← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 145

Sashe 25

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Khairy da Jannat Kallonta sukai, this is the first time that Abra spoke a lot in the class.
Khairy ta buÉ—e baki tace.
"Wow! So interesting, gsky Abra ki gode Allah, I have never seen someone as knowledgeable as you"
Jannat ta taɓe baki tace "Amma karatun na yawa, data rage dai"
Khairy tace "Ta ya ya karatu zai yawa Jannat Yusuf?" Jannat ta watsa hannunta tare da Miƙewa tsaye tace.
"It's just a suggestion"
"Oh, i see" cewar Khairy.

Da ga nan Jannat office É—in staff É—in makarantar ta yi, domin ya ce ta zo yana son ganinta idan har tana son passed all her exams, a hanya ta tsaya ta fesa turare a jikinta.

Abra Idanunta a ƙasa suna zaune Salman ya shigo hannunsa riƙe da takeaway da rubber ice cream, idanunsa akan Abra.
"Salman, you are not seen unless you bring Abra something to break" Khairy tayi Mgnar tana dry, Murmushi kawai yyi yana girgiza kansa can kuma yace.
"To É—an matsa, aku Sarkin surutu" Khairy tace "Oh, haka zaka ce ko?" Bai ce komai ba ya zauna kusa da Abra dake Murmushi tana buÉ—e littafin English na gabanta yace.
"Yaya ya zaki karatu ne?"
Ta buÉ—e masa Idanunta tace "like how?"

Ya kalleta ya kalli littafan gabanta yace "kamar dai haka" lumshe idanunta kawai tayi, yabi zara zara eyes lashes É—in ta da kallo kafin yace.
"Me za kici? Meat pie? Cake? Dunot? Shawarma? Pizza? Hamburger? Me za kici Yaya tell me"
Kamar zatai kuka tace
"Please Faris surutun yana yawa" shima ya marairaice mata yace "kefa kawai na kewa, yanzu me za kici"
Tace "I'm full, ina karatu yanzu..."
Kafin ta Ƙarasa maganar taji hannunsa cikin bakinta ya sanya mata cake a baki, da sauri ta amshi cake ɗin tana zaro idanunta waje, bayan ta ciye ta kallesa muryarta na harɗe wa tace.
"Faris"
"Angel" Salman ya faɗa yana kashe mata Idanunta ɗaya tace "but kasan ban fiya son zaƙi ba ko?" Yace "i knw Yaya, ni wlh karatun nan yana yawa, nifa ina mace ba ruwana da wani karatu tunda aure zan"
Shiru tayi masa, a hankali yace "nifa ba zan fita ba Yaya, sai kin faÉ—a min abinda za kici" ta girgiza kai tace.
"Bani da appetite, kuma ban san ɓata hannu"

Kallonta ya yi sai kuma ya girgiza kansa, a hankali ya dinga bata cake É—in tana ci, yana bata exotic tana sha har taci sosai.
Kallonsa tayi sai kuma ta saki murmushi tace.
"Thank you Ɗan ƙanina"
"Uhm" yace kawai kafin ya miƙe har yaje waje sai kuma ya tsaya da ƙarfi yace.
"Angel" da sauri ta É—ago kanta tace "What happening Salman?" Gira ya É—aga mata tare da kashe mata idanu yayi waje da gudu.
Ta girgiza kai tace
"Allah ya shirya"

