← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 127 OF 145

Sashe 127

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"I can't dole na fara jin damuwarki a gigice na tahu" ta gyara zama cikin damuwa ta ce "Abubuwa ne suke ta fara, gaba É—aya dukiyata na neman lalacewa kullum cikin asara da rasa kuÉ—aÉ—e nake, na rasa inda abin ya samu tushe ina son magance matsalar, wannan dalilin ya sanya na saka Abdullah ya rufe company ta kalman dana buÉ—e" Ya runtse idanunsa domin abin ya zo masa a bazata bai É—auka abin zai sauri har haka ba, shi bama wannan ce damuwar shi ba.
Yana ƙoƙarin magana wayar shi tayi ringing ganin wata number ya share, Ummi ta kafe shi da idanu can dai ya ɗaga a fusace ya ce.
"Wai mene?" Tsaki kawai yaja ya ce.
"Allah ya sawwaƙe" Ummi ta ce "Waye ba lafiya?" Yaja tsaki ya ce "No wani ma'aikacina ne" tana ƙoƙarin wata maganar aka sake kiran shi da sauri ya miƙe ganin number wanda yake ta jira. Jikinsa na rawa yama mance a gaban waye yake.
"Hello, Assalamu alaika" daga can wayar aka ce "Muna magana da Dr Bulama" ya juya ya kalli Ummi ya ce "E, shi ne" aka ce "Mahaifin Adnan Aliyu Matawalle ke magana, ina son ganinka domin samun tabbaci shin da gaske Abra da Afra yaranka ne kai ne real father nasu?" Gaba É—aya jikin Uncle ko nace Dr Bulama rawa yake ya ce "Oh!ok yanzu haka Ina Dubai, amma zuwa gobe zan sauka Nigeria I'll call you" Abba da Abbi suka kalli juna a tare suka ce "Dubai????" Ya ce "Eh, amma gobe zan zo Insha Allah" kashe wayar ya yi gaba É—aya jikinsa rawa yake ya ce. "Rumaisa daman yaranmu ba mutuwa sukai ba???" Ummi da Abdullah suka ce "What???....
[11/22, 4:52 PM] Abk: Cikin gigicewa, da gurɓatacciyar hausarta, ta fara haɗa larabci, turanci da kuma hausa, ta kalli Bulama ta ce "Wane irin zance ne kake mini haka? Kamar yaya yaranmu ba mutuwa suka yi ba? Bayan ina labor room, aka ce mini na haifi yara tagwaye amma babu rai?".
Jiki a sanyaye Bulama ya ce "Nima abin da nake mamaki kenan, ta yaya za ce suna raye?".

Ummi ta ce "Wai wani irin zance ne wannan? Baka tabattar ba kenan, ya kake son ka yi mini wasa da hankali Yusuf Bulama?".
Abdullah ya tattaro nutsuwarsa ya kalli Bulama, shi ya iya hausa sosai ba kamr rumaisa ba, ya ce "Ka sakamuna ruÉ—u ya kai Yusuf, ka sani cewa wannan maganganun naka barazana ne ga tunaninmu, da kuma zukatanmu, amma kuma biri ya yi kama da mutum, zan iya gasgata ka akan abin da kake faÉ—a, amma bamu labari, kafin ni in sanar da ku wani abu mai mahimmanci da Yakamata in faÉ—a".
Bulama yayi jimm, sannan ya basu labari tiryan-tiryan yadda abubuwa suka wakana, har zuwa lokacin da Abra ta rasu.
Gigicewa Rumai ta yi, yarana suna raye, ɗaya ta mutu? Waye ya yi mini wannan zaluncin, na rayu shekaru Ashirin da huɗu cikin ɗacin rai da ƙunar zuciya, yarana na raye amma suk rayu nesa da ni, ya za ayi ace na haifi yara aka ce mini sun mutu? Meyasa aka mini haka Ya kai Yusuf, ya a kai ka tabbatar da yarana na raye? Ka kaini in gansu a ina suke, ko da yake kace mini ɗaya ta mutu, to ina ɗayar a ina take? Dan Allah kar ka gaya mini abin da ba zai yiwu ba, in saka rai kuma in zo ba yarana ba ne".

