← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 138 OF 145

Sashe 138

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Dining ɗin ya bi Abra ya zauna, yana satar kallonta da yadda ta ƙara kyau da ƙiba, wata irin kewarta na kuma ratsa shi, wannan dogon gashin da ya zube lokacin da tayi rashin lafiya, duk ya dawo. Yayi mata do tun daga gaban goshinta gashin yake, baƙi ƙirin ya kwanta a bayanta.
Tana ankare da yadda ya zuba mata ido kamar bai taɓa ganin mace ba, ta fara karyawa tana kaɗa ƙafarta, kamar ba san da wanzuwar sa a wurin ba.
Shima karyawar yake yi, amma hankalinsa gaba ɗaya yana kanta, can ba tare da yayi tsammani ba yaji ta ce "Ammm nace ba, ina ka kai mini 'ya ta ne? Ina buƙatar ka bani abata".
" 'yarki tana nan lafiya"
"Ba lafiyarta na tambaya ba, ina ka kai mini ita, ina buƙatar a dawo mini da ita".
"Tana wurin... Bai ƙarasa ba, suka ji ana kaɗa ƙararrawar falo. Adnan ne ya miƙe ya tafi ya buɗe.
Direban gidansu ne, ya kawo Abinci daga gida, wanda Hajiya Mama ta aiko musu da shi.
Adnan ya karɓa ya maida ƙofar ya rufe ya dawo dining.
"Angel kinga Mama ta aiko da Abinci, bari in ajiye a kitchen maci da rana ko?" Ba ta ko É—aga kai ta kalleshi ba,balle ya sa ran zata amsa masa. Ya tafi kai fulasan kitchen kar ya dawo ta bar falon.
Akwatunan dake É—akinsa ya kwaso, ya kai É—akin Abra, Akwatuna duga shida ya zube a gaban Abra, da murnarsa ya ce "Angel, ga kaya na saya muku ke da little, gashi nan naki akwatuna huÉ—u nata kuma biyu, dama sauran kayan lefenki na wancan gidan ma suna gidanmu, suma zan É—auko miki su".
Abra ta kalli Akwatunan ta ce "Madalla, little ta gode, ni kuma ka bar kayanka, babana na riƙo bai bar ni tsirara ba"

"Abra Wannan ai wani abu ne na daban, wannan hakkina ne nayi muku".

"Ka yiwa 'yar ka dai, ai ni ban cancanci ka mini ba, ni da nake jinin Bulama, ai bai kamata ka mini abin da zaka kyautata mini ba, tunda auren na fansa ne" Dafe kansa Adnan ya yi ya ce "Abra why, na gaya miki nayi nadama, mai yasa kika canza hali ne?".

"Koma menene ai kai ka koya mini ba wani ba, a waccan rayuwar ka sanar mini zaman bauta zan yi, ka É—au fansa, ban sani ba ko a wannan karon ma fuska biyu kake mini kamar yadda ka saba".

Sunkuyar da kai ya yi, a hankali ya matsa kusa da ita, yana kallon yadda doguwar rigarta ta ɗage santala santalan ƙafafuwanta suka bayyana, ya dubeta tare da ɗora hannunsa a kan cinyarta, ya ce "Believe me please, ba zan sake cutar da ke ba Abra"
Kallonsa tayi ido cikin ido, yadda suka samu kusanci da juna, har tana iya jin saukar numfashin sa a jikinta, ta kalli faffaɗan ƙirjinsa da take missing, ta cigaba da kallonsa zuwa kan lips ɗinsa, da idanunsa da suka yi jawur cike da nadama, ji tayi wani abu na taso mata, tsohuwar soyayyar Adnan na ƙoƙarin taso mata. Dakewa tayi a lokacin da wani sashi na zuciyarta ya gargaɗeta 'Me kike shirin yi ne Abra, kamar baki da zuciya?'.
Haɗe rai tayi ta ce "Ka zo ne dan kayi abin da ka saba, ka biya buƙatar ka sannan ka koreni a wulaƙance, kar warin abin da na fitar ya hautsina maka ciki? Ko kuma fyaɗen kake ƙoƙarin sake yi mini, kamar yadda kayi mini a ranata ta farko da kasancewa da ɗa namiji?"
Wata irin ajiyar zuciya Adnan ya sauke, ya dubi Abra yana tuna abubuwan da suka shuÉ—e, da wasu ya manta ma da ya aikata hakan.
"Ba zan gaza da cigaba da baki haƙuri ba Abra, na san ni mai laifi ne a wurinki, dan Allah ina mai kuma sake baki haƙuri".
"Can You excuse me please?" Abra ta faɗa in a serious tone, tana sake nuna masa bata buƙatarsa a in da take. Jiki babu ƙwari haka Adnan ya tashi ya bar mata ɗakin.
Kwanaki biyu da tarewar Abra, Hajiya Mama da Abba suka zo gidan da daddare, tare da little kasancewar dama tana wurin Hajiya Mama.
Abra tayi murna da zuwansu, tayi musu kyakywar karɓa cike da farinciki. Gefe guda ga murnar ganin 'yarta da tayi.
Abba ya yi musu nasiha me shiga jiki, da mahimmancin yafiya da haƙuri a zamantakewar aure, da kuma sake kashedi da jan kunne ga Adnan, a kan mahimmanci amana da riƙon iyali da adalci. Abra nasihar Abba ta ratsata, amma ba ta iya ji a ranta ta yafewa Adnan muzgunawar da yayi mata ba.
Da zasu tafi ta so Mama ta bar mata little, amma Mama ta ce ba yanzu ba, sai an kwan biyu tukuna.

