Sashe 2
Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Captain Khamal yabi cikin dajin da kallo yana mamakin girman da yake dashi, ta ina zasu fara lalubar waɗan nan ƴan matan? Zasu koma gida duka da ransu ko yaya ne? Yana tsaye hannunsa zube cikin Aljihu gaba ɗaya jikinsa kayan yaƙi ne, Daga baya yaji an dafa shi da sauri ya juya yana zare Bindiga, Captain Denial yayi Murmushi yana busa hayaƙin sigari yace
"Kai da kake a daji ai ba kai babu tsoro" Khamal dai ya taɓe baki yana jin warin Tabar na juya masa ciki, Denial ya ɗauki photo daga cikin aljihun Wandonsa ya miƙewa Captain Khamal photon yace "Ka ajjiye a wajanka" A hankali Captain yake bin photon da kallo ganin photon mace da kuma ƙaramar yarinya ɗauke a hannunta, cikin rashin fahimta yace. "me zan dashi?" Denial yace "Koda zan mutu a nan, ka bawa matata domin jikina yana bani ba kowa zai bar dajin nan da ransa ba a cikin mu, za'ai artabu duba da information ɗin da muka samu akan 'yan bindigar"
Khamal kallon Denial kawai yake, ba tare da yace komai ba ya saka photon cikin aljihun Wandonsa.
Tunda suka sauka cikin jejin basa jin motsin komai sai na kukan mugwayen dabbobi, A hankali Khamal ke tafiya yana zuwa wajan wata Bishiya ya yi saurin É—auke kansa, saboda ganin Denial da yayi tsaye da wata Sojan mace suna murje jikin juna, ko tsoran a kawo musu hari basa yi.
Ya bar gurin yana jin ɓacin rai akan abunda ya gani, ya koma in da sauran sojojin suke, Jamil ne yace "Captain yanzu idan ka samu nasara shi kenan ka daina fita yaƙi?"
Captain ya ɗaga kafaɗa alamar bai sani ba, waje suka nema suka zauna, suna kallon yadda ake ta haɗa kayan yaƙi da alama abokan harin nasu basu farga dasu a dajin ba, ko kuma suma duk cikin irin na su shirin ne ba wanda ya sani sai Allah.
Jamil ya ɗauki Wayarsa zai vedio call da watsastsiyyar budurwarsa amma babu network gaba ɗaya cikin dajin, sai kawai ya ɗauki pen da paper ya fara Rubutu, yana tsaka da Rubutun suka fara jiyo ƙarar bindigogi ta ko'ina.
Garin sauri Jamil ya danƙawa Captain paper hannunsa. Kafin kace wani abu dajin ya ƙaraɗe da ƙarar Bindigu.
Cikin azama suma zaratan sojojin suka fara maida martani, tare da fara sakin harsashi cikin ƙwarewa da dakiya irin ta aiki, kan kace kwabo amsa kuwwar sautin bindigogin ya karaɗe dajin gaba ɗaya.
Sun kwashi dogon lokaci suna bata kashi, babu Sallah ga Musulmin cikin su babu abinci, hankalin duka sojojin a tashe ganin an fara kashe su ana neman aci galaba a kansu, ba tare sun kai ga in da 'yan mata suke ba.
An raunata da dama daga cikin sojojin, bayan komai ya lafa nan likitocin cikinsu suka fara aikin ba su taimakon gaggawa.
Cikin dare kowa ya ɓoye a inda yake, wayar Khamal ya fara haske da mamaki yake kallon wayar ganin screen ɗin wayar ya nuna sunan _My wife_ har zai katse sai ya tuna rabon da yayi waya da matarsa wata biyu kenan ciff. Bashi da tabbacin zai bar nan a raye, a nutse ya ɗaga kiran yana faɗin "Hey Beb..." Daga can Garin Kano matar Khamal mai suna Na'ima tace
"Hankali na, yaƙi kwanciya Dear" shiru yayi mata saboda motsin da yaji a daf da in da yake, A hankali Na'ima tace "Nayi kewarka tare da Babynka dake cikina, gaba ɗaya hankalina a tashe yake, ga bana samunka a waya, bana son wani abu ya sameka" idanunsa ya lumshe cikin ƙasa da murya yace "I miss you, ki kula, ina aiki ne yanzu" yana faɗin haka ya kashe wayar baki ɗaya.