Abdallah yayi ajiyar zuciya ya ce "A shekarun baya,  da naje Nigeria, a garin Kano, naje sayayya wani mall, na haɗu da wata yarinya da sai da hantar cikina ta kaɗa saboda mamaki. Tana tsananin kama da shi Yusuf, kuma akwai wasu kamanni da ta ɗauko na ki, hatta wannan ɗigon baƙin na gefen idonki ta na da shi, mamaki da rikicewa ya sanya na kai hannu fuskarta, wanda suke tare da shi ya mareni, ina tunanin mijinta ne a wannan lokacin, ita yarinyar ta tsorata, har ta suma, ya ɗauketa suka bar wurin. Still a watannin da suka shuɗe, na haɗu da ita a nan Dubai, amma ita da wani daban n kuma ganinta, amma ban yi mata Magana ba saboda wanda suke tare ya mini kwarjini da yawa, kuma ina tsoron abin da ya faru wacan lokacin ya kuma faruwa, idan kuwa haka ne ina kyautata zaton ko da duk mutum ɗaya na gani, ko kuma su biyun ne Amma sanin gaibu sai Allah".

Fashewa da kuka Ummi tayi, tana fitar da tulin damuwar da ke mamaye a ranta, saboda tun bayan haihuwar yaran nan ba ta kuma samun wani rabon ba, kuma gashi Allah ya jarabce ta da son yara, yo ta ina ma zata samu rabo, miji ma wata ƙasar ita ma tana wata ƙasar daban, sai su shafe watanni huɗu wani bai sa wani a idonsa ba.
Cikin kuka ta ce "Abdallah, a gaggauta neman mini visa Nigeria, muje ya nuna mini 'ya'yana, ni da da yadda za ayi, a yanzun nan zamu tafi, amma ni haryanzu na kasa gazgata hakan"

Bulama ya rungumeta a jikinsa yana rarrashinta, tare da bata tabbacin cewa zasu tafi Nigeria tare, dan tabattar da abin da yake faÉ—a mata.

Afra kuwa ta ɗan fara tausayin Adnan, saboda yadda aka ce yana aman jini, gaba ɗaya baya hayyacinsa, amma sam ita Adnan bai mata ba, kallon mugu take masa, saboda yanayinsa yadda yake wasu abubuwan da zafi, Salman ya fishi kirki da bin komai a hankali, dan haka ita ba ta ga ta yadda zata zaɓi Adnan ba, ga salihi mai lallaɓata.

Adnan kuwa yana kwance a gadon asibiti, an ɗaura masa drip, sai dai yadda yake numfashi kawai ya isa ya tabbatar maka da cewar, yana jin jiki, daga nesa ana iya ganin yadda ƙirjinsa ke fat-fat da sauri da sauri.

Abbi kam mamaki ya cigaba da yi, dama Adnan ya san mahaifin Abra, amma yayi shiru da bakinsa bai faÉ—a ba? To yaya ma aka yi ya tabattar da Bulama ne mahaifinsu, ko dai zafin ciwo me ya sanya shi faÉ—ar hakan, suka biye masa suka kira bawan Allah.

