← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 141 OF 145

Sashe 141

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Washegari da safe Abra ce tsaye a kitchen tana soya egg, sanye take cikin wata red ɗin riga mai ƙaramin hannu wadda ta tsaya mata iya gwiwarta, ta faka gashin kanta wanda ya sauka har gadon bayanta da red ribbon. Ta yi kyau sosai duk da ba make up ta yi, daddaɗan ƙamshi na tashi a jikinta. Sauri take ta kammala haɗa breakfast ɗin kafin Adnan ya tashi, don da ƙyar da dabara ta raba jikinta da nasa ta fito. Jin kaman ana kallon ta ya sa ta juyawa, yana tsaye ya harɗe hannunsa a ƙirjinsa yana kallon ta, babu riga a jikinsa sai ƙaramin wando da bai gama rufe masa cinya ba. Murmushi ya sakar mata lokacin da suka haɗa ido tare da ƙarasowa ya rungume ta, ta baya.

"Morning my Queen."
Ya faɗa a saitin kunnenta da murya ƙasa-ƙasa. Lumshe ta yi ta buɗe ta ce. "Morning Hero, how was your body?"
"Alhamdulillah."
Tana zare hannunsa dake kan cikinta ta ce. "Bari na yi sauri na gama ka samu ka ci abinci ka sha magani." Mayar da hannun ya yi tare da cusa kansa a wuyanta yana shaƙar ƙamshin jikinta ya ce. "Na warke fa Angel, ni na manta ma ba ni da lafiya, saboda ba na jin ciwon komai a jikina tunda na same ki."
"Sure?"
Gyaɗa mata kai ya yi tare da cusa hannunsa a cikin rigarta. Cikin shagwaɓa ta ce. "Girki fa nake Baby." Murya ƙasa-ƙasa ya ce. "Ki bar shi ki huta Wifey, na san Mama za ta aiko mana." Ciro hannun nasa ta yi ta ce. "Mu ya kamata muna kai mata abinci ba ita za ta dinga girkawa tana kawo mana, ka bar ni na yi Please ita kuma ta huta." Maraicewa ya yi ya ce. "No." Bai jira abin da za ta ce ba ya juyo da ita ya haɗe bakinsu guri ɗaya. Da ƙyar ta ƙwaci kanta ta cigaba da aikinta, tare da suka ƙarasa aikin yana manne a jikinta, duk a cewar shi taya ta yake. Bayan sun gama suna zaune a parlour tana manne a jikinsa ta ce. "Ka cinye abincin nan duka Please, ba ka cin abinci ne shi ya sa duk ramar taka ta yi yawa." Girgiza kai ya yi ya ce. "I can't dear." Ɓata fuska ta yi tare da barin jikinsa, janyo ta ya yi ya ce. "I'm sorry, amma ba abinci ne zai saka na koma yadda nake ba."
"To mene?"
Ta faÉ—a tana sakin fuskarta. RaÉ—a mata ya yi a cikin kunnanta, saurin waro ido ta yi tare da rufe fuskarta tana murmushi. Shi ma murmushin yake, É—aukar ta ya yi ya É—ora ta a kan cinyarsa ya fara ba ta abincin a baki, duk spoon É—aya sai ya yi kissing lips É—inta. Ba su tashi daga gurin ba sai kusan azhar, saboda lalacewar da suka yi suna zuba soyayya. Bayan sun yi wanka tare Adnan ya fita Masallaci. Bai dawo ba sai bayan la'asar.

Tana zaune a parlour suna chat da Afra ya shigo, ta ci kwalliya cikin English wears. Ɗago kanta ta yi a hankali tare da amsa masa sallamar da ya yi. Ware mata hannayensa ya yi cikin kewar ta, cikin nutsuwar ta ta miƙe ta ƙarasa ta faɗa jikinsa. A tare suka saki ajiyar zuciya lokacin da zagaye bayanta da hannunsa.
"Welcome Baby."
"Yawwa love ya gidan?"
Ya yi maganar yana shafa gashin kanta. Shagwaɓe fuska ta yi ta ce. "Ina ka je ka daɗe ka bar ni, ni kaɗai? Kuma ka san ba ka da lafiya."
"I'm sorry, wani guri na je."
"I thought gidan Mama ka je."
Yana shafa lips ɗinta dake zuba ƙyallin white lipstick ya ce. "Yanzu dai za mu je mu gaishe ta idan na yi wanka." Cikin murna ta ce. "To mu je ka yi wankan mu tafi kar mu ɓata time."
"Ɓata time ya zama dole tunda kika yi wannan kwalliyar."
Langwaɓe kai ta yi don ta gane me yake nufi ta ce. "Please Bab...."
"Please Angel." Ya katse ta cikin kwaikwayar muryarta tare da jan karan hancinta. Kanta ta cusa a cikin ƙirjinsa cikin sigar shagwaɓa. Cak ya ɗaga ta don hakan da take ƙara birkita shi yake, dama ƙamshinta gabaɗaya ya gama ruɗa shi. Sai kusan Magriba suka fito tana zuba masa rigimar ya sa ta sake wanka da yamman nan, shi kuma yana ta lallaɓa ta.

Rantsatstsiyar sabuwar motar da ta gani ya sa ta tsayawa tana yaba ta. Murmushi ya yi ya kamo hannunta ya saka mata key a ciki tare da faɗin. "It's yours my lady." Waro ido ta yi cikin mamaki da farincikin da suka yi mata rufdugu a lokaci ɗaya ta ce. "Sure?" Gyaɗa mata kai ya yi. Rungume shi ta yi ta ce. "Alhamdulillah, thank you, thank you Baby, Allah ya saka da Alkhairi ya ƙara buɗi mai albarka da amfani." Cikin jin daɗin addu'ar ya ce. "Amin Angel, You deserve more than this a waje na, and babu godiya a tsakanin mu, duk abin da na mallaka naki ne." A bazata ya ji ta haɗe bakinsu guri ɗaya tana ba shi wani zazzafan kiss, bayan ta zare bakinta daga nasa ta ce. "Tukuici na farko kenan, sauran sai mun haɗu later."
"Mu koma yanzu ma a ba ni."
"Um'um." Ta faÉ—a cikin dariya tare da yin gaba gurin motar cikin farinciki. A cikinta suka je gidan Hajiya Mama.
Chapter 141 · 0% Book details