← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 145

Sashe 70

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana zaune takure a bakin gado ta yi tsumu cikin alamun tsoro, ita kaɗai a gida har tara ta yi amma babu Adnan babu labarin shi. Ƙwaƙwalwarta har ta gaji da tunanin dalilin da ya sa Adnan yake yi mata haka, kanta kamar zai tsage saboda ciwo. Unexpected ta ji an buɗo ƙofar ɗakin an shigo, lumshe ido ta yi cikin jin daɗi dalilin shaƙar ƙamshinsa, a hankali ta buɗe idonta ta kalle shi, yanda ta ga ya murtuke fuska ne ya sa gabanta mummunar faɗuwa, amma duk da haka ta daure cikin raunin murya ta ce. "Sannu da zuwa." Ta ƙarashe maganar hawayen da take ƙoƙarin ɓoyewa suna zubo wa. Bai kula ta ba, wayarta dake chaji kawai ya ɗauka ya fice. Da ido ta bi shi cikin kokawa da numfashinta dake barazanar ɗaukewa. Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un ta shiga maimaitawa hannunta dafe da kanta, wani irin raɗaɗi da zafi take ji a cikin zuciyarta. Tambayar kanta ta shiga yi, dama haka Auren yake? Ko kuma ita kaɗai ta fara da matsala? Ina tarin ƙauna da soyayyar da Adnan yake yi mata? Ina tanadin kulawa da tattalin da ya ce ya mata? Ko dai mafarki take yi? Ta rasa da wanne za ta ji, da rashin Faris a kusa da ita ko kuma da kewar su Abbi ko da abun da Adnan yake mata? Sunan Allah ta dinga ambata har ta ji sauƙin radad'in da zuciyarta ke mata. So take ta tashi ta je gurin Adnan ta ji me ta yi me masa? Amma a yanda take jin jikinta kamar ba nata ba ta san ba za ta iya tashi ba. Kwanciya ta yi saboda juyawar da kanta yake yi mata.

Wannan shi ne dare mai tsayi da muni da Abra ta gani a rayuwarta, dan bacci duk iya satarsa bai sace ta ba. Nasihar Ammi da ta ce ta dinga tashi cikin dare tana yin Sallah ko raka'a biyu ce ta dawo cikin kwanyarta, hakan ya sa ta lallaɓa ta tashi ta shiga toilet ta ɗaure alwala ta raya daren, ta kai wa Ubangiji kukanta tare da roƙon ya kawo mata ɗauki. Bayan an yi Sallar Asuba ta ɗauko alƙur'ani mai girma ta karanta, bayan ta gama ta yi azkar ɗinta. Hakan ya sa ta ji sauƙin damuwar dake cunkushe a cikin ranta. Sai kusan takwas ta fita parlour bayan ta yi wanka. Gyaran gidan ta fara yi cikin matuƙar sanyin jiki, tana cikin yi Driver'n gidan Hajiya Mama ya kawo breakfast, ta karɓa ta yi masa godiya ta kai dinning ta ajiye. Tana zaune har 10 tana jiran fitowar Adnan amma shiru ko motsinsa ba ta ji ba.

Wasa-wasa yau har Magriba ba ta ɗora Adnan a idonta ba, sauƙinta yau ma ta yi baƙi har sau biyu sun ɗebe mata kewa. Sai bayan Magriba ya shigo gidan, lokacin tana zaune a parlour ta kunna kallo, a ƙoƙarinta na son ya ɗebe mata kewa, sai dai damuwar dake cikin ranta ta hana ta gane me firlm ɗin ma ya ƙunsa.

