Sashe 113
Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Innahu Sulaimanu wa'innahu bismillahirrahmanirrahim." Ta faÉ—a tare da ja baya cikin tsoro da faÉ—uwar gaba, don zuwa yanzu ta fara tantamar anya ba aljani ba ne? Duk inda ta yi sai sun haÉ—u.
"Angel!"
Ya faɗa cikin murmurshi tare da haske fuskarta. Turo baki ta yi ta ce. "Wai kai a ina ka san ni ne? Don Allah ka daina bibiya ta, ni fa ban san ka ba ban taɓa ganin ka ba."
"To ai yanzu kin san ni ko?" Ya yi maganar yana ƙoƙarin kamo hannunta."
"Na shiga uku! Wai da wa Allah ya haɗa ni ne?" Ta yi maganar tare da tattare siket ɗinta ta manna da gudu. Da kallo ya bi ta har ta ɓace wa ganin shi, zuciyarsa cike da mamakin yadda ta ƙware a iya gudu haka.
"Who is she?" Ya tambayi kan shi cikin rashin sani, yana son sanin wacece ita da gidan da take da tarihin rayuwarta, don kamar su da Abra ta fi ƙarfin a ce kama ce kawai, sai dai in da wata alaƙar, domin hatta muryar su iri ɗaya ce, yadda suke magana ne kawai ya banbanta.
Kamar kodayaushe cikin gudu ta ƙarasa gida, tana tafe tana murguɗa baki da zancen Adnan a cikin ranta. Labarin na cin ta a rai amma ba ta faɗa wa Inna ba, saboda ɗazu ta riga ta ce mata ƙarya take.
Nai'ma na zaune a main parlour ta yi tagumi abun duniya duk ya bi ishe ta Abbi ya yi sallama fuska babu walwala. Ba ta amsa masa ba sai ma haÉ—e rai da ta yi. Kallon yadda ta rame ta lalace ya yi, sai ya ji tausayin ta ya tsirga masa, takaicin ta na kiran Ammi da ta yi ya fara gushewa daga cikin ransa. Jakar hannunsa ya ajiye tare da zama a kusa da ita, cikin taushin murya ya kira sunanta.
"Na'ima"
"Kar ka ƙara kiran sunana, don bai dace da bakin macuci azzalumi mayaudari irin ka ba, wallahi Khamal ka ci amanata." Ta yi maganar cikin kuka.
ÆŠage kafaÉ—a ya yi ya ce. "Idan kina ganin wannan borin da botsarewar da kike ne zai saka na fasa aure to ki cigaba, amma ki sani idan kika kai ni bango duk abin da ya faru ki kuka da kan ki."
"Ko me zai faru sai dai faru, ƙarkari ka ce ka sake ni ko? To ka sake ni ɗin sai me?"
"Okay, maganar kayan faÉ—ar kishiya, kuÉ—i kike so ko kaya?"
"Ban sani ba, ba na son komai naka Khamal, idan ka ga ina yawo tsirara don Allah kar ka siya mini ko ƙyalle, ka bar ni in cigaba da yawo a haka."
Girgiza kai kawai ya yi bai ce komai ba ya wuce part ɗinsa. Kuka ta fashe da shi mai tsananin gaske tare da ɗaukar pillows ɗin kujera tana cilli da su, ita kaɗai ta san me take ji a cikin ranta, ita kaɗai ta san zugi da raɗaɗin da zuciyarta take mata. Kamar wata mahaukaciya ta miƙe ta shiga ɗakinta da gudu ta ɗauki wayarta ta kira numbern Mama, bayan ta ɗaga ta fara magana cikin kuka. "Mama da gaske auren nan zai yi, don Allah ki faɗa mini mene ne mafita, na rasa madafa." A fusace Mama ta ce. "Taurin kanki ne ya yi yawa Na'ima, na faɗa miki ki ajiye wannan yarinyar ki baro masa gidansa amma kin ƙi." Kallon A'isha Humairah dake bacci ta yi, a raunane ta ce "Ba zan iya tafiya in bar ta ba Mam......"
"Sai ki ta zama ciwon zuciya ya kama ki akan Namiji." Mama ta katse ta da faÉ—in haka tare da kashe wayarta. Tsugunnawa ta yi ta kifa kanta a jikin gado tare da toshe bakinta da hannunta, gudun kar ta tashi A'isha daga bacci, ta shiga rera kuka mai ban tausayi.
Washegari ta tashi da zazzaɓi da matsanancin ciwon kai, da ƙyar ta iya tashi ta yi sallar asuba ta ba wa A'isha Humairah abincinta ta ci. Tana kwance Khamal ya shigo ɗakin, ko Kallon shi ba ta yi sai ma juya masa baya da ta yi daga kwancen da take, wasu hawaye masu ɗumi na zuba akan kuncinta. Bai kula ta ba shi ma ya ɗauki A'isha ya yi mata wasa tare da shishshilla ta, ita kuwa sai dariyar ƙuda take masa. 500k ya ajiye a kan madubi, yana duban Na'ima ya ce. "Ga kuɗi nan duk da kin ce ba kya so na ajiye miki, sannan gobe masu jere za su zo, idan akwai wani abun da kike buƙata bayan wannan sai ki sanar mini." Idan kuɗin da ya ajiye sun yi magana to Nai'ma ta tanka masa, ɗan murmushi ya yi ya kwantar da A'isha a gabanta, ba zato ta ji ya yi kissing forehead ɗinta tare da faɗin. "Sai na dawo uwargidan major Khamal Khamis." A zuciye ta ce. "Kar ma ka dawo, ka zauna a inda zaka je." Ta ƙarashe maganar tare da goge inda ya yi kissing ɗin." Tattausan murmushi ya sakar mata ya juya ya fita.