A sati na gaba su Abra aka fara exam, Salman sam bai damu da karatu ba, ita kam ta dage tana fata ace wannan karan Mami ta sanya mata albarka idan ta ɗauki 1st position, Salman yana sane yaƙi mai da hankali sbd ya faɗi wanwar ta inda position ɗin Abra zai fi nasa.
Yau ma a gajiye Abra suka dawo daga Islamiyya ko kayanta bata cire ba ta faÉ—a saman bed sai bacci. Har aka kira magrib tana bacci.
Salman na zaune da Abbi wanda ya dawo gari a ranar cikin kulawa Abbi yace "Salman ina yayar taka?" Salman ya ajjiye handle É—in game É—in da yake yace "Tun da muka dawo islamiyya bata fito ba"
Abbi ya yi shiru sai kuma yace "is she alright?" Salman yace "not sure Abbi" yace "ok jeka kirata, zamu je shopping daga nan Granny na son ganinku sai mita take fa"
Salman ya miƙe daga shi sai farar vest wacce ta kama cikinsa wanda ya buɗe alamun zama saurayi, sai 3Qauter a jikinsa kai tsaye ya nufi bedroom ɗin Abra.
Abra na tsaye gaban mirror ta fito daga wanka, tana ƙoƙarin saka lace rapped bra a jikinta taji Salman na faɗin.
"Yaya.. Yaya..Yaya"
Gaba ɗaya ruɗewa tayi gashi ƙofar a buɗe take bata saka mata key ba,
Ruɗewar da tayi yasa bra ɗin kwacewa daga hannunta ta faɗi, daidai nan kuma Salman ya shigo yana faɗin "Angel..." Bai ƙarasa faɗa ba yaji ta fasa wata ƙara tace "No!! Salman get out I'm naked.......

*We are still in free pages.... A koda yaushe zamu iya tsayawa... Ka hanzarta biyan kuɗin ka domin a dama dakai.. littafin daban yake.. kada ku manta marubuta uku ne suke rubuta muku wannan Labarin Nimcyluv🤘🏼 Ayushercool🍷Zee kumurya💘*
[9/30, 8:55 PM] Abk: *DARE DA DUHU*

_Brigh pens✍️_
Nimcyluv
Ayushercool
Zee Kumurya

                               P11

Domin samun complete litattafanmu, ku yi following É—in wannan accounts É—in a Arewabooks

https://arewabooks.com/chapter?id=6316f4af434cfeb9e7fe2949

https://arewabooks.com/u/nimcyluv
https://arewabooks.com/book?id=

Elegant online writers

LITTAFIN DARE DA DUHU, ₦300 NE KACAL, ZA KU TURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0116886423 Sulaiman Na'ima s union Bank.
KU TUNTUƁI WANNAN LAMBAR DAN TURA KATIN WAYA NA NAIRA 500 TA WANNAN 09047871750
DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU AKAN WANNAN LAMBAR 07063065780\09047871750
MUNGODE.

Cak ya tsaya kamar wanda aka dasa shi a gurin cikin rashin sanin abun yi, shi kansa ya rud'e balle kuma ita, cikin rawar murya ya ce. "I'm
.so.. sorry Yaya."

Juya masa baya ta yi da sauri tare da ƙanƙame jikinta guri guda, kamar za ta yi kuka ta ce. "Salman! I said get out please!"

Bai ce komai ba ya juya ya fice daga É—akin cikin wani irin yanayi na sanyin jiki.

"Ya dai? Ko wani abu ne ya same ta?" Abbi dake duban sa bayan ya dawo ya zauna, ya faÉ—i haka.

Daidaita nutsuwarsa ya yi ya ce. "Nothing Abbi, tana wanka ne."

GyaÉ—a kai Khamal ya yi ya cigaba da latsa wayarsa.

Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi jin ƙarar buɗe ƙofa tare da fitar shi, kamar mai tsoron wani abu ta juyo a hankali, saurin ɗaukar brar ta yi ta saka ta ƙarasa shiryawa, cikin wani hadadden less wanda aka yi masa ɗinkin tea bubu. Ta yi kyau sosai duk da ba wata kwalliya ta yi ba, bayan ta feshe jikinta da tsadaddun turaren da Abbinta yake siyo mata, ta ɗauki medium vail ta yafa sannan ta fice, bayan ta ɗauki Small handbag ɗinta.

Tunda ta fito Na'ima ta kafe ta da ido wanda hakan yasa ta jin kamar za ta faɗi, Salman ma jin ƙamshinta ya ɗago kansa a hankali yana kallon ta, a ransa yana yaba tsananin kyawun Yaya tasa. Ita kuwa Na'ima baƙin ciki ne ya cika mata zuciya, na kyawun da Abra take shi da kuma takaicin yanda Khamal yake siya mata suturu masu kyau da tsada, gami da duk wani abu na kwalliyar ƴa mace. Duk abun da ya gani indai na gayu ne sai ya siyo mata, idan ta yi magana ya ce, ai ita ƴa mace ƴar kwalliya ce, idan bai siya mata ba wa zai siya mata? Ita ma babu yanda ta iya haka take siya matan saboda gudun kar ya gane har yanzu ba ƙaunar Yarinyar take yi ba.