A hankali ya fara tafiya a ƙasa, yana jan cikinsa a ƙasa zuwa inda yake hango mutum a kwance, mamaki ya kama shi ganin wata matashiyar yarinya kwance cikin jini se numfarfashi take, duk an yage suturar jikimta, da alamar fyaɗe akai mata, ba mutum ɗaya bama, saboda yanayin da take yafi ƙarfin ace mutum ɗaya ne yai mata.
Yarinyar ta kama hannun Khamal ta riƙe sosai muryarta na rawa, ganin ta kasa magana gashi se rirriƙeshi take yasa Khamal ya ɗora kunnansa a bakinta, A hankali yarinyar tace
"Ya...Ya... Yaaya" sai kuma tai shiru numfashinta na fisga da ƙarfi, tana ƙanƙame hannun Khamal tace "Basu da imani, basu da tausayi, kada ka barsu Yaya, kada ka barsu Yayaaa in ba kuyi sauri ba sauran ma haka za suyi musu, fyaɗe suke mana" ta ƙarasa maganar tana shaƙuwa.
A kiɗime Khamal ya shiga girgiza yarinyar amma ina tuni rai yayi halinsa, wani irin numfashi ya fara fitarwa jikinsa ya ɗauki rawa, yana da tabbaci tana ɗaya daga cikin ƴan matan da aka sace, runste idanunsa yayi a hankali ya rufe mata Idanunta tare da jan zanin jikinta ya rufeta, har yanzu tana riƙe da hannunsa, wani irin baƙin ciki yana ratsa zuciyarsa, ace a ƙasarka amma ranka da mutuncinka ba a bakin komai yake ba, kai mutuwar wulaƙanci irin wannan saboda son zuciyar wasu tsirarun mutane.
Cikin dare Khamal ya dinga bincikar dajin, yana zagawa da map É—in da ke hannunsa, da yake akwai hasken farin wata.
A haka Khamal ya gano suna daf da in da yaran suke, saboda hayaniyar da ya dinga jin tana tasowa nesa kaɗan da in da yake, dan haka cikin ƙwarewa irin ta aiki Khamal da jama'arsa suka ƙarasa in da suke, Nan da nan suma suka farga, suka fara musayar wuta, wasu daga ciki ga yara a hannunsa,wasu kuma jikinsu duk jini alamar ba'a jima dayi musu fyaɗe ba. Yaran suna a matuƙar galabaice.
A daren su Captain basu iya bacci ba, duk yawan bataliyar nan ta sojojin, an kashe da dama daga cikinsu, an illata wasu, a daren suka kama wasu daga cikin 'yan ta'addan yayin da wasu daga cikin su suka samu nasarar tserewa zuwa cikin dajin.
Sanyin safiyar yasa Captain Miƙewa yana tafiya a hankali, suka tattare 'yan matan guri guda, duk sun galabaita saboda wahala, wasunsu ba su da lafiya wasu babu suturar kirki a jikinsu, nan sojojin suka fara yiwa 'yan matan jagora dan fitar da su daga cikin sarƙaƙiyar dajin, yayin da wasu sojojin ke ta kwaso gawarwakin'yan uwansu da aka kashe.
"Khamal" aka kira sunansa, da sauri ya juya ganin Jamil kwance cikin jini, anyi masa harbi kusan guda uku, jikinsa na rawa yace "Jamil" Jamil ya girgiza kai yace "Khamal ina maka fatan tsira da ranka, kaje wajan matata kace ta yafe min, wlh ban san adadin Æ´an matan da nayi mu'amala dasu ba, yanzu haka ina É—auke da Hiv, ina da tabbacin matata ma tana dashi, bata san hawa ba bata san sauka ba, na É—ora mata mugun ciwo" Khamal ya Girgiza kansa yace
"Kayi salati" Khamal ya fara salati Jamil yana maimaita wa, a nan jikin Khamal Ubangiji ya É—auki ran Jamil....
