Sashe 133
Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abba ya ɗora da "Ya auri Abra, duk muna sa ran ya samu yarinyar kirki, suna zaune lafiya, ashe ba baka bane ba, sai ranar da Abra ta kusa rasa ranta, ya gigice ya dinga faɗar irin zaman da yai da ita, ya dinga azabtar da ita, bayan mun dawo daga wurin likita, ya bamu shawarar idan ta warke daga C.S ɗin da aka yi mata, a kaita India, saboda suna da ƙwararrun likitoci da Asibitocin da suka ƙware, a wurin bada kulawa ga masu ciwon, kuma tun da bata kai last stage ba, zata iya warkewa.
Daga nan na fara processing yadda Abra zata tafi India, katsam Adnan da bakinsa ya dinga faɗar yadda ya rayu da Abra, bayan an mata C.S jikinta ya rikice, duk mun ɗauka ta rasu, a lokacin da shi mijint, da Salman da ita Maman Salman duk sun suma, Nurses sun basu ɗaki, likitoci suka zo suka dudduba Abra, ba su ce mana komai ba, suka dinga mata ƙoƙari, suna dannna ƙirjinta suna mata allurai, har Major yana cewa kar su wahalar da gawar Abra, suka ce masa bata mutu ba, suganta ne yayi ƙasa fiye da kima, jinint ma ya sauka. Cikin ikon Allah ta cigaba da numfashi, amma bata hayyacinta, a ranar na buƙaci Major, da kar mu kuskura wani ya san Abra bata mutu ba, saboda za'a kaita India ne babu tabbacin ta dawo da rai, dan haka kar musa musu rai, na ɓoye masa ainihin dalilina na rashin san kowa ya san Abra bata mutu ba.
Muka tafi da Abra Abuja, na barota ita da Major, kwanan su ɗaya a General Hospital Abuja, suka tafi indiya, likitan da ya dubata ya mata cs, suka haɗamu da da likitocin Asibitin da za'a kai Abra. Cikin ikon Allah ana kaita suka karɓeta, muka biya komai aka fara bata kulawa ta musamman.
Lokacin da Maman Salman ta farfaÉ—o mun sanar da ita, an kaita gidana an mata sutura a binneta, duk da tayi mita a kan danme za a rufe Abra ko sallama ba suyi ba. Haka Adnan muka tabattar masa da an kai gawar Abra Kano, an binneta. Major ya baro Abra a can india, amma duk sati biyu ko ni ko shi, muna zuwa mu dubata, a nan Nigeria kuma, mun saka anata saukar Alqur'ani, har umara muka biya akaje aka yiwa Abra É—awafi, Allah ya bata lafiya, idan kuma ba zata rayu ba, Allah ya sa ta cika da imani.
A cikin ƙudirar ubangiji sati uku, Abra ta fara samun Lafiya, na samu Abra na sata a gaba, ta gaya mini komai a kan zamanta da Adnan, dan da farko so tayi ta rufawa Adnan Asiri. Na roƙeta a kan kar ta gaywa Major, halin da ta zauna da Adnan.
Cikin ikon Allah watanni biyar kan na shida, aka tabattar mana da Abra ta warke ras ba wata damuwa da take damunta Yanzu.
Alhamdilillah, a jiya ni da Major muka ɗauko Abra daga airport, ta kwana a gidan wani abokinsa, da safe muka wuce da ita Asibitin da mijinta yake, muka taho nan, haƙiƙa mun ɓata muku na ɓoye muku gaskiyar cewa Abra na raye, amma dan Allah kuyi mana afuwa. Zan yi amfani da wannan dama, wajen karɓar takardar sakin Abra daga hannunka Adnan, ka rubuta saki ka bani na Abra, zan mayar da ita Makaranta".
"Haba Abba, Wallahi nayi nadama ka duba halin da nake ciki, na san tabbas a kowane lokaci zan iya rasa raina, dan Allah ku bari mu ƙarasa rayuwarmu tare, ko dan saboda yarinyar mu*.
Rumaisa kuwa cewa ta ke "Dan Allah ita dai in ya saki Abran, a haÉ—a mata kan yaranta ta tafi da su".
Adnan a ransa ya ce "Ji wannan matar da son kai, Wallahi ba in da matata zata da Aurena".
Bulama ya ce "Dan Allah Afra, da kuma Abra dan Allah ku yafe mini, ku kalleni a matsayin uba ko sau É—aya a rayuwata, yanzu bani da wani abu da yayi mini saura idan baku ba, hatta 'yan uwana basa ta tawa, saboda Saudat ta rabani da su".
Gaba daya duk ɗokin da Afra take a kan son ganin mahaifinta, taji baƙi cikin kasancewar wannan azzalumin shine mahaifinsu, ba zata manta yadda aka bata labarin yadda ya wulaƙanta Baba har ya mutu ba, gaba ɗaya bai bata tausayi ba, mussaman da aka bada labarin cin amanar da ya yiwa mahaifiyarsu.
 Kowa da abin da ya dame shi a falon nan, kowa neman mafitar kansa kawai yake yi, gaba ɗaya kan Abra ya fara ɗaukar zafi, dan haka ta miƙe ta nufi ɗakinta, wanda Afra ce a ciki Yanzu.
Kan gadon taje ta haye tana kuka, yau ranar farinciki ce a gareta, ko ta baƙi ciki? Ya aka yi suka fito daga tsatson azzalumi irin wannan mutumin?
Duk yanayi na rashin lafiya da Adnan yake ciki, haka ya tashi yabi bayan Abra.
