Sashe 79
Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Baby kaina ciwo yake, jiri nake ji" ta faÉ—a a raunane.
"I don't care, ki tashi kawai" ya ƙarasa maganar cikin tsawa.
Abra ta sauko a hankali daga kan gadon, tana dafa bango ta bar É—akin.
A hankali take gudanar da komai a kitchen ɗin saboda ji take tamkar zata faɗi ƙasa. Allah sarki, da a gida ne duk da faɗan Mami, idan ta shiga wannan yanayin Mamin ma na ɗaga mata ƙafa, ko ba zata je kanta ba, amma tana ƙyaleta ta huta, her Faris kuwa yana kusa da ita yana sannu, da ta motsa zai fara "me kike so?"
Take maganganun da Adnan ya gaya mata da safe suka faɗo ranta, ta tuna ko salloli ba tayi ba, tuno maganganun nasa tayi, kamar saukar wuta a kanta, cikin rashin sani, da firgici ta ture tukunyar da ke kan gas, aikuwa ruwan zafin ya zubo mata a ƙafa.
Wani uban ihu ta saki, wanda ya sanya Adnan tasowa da sauri, ya shigo kitchen ɗin, ya kalli yadda tunkuyar ta faɗi ƙasa, ruwan zafi ya zube mata a jiki da ƙafarta, sauran ya malale a kitchen ɗin.
"Wai ke wace irin Yarinya ce mara hankali da nutsuwa? Mai yasa baki da tunani ne? Ko da yake babanki ma haka yake, ba shi da lissafi balle tunani, Wallahi kika kuma yi mini ihu haka a cikin gida sai na tattakaki" yayi maganar yana huci ya juya ya bar kitchen É—in.
Toshe bakinta Abra tayi, ta dinga wani irin kuka, mai tsuma zuciya, a hankali tana ɗingisa ƙafarta da ke mata wani irin azabar zugi, ta fito falo, sai dai ta kasa cigaba da tafiya saboda yadda ƙafar tayi jawur, take mata wani irin zafi.
Adnan ne yake waya a falon "Wallahi Abbi duk lafiyar mu ƙalau Alhamdilillah".
"Adnan lafiya kuwa har yanzu wayar Abra ba ta shiga, hankalin mahaifiyarta ya tashi da nasu Ammi, ta ce tun da aka kawota ba su kuma waya ba, nima sai dai muyi waya da kai amma ba'a samunta?".
Adnan ya ce "Abbi wayar nake so na canza mata, ban zauna bane abubuwa sun yi mini yawa sosai, amma a satin nan nake sa ran za'a kawo mata".
Abbi ya ce "Ok, shikenan haÉ—ani da ita dan Allah".
Adnan ya kalli in da Abra ke zaune, ta zubo masa idanu tana jiran ya bata waya, amma sai ya ce "Abbi bacci take yi".
"Bacci kuma da la'asar haka?".
"Eh ba ta jin daÉ—i ne, an mata allurai".
Abbi ya ce "subhanallah, amma shine baka gaya mini ba? Mai ya sameta?".
Adnan ya ce "Abbi É—an menstrual pain ne, kuma an mata allura ta samu releif".
"To shikenan, a kula da ita please, in an jima zan kuma kira inji jikin nata".
Adnan na gama wayar, ya kashe wayar gaba É—aya ya ajiyeye a gefensa ya cigaba da kallo.
Wani sabon kukan ta sake fashewa da shi, mai tsuma zuciya da nuna tsantsar damuwa, amma Adnan ko a jikinsa, ƙarshe ma sai tashi yayi ya bar mata falon gaba ɗaya.
Da ƙyar ta ja jikinta ta koma ɗakinta, tayi sallolin da suke kanta, ta nemi guri ta zauna ta takure, tana sake jujjuya maganganun Adnan, da ƙoƙarin gano gaskiyar lamari, sai dai babu yadda za'a yi ta san gaskiyar lamari, in dai bata bakin wani taji a gidan su ba, wani irin abu mai ɗaci ya zo ya tokare mata tun daga ƙirjinta zuwa wuyanta da kan harshenta, ƙirjin yayi mata wani irin nauyi, da ƙyar take iya numfarfashi saboda tsananin damuwa.
