← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 145

Sashe 26

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wata Uwar harara ya galla masa ya ce. "Yaya tashi ki je Mota ki ƙarasa sha, kafin Abbi ya gama mu wuce." Ya ƙarashe zancen tare da ajiye meatpie ɗin hannunsa, dan ji ya yi gaba-d'aya ya fice masa daga rai.

Da mamaki take duban shi amma ba ta ce komai ba, Khamal da ya ji abun da Salman ya faÉ—a, ya dube shi ya ce. "Me yasa zaka ce ta tashi?"

"Abbi na ga sai kallon ta ake yi a gurin nan, kar ido ya yi mata yawa ta je ta ƙware."

Ya yi maganar da iya gaskiya. Murmurshi Khamal ya yi, cikin ransa yana jinjina al'amarin Salman, yanda yake acting akan Abra sai ka ce shine sama da ita.

"Ki tashi Please." Ya faÉ—a yana narkar da idanunsa a cikin nata.

"Ka fiya takura Faris, mu jira Abbi ya gama mana, sai mu fita gaba-d'aya."

Ɗan ƙaramin tsaki ya ja idanunsa akan Matashin nan da ya kasa ɗauke idonsa daga kan Abra, wani irin kallo yake wurga masa. Har suka bar gurin mutumin nan bai daina kallon Abra ba, Salman kuwa sai cika yake yana batsewa. Sai da Abbi ya yiwa Mami da su Ammi take away sannan suka tafi. Suna hanya aka yi Sallar Magriba, hakan yasa Abbi tsayawa a wani Masallaci suka yi Sallah shi da Salman sannan suka wuce.

"Wai kai lafiyarka kuwa kake ta ɓata rai?"

Abra ta tambayi Salman cikin kulawa, bayan sun fito daga cikin Mota lokacin da suka ƙarasa gidan Ammi."

"Babu komai, Ni ma kawai a haka na ji ni."

"Ka fiya rigima kai dai"

"Na kai ki?"

"Ka ma fi ni, Ni dai bana son ganin ka a haka, Please ka saki ranka ka ji ɗan ƙanina." Ta ƙarashe maganar cike da shagwab'a.

"Sai kin ce mun Yaya gaskiya." Ya yi maganar yana wani shan kunu.

Dariya ta yi ta ce. "Ba zan faÉ—a ba É—in, Sarkin son girma." Ba ta jira amsar shi ba ta wuce cikin gidan. Murmurshi ya yi tare da shafa sumar kansa ya bi bayanta.

Da sallama suka shiga main parlour'n gidan, Ammi tana tsaye a dinning area tana yayyankawa Baffa fruits, Hajiya kuwa na kame akan kujera tana jan carbi mai dubu, da alama ba ta jima da idar da Sallah ba dan sanye take cikin Hijabi, ta ƙara tsufa amma har yanzu bakin nan nata yana nan bai mutu ba.

Cikin fara'a da murnar ganin su Ammi ta amsa musu tare da yi musu sannu da zuwa, Ƴaƴan Shureim guda biyu da suka zo Weekend suka taho da gudu suna faɗin. "Oyoyo Yaya da Ya Salman." Abra ta ajiye ledar hannunta ta rungume su a jikinta cikin murmurshi. Salman ya shafi kansu ya ce. "Oyoyo ƴaƴan gidan Ammi, kodayaushe aka zo gidan Ammi a gan ku."

Granny dake bin su da kallo ta cikin White medicated glass ɗin dake idonta ta ce. "Su masu zumunci kenan ai, ku kuwa uwarku saboda baƙin hali ba ta barin ku zuwa, ita ba ta zo ba ku ba ta bar ku kun zo ba." Ta taɓe baki ta ce. "Ba ruwana ma dai, lazimi nake yi bazan ce uffan ba sai na gama tunda babu kyau ana yi ana surutu."

Salman ya ƙarasa ya zauna a kusa da ita, ya ce. "Ai kin ɓata lazimin tunda kin riga kin yi maganar, sai dai ki sake daga farko."

"Ka ci kanka, ni ba zan biye maka ba, sunan Allah nake ambata bana wani garÉ—i Khamalu ba ko na wata garÉ—iya Nai'ma ba, ato, a sarara mun a bar ni in yi abuna cikin nutsuwa."

Abra ta ƙaraso cikin parlour'n hannunta riƙe da na Fadeela, Fadil kuma ya ɗauko ledar da ta ajiye, zama ta yi a kusa da Granny ta gaishe ta, ɗaga mata hannu ta yi tana ƙara fito da carbinta daga cikin hijabi tana ɗaɗɗaga shi, ita a dole a ga lazimi take yi ba za ta yi magana ba. Murmurshi Abra ta yi ta miƙe ta ƙarasa gurin Ammi ta gaishe ta, Ammi ta rungume ta tare da amsa masa mata. Daga nan ta wuce bedroom ɗin Ammi dan yin Sallah.

Sai wajen goma da wani abu suka bar gidan, kamar kar su tafi saboda yanda ake tarairayar su, da yanda suke cin dariyar Granny, har Baffa ma ya sakko anata hirar da shi tare da Khamal wanda ya shigo daga baya, bayan sun gama gaisawa da mai gadi. Granny sai mitar rashin zuwan su gidan akai_akai take yi, idan Khamal ya ce makaranta ce ta sa ba sa zuwan sai ta ƙanne ido ta ce. "To ni ina ruwana ma da zuwansu da rashinsa, tunda ba wata tsiyar suke mini ba in sun zo? Sai dai ma su sace mun ɗan tsirena da kilishina, da ɗan Albarkana yake siyo mini ban sani ba." Da za su tafi ta ce kar su tafi su zauna su kwana, Khamal ya ce gobe Monday akwai school sai dai in an yi hutu za su zo su yi hutunsu a nan insha Allahu. Sai ta tsuke fuska ta ce, "Allah ya raka taki gona."

