← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 145

Sashe 35

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Labarin duk abin da ya faru Salman ya ba su, lokaci ɗaya Aunty Iman da Ammi suka kalli juna kamar wanda suka fahimci wani abu. Cikin mamaki Ammi ta ce. "Wani kuma? Wane ne wanin?" Gyaɗa mata kai kawai Salman ya yi dan ba ma ya san zancen mutumin, saboda wani irin zafi yake ji a cikin zuciyarsa idan ya tuna riƙe wa Abra hannu da ya yi.

Aunty Iman ta ce. "Ikon Allah, yanzu kuma kafin mu shigo nan mun haÉ—u da wani Doctor, ya ja mu ofis É—insa ya yi mana bayanin abun da yake damun ta bayan ya tambaye mu mu ne iyayenta, ya sanar mana firgici ta shiga, shi ne ya jefa ta a wannan halin, may be ta ga wani abu da ya firgita ta ne ko ya tsora ta over."

Salman ya yatsina fuska ya ce. "Wa ya sani ko maye ta haɗu da shi." Ammi ta ce "Allah ya kiyaye, ba ma fatan haka, kar ka kuma faɗar haka Salman, na san daƙyar in ka yi Sallar la'asar yanda na gan ka agigicen nan, ka je ka yi yanzu tunda mun zo." Salman ya ce. "To, tare da muke da driver kuma na ga bai shigo ba." Ammi ta ce. "Mun haɗu da shi, na aike shi can gida ne ya karbo mana ruwan zafi da kayan tea a wajen Matar Shureim, saboda kiɗimewa mun manta ba ba mu ɗauko ba." Salman ya miƙe ya fice, Aunty Iman ta bi bayansa dan zuwa ta siyo magungunan da aka rubutawa Abra, ta kuma biya kuɗin charges ɗinsu da aka yi.

Na'ima tana kwance akan gadonta tana chatting da ƙawayenta hankali kwance Major ya kira wayarta, bayan ta ɗauka sun gaisa ya ce. "Ina Daughter da Salman? Na kira general phone ɗin gidan na ji ba su ɗauka ba." Jim ta yi na wasu sakanni sannan ta ce. "Suna islamiyya, ni kuma ina ɗaki ban ji kiran ba."

"Wacce Islamiyyar? Yau fa Thursday."

"Oh sorry na manta, ka san na saba kafin su yi sauka suna zuwa har Alhamis da Juma'a, sun je shopping ne."

"Na'ima wannan wacce irin magana ce? Yarana sun fita amma saboda careless baki san takamaiman inda suka tafi ba, sai kin yi kame_kame kafin ki sanar mun? Shopping É—in kuma da aka fita tun 12 shine har yanzu ba su dawo ba?"

Ɓata fuska ta yi ta ce. "Haba Khamal, ya kake so in yi, duk ƙoƙarin da nake akan yaran nan baka gani, dan yau ɗaya ka tambaya na yi mantuwar inda suka je sai ka kama faɗa, ni fa ɗan Adam ce ajiza kamar kowa, zan iya mantuwa. Kuma da kake cewa sun tafi tun ɗazu ba su dawo ba, nima ina zaune ni kaɗai faɗan da nake yi kenan, amma na kira driver ya ce mun suna hanya sun kusa ƙarasowa."

Ajiyar zuciya Khamal ya sauke ya ce. "Shikenan Allah ya dawo da su lafiya, in sun dawo na san za su kira ni, ina zaune ni kaÉ—ai a office kawai na ji hankalina bai kwanta ba, kamar something bad happen to you."

"No..no babu komai, muna lafiya dukanmu."

"To Allah ya ƙara muku lafiyar, ya cigaba da ba ku kariyarsa a kodayaushe."

"Amin ya Allah Mijina, tare da kai."

Ya amsa da Amin sannan suka yi sallama. Tsaki Na'ima ta ja a fili cikin takaici, wato har jikinsa ya ba shi babu lafiya, saboda waccan shegiyar yarinyar ba ta da lafiya. Taɓe baki ta yi ta cigaba da chat ɗinta.