Daf da magariba ta kuma jin fitar Adnan, wata irin yunwa ce ta ke sassaƙarta, haka ta kuma fitowa ta tafi kitchen, ta fara ƙoƙarin ɗora abincin dare.
Abbi yayi mamakin yadda yake cigaba da kiran wayar Adnan, amma shiru ba ta shiga, haka Salman ma kusan wata guda kenan, ba'aji daga gareshi ba.
Gefe Na'ima ta uzzurawa Abbi da kira, da cewar ba fa ta samun yaran nan a waya gaba ɗaya, mussaman Salman, da ta tsorata da lamarin Salman sosai da sosai, dan alamu sun fara nuna cewar abun da ya bar mata wasiƙa na shirin faruwa, gashi babu damar ta sanar da Major abun da ya bar mata a wasiƙa.
Da daddare Adnan ya dawo, ya tarar Abra tayi girki, ba kunya ya zauna yana cin Abincin sa, har Abra ta fara shirin kwanciya, amma ta fasa ta fito falo, tana ɗingisa ƙafarta.
Kusa da Adnan taje ta zauna, bai ko kalli in da take ba, ya cigaba da abun da yake yi.
"Baby" ta faÉ—a a hankali.
Ya amsa mata da Angel, ji tayi sunan ya tsirga mata kamar yau ya fara gaya mata, duk da suna ne da Salman yake kiranta da shi, amma idan Adnan ya faÉ—a jin sunan take na musamman a bakin sa.
"Baby, dan Allah dan Annabi, tun da kace ba Abbi ne mahaifina ba, ka gaya mini waye mahaifina ka nuna mini shi".
Wata makirar dariya Adnan yayi ya ce "Ashe ma ba fansar zan ɗauka ba, idan har zan haɗa ki da shi, ai Abra ke da mahaifinki ya sanya ki a idanunsa sai a lahira, dan nayi ƙoƙarin toshe duk wata kafa da zata sada ki da shi har Abada"
"Dan Allah kar ka yi mini haka, ka yafe masa koma me yayi maka, dan girman Allah ka haÉ—ani da shi ko sau É—aya ne, ba dan halina ba".
"Tashi ki bani guri, kafin in tashi in ƙwallo dake a gurin nan, zancen mahaifinki kawai in ana yi ji nake tsanarsa da duk wani abu da ya raɓe shi yana sake ninkuwa a zuciyata, ki tashi ki bani guri kafin in miki illa, 'yar zuriyar masu baƙin hali"
Abra ta miƙe, maganganun Adnan na mata amsa kuwwa a kunnuwanta 'yar zuriyar masu baƙin hali! Gani take tamkar an canza mata Adnan ɗin ta, da ta san haka Aure yake, da har gaban abada ba zata yi shi ba.
Ta koma É—akinta, ta takure a kan gado, tana ambaton sunan Allah, ko ta samu sassauci a zuciyarta.
Tana nan zaune a kan gado, fitilar É—akinta a kashe, Adnan ya shigo É—akin, yana shigowa gabanta ya faÉ—i, dan ba ta san da wacce ya zo ba a wannan tsohon daren.
Ba kunya ta ga ya hawo kan gadonta, ba tsoron Allah, ya janyota jikinsa da ƙarfi, ba wani tunani ko tausayawa ya nemi haƙƙinsa na Aure, ya sauke mata duk wata gajiyarsa ta wunin ranar kamar wata Akuya ba ɗan Adam ba, kuma ya tashi ya shiga toilet ɗinta, ya tsarkake jikinsa ya fice ya bar ta ko kallonta bai yi ba.
Al'amarin Adnan ya dai na bawa Abra mamaki, sai dai tsoro babu alamar rahama ko tausayawa a tare da shi, zuciyarsa a dake take, ta bushe da rashin imani.
