← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 145

Sashe 38

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ok zan turo ta yanzu, kada ki damu kawai ki Ajjiye min aini nace ina so kuma wannan haÉ—in ya yi" jim tayi sai kuma tace "Ni bani da damuwa, kuma nasan Man zai amince so kada ki damu kici gaba da tsara komai" shiru ta sakeyi alamar tana sauraran mai maganar daga cikin wayar tace "Shi ke nan, ki É—an jira yanzu ne in sha Allah" tana faÉ—in hakan tayi hanging up na kiran Idanunta still akan Abra tace.

"Daughter"
Ba Abra ba hatta Salman sai da ya ɗaga idanunsa ya kalli Mami, abin yazo musu unexpected ya zama wani extraordinary a gare su, ko sunan Abra da wahala aji Mami ta faɗa amma yau ita take kiran Abra da Daughter? Tsananin murna yasa Abra har wani hawaye Idanunta ya tara muryarta na rawa tace "Na...n... na'am Mami" Mami tai Murmushi ta kama Hannun Abra tace "Be patient my dear, zan aikeki gidan Hajja Amina yanzu kinji" Abra ta ɗaga kai da sauri tace "Ok Mami bari na shirya" da sauri Salman ya miƙe tsaye.

"Mami aike kuma? Yaya zaki aika bayan Abbi yace kada ta dinga fita, kuma ba gani ba ki faɗa min aiken yanzu naje na amsu maki" Mami tace "ai na ganka ko ka taɓa ji ance ni makauniya ce, bana kula Abra ace bana sonta idan na nemi kusanci da ita kuma a fara wani zance, kada ka sake ina magana kana saka min baki Salman it will be the last time da zakai min haka" Salman ya buɗe baki zai magana Abra ta girgiza masa kai tace "No Faris,stop arguing with your mother. Ka bari yanzu zanje na dawo" idan ran Salman ya yi dubu to ya ɓaci idanuna tuni ya yi jajur sbd saɓar abinda yake ci masa zuciya, a fusace kuma ya nufi waje zai fita ganin haka yasa Mami faɗin "kada ka kuskura kabar gidan nan, tunda ni Matsayin Shasha ka ɗauke ni" juyawa yayi daga inda yake zuwa bedroom ɗin sa, ganin hakan yasa Mami kallon Abra tace "Kaya zaki amsu min wajan Hajja Amina, kada ki sake ki dawo ba kayan saura ki tsaya a hanya"

"Yanzu zan dawo, bari na ɗakko mayafina driver ya kaini" "A'a ba wani driver, ka kuɗi zan baki ki hau napep ok?" Ta ɗaga kanta 1k ta miƙa kuɗin napep tana bata ta nufi dining room. Abra kuma ta juya zuwa bedroom ɗin ta. Tana tsaye gaban mirror zata ɗauki turare ta fesa a jikinta ya yi saurin riƙe hannunta mai ɗauke da turaren, kallonsa tayi sai da gabanta ya faɗi ganin irin kallon da yake binta da shi. Wardrobe ɗinta ya buɗe ya ɗauki wani ƙaton hijab har ƙasa bakinta na rawa tace "Ni ba zan saka hijab ba gsky" idanuna cikin nata ya ce "Ni kuma nace sai kin saka" murguɗa masa baki tayi tace "Ni ba zan saka ba, kana wani abu kamar kaine yanae, shekara uku na baka yaro sai son girma da manyan can Masifa" Salman na warware hijab ɗin ya ce " say whatever you want to say, but kada ki sake ce min yaro age is just a number ba'a goshi ake rubuta su ba"

"Idan na kuma faɗa me zakai min? Kwana biyun nan naga ka fara raina ki ko? Sbd kana kallonka ƙato babu mai cewa nice babba shine kake son faɗa min abinda kayi niyya" bakinta dake ta motsawa yana zuba masifa yake bi da kallo sai da ta kama faɗan ta ce "kuma sai ka faɗa min abinda zakai min idan na sake faɗa" girgiza kai kawai ya yi ba zato taji gaba ɗaya ya ɗaga ta cak ya dire ta a gabansa tare da kama ƙugunta ya saka mata mayafin. Yana gamawa kamar sai saketa sai ya ɗora bakinsa a saitin kunnanta ta cikin hijab ɗin ya ce.

"Yaa Subuhanallah!
جعلنا الله معًا إلى الأبد"
Wato “Ubangiji ya Sanya mu kasance tare har abada” Abra hankalinta baya jikinta murna take yau Mami ta aiketa dan haka bata tsaya tantance maganganun na Salman ba tayi waje sanye da ƙaton hijab.
Abra na barin gidan motocin Major Khamal Khamis suna shigowa, wani soja ya buɗe masa ƙofa ya Fito dake gaba ma'aikatan gidan sojoji ne.

Cikin nutsuwa Abbi ke tafiya zuwa gidan yana shiga Mami ta miƙe tsaye, da ɗan sassarfa ta nufi wajan Abbi tare da rungomesa tana faɗin "Wlcm Back Yallaɓai na" Murmushi ya yi yace "Thank you Madam" Jin shiru yasa yace "Ina Daughter,ina Salman?" Tace "Salman na nan baya jin daɗi, Abra na aiketa tun ɗazo naji shiru amma nasan tana hanya"

Shiru ya yi yana son fahimtar zan can nata sai kuma ya ce "Ok, lemme take a shower" bayansu tafi har zuwa sashinsa ta haÉ—a masa ruwan wanka. Bayan ya yi wanka yana cikin cin Abinci yaga ta zabga tagumi yace "Meke faruwa Madam?" Ta girgiza kai ya kama hannunta ya ce "please" ajjiyar zuciya ta sauke ta ce "Ko Abinci yau Abra bata samu yi maka ba, jiya da yau idan na aiketa sai ta shafe wasu lokuta bata dawo ba" Ajjiye spoon É—in hannunsa ya yi cikin damuwa ya ce "ita Abra? To ina take tsayawa?"