Sai da biyar ta wuce Abra ta farka, lokacin su Ammi suna tattaunawa akan abun da Na'ima ta yi na ƙin zuwa asibiti, da yake Salman ya ba su labari saboda yanda abun ya tsaya masa a rai.

"Salman! Faris!"

Da abun da ta farka a bakinta kenan cikin sanyin murya irinta marasa lafiya.

A tare Salman da Ammi suka yi kanta, Ammi ta riƙe ta hannunta tana ambatar sunanta. Idanunta a lumshe amma sunan Salman kawai take kira. Wata sassanyar ajiyar zuciya ya sauke amma bai ce komai ba. Fita Aunty Iman ta yi dan kiran likita. Cikin kulawa Ammi ta ce. "Sannu Abra, Allah ya baki lafiya, ciwon lokaci ɗaya amma har kin faɗa."

A hankali ta buɗe idonta ta sauke su akan kyakkywar fuskar Salman, idanunta a cikin nasa ta amsawa da Ammi da Amin. Ba yabo ba fallasa ya ce. "Sannu Yaya." Gyaɗa masa kai ta yi tana ƙara narkar da idanunta a cikin nasa. Lumshe idonsa ya yi ya buɗe wani baƙon al'amari na yawo a cikin zuciyarsa, bai kuma magana ba sai zama da ya yi a gefen gadon.

Ammi ta gyara mata kwanciya tana jera mata sannu. Tare Aunty Iman suka dawo ɗakin da Doctor, ya dudduba jikin Abra tare da yi mata tambayoyi sannan ya tabbatar musu babu watar matsala, drip ɗin da aka saka mata yana ƙarewa za a sallame su.

Kulawa sosai Ammi da Aunty Iman suka ba wa Abra, Salman ma ya nuna mata kulawa sosai amma ya ƙi sakar mata fuska, sai ta yi masa magana yana ji ya fuske kamar bai ji ba, duk sai ta ji ta damu, ta rasa sukuni a cikin zuciyarta.

Bayan Magriba aka sallame su, Alhamdulillah jikin Abra ya yi sauƙi, kamar ba ita ce awanni uku zuwa huɗu da suka wuce take kwance cikin mawuyacin hali ba. Gidan Ammi Salman ya ce su wuce, dan ya san sai ta fi samun kulawa a can akan gurin mahaifiyarsa.

Na'ima na jin shigowar Motar da su Abra suka fita ta yi saurin saukowa falon ƙasa, a tunaninta su ne suka dawo, ba ta san driver ne kaɗai ba. Jin shiru-shiru ba su shigo ba yasa ta ɗaukar mayafinta ta fita compound ɗin gidan.

Kiran shi ta yi a waya ya zo inda take, cikin mamaki ta tambaye shi ina su Salman ta gan shi ya dawo shi kaÉ—ai?

A ladabce ya ce, "Hajiya Babba ta zo asibitin, daga nan suka wuce gidanta."

"Wacce Hajiya Babban?"

"Mahaifiyar Sir Khamal?"

Jinjina kai ta yi ta ce. "Alright" Sannan ta juya ta koma ciki ranta a matuƙar ɓace.

Abra tana kwance akan gadon ɗakin Ammi, idanunta akan Salman wanda har lokacin ya ƙi sakar mata fuska ta ce. "Faris cikina ciwo yake mini." Cikin kulawa ya ce. "Sannu Allah ya ƙara sauƙi, bari na karɓo miki magani a gurin Ammi."

Ɓata fuska ta yi ta ce. "Me ya faru na gan ka a haka? Kamar kana cikin damuwa, tun ɗazu kuma ina tambayar ka, ka ƙi ba ni amsa."

"Nothing."
Ya faɗa yana ƙara haɗe rai.