Labari ya ishe sauran 'yan uwan Bulama, a kan iftila'in da ya afka masa, amma babu mutum guda da ya iya jajanta halin da yake ciki, ciki kuwa har da 'yan uwan mahaifinsa, saboda yadda ya watsar da su, tun bayan aurensa da Saudat, da yadda ya daina zuwa inda suke, shi kuma babu wanda ya san in da yake zaune a cikinsu, dan haka babu wanda yabi ta kan a tallafa masa saboda yanayin da yake ciki.
Hajiya Saudat kuwa Nijar ta gudi can wurin wata ƙawarta ita da Meenal, sai dai tun bayan aikin da aka yiwa Meenal, aka cire mata mahaifa, ba ta samu lafiya ba, take ta rashin lafiya, duk ta ƙare ta rame, saboda kullum cikin ciwon ciki da zubar jini take. 'yan sanda kuma tuni suka baza komarsu dan ganin an daƙumo Hajiya Saudat bisa ga laifin da ta aikata.

Adnan yana ji yana gani, yana zaune gida ɗaya da Abra, amma tafi ƙarfinsa, saboda a wannan karon zama ne yake son su yi shi na soyayya wanda zai mantar da ita waccan rayuwar da suka yi, sam baya son takura mata gaba ɗaya.
Abra ko aikin gida sai ta ga dama take yi, Adnan ne yake komai, sai dai tana yin girki ta ajiye masa, saboda ko a lokacin da suka yi wancan zaman bai barta da yunwa ba. Shiga sai wadda ta ga dama take yi, wani lokacin haka zai kalleta ya haƙura ya bar mata falon ya koma sashinsa. Maganar arziƙi bata haɗasu saboda yana gudun samun matsala.

Gefe guda kuwa Abra damuwa ta fara yi mata yawa a kan halin da mahaifinsu ke ciki, gaba ɗaya media ta ɗauka kasancewar sa shahararren likita ne, har ga Allah duk da tarin laifukan da Mahaifin nasu ya aikata, tana jinsa a ranta, kuma ta fara tunanin tunda tana garin Kaduna, akwai buƙatar ta je ta ganshi, dan tuni an fara gabatar da shari'arsa, sai dai ana nema ayi defeating ɗin lawyoyinsa, saboda ƙwararrun lawyoyi ne suke tsagin gwamnati, kuma a yanzu babu kuɗin da Bulaman zai iya ɗaukar wanda zasu tsaya masa.

Kwanci tashi asarar rai, a daren yau Abra taci karo da message É—in Salman, yake sanar mata da cewa ta tambayi izinin Adnan, zasu je Dubai tare da ita suje wurin Ummi, ita ta dawo gida, su kuma su wuce China shi a Afra.
Farincikin da Abra ta shiga ba zai misalitu ba, dan haƙiƙa ɗan zaman da suka yi da mahaifiyarsu bai ishe su ba, duk da ba wani sabo da shaƙuwa a tsakanin su.
Shirinta ta fara yi, ba tare da ta sanar da Adnan batun tafiyarsu ba, sai dai ta lura kamar ba shi da lafiya, rashin lafiyarsa ya É—an tayar masa, amma bai gayamata ba, ita ma kuma ba ta nemi ta sani ba, ta shirya kayanta tsaf tana jiran zuwan su Faris.

Sam Adnan bai san da zuwan da su Salman ba, dan bata gaya masa ba sai ganinsu kawai ya yi a gidan, Abra ta rasa in da zata saka kanta dan murna, Afra ta ƙara ƙiba Salman ma haka, kana kallonsu ka san farinciki da kwanciyar hankali sun sami kyakykyawan matsuguni a tare da su.
Adnan ya dake ya daure, ya ɗan sake suka gaisa da Salman. Gefe guda kuma yai ta tsokanar Afra 'Su 'yar fara an auri fari, ni kuma Allah ya dawo mini da matata wurin ɗan baƙinta" Afra ta tura baki tana murmushi.
Ɗaki Abra ta janye 'yar uwatta, suka ƙule suna hira, Afra ta ce "Sister, wai haryanzu jikin baban little bai warke bane, naga sai kuma rama yake yi?".

"Oho masa" Abra ta faÉ—a cikin ko in kula.

"Ba dai kina nufin haryanzu ba kwa jituwa ba?".

"Kinga mu bar wannan maganar, me zamu dafa ne?".

"A'a magama ce me mahimmanci da Yakamata mu tattauna ta"
Abra ta miƙe ta ce "Sai kuma kiyi ai" ta fice ta bar ɗakin, ko da ta dawo falo da Salman da Adnan duk basa nan, dan haka ta mayar da hankali wurin ƙoƙarin ɗora girki. Hankalinta ya yi nisa a kan aikin da take yi, taji ƙamshin turaren sa ya mamaye ilahirin kafofin hancita. A hankali ya tako har in da take ya tsaya yana ƙare mata kallo.
"Chef Yaya, girki in bana ki ba ƙanzo".
Abra tayi dariya ta ce "Allah yasa matarka ta jika" dariya yayi yace "Sarkin daru ba" ya cigaba da tsurawa Abra idanunsa, ta É—ago ta kalleshi ta ce "lafiya wannan kallon fa?".
Chapter 138 · 0% Book details