Adnan kam, baccinsa yayi mai daÉ—i ya bar Abra da matsanancin ciwon jiki, duk lokacin da zai kasance da ita, yana tsintar kansa cikin tsantsar nishaÉ—i da jinsa free from any sadness, halin da zata shiga kuwa sam baya damunsa.
GY BULAMA HOSPITAL AND MATERNITY.
Nurse Jamila ce tsaye a gefen Bulama, yana duba wani scaning da ta kawo masa na wata mata, rufe file É—in gabansa yayi ya kalli Nurse Jamila ya ce "Yi min magana da mijin matar nan, aiki za mu yi mata"
ÆŠan waro idanu ta yi ta ce "Doctor, na ga kamar scanic É—in ya nuna bakomai, kamar peptic ulcer ne kawai, kuma kace aiki zaka yi mata"
"To doctor Jamila, mai Yakamata ayi?"
Shiru tayi, bayan tuna cewar ya hanata yi masa shishshigi a cikin lamarin aikinsa, ba ta kuma cewa komai ba ta fita ta kirawo mijin matar .
Nan Bulama ya din ga yi masa wani surkullen bayani irin na su na likitoci, yadda mutumin ba zai wani gane ba, ya ce mutumin ya je ya biya kuÉ—in aikin a shiga da ita da gaggawa.
Lamarin Adnan da muguntarsa ƙara gaba yake yi, dan yanzu duk lokacin da ya buƙaci Abra ko da dare ko rana, haka yake zuwar mata kansa tsaye.
Hakan ya ƙara jefa Abra cikin tsoro da firgici, ko muryar Adnan taji sai gabanta ya faɗi hankalinta ya tashi, ga tsananin damuwar rashin jin Muryar kowa daga gida dan ba ta da waya. Tana cikin wannan zullumin Dodon nata wato Adnan ya shigo, tana ganinsa jikinta ya hau rawa.
A kausashe ya ce "In Allah ya kaimu anjima, su Hajiya Mama za su zo, idan kin ga dama ki yi wani misbehaving ki ga yadda zan yi dake". Ba tace masa ci kanka ba, ya gama maganganunsa ya fice.
Kitchen ta shiga ta shirya girke girke, domin tarbar su Hajiya Mama, dan iyayen Adnan ba dai karamci ba.
Sai azahar sannan suka zo, Abra taji daɗin zuwansu, sai dai a kallon Farko da Maman ta yiwa Abra, ta ga yadda yarinyar ta ƙara ramewa, tai duhu.
Mama ba tace Komai ba, suka dinga hira da Abra, sai da zasu tafi sannan ta bi Abra É—akinta ta kalleta tace "Abra, meke faruwa ne?"
"Mama me kika gani?".
"Abra alamu sun nuna akwai wata damuwa a ƙasa, menene ke faruwa?".
"Ai kamar Mama ta taɓo mata abun da yake mata ƙaiƙayi, ta fashe da kuka, sai da tayi mai isarta sannan Mama ta ce "gaya mini ina jinki"
Abra ta ce "Mama ni gida nake so, gida zan koma".
"Haba Abra, saboda me?"
"Bakomai, kawai gida nake son komawa"
Mama ta ce "kiyi haƙuri, haka Aure yake a hankali kowa yake sabawa, ke dai ki kwantar da hankalinki ki dinga ci kina ƙoshi". Ita Abra ma sam ba ta gane me Mama ke nufi ba.
Bayan sun fito daga É—akin Abra sai ga Adnan ya dawo.
"Mama wai tafiya zaki yi ba tare da kin ganni ba, wato tunda kinga Angel shikenan"
"Eh shikenan Mana, kai É—in da kusan kullum sai ka zo gida ka isheni, ai gara in zo in ga 'ya ta'
Adnan ya kwaɓe fuska ya ce "My Angel kin ƙwace mini Mama, gaskiya kishi nake, haka ake yi". Kallon Adnan take da mamaki, a gaban mutane yayi ta nuna mata kulawa, amma daga ita sai shi, yayi ta cuzguna mata.