci, bai ce mata uffan ba ya ci Abincinsa ya cigaba da sabgar gabansa.

Ta É—an gyara zama ta ce "Amm, Man Abra ta zo ita da Adnan kwananta biyu sannan suka tafi".

"Good, Allah bai yi zamu haÉ—u ba, na je gidan nata da kaina in dubata".
Chapter 97 · 0% Book details