Duk yanda yunwa da ƙishirwar son ganin shi suka cika mata zuciya amma sai ta kasa ɗaga ido ta kalle shi, ƙasa ta yi kanta tana sauraren yanda zuciyarta ke bugawa. Karon farko tun bayan da aka kawo ta, ta ji muryarsa ya yi mata sallama, sai dai ba a yanda ta so jin maganar tasa ta ji ba, ba cikin soyayya da kulawa ba. Fuskarsa a murtuke tamkar aka yiwa saƙon mutuwa, cikin isa da gadara kamar an masa dole ya ce. "Je ki ɗauko hijabinki." A hankali ta ɗago ta dube shi idanunta cike da ƙwalla, kafin ta kai ga yin magana ya juya ya shige ɗakinsa. Kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki haka ta miƙe ta je ta ɗauko hijabin ta saka, tana cikin kashe kayan kallon ya fito daga ɗakinsa ya yi hanyar waje ba tare da ya kalli inda take ba. Bin bayansa ta yi cikin sanyin jiki tana sharar hawaye.

Ganin ya shiga Motor ta buɗe front seat ta shiga, wai mugun kallo ya watsa mata tare da faɗin. "Kar ki bari na ƙara ganin wani abu mai kama da hawaye a fuskarki." Ba ta ce komai ba ta share hawayen tare da lumshe idonta. Gidan Hajiya Mama suka je. Abba da Hajiya Mama sun karɓe ta cikin fara'a da soyayya, sai nan-nan suke da ita. Ita kam kanta na ƙasa kunya duk ta ishe ta, idan an yi magana sai dai kawai ta murmusa. Adnan kuwa sai shagwaɓa yake musu wai yanzu sun daina son shi Abra suke so. Abun da ya ba wa Abra mamaki yanda ya dinga yi mata magana cikin kulawa da sakin fuska a gabansu Abba, hakan ya jefa ta cikin tunanin me Adnan yake nufi da ita?

A nan suka yi dinner tare da su Abba, tun tana jin kunyar su har ta ɗan ware, saboda su babu ruwansu, musamman Abba he is so friendly, yanata jan ta da hira. Sai ta ji dama Adnan ɗinta ne haka. Hajiya Mama ta lura da yanayin Abra kamar wani abu yana damun ta, idanuwanta ma sun nuna alamun ta yi kuka. Ba ta yi tunanin komai game da hakan ba, sai ta alaƙanta hakan da kewar gida take yi da kuma rashin sabo na mu'amalar Aure. Kafin su tafi Adnan ya sanar da su zai yi tafiya zuwa Abuja akan wani muhimmin aiki da ya taso masa, za su tafi tare da Abra. Addu'a fatan isa lafiya sukai musu. Sai wajen 10 suka dawo gida. Bai ko kalle ta ba bayan ya yi parking ya buɗe Motar ya fice. Bin bayansa ta yi kallo cikin wani irin yanayi na ƙuncin zuciya. Ajiyar zuciya ta sauke tare da buɗe Motar ta fita. Tun daga lokacin ba ta ƙara saka shi a idonta ba sai washegari bayan Sallar Asuba ya shigo ɗakinta.

Time ɗin tana karatun Alkur'ani, bayan ta kai ajiye ta rufe tare da gaishe shi cikin girmamawa. Bai amsa mata ba sai bin ta da wani wulaƙantaccen kallo da ya yi. Cikin ƙaunshin murya ya ce. "Zan yi tafiya yanzu, ba na zo kuma dan in sanar miki ba ne saboda ba ki kai wannan matsayin ba a gurina, na zo in ja miki warning ne akan ko da wasa kar wani ya ji labarin ba da ke na yi tafiyar ba, idan kunne ya ji jiki ya tsira." Ya ƙarashe maganar tare da jan tsaki. Cikin kukan da ya taho mata ta ce. "Dan Allah kar ka tafi ka bar ni, ni kaɗai, wallahi tsoro nake ji."

"Abun da kike jin tsoron ya kashe shi."
Ya faÉ—i haka tare da juyawa da niyyar ficewa."

"Please where is my phone, ka dawo mini da ita Dan Allah." Ta faÉ—a cikin matsanancin kuka.

Ko juyowa bai yi ba ya yi ficewarsa abunsa.

