← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 112 OF 145

Sashe 112

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai washegari da safe, sannan ya fara shirin tafiya ƙauyen.
Har ya gama shiri, ya ga dacewar yakira Abba, ko ba zai amsa ba ya gaishe shi.
Sai dai yadda Abban ya amsa gaisuwar ne, za ka tabattar da haryanzu Abba yana fushi da Adnan.
A sanyaye ya shiga motarsa, ya cigaba da tafiya.

Yaran garin kamar ba su taɓa ganin mota ba, da zarar Adnan ya yi parking ɗin mota, suke zuwa su kewaye motar suna kallo, saboda haka mai gari ya sa aka samo wuri na musamman da yake ajiye motar, gudun kar yaran su mata illa.
Da yake har yanzu gajiya na damun Adnan, dan haka a É—aki ya wuni, salla ce kawai take fito da shi.

Bayan la'asar ya ga dacewar ya zazzaga garin, ya jefi tsuntsu biyu da dutse É—aya, ya ga ta ina zai fara bincikensa, kuma ko Allah zai sa ya sake ganin Abra.

Sannu a hankali ya nausa cikin ƙauyen yana zagawa, sai ya ga wurin ya burgeshi, dan haka ya cigaba da kutsawa yana zagaye, har ya bar in da mutane suke.
Tafiya ya yi sosai mai nisa, wurin ba kowa sai bishiyu da kukan tsuntsaye, ga manyan bishiyun fruit kala kala a wurin.
Can ya hango wani tafki, ruwan ciki garai da shi, dan haka ya nufi wurin yana son ganin girman ruwan, sai ya tuna zamansu a Dubai, yadda Abra ke son ruwa, kuma tana tsoronsa.

Kamar Aljana, haka zalika kamar a yadda ya ganta wancan lokacin, ta juya bayanta, ta zuba su a cikin ruwan, tana ta kaɗa ƙafafuwan ta a ciki.

Da wata irin gaggawa, ya nufi in da take zaune.

Jikinta ya bata a na tsaye a bayanta, ga kuma ƙamshin turaren da ba zata ta;a mantawa da shi ba ya daki hancinta.

Ba tare da ta waigo ba, ta tashi da sauri, aikuwa gabanta ya faÉ—i da ta ga Adnan a tsaye kamar gini.

Juyawa ta yi zata taka da gudu, dan ba ta gama yadda mutum ba ne, wannan mutum haka mai siffar shago.

Yana gano nufinta ya danƙota, ya ja ta gefe, jikinta ne ya hau rawa "Ka ga dan Allah ka cika ni".

"Abra, wai har yanzu ba ki gane ni ba? Na san loosing memory ki ka yi".

"Allah ya sawwaƙe, kana nufin na haukace fa kenan, to Wallahi ni ba mahaukaciya ba ce".

"Abra dan Allah ki saurareni"

"Kai karka sake kirana da wannan sunan, wani suna kamar babur, kamar burabusko, ni ba sunana kenana ba, dan Allah ka cikani kar Inna ta gane Namiji yataɓa ni"

"To ai ni mijinki ne Abra"

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ko dai aljani ne ya aure ni ban sani ba?"

Ƙara matso da ita jikinsa ya yi, yana ƙare mata kallo, duk da yamma ta ti sosai, Abransa ta fi wannan fari da ja, amma wannan ma fara ce tas, dan ba ta samu hutu bane, Abransa muryarta a hankali take yin ta, wannan kuwa muryar ta a tsaye take, cike da tsiwa da rashin kunya. Abra ta fi shagwaɓa a kan duk al'amuranta, wannan a tsaye take da ƙwarinta.

Mutsu mutsun ƙwacewa take yi, tana ta kurma ihu.

Adnan ya ce "Zan cika ki, amma muje in ga gidanku, zan magana da ke"

Ta ce "To, na yadda".

Adnan na cikata, kamar ya saki tattabara, ta watsa da gudu, ta nemi hanyar barin wurin.

Littafin kuɗi ne, don biya ku tuntuɓe mu ta wannan lambar. 09047871750
[11/9, 11:32 AM] Abk: Ƙoƙarin kamo ta ya yi, amma yadda take gudu kamar mai fukafukai ya sa cikin sakanni ta ɓace wa ganin shi. Ajiyar zuciya ya sauke tare da shafa sumar kansa, lallai wannan aikin da ya zo yi ba ƙaramin Alkhairi ya zamo a gare shi ba, bai taɓa tunanin zai ƙara yin farinciki a rayuwarsa ba, amma ganin wannan halittar mai kama da Abra da acting ɗinta ya fara saka shi cikin nishaɗi. Ya yarda Abransa ta tafi ta bar shi wannan ba ita ba ce, amma tsananin kamar da suke yi idan ba wanda ya yi wa Abra mugun sani ba idan ya ga wannan zai ce ita ce. Saboda yadda komai nasu yake iri ɗaya, ido, dogon hanci da dogon baƙin gashi, cikakkiyar gira da ɗan ƙaramin bakinsu gami da jerarrun fararen haƙora, hatta hannu da ƙafarsu duk iri ɗaya ne. Banbancin su kawai Abra ta taso a birni gidan hutu, ita kuma wannan yar ƙauye ce. Murmushi ya kuma yi a karo na biyu ya juya ya tafi don aiwatar da abin da ya kawo shi, zuciyarsa cike da addu'ar Allah ya sa ya kuma ganin ta a yau.

"Wai don Allah ƴar Baba yaushe za ki yi hankali ne ki san kin girma? Sau nawa nake ce miki ki daina faɗo mana gida da gudu kamar wani filin ƙwallo"

Zama ta yi tana haki tare da turo baki gaba ta ce. "Wai Inna ba ki san me ya faru ba za ki fara yi mini faɗa, ba ke ba ce kullum kike cewa kar in bari Namiji ya taɓa ni ba?"