Abra tana son su je gidansu Ammi sosai, saboda nishaɗi da farincikin da take tsintar kanta a ciki, gashi ai ta nan_nan da su ana nuna musu ƙauna da kulawa.

Washegari da sassafe Khamal ya wuce Abuja gurin aiki.

G.Y BULAMA HOSPITAL AND MATERNITY.

A hankali take tafiya cikin sanyin jiki, tana sanye cikin fararen uniform na Nurses. Ƙofar wani office ta tura a hankali ta shiga bakinta ɗauke da sallama.

Wani baƙin likita dake zaune a mazauninsa shi kaɗai a cikin office ɗin, yana operating system ya amsa mata Sallamar ba tare da ya ɗago ba. Ƙaraso ta yi ta zauna a ɗaya daga cikin kujerun dake gaban table ɗin.

"Barka da safiya Doctor."

Sai a lokacin ya É—ago tare da yin murmurshi ya ce. "Kin tashi lafiya Jamila? Ya su Mama?"

"Lafiya ƙalau, na zo ai Sister Basira ta ce mun ka zo kana nema na."

Ya ce, "Eh, me yasa yau baki zo akan lokaci ba?"

"Abun hawa ne ban samu da wuri ba."

"Da kin kira ni ai, da na biyo na É—auke ki."

Yaƙe kawai ta yi ba ta ce komai ba, ɗan ƙura mata ido ya yi na sakanni, cikin kulawa ya ce. "Kamar wani abun yana damun ki Jamila." Numfashi ta sauke ta ce. "Babu komai Doctor." Ya ce. "Ban yarda ba, ga damuwa nan ƙarara a fuskarki."

Cikin yanayin damuwa ta ce. "Akwai abun da yake damu na, amma bazan iya faÉ—ar shi ba."

"Saboda me? Please Jamila tell me, har kin saka hankalina ya fara tashi."

"Ba fa wani abu ne, kawai dai ina tsoron yin maganar ne."

"Oh My God! Tsoron me? Ni ne fa? You are free to tell me everything da yake ranki, ko baki yarda da ni ba ne?"

Ɗan jim ta yi kamar mai nazari sannan ta ce. "Yardar da na yi da kai ne yasa zan faɗa maka abun da yake raina, wani abu ne ya daɗe yana damu na, amma na rasa da wa zan yi sharing ɗinsa, Doctor! Abun da yake faruwa a cikin asibitin nan ya yi yawa, zaluncin ya yi yawa, Matar nan da Doctor Bulama ya hana ka, ka duba ta jiya mai naƙudar nan da ta matuƙar galabaita akan ba su biya kuɗin gado ba ta rasu, bayan ƴan'uwanta kuma sun yi fafutuka sun kawo kuɗin, wallahi jiya da ita na kwana a cikin raina, lokacin da ta zube a cikin reception ɗin nan tana mu taimaka mata kawai nake tunawa, ga ɗa ya kawo kai zai fito amma ya hana mu, mu taimake ta." Ta ƙarashe maganar kamar za ta yi kuka.

Doctor Lukman ya sauke numfashi ya ce. "In dai Doctor Bulama ne abun da ya fi haka ma zaki ga ya yi, ke baƙuwa ce a asibitin nan shi yasa abun da yake damun ki, amma mu mun riga mun saba da irin waɗannan abubuwan."

"Gaskiya idan aka cigaba a haka ba zan iya zaman asibitin nan ba Doctor, dan watarana sai zuciyata ta buga, a ce mutum babu abun da ya sani yake bawa muhimmanci a rayuwarsa sai kuɗi? Kuɗi abun banza da zaka mutu ka bar su, a yanda aka san likitoci masu tausayi da jan patients ɗinsu a jiki gami da kwantar musu da hankali, amma shi ko kaɗan bai san hakan ba. Abun da yake bani mamaki kuma yanda har yanzu asibitin nasa yake ƙara haɓaka, mutane suke ta yabon sa suna ƙwararrun likitoci ne a ciki waɗanda suka san aikinsu."

Murmurshi Doctor Lukman ya yi ya ce. "Ai komai da iyawa ake yi Jamila, ma'aikatan cikin asibitin nan kawai suka san halin da ake ciki, amma sauran mutane gani suke yi ana yin iyakar bakin ƙoƙari dan ganin an kula da mutum da yi masa abun da ya dace. Kuma kar ki manta, shi fa Doctor Bulama indai zaka cika masa ƴaƴan banki to zaka ga aiki yanda ya kamata, zai kula da kai tamkar ɗan cikinsa."

"Kai amma abubuwan nasa sun yi yawa, ya kiyayi ƙarshen sa, dan ba zai masa kyau ba, matuƙar bai tuba ya daina abun da yake yi ba."

"Ke dai kawai Allah yasa mu dace, amma ana abu a ƙasar nan, gashi shuwagabanninmu babu ruwansu, tunda ba su ko Ƴaƴansu ake yiwa ba, su in dai zaka ba su Haraji mai tsoka to duk ma abun da zaka yi ka je ka yi."

"Akwai Allah."

Jamila ta faÉ—a cikin rauni da damuwa.

Sha biyu da Æ´an mintuna na rasa su Abra suka dawo gida, yau sun yi final exam gaba-d'ayansu.
Chapter 26 · 0% Book details