← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 120 OF 145

Sashe 120

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Taɓ, wallahi ni bana son ka ba zan aure ka ba." Ta katse shi da faɗin haka cikin serious dake tabbatar da abin da ta faɗa har cikin zuciyarta haka ne.

Littafin kuÉ—i ne, ku biya kafin ku karanta. 09047871750
[11/14, 9:13 PM] Abk: "Are you sure baki so na ba zaki aure ni ba?" Adnan ya faÉ—a cikin tsoro da fargaba maganar data nemi ta sar masa da mikin dake damun zuciyarsa na rashin Abra.
"Ni fa ba zan taɓa aurenka ba, gaskiya kayi mini baƙi da yawa kuma bana son ka shi ne kawai....,"

"Stop it.." ya faɗa a tsawa ce yana riƙe saitin zuciyarsa dake masa zafi lokaci guda, kalaman bakin Afra na neman sauya masa lissafi. Kasa magana ya yi sai idanunsu daya rufe zuciyarsa na harbawa.

"Na kawo maka ruwa kasha ne, naga kamar ka ƙware?" Ɗago jajayen idanunshi ya yi tare da zuba mata akan fuskarta wanda a kullum take masa gizo, ƙarfin hali yake kawai na Kasancewar su tare da yawan lokota sai ya ji kamar ya jawota ya rungometa ya faɗa mata how much he loving her!

Ya sauke numfashi a galabaici yana kallon yadda tai shiru tana binsa da idanu. Ba tare da ya ce komai ba ya juya ya bar ƙofar gidan nasu.
Ita ma bata kira shi ba, amma har zuciyarta ta ji babu daÉ—i a shirunsa da tafiyar ta shi, zuwa yanzu ta fara sabawa da shi.

"Wannan karan kuma mene ya faru kika shigo jiki a saɓule kamar kazar da ƙwai ya fashewa?" Inna ta tambayi Afra wacce ta shigo tana bin bango ta luuula duniyar tunani da alama bata ma san abin da Innar ke faɗa ba.

"Yau naga abin da ya ishe ni, anya yarinyar nan lafiyarki ɗaya kowa? Ina ta ɓaɓatu kin yi mini shiru?. Haka kurum kada naje ina tufka wani na warware mini ita na shiga uku"
Nan ma dai Afra ba ta ce komai ba sai bin bango da tayi ta zauna tana wawware idanunta. "Kee! Kee!! Ƴar Baba?"

"Na'am Inna"
Afra ta faÉ—a a gigice bayan Inna ta girgiza kafaÉ—arta.

"Lafiya ke dawa,ina kika je bayan kin kawo ruwan?"

"Gasky Inna tambayarki ba zata mutum ya yi ilimi ba, tunani nake fa amma gaba ɗaya kinsa na manta abin da nake ina jinki fa" Inna ta riƙe haɓa tana faɗin..

"Tunanin uban me kuma? Salon ki kawa kanki ciwo" ganin hawaye a fuskar Afra ya sanya jiki babu ƙwari Inna ta tana tambayar lafiya Meke faruwa da ita haka?..

"Inna tun bayan mutuwar wanda zan aura har yanzu babu wanda ya ce yana so na zai aureni, haka zan ta zama kenan kalli ƙawayena ko wacce tana yaranta abin sha'awa wasu kuma ciki garesu"

Cikin kulawa irin ta Uwa da Ƴa Inna ta kama hannun Afra tana cewa.

"A'a Ƴar Baba shi aure lokaci ne, na sha faɗa miki da lokacin ki ya yi ko bakya so sai kinyi auren nan, zaki auri miji wanda babu irinsa a garin nan ƙyakƙyawa ƙin kowa sai wanda ka taɓa,
Ba kiga kalarki ba wanke hannu ka taɓa kada ki saka wannan a ranki muna ta addu'a kema kici gaba da yi"

"Kuma bakya tunanin sbd bani da iyaye ba a zuwa neman aure na Inna?" Yanayin yadda ta yi maganar a raunace ya sa Inna yin shiru ita ma abin yana susa mata zuciya ainun bata da yadda za ta yi ne.