Cikin marairaicewa ta ce. "Please Faris tell me, ko so kake ka ganni a cikin damuwa ni ma? Ka san bana son na gan ka a cikin damuwa"

Bai ce komai ba ya miƙe da niyyar fita, kukan da ta fashe da shi ne yasa shi dakatawa. Da sauri ya koma ya zauna a kusa da ita tare da kama hannunta, a rud'e ya ce. "Mene ne Yaya? Jikin ne ko ciwon cikin ne?" Cikin shagwab'a ta ce. "Kai ne Salman, ka ƙi faɗa mun abun da yake damun ka, ka san kuma ba zan jure ganin ka a haka ba, cikin ɓacin rai." Numfashi ya sauke ya ɗauki kanta ya ɗora akan cinyarsa, hawayen fuskarta ya fara share mata ya ce. "Babyn Abbi, zaki karyar mini zuciya da wannan shagwab'ar taki, har kin sa hankalina ya tashi, na ɗauka wani abun ne ya same ki."

"To ai kai ne"

"I'm sorry na daina My Angel" ya yi maganar yana shafa kuncinta.

"To faɗa mun me yake damun ka, me ya ɓata maka rai?"

"Tsayawar da kika yi har wani banza ya riƙe miki hannu, maimakon ki tsinka masa mari sai kika tsaya kina kallon shi." Ya yi maganar cikin ɓacin rai da takaici.

"To ya zan yi Faris? Ni ma abun a bazata ya zo mun, amma ka yi haƙuri insha Allahu hakan ba zai kuma faruwa ba."

"Allah yasa, dan bana fatan hakan ta kuma faruwa akan wani mai tsautsayin, dan tsaf zan karya hannun duk wanda ya kuma gigin taɓa mun jikinki."

Da mamaki take kallon shi, yanda ya dage yake magana iya gaskiyar shi. Murmurshi ta yi ta ce, "To ka saki ranka mana in ji daɗi a cikin raina, ka ji ɗan ƙanina." Karan hancinta ya ja tare da yin murmurshi bai ce komai ba.

Ƙarfe goma da ƴan mintuna na dare Salman yana zaune a parlour suna magana da Ammi Khamal ya kira wayar Ammi, bayan ta ɗauka sun gaisa ya ce ta bawa Salman wayar.

"Hello Abbi."

"Na'am Salman, me yasa kuka wuce gidan Ammi daga shopping ba ku sanar da Maminku ba?"

Kallon Ammi ya yi sannan ya ce. "Abbi na kira wayarta zan sanar mata da wayar Driver ba ta shiga ba."

"Duk da haka da kun koma gida kun fasa zuwa gidan Ammin, yanzu gashi duk kun É—aga mata hankali, ta kira ni tana ta faÉ—a wai sai driver ne ya sanar mata, har yanzu ku ba ku kira ta ba."

Shiru Salman ya yi dan ya rasa abun cewa, Khamal ya ce. "Kar ku sake haka, ba daidai ba ne." Cikin ladabi ya ce. "Insha Allahu Abbi za mu kiyaye."

"Yawwa É—an albarka, ina Yayar taka?"

"Ta yi bacci."

Daga haka suka yi sallama, zai faɗawa Ammi abun da ya faru ta dakatar da shi da faɗin. "Na ji komai ba sai ka maimaita mini ba, ka yi haƙuri Salman, mahaifiyarka ce Na'ima amma abubuwan da take yi ba ta kyautawa, ban yi tunanin duk shekarun nan har yanzu ba ta ƙaunar yarinyar nan ba, na ɗauka ta haƙura komai ya wuce, ashe da sauran rina a kaba. Abun da nake so da kai kar ka bari mahaifinku ya ji wannan maganar, kamar yadda na faɗa tun ɗazu kar a sanar masa wannan ciwon da Abra ta yi, to ko nan gaba kar ka faɗa masa, saboda ba na son ya san da batun ƙin zuwa duba Abra da Nai'ma ta yi."

Jiki a sanyaye Salman ya ce. "Insha Allahu, wai ina Granny ne?"

"Ta je gidan Gwaggo tun safe, a can za ta kwana, sai gobe za ta dawo."
Chapter 35 · 0% Book details