Hajiya Saudat ta rasa in da zata saka kanta, abin duniya ya isheta, ga Meenal a kwance ba lafiya tun da aka yi aikin nan, ta ƙi lafiya, an cire mahaifa ɗungurun gum, ba ta taɓa sanin Meenal na bin maza ba, ga uwa ba, abin da Bulama ke shirin yi, idan bar tone tone yayi yawa, tabbas akwai Matsala, dan daga ita har shi suna cikin tsaka mai wuya, nan ta koma tunanin yadda zata shawo kan lamarin.
Wayarta ta ɗauko, ta kira layin Bulama, ba ta damu da kuɗin da za a ja ba a waya, saboda kiran lambar ƙasar waje.
Har ta fidda ran zai É—aga, ya É—aga wayar.
"Hello, kana ina ne?"
Haushi ne ya kama Bulama ya ce "Meye hak sai kace wani É—anki? Ya ma dace ki kirani a halin yanzu? Kin fi kowa sanin ina na tafi, ina tare da Rumaisa, kuma sai ki kirani a waya?"
"Dan me ba zan kirak a waya ba, in ruwana da wata Rumaisa? Ka tafi ka bar ni da yarinya da larura, ko ka kira kaji ya jikin nata"
"Saudat, abin da ya samu Meenal, ke ta shafa da ke da ita, ni ban yiwa Meenal tarbiyyar taje ta bi maza a waje ba, har ta zubar da ciki wanda ya kusa ajalinta ba, dan haka ki gaggauta rabata da gidana kan in dawo, i disowned her as my child, taje ta nemi wani uban".
"Wallahi ƙarya kake yi, Meenal jininka ce, 'ya ɗaya tilo da Allah ya baka, dan haka dole muyi haƙuri da ain daya sameta mu riƙeta".
"Dole kiyi haƙuri dai, amm banda ni ku san yadda zaku yi ke da ita" ya katse wayarsa.
Jifa tayi da wayar tare da taune lips ɗinta na ƙasa 'Anya zancen nan bai tabatta ba na cewar yaran nan suna raye ba, tun da har ya iya nuna halin ko in kula ga 'yar da ya ƙallafa ransa a kanta kasancewar ita kaɗaice ba? To yaya aka yi yaran suka rayu, bayan tun a Asibiti aka ce ba su zo da rai ba? Wane al'amari ne haka mai ban mamaki? Anya ba ƙarya bace da rainin hankali kawai? To amma hotunan da aka aiko masa fa kika ƙona' wata zuciyar ta tambayeta. Tabbs yarinyar jikin wannan hoton duk in da ta fito tana da alaƙa da Bulama. To ko dai matan banza ya fara bi? Aka haifa masa ita? Haka ta dinga tunani barkatai, ba tare da ta samo amsoshin tambayoyin ta ba, sai dai ta san tasowar wannan lamari barazana ne a gareta da Bualaman kansa, mussaman a kan sirrin da suka yi shekaru suna binnewa.

Abba ne da Abbi tsaye a kan Adnan, da aka samu ya É—an farfaÉ—o daga fita hayyacin da yayi, lokaci É—aya duk ya yi rama, yayi zuru-zuru, Mami da Hajiya Mama kuwa suna reception, suna wa Adnan Adduar samun lafiya, saboda ya sha wahala.

Abbi ya numfasa ya ce "Yanzu muna jiaran dawowar wannan mutumin, sannan shi Adnan ya ƙarasa warkewa, mu ji yaya aka yi suka zama 'ya'yan mutumin?".

Abba ya ce "Ba zamu jira sai ya warke ba, dole ai wadda za ayi idan mutumin ya dawo gari, ko mu muje, ko shi ya zo ya same mu".

Abbi ya gyara tsayuwarsa, yana kallon Adnan, a lokacin da Adnan ya gyara kwanciyarsa, yana bin sun Abbi da ido.

Abbi ya ce "sannu Adnan, Allah ya baka lafiya, in dai a ka Afra ne, ka kwantar da hankalinka, ni zan rarrasheta, za a aura maka ita insha Allah, dan ita ya dace ta maye maka gurbin 'yar uwatta".

Abba ya ce "In ji wa? Ai ida har ina raye Adnan ba zai auri Yarinyar nan ba, Salman shi ya dace ya auri Afra".

Abbi ya ce "Me yasa zaka ce haka?".

"Wa zai bawa Mutumin banza 'ya, ai shi ya san mai nake nufi"

Adnan ya haɗa hannayensa biyu, alamar ban haƙuri, yana girgiza kansa, hawaye na fita daga idonsa.
Abbi ya ce " Bai kamata ka faÉ—i haka a gabansa ba, bayan ga halin da yake ciki".
Chapter 127 · 0% Book details