"Ƴar Baba! Ƴar Baba."
"Wai don Allah Inna ba za ki bar ni na yi baccin nan ba." Ƴar Baba ta faɗa tana tashi zaune.
"Ko kasa ce ke sai kin tashi kin yi wanke-wanken can, don gidanku idan kin je gidanki haka za ki na kwanciya kina bacci ki bar gida da ƙazanta."
"Gaskiya Inna kin daina so na yanzu, dama can Babana ne kaÉ—ai yake so na, da yana raye babu mai tashi na daga bacci." Ta yi maganar cikin hawaye. Inna ba ta kuma magana ba ta fice daga É—akin, tashi ta yi ta bi bayan ta ta kama wanke-wanken. Bayan ta gama ta share tsakar gida tare da wanke banÉ—aki. Inna ta ce. "To ko ke fa Æ´ar albarka, sannu da aiki, Allah ya saka da Alkhairi, yanzu sai ki wanke baki ki yi wanka ki zo ki ci abinci."
"Ni dai ba zan yi wanka yanzu ba sai rana ta fito, safiya ce fa."
Inna ta ce. "Kar ki yi ɗin, ke da ba a miki gwaninta, gwara ki koya tun yanzu, don watarana na asuba ma za ki yi ko na tsakar dare." Zunɓura baki ta yi ta ce. "Alkur'an ba zan yi wanka da tsakar dare ba, sai ka ce wata sabuwar aljana." Inna ta ce. "Idan lokacin ya zo kar ki yi, ki zo ki karya ni ki je ki karɓo mini gyaɗa, yau ma ki ƙara zubar mini da ita, ki ga yadda zan yi dake a gidan nan."
"Allah Sarki Babana, Allah ya ji ƙan ka, saboda ba ka nan kullum sai an mini faɗa."
Inna ba ta kula ta ba ta cigaba da sabgogin gabanta.
Kamar yadda Abbi ya faɗa washegari ƴan uwan amarya suka zo suka yi jere a part ɗin da aka gyara, duk da ƙofar shigar shi ta cikin main parlour take amma ba su haɗu da Nai'ma ba, don ƙin fitowa ta yi daga ɗaki. Abinci ma sai Aunty Iman Abbi ya yiwa waya ta aiko aka kawo musu. Zaman kaɗaici ya ishi Nai'ma, ga shi tana ta kiran Salman a waya ba ta samun shi, hakan ya sa ta kira wasu cousins ɗinta guda biyu suka zo don taya ta zama. Ganin yadda ta tayar da hankalinta duk ta fige sai abun ya ba su mamaki. Ɗaya daga cikinsu mai suna Wasila ta ce. "Me zan gani haka? Cuta kika yi ne Na'ima? Ko duk alhinin yi miki kishiyar ne?" Maimakon ta ba ta amsa sai ta fashe da kuka, da ƙyar suka rarrashe ta ta yi shiru. Ɗayar mai suna Hajara ta ce. "Haba Aunty Na'ima, yanzu akan kishiyar kike haka? Ai idan ta zo ta tarar kina haka sai ta raina ki."
"Mene ma ba zan yi ba, kun fi kowa sanin irin so da ƙaunar da nake wa mijina, amma ya ci amanata yake ƙoƙarin yin aure, me na rage shi da shi da bana masa?"
"Haƙuri ake yi Aunty Nai'ma, abun da ciwo amma sai kin danne zuciyarki, idan kika yi haƙuri komai zai wuce."
"Ba ni da wannan haƙurin kuma ba zan iya yi ba, wallahi ba don A'isha ba da tuni na bar masa gidansa, don ko ganin shi bana ƙaunar yi, ji nake kamar na cinna wa gidan wuta duk mu ƙune."
Da sauri Wasila ta ce. "Subhanallahi! Me ya yi zafi shi ba wuta ba Na'ima? An sani kishiya babu daɗi, amma ya za mu yi sai haƙuri. Ki rage damuwar nan da kike, tunda mijinki yana son ki ni ban ga abun damuwa ba, domin na tabbata duk macen da Khamal zai so a bayan ki take. Yanzu ki tashi ki yi wanka mu je a yi miki wankin kai da ƙunshi da gyaran jiki, duk da lokaci ya ƙure amma ba za ki zauna haka ba, yadda Amarya za ta zo fess ke ma haka za a gan ki."
Na'ima ta so ƙi amma suka tursasa mata, dole ta haƙura ta miƙe suka tafi ita da Wasila. Hajara kuma ta ɗauki kuɗin da Khamal ya ajiye ta tafi kasuwa ta yo sayayyar kayan sawa da takalma da jaka da mayafai masu kyau da tsada, wanda Nai'ma za ta yi fitar biki da su, daga kasuwa direct gurin tela ta biya ta ba shi kayan tare da cika masa kuɗi saboda ɗinkin urgently suke buƙatar shi. A daren yau ba su yi bacci ba sai da suka canza sabbin labulaye da Carpets part ɗin Nai'ma, suka sauya tsarin parlour'n da na kitchen, sai parts ɗin ya yi kyau ya haska shi ma.
Wasila da Hajara Ya da ƙanwa ne, the same Mother the same Father, mahaifiyarsu ce k'anwar babansu Na'ima, suna da hankali su da sanin ya kamata, don shawarwarin da za su amfane ta suka dinga ba ta. A ɓangaren ta ita ma sosai ta ji daɗin zuwan su, sai ta ji dama tun saura sati ɗaya bikin ta kira su.
Yau kwata-kwata Adnan ba su haÉ—u da Æ´ar Baba ba, hakan ya jefa shi cikin damuwa, ya dinga zagayawa a garin ko Allah zai saka ya gan ta amma bai gan ta ba.