Kwanan su wajan uku, cikin dajin gaba É—aya kuma sun kwashe Æ´an matan an fita da su, a kwanaki ukun nan, kullum se sunyi musayar wuta da 'yan bindiga.
sojojin duk sun ƙare, se wanda ba'a rasa ba, da gudu Major yake tafiya ganin wata budurwa yashe a ƙasa, kafin ya Ƙarasa wajanta yaji ance
"Kaiiii" Aka daka masa tsawa da karfi, Juyawa yayi ya ware idanunsa ganin wani riƙe da bindiga zai harbeshi, Denial ya tare harbin hakan yasa aka harbi Denial a ƙirji...
Captain ya zaro bindiga ya fara Harbin ɗan ta'addan , sai daya kashe shi sannan ya nufi wajan Denial yace "Mene yasa haka Denial?" Denial ya girgiza kai yace "Kai na musamman ne, gwara na mutu kai ka rayu, bana faɗa maka ba? Daman nasan mutuwa zan, kada ka manta da abinda na baka, a cikin mu akwai maciya amanar ƙasa, amma kai da gaske kake naka aikin, Khamal na baka amanar iyali na.. zaka iya, nasan zaka iya ka kula dasu"
Yana faɗin hakan rai yayi halinsa, wani irin ihu Khamal ya saki mene yasa haka ke faruwa? Su sojoji a haka rayuwarsu zata ƙare ne? Sunyi shiri na gaske akan faɗan nan, amma kamar 'yan ta'addan sun san da zuwansuz duk sun samu nasarar kashe zaratan sojoji masu ƙoƙari, ciki har da makusantan abokansa, Miƙewa ya yi, gaba ɗaya jikinsa jini ne kayansa duk sun yage, ga yunwa, ƙishirwa.
Yana zaune a ƙasa yaji shawagen Helicopter, da alamar General ne ya ƙaraso,yasan ɗauki gaggawa aka kawo musu, kasa Miƙewa yayi har sai da wani soja yazo wajansa ya ɗaga sa, yana faɗin "Komai yazo ƙarshe Captain"
Sauran gawarwakin aka kwashe zuwa cikin wata babbar motar sojoji, raguwar 'yan ta'addan da sojojin suka kama suka ɗaure, suma aka zuba su cikin mota, suma sauran mutanen da suka tsitstsinto anyi garkuwa da su, a wata mota aka zuba su, Khamal ya miƙe ya na tafiya a hankali, kamar daga sama kunnansa ya fara jiyo masa kukan ƙaramin yaro, tsaye yayi, yai shiruu, jin kamar ba kuka bane yasa ya cigaba da tafiya. yana ƙoƙarin sanya ƙafarsa cikin mota, ya ƙara jiyo sautin kuka, a wannan karon kuma ya tabbatar gaskiya kunnansa ya jiyo masa, kuka ne da gaske, fasa hawa motar yai, sauran sojojin na kiransa amma be kula ba, a hankali yake tafiya jiki a sanyaye da ƙyar yake ɗaga ƙafarsa saboda wahala, ganin baiga kowa ba sai ya fara tunanin ko aljanu ne? Ko kuma kukan wata dabbar ce, wani kukan ya sake jiyowa da sauri ya juya zuwa inda yake jin kukan, ya ƙara nausawa cikin dajin, ware idanunsa yayi kan ƙaramar yarinyar dake zaune a ƙasa ta ƙanƙame jikinta waje guda, Idanunta rufe da alama gaba ɗaya a firgice take, Khamal ya ware idanunsa akan yarinyar gaba ɗaya ba zata shige shekara uku ba (3Years) fara ce sosai kamar buzuwa kamar kuma Balarabiya, tafi kama da ruwa biyu (Half-caste) domin gashinta wanda yafi ƙarfin kanta ya sauka har ƙasa kasancewar a zaune take, farar fatar jikinta tayi baƙi sosai, ga raunuka a jikinta..
Sosai Khamal ya girgiza da ganin ƙaramar yarinya a cikin jejin nan, sai ya fara tunanin ko dai Aljana ce?ko a cikin matan da akai kidnapping take, Samun kansa ya yi da cewa