Kifa kanta ta yi akan cinyoyinta ta shiga rera kuka mai ban tausayi. Why Adnan? Me nake yi maka da ka zaɓi mu yi irin wannan rayuwar mai cike da ƙunci da damuwa? Ya Allah ka kawo mini ɗauki akan sabon babin ƙaddarata da ya buɗe, Allah ka sassauta mini. Abun da take faɗa a ranta kenan cikin tsantsar damuwa.

Yau kwana biyar da kai Abra gidanta, wadda waɗannan kwanakin suka kasance kwanaki mafi muni da tsaho a cikin rayuwarta. Gabaɗaya ta rame ta fita daga hayyacinta, ga babu waya balle ta kira su Abbi ko ta ji sauƙi a cikin ranta, ga kewar Salman da kullum ƙara yawaita take a cikin zuciyarta. Alkur'ani shi ya zamto abokin hirar ta akodayaushe, sai kuka da kullum sai ta yi shi ba adadi.

Misalin ƙarfe goma sha biyu na rana tana kwance a parlour akan carpet, idanunta a lumshe hawaye na zirara ta ƙasansu. Tana jin yanda cikinta yake ta ƙugin yunwa amma ta kasa tashi ta samar wa kanta abin da za ta ci, ga wani azababben ciwon kai da ya aure ta, kullum da shi take kwana take tashi. Kamar a mafarki ta ji an buɗe ƙofar parlour'n an shigo, ko ba a faɗa mata ta san Adnan ne ya dawo, saboda da zai tafi ya kulle ƙofar parlour'n ta waje, ta gane hakan ne a lokuta da dama da ta yi yunk'urin fita harabar gidan ko za ta ga abun da zai ɗebe mata kewa damuwar zuciyarta ta ragu. Ko matsawa ba ta yi ba da niyyar tarɓar shi, sanin da ta yi ko ta masa magana ba amsawa zai yi ba. Sai dai jin kamar ba shi kaɗai ya shigo ba ya sa ta buɗe idonta da sauri tare da goge hawayen fuskarta ta tashi zaune. Abun da ta yi tozali da shi ne ya sa numfashinta ɗaukewa na wucen gadi. Adnan ne tare da wata mace wadda kallo ɗaya za kai mata ka gane ƴar duniya ce ta ƙarshe, duba da yanayin shigar jikinta da uban bleaching ɗin da ta ci, ga kitson attachment a kanta gami da gashin ido maƙale a saman idanunta. Wannan duk ba shi ne abun da ya fi ɗagawa Abra hankali ba, jakar matar da Adnan ya riƙo a hannunsa da kallon da yake jifan ta da shi mai nuni da tsantsar soyayya, a ƙarshe kuma ya tsugunna yana cire mata hill shoe ɗin dake ƙafarta.

Littafin kuɗi ne,biya ₦300 via 0116886423 Sulaiman Na'ima s union Bank... Idan katin waya ne zaka Turo 500 shaidar biya 09047871750 or 08081012143.
[10/12, 7:18 PM] Abk: Mugun ganin da Abra ta yi, ya sanya ƙirjinta fara ɗa gawa zuciyarta tai mata nauyi. Rutse idanunta ta sakeyi tana ganin abin kamar almara, amma ta hana Zuciyarta gasgata abin da ta ke raya mata.

A hankali ta yi ƙasa da kanta ta shiga wasa da yatsun hannunta, jikinta duk rawa ya ke, ji ta ke kamar zuciyarta tai bindiga sbd fargaba. Juyawa Adnan ya yi tare da kallon budurwar ta ke tsaye a gefensa, cikin nutsuwa ya sakar mata wani kwantaccen Murmushi mai nakar da zuciyar ko wacce ƴar mace.
Fari ta yi masa da idanu tana girgiza ƙirji ganin hakan ya sanya Adnan, janye nasa idon ya lumshe kafin a hankali ya ce "My Surry" kashe murya wacce aka kira da Surry ta yi ta na shafa fuskar Adnan ta ce.
Chapter 70 · 0% Book details