Inna ta ce. "Eh ni ce."

"To wannan mutumin da na ce miki ya biyo ni jiya yau ma shi na ƙara gani a bakin teku, ya riƙe ni yana kira na da wani suna kamar babur, wai don Allah in daina gudun shi."

Ido a waje Inna ta ce. "Wane shi? Me yake nema a gurin ki? Ɗan gidan waye a garin nan? Don ba zai yiyu ba sai mun je an kira iyayensa an yi wa tufkar hanci, akan me zai dinga taɓa ki?"

"Kai Inna ya na ga duk kin tsora ta?"

"A'a, kar na tsorata? Na san mugun nufin shi a kan ki?"

"To Inna daga ganin shi ba ɗan garin nan ba ne, irin yan gayun nan ne yan birni, sai ma kin ji ƙamshin da yake mai daɗi." Ta ƙarashe maganar tana murmushi.

Tsaki Inna ta yi ta ce. "Ko ma ɗan ina ne ba ruwana, bari Musa ya fito daga wanka mu je gidan mai gari". Ganin da gaske Inna take sai Ƴar Baba ta ce. "To ƙarya ma nake yi duk abin da na ce miki." A ƙufule Inna ta ɗauki mafirficin kaba za ta kwaɗa mata tana faɗin. "Ja'irar kashi, wato kin mayar da ni kakarki ko?" Kafin maficin ya sauka a jikinta ta kwasa da gudu ta yi ɗaki tana dariya. Musa da ya fito daga bayan gida a lokacin shi ma dariyar yake. Yana ajiye bokitin hannunsa ya ce. "Wani lokacin Inna kamar ba ki san halin ƴar Baba ba, ta zo ta zauna ta tsara miki zance na ƙarya, ke kuma ki hau kai ki ta banbanmi, sai kin gama ta ce ƙarya take." Inna ta ce. "Na daina yarda da ita ai, ja'ira kawai, Allah ya shirya mini ke."

Ita kuwa tana shiga ɗakinta ta yi tsalle ta faɗa kan katifarta, haka kawai ta ji mutumin da take haɗuwa da shi ya tsaya mata a rai, ta rasa me ya sa kuma da Inna ta ce za ta kai ƙarar shi gurin mai gari ta yi saurin cewa ƙarya take, ita da take jiran ƙiris mutum ya yi mata abu ta kai shi ƙara. Tsaki ta ja a fili ta ce. "Ƙila ma aljani ne, ɗan baƙi kawai, bai san ma ni na fi son farin mutum ba, ta ƙarashe maganar tare da murguɗa baki. Tunowa ta yi wata ƙawar su ta haihu jiya, hakan ya sa ta miƙe ta fice daga ɗakin don zuwa ganin ɗa.

"Inna zan je na ga jaririn Atine." Ta yi maganar tana saka takalmi.

"Ki bari a yi Sallah mana, ko kuma gobe da safe kya je."

Diddira ƙafa ta fara yi tare da faɗin. "Don Allah ki bar ni na je, duk su Lantana fa suna can tun ɗazu."

"Allah ya tsare." Inna ta faɗa a takaice, don ta san idan ta hana ta ma zama zata yi ta cika musu kunne da ihu, don ba ƙaramin aikinta ba ne.

Bayan Magriba Abbi ya sauka a Kano, direct gidan Ammi ya wuce, saboda ta kira shi akan tana son ganin shi. Bayan sun gaisa Ammi ta gyara zama ta ce. "Babana, ɗazu matarka ta kira ni tana ta kuka akan wannan auren da za ka ƙara, don Allah ka tausaya mata ko ɗaga bikin nan ne a yi mana, ka ga har yanzu tana cikin alhinin rashin Abra, wallahi tausayi take ba ni, duk ta bi ta ɗaga hankalinta." Cikin ladabi Abbi ya ce. "Ko shekara za a ƙara akan Auren nan idan aka tashi yi sai Nai'ma ta ƙara ɗaga hankalinta Ammi, kuma kin ga babu daɗi biki saura kwana biyar sannan a ce za a ɗaga saboda wani dalili mara ƙarfi, an riga an gama buga IV an raba, yarinya sun fitar da anko sun yi komai, sai a ɗauke mu ƙananun mutane." A sanyaye Ammi ta ce. "Shikenan, Allah ya tabbatar da Alkhairi ya ba ku zaman lafiya, Allah ya ba ka ikon yin adalci a tsakanin su."

"Amin Ammi, bari na ƙarasa gida don sauka ta kenan na ce driver ya fara kawo ni nan, idan na je na yi wanka na huta zan je gidan Iman, ta dame ni akan za su yi Mother's day da sauran su."

"Da ka rabu da su Babana, muna cikin alhinin mutuwar Granny da Abra babu wasu bidi'ebidi'e da za mu yi."

"Na mata maganar hakan ni ma, amma ta ce mini ai ba kiÉ—a za a yi ba, kamar walima abin zai tashi, za a ci a sha ne kawai."

Ammi ta ce. "Toh shikenan, Allah ya kai mu."

Ya amsa da Amin tare da miƙewa ya yi mata sallama ya tafi.

Sai kusan isha'i ta baro gidan Atine, tana tafe ita kaɗai cikin sauri ta ji ta yi karo da mutum. Cikin masifarta ta buɗe ba ki za ta yi magana amma maganar ta kakare, sakamakon ganin wanda ba ta yi zato ba. Adnan ne shi ma ya dawo daga inda ya je, hannunsa riƙe da torchlight yana haska hanya. Duk da ba ta kalli fuskarsa ba amma ƙamshinsa ya sanar mata shi ne.
Chapter 112 · 0% Book details