Yana zuwa ya fara ƙoƙarin abin da zuciyarsa ke muradi, wato ya rungumi Abra a jikinsa. Duka ta fara kai masa ta ko ina tana kuka "Adnan ka cikani na tsaneka, Azzalimi sai ka sakeni ka daina wani pretending ma".
"Abra nayi kewarki, harshe ba zai iya bayyana abin da ke cikin zuciya ba, dan Allah ki yafe mini, mu koma mu zauna na miki tanadin soyayya irin wadda baki taɓa tunanin akwai taba".
"To hell with your fucking useless love Adnan, duk wata soyayya idan har daga gareka take iska ce da shirme, kuma aikin banza, maƙaryaci, mayaudari, kuma maha'inci, ka aureni ka cutar da ni cutarwa mai muni, na tsane ka ko ƙaunar ganinka bana yi".
Cikin hawaye Adnan ya ce "Abra, nine fa Adnan, baban yarinyarki amma kike gaya mini haka?".
"Kaje kai da 'yar na bar maka, bana son duk wani abu da ya shafeka, dan haka ka tafi da 'yar ka na baka, kar ka sake zuwa in da nake"
"Abra dan girman Allah.
"Dan Allah Adnan ka rabu dani, ka bar mini wurin nan, tun kan in maka illa, Wallahi na tsnake, baka da bakin da zaka iya bani haƙurin da zai wanke zaluncin da ka yi mini, rashin lafiyata ƙuruciyata da maraicina a wannan lokacin bai sa ka tausaya mini na tsira daga rashin imaninka ba, na dinga binka a kan gwiwowina ina kuka, amma sau ɗaya baka kalleni da idon rahama ba, kome nayi maka kai ka koya mini, dan haka ka rabu da ni" ta ƙarasa Maganar tare da ficewa daga ɗakin ta bar Adnan saroro yana kallonta, bai taɓa zaton Abra ta iya wannan rashin mutunci ba.
Falo fa ya rikice, dan Bulama har da hawaye, amma Afra taƙi ko kallonsa, dan ko fuskarsa bata son gani, ga rigima ta kacame tsakaninsa da Rumaisa na sai ya dawo mata da duk dukiyarta, kuma ta saka rigima a kan da yaranta zata tafi.
Salima dai ta zama 'yar kallo, komai ya kwaɓe ba mai jin kan wani.
Abbi kuwa ya ce "Ko nan da airport babu mai zuwar masa da yaransa, ba za su bawa Rumaisa yaran nan ba" aikuwa ta sa musu kuka ta ce bata yarda ba.
Abbi ya ce "Ba muna son mu rabaki da yaranki bane ba, amma kinga Abra tana da Aure, Afra kuma very soon za'a É—aura mata aure, kinga ba zasu bar aurensu su biki ba, sai dai ki dawo ki zauna da mijinki, wato babansu a Nigeria, yadda zaki dinga ganinsu.
Aikuwa Rumaisa tai tsalle ta ce ko ana ha maza ha mata, ba zata zauna da Bulama ba, itama wataran kasheta zai yi, ko ya dawo ya kashe mata 'ya'ya, dan haka kotu zata kai shi, a raba aurensu a bata yaranta, dan kar a kuma kashe mata su.
Gaba ɗaya fa gida ya sake rikicewa, ana wannan turka turka, Adnan ya kuma dawowa falo, ya zube a gaban Abbi ya haɗa hannayensa ya ce "Dan Allah Abbi, na tuba nayi nadama, na san nayi wauta, amma dan Allah ayi haƙuri, ina cike da baƙincikin rashin mahaifiyata, da kusan aka kashe mini ita a kan idona, saboda sakaci da son zuciya na wannan mutumin"
"Ka gayar kalamanka, kar ka sake ka kausasa harshe a kan mahaifina, duk lalacewar iyaye iyaye ne, balle babu lalacewa a iyaye, ƙaddara bata wuce kan kowa ba" Abra tayi maganar cikin rauni, tana kallon Bulama amma ta kasa jin ɗigon soyayyar Bulama a ranta, tabbas ya cutar da Adnan, mussaman yadda ya bada labarin a yadda mahaifiyar tasa ta rasa ranta.
Abba ya girgiza kai ya ce "Adnan ka bani kunya, yarda da irin soyayyar da Abra take maka, ya sa na haƙura na aura maka ita, ba dan ina so ba, dan a son samuna tayi karatu, amma ganin tana sonka ya sanya na aura maka ita, amma kaci amana Adnan, ina son Abra a zuciyata fiye da yadda nake jin Salman ɗan da na haifa, dan haka nima ba zan takurata ba, ka rubuta takardarta ka bani kan ka bar garin Kano".
"Mama dan Allah ki saka baki, Mami kema kiyi magana su bani matata dan girman Allah".
Mami ta haɗe rai ta ce "A'a ka bar mini 'ya ta ta huta, gara ta dawo gabana ban gaji da ganinta ba, balle ka kashe ta a banza da baƙinciki a kan laifina da baita ta aikata ba" Wata irin Soyayar Hajiya Na'ima ta kuma mamaye zuciyar Abra, duk da irin wahalar da ta sha a hannunta, amma tana son baiwar Allah nan, saboda ta bawa ratuwarta gudunmuwa sosai.
Hajiya Mama tace "Allah ya sa ya zame maka darasi, har kullum da laifukan da kake yiwa Allah, da su yake maka hukunci, da baka rayu yadda kake so ba, amma ka ɗau fansa a kan wadda ita kanta bata san waye mahaifin nata ba, kuma tai shiru ta rufa maka asiri, duk da tana ƙishirwar son sanin mahaifinta, amma hakan bai sanya ta tona maka asiri ba, lallai Abra ta cancanci yabo, ta soka tsakani da Allah amma ka rusa damarka".