"Kai Masha Allahu laƙuwwata illabillah, ƴata tafi kowa a kyau da iya ɗaukar kwalliya, gaskiya sai ɗan Sarki ko ɗan gwamna zan bawa, dan Ƴata mai tsada ce."

Na'ima ta faÉ—i haka cikin murmushin da bai kai zuci ba.

Sai a lokacin Khamal ya É—ago ya dubi Abra, cikin murmushi ya ce. "To Allah ya kawo mana na gari." Lumshe ido kawai Salman ya yi ya buÉ—e bai ce komai ba.

"Sannu da hutawa Mami."

"Yawwa Daughter, kun dawo daga islamiyya ina sama ina shiryawa, sai yanzu na sakko, ya makarantar?"

"Alhamdulillah."

Ta faÉ—a cikin siririyar muryarta.

Mayar da duban ta, ta yi ga Abbinta ta yi masa sannu da gida, ya amsa cikin fara'a sannan ya miƙe ya ce su huce. Abra da ba ta inda za su je ba ta yiwa Mami sallama ta fara fita, ita wannan shiryawar da ta yi da niyyar ta tambayi Abbinta za ta gidansu wata friend ɗinta, dan su yi totorial akan last paper ɗinsu da za su yi ranar Monday ta literature. Amma kasancewar ba ta saba musu ba sai ta hak'ura ta fasa zuwan, tunda Abbi ya ce za su fita.

"Kai kuma lafiya kake ta bin mutane da ido?"

Cewar Na'ima tana duban Salman.

"Lafiya Mami, bari mu wuce sai mun dawo." Ya yi maganar tare da miƙewa ya fice.

Na'ima ta ce. "To Allah ya kiyaye, sai kun dawo É—in."

"Yaya! Angel."

Salman ya faɗa bayan ya fito cikin ƙoƙarin cire moment ɗin ɗazu daga cikin zuciyarsa, na ganin ta nicked da ya yi.

Abra dake tsaye ta ɓata fuska ba ta ce komai ba.

Ya ƙaraso ya tsaya a gabanta ya ce, "Kin yi kyau sosai." Tana ware manyan idanunta a kansa ta ce. "Ko? Kai da ba ka gajiya da faɗar haka as always." Ya ce. "Ai hakan ne shi yasa, kullum fa ƙara kyau kike yi da wani irin fresh kamar sabuwar amarya." Ta ce. "Kai kuma fa? ai kai ma haka Handsome ɗin Mami." Murmurshi ya yi cikin jin daɗin yabon shi da ta yi. A haka khamal ya fito ya same su suna hira gwanin sha'awa.

Wani haɗɗaɗen gurin sayar da snaks da ice_cream dake cikin Nasarawa Khamal ya kai su, ya yi musu order na abin da kowa yake so. A hankali Abra take shan Vanilla ice cream ɗin dake gabanta, duk da ba wannan ne first time da suka saba zuwa irin guraren nan ba, amma duk a takure take jin kanta. Sai gyaggyara mayafinta take ta kasa zama guri ɗaya. Salman dake gefenta yana lura da yanayin da take ciki ya ce. "Ko in baki a baki ne, na ga kamar ƙiwar sha kike yi?" A hankali ya yi maganar yanda Khamal ba zai ji ba.

Tura masa baki kawai ta yi ba ta ce komai ba. Murmurshi ya yi ya cigaba da cin meatpie ɗinsa, lokaci ɗaya murmushin ya ɗauke daga fuskarsa sakamakon four eyes da suka yi da wani matashin Saurayi da yake pacing ɗinsu, wanda ya ƙurawa Abra ido kamar zai lashe ta.
Chapter 25 · 0% Book details