ÆŠaki Afra ta shige zuciyarta babu daÉ—i abubuwa suka dawo mata sabbi a rai. Tana jin kamar bata kyautawa Adnan ba, bata ji daÉ—in yadda ya tafi ba babu farin ciki akan fuskarsa kamar kullum. Kuma ba lallai ya dawo ba. Kuka ta fashe da shi na rashin abin yi a haka bacci ya É—auke ta.

Tun da ya shigo ɗakin ya kasa zaune ya kasa tsaye "Bana son ka" kalmar ta tsaya masa a rai, ashe haka ake ji idan an cewa mutum ba a son shi? Yaya matan da suka dinga son shi a baya suka ji a zuciyarsu? Afra akwai wauta amma zantunkan bakinta daga zuciyarta suke, babu alamar ƙarya ko wasa a cikinsu tana nufin abin da ta ce ne.

"What should I do? Adnan think, think" ya faɗa a hankali yana rufe idanunshi. Ba zai fushi da ita ba,amma dole ya ɗaga mata ƙafa domin fahimtar zuciyarta.

Wayarsa ya ɗauka ya kira Hajiya Mama tana ɗauka ya kwaɓe fuska tare da langwaɓar da kansa gefe guda.

"Son ya dai?" Cikin ƙasa da murya ya ce "Evening Hajiyata" ta amsa da "How are you? Ya zaman village? The you like it"

"Sure Mama, kawai ki tayani da addu'a wani abu na neman tunkaro ni kamar zai bani wahala kuma" Hajiya Mama bata fahimta ta É—auka al'amarin aiki ne hakan ya sa ta ce.

"Addu'a kam kullum muna yinta Sp Adnan Aliyu Matawalle, Allah ya taimaka ya baka sa a Insha Allah zaka samesa cikin sauƙi"
Idanunshi ya lumshe yana jin nutsuwa na saukar masa a hankali ya mirgina gefe yana jan numfashi ya ce.

"That's why i always love you Mom..."

Murmushi tayi cike da jin daɗi domin tana ƙaunar Adnan ji take kamar ita ta haife shi duk da cewa ita bata taɓa haihuwa ba, maybe bata ɗaya daga cikin matan da suke haihuwa a nan duniya.

"Hajiya, Abba...." Ya faÉ—a cike da rauni domin ya fara gajiya Abba shi ne cikon jin daÉ—insa dama samun nasarar baki É—aya, sai da shi duniyarsa ke zama cikakkiya.

"Me Abba ya yi kuma Adnan?" A kasalance ya ce. "He still angry with me na rasa yaya zan yi ne bana jin daÉ—in"

"Adnan my Son kada ka damu da hakan, Abbanka surprise ɗinka zai yi very soon ka mai da hankali kawai wajan yin aikinka Please" Hira su kaci gaba dayi cikin nuna soyayya a haka Adnan ya manta da ɓacin ran da Afra da haddasawa zuciyarsa.

Yau ranar kirkin Mami ne tana zaune gefen gadonta lokacin kusan ƙarfe goma na dare ne, ta shirya cikin wasu haɗaɗɗun kaya na barci, hannunta ɗauke Aishatul-humaira wacce taƙi yin barci yau sai dry ta kewa Mami tana ɗaga ƙafa duk ta cire sosan da aka yi wa kanta ado da shi.

"Sweetheart yau hirar dare za mu yi kenan, kwana biyu daddynki bai neme mu"

"Idan ba Dady ai akwai grandfa right?" Abbi ya faɗa yana shigowa cikin bedroom ɗin sanye yake da ƙyakkyawar shiga ta barci sai ƙamshi yake zabgawa.
Mami bata kallesa ba hankalinta akan Aishatul-humaira iya kuzarin yarinyar abin sha'awa ne. Hannu ya sa ya ɗauki little yana mata wasa amma ta ɓata fuska alamar anyi mata ba daidai ba.