"I have no idea. Bari na kira Hajja Amina" wayarta ta ɗauka ta kira Hajja Amina tana ɗauka tace "Hajja Amina me Abra take har yanzu shiru?" Hajja Amina tai salati da ga cikin wayar kasancewar a Speaker Mami ta saka tace "Wacce Abra kuma ni Amina, yarinyar da ko minti biyar ba tayi ba ta amshi kayan ta fita tace akwai inda zata daga nan gidan" kashe wayar Mami tayi ta ce "To ina yarinyar nan tayi?" Kasa cewa komai Abbi ya yi sai miƙewa kawai da yai tare da nufar sashinsa.

Ana ƙwala kiran Sallar Magrib Abra na shigowa cikin Main Parlour sai da gabanta ya faɗi ganin Abbi tsaye fuskarsa babu walwala wani irin kallo yake binta da shi, musamman da yaga leder shopping a hannunta. Bakinta na rawa tace "Sannu da dawowa Ab..." Tau!!!!! Abbi ya ɗauke Abra da mari wanda ya sanya tayi baya zata faɗi cikin sauri Salman ya tareta ta faɗa jikinsa, Wani marin Abbi ya ƙara saukewa Abra daya sanya ta saki wata gigitacciyar ƙara tare da saka hannu gaba ɗaya ta ƙanƙame Salman. Wani irin kukan Abra ta fashe dashi bakinta sunan Faris yake faɗa akan ya taimaketa daga dokan Abbi.

"Wato har kinyi girman da za'a aikeki ki tsaya yin shopping da wani? Yaushe kika zama haka Abra? Ina tarbiyyar da nayi maki kuma yanzu yanzu ki haɗiye kukan nan ki faɗa min Shegen daya kaiki shopping Wlh yau a ɗaure zai kwana, ba zai taɓa yiyuwa ina tufka wani yana warware min ita ba, ba zai taɓa yiyuwa ba" bakinta na rawa jikinta na ɓari tace "Abbi kayi haƙuri, wlh babu wanda nabi ɗan gidan...."

"Shut up" Mami ta daka mata tsawa tare da faɗin "tun ɗazo na kira Hajja Amina tace ko minti biyar baki ba a gidanta, shine yanzu zaki shirya ƙarya domin kare kai fita a nan kiban waje" da gudu ta saki Salman ta nufi bedroom ɗin ta, Salman kallon Mami kawai yake domin har ransa bai yarda da wannan zan can ba akwai abinda yake faruwa. Juyawa ya yi zuwa masjid ɗin domin yin sallar Magrib.

Kuka kawai Abra take lallashin duniya Salman ya yi amma taƙi yin shiru, da ƙyar ya lallaɓata tai sallah ya faki Idanunta ya saka mata maganin bacci cikin ruwa tana sha bacci ya yi gaba da ita.
Da Subhi bayan ta tashi da ƙyar saboda nauyin da Idanunta ya yi mata, bayan tai wanka tare da yin tana zaune saman sallaya aka turo ƙofar ɗakin tare da shigowa. Ƙamshin turarensa da taji yasa bata ɗago kanta ba, haka kurum ta tashi da ƙuncin zuciya.
Zama Salman ya yi a gefen inda take zaune Murya a ƙasan maƙoshi yace.

"Sabahul khair Angel"
Ba tare data kallesa ba Idanunta akan Azkar É—in da take tace "Ka tashi lafiya?" Bai amsata ba domin shi kaÉ—an yasan yadda yake bacci kullum shiru ne ya biyo baya kafin Salman ya kau da tunanin zuciyarsa ya ce.
"Wane ya yi maki shopping?" Sai a wannan lokacin ta É—ago kanta suka haÉ—a idanu ita kanta tai Mmkin yadda fuskar Salmam tai jajur idanunsa ya kumbura Sbd rashin bacci.
"Ina tambayarki kin tsaya kallo na kamar baki sanni ba?" Juyowa tayi baki ɗaya tare da kallonsa cikin sakin fuska tace "Maybe bana ɗaya daga cikin mutanan da za su yi farin ciki a duniya, ƙilan rabona sai bayan bana numfashi Salman" tana faɗin hakan ta miƙe tsaye hannunta riƙe da Alkur'ani bayan ta Ajjiye ta juya zata fita zuwa kitchen. da sauri Salman ya rufe ƙofar tare da murɗa key a jiki. Hannayensa ya harɗe a ƙirji idanunsa akan Abra da tayi tsaye tana binsa da kallon Mmki.

"If I am alive, you must be happy" a hankali ya matsa inda take idanunsa cikin nata ya ce "Ki faɗa min wanda ya yi maki shopping da kuma yadda kika daɗe a waje" banza tayi masa. "Ki faɗa min" a hassale tace "Salman ka barni dame zanji ne pls? Ka barshi a wani nabi shi ke nan....," gigitacciyar tsawar da Salman ya daka mata ya sanya tayi sauri rufe bakinta jikinta ya ɗauki rawa da ɓari, shi ne karo na farko da ya ɗaga mata Murya harda tsawa bata san lokacin data fashe da kuka ba tana durƙoshewa a wajan.
Chapter 38 · 0% Book details