"Wato Na'ima na saka ki a bedroom tana hure miki kunne akan Granny naki ko, shi ne zaki ɓata fuska?" Kamar Aishatul-humaira ta fahimci abin da ya ce ta fashe da kuka sosai tana cilla ƙafa, Abbi ya waro ido yana miƙa wa Na'ima ita ya ce.
"Wannan soyayyar taku daga Allah take, maza ki bata haƙuri" jijjigata ta dinga yi a haka tai barci tana sauke ajjiyar zuciya. A nutse Mami ta kwantar da ita bayan tai mata addu'a ta miƙe zata bar ɗakin "Na'ima" Abbi ya kira sunanta yana bin jikinta da kallo ƙamshinta na fisgarsa zuwa gare ta.
Wajanta ya ƙarasa ya tsaya daidai bayanta tare da saƙalo waist ɗinta da hannunsa biyu cikin ƙasa da murya ya ce "Ni kike azabtarwa haka Na'ima? Ba zaki amshi wannan auren matsayin ƙaddararmu baki ɗaya ba? The you know how much i miss You? Baki san adadin son da nake miki ba ko?" Juyo da ita ya yi gabansa yana kallon yadda hawaye duk ya ɓata mata fuska ta wani shagwaɓe fuska.

"Am sorry first love uwar gidan Major Khamal Khamis, ki yafe masa mana?" Ɗaga ta yi suka haɗa idanu ta ɓalla masa harara dry ya yi mai sauti yana jawota baki ɗaya zuwa jikinsa ya matse ya ce "Ohhhu dai naji, muje na nuna miki wani abu?" Ya faɗa yana sumbatar wuyanta tare da janta zuwa other bedroom.

Washegari abin har mamaki ya bawa Salima ganin har 12 Abbi bai fito ba, kamar yadda ya saɓa ɗakinta ya tashi da wuri ya duba Na'ima da little ɗin. Tana zaune a Parlour watching TV taji dry ƙasa ƙasa da sauri ta juya zuciyarta ce ta buga ganin Na'ima cikin wani dakakken lace mai masifar kyau, sai Little a hannunta wacce ta farka tuni ita ta tashe su ma, Abbi ya saƙalo jikin Na'ima shi kansa bai san adadin son da yake mata ba. Zama sukai a saman Kujera Salima tai murmushi ta ce "Barka da fitowa honey?"

"Yawwa Barka baby" ta juya kan Na'ima wacce take latsa waya tana ƙoƙarin ɗaukansu a photo ta turawa Salman "Maman Salman an tashi Lafiya?" Mami na ɗora kai a shoulder ɗin Abbi kamar dole ta ce.

"Ya kike?" Kalmar ta daki zuciyar Salima sai kawai ta share, Naima na ƙoƙarin turawa Salmanun-faris photos taji Sallamar sa da sauri ta miƙe tsaye tana mmki, yana tsaye bakin ƙofa cikin wata dakakken shadda kyan da Salman ya yi ya ɓaci, ya zama cikakken matashi wanda samun kamarsa za a daɗe ga haiba da kwarjini. Cikin sauri ya ƙarasu yana ɗaukan Little wacce ta kafesa da idanu irin ta ganesa ɗin nan "My sweetheart my happiness daddy is here...

Tsayin kwanaki uku ciff Adnan ya ɗauka bai sake haɗa hanya da ƴar Baba ba, hankalinsa akan aikin daya kawosa baya son haɗa abu biyu domin ya fahimci yarinyar na neman bashi ciwon kai. Cikin ikon Allah ya samu nasara cikin daren wata rana aka zo aka tafi da Ɗan kunama da sauran muƙarrabansa. Adnan kuma ya ce akwai abin da ya ke jira. Amma duk wanda ya gansa ya san baya cikin nutsuwar ya faɗa tsoro da zullumin yadda zai ƙara tunkarar Afra a lokaci na barkatai suka ƙara wanzuwa a ransa, neman aurenta ya bambanta dana Abra domin cikin lokaci kaɗan ta amince masa.
Chapter 120 · 0% Book details