← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 145

Sashe 66

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Me zakai to?"
Ta tambaya tana gyara kwanciyarta "idan Kinyi zaki gani, now tell ya Faris ya kiraki?" Kamar mai jiran kaÉ—an ta saka masa kuka sai ka É—auka shi ne yai mata ba daidai ba, shiru ya yi mata tayi kukan yadda ta keso kafin ya ce.

"Cry... Cry... Cry as so much as you can" kukanta ta ƙarawa sauti sai da numfashinta ya fara fisga ya ce "Ya isa, kada na ƙara jin sautin kukan nan" ya faɗa babu wasa kuma alamar warning.
Shiru ta yi masa shi ma bai sake cewa komai ba, sai sautin bugun zuciyoyinsu dake fita lokacin É—aya, idan akwai abinda Sp Adnan Aliyu Matawalle ya tsana ya ji mace na kuka, balle yanzu da ya kewa Abra kallon komai na rayuwarsa ta yaya zai so yaji kukan ta? Sam zuciyarsa ba zata jure ba. Kashe wayar ya yi baki É—aya tare da kwanciya zuciyarsa babu daÉ—i.

Da ga can ɓangaren Abra lumshe idanunta ta yi hawayen da ke maƙale ya silalo zuwa saman fuskarta, tana ƙanƙame wayar a jikinta numfashinta na fita da ƙyar murya a daƙushe ta ce.
"Why Faris? Ban cancanci hakan a gareka ba, mene ya sa zakai nisa da duniyata? Mene ya sa zaka barni a lokacin da nake tsananin buƙatar ka kusa dani, please come back to me wallahi na maka Al'ƙawarin na fasa auren ba zanyi ba, ina jin tsoro gabana faɗuwa kamar wani abu ne ya sameka"

Wani raunataccen kuka ta saki sai da tayi mai isarta kafin ta miƙe zuwa toilet ta wanke fuskarta tare da ajjiye wayarta, fita ta yi da ga cikin ɗakin kai tsaye bedroom ɗin Salmanun-faris ta nufa ta ci sa'a a buɗe ya ke.
Tana shiga ta kwanta a kan gadon sa, tare da jan pillow ta rungome kewarsa na fisgarta, a hankali ta saka hannunta ta shafi laɓɓanta sai a yanzu Abinda Ya yi mata ya shiga dawowa cikin kwakwalwarta, tana ganin abun tamkar a mafarki ƙara ƙanƙame pillown ta yi domin ji tayi kamar yanzu ne Faris ke sumbatar bakinta.

"I miss You Faris, I love you ɗan ƙanina please ki sau ɗaya ne ka kirani just to say hi to me"

Washe gari da sassafe Mami ta shirya ta nufi gidansu sbd kiran da Anuty Suwaiba tai mata, Abra bata san tafiyar ta ba, sai farkawa tayi ta ga mata nan, daman Abbi ya koma wajan aiki.
Tana zaune a Parlour ita É—aya kamar mayya tunanin Faris da Unknown É—inta ya addabi zuciyarta, wayarta ce ta fara kawo haske ganin sunan da tayi Saved number Abbi ya sa ta É—auka da sauri tana faÉ—in "Abbina"

"Sweetheart"
Abbi ya faÉ—a a taushashe yana gyara zamansa akan kujerar da ya ke zaune tare da sakin Murmushi. "Abbina gidan babu daÉ—i ni É—aya ce Abbi please ka dawo min da Faris"

"Ohh na É—auka zaki ce na dawo? Ni ba'a damu dani ba sai Faris Faris, ga kuma kamar Jaririya?"
Kamar ya ce tayi ta sakar masa kuka gaba É—aya ta addabi zuciyarta da kanta baki É—aya. Baya Abbi ya yi yana ta shi tsaye tare da goya hannunsa É—aya a baya ya shiga takawa cikin nutsuwa.

"Zaki tarwatsa min zuciya sweetheart? Kullum kuka Ohhh yaaaa shiru da bakin ki a nan wajan"
Shiru ta yi masa sai ajjiyar zuciyar da ta ke saukewa wanda ya ke jinta sosai ta cikin wayar a kame ya ce.

"Ki daina kuka sbd Allah da kuma ni Abbinki bani da nutsuwa" a sanyaye ta ce "na daina Abbi ya aiki? Ka yi waya da Salman?"

"Kince ke É—aya ce ko?"
Ya tambaya tare da yin rejecting questions É—in ta."E,Abbi" jinjina kansa ya yi kafin ya ce.

"Ta shi kije Garden ki sha fresh air zaki ji sauƙin zuciyarki,amma idan kika sake kuka mun ɓata ba ruwana da ke" da sauri Abra ta ce "ban sakewa Abbi"

"That's my girl Abra Khamal Khamis smile"
Murmushi ta sakar masa "Thank you Abbi" bai ce komai ba ya kashe wayar baki É—aya.
Wayar ta bi da kallo sai kuma ta miƙe tare da ajjiye ta a Parlour ta nufi Garden.

Uncle Faisal ne tsaye a gaban Mami sai Masifa ya ke. "Ni nace ina son Yarinyar nan kuma auren ta zan amma sbd an raina min hankali aka bawa wani ita, na cire kunyata har wajan fake father É—in nata naje amma ya nuna bai amince ba"

"Saurara Faisal ni kake son tunawa asiri? Matsayin ƙanin uwa kake wajan Abra sai kuma kace kana son ta? Kasan abinda hakan ke nufi? Yana nufin tona asirin shekaru kusan ashirin ke nan, wanda kuma daidai ya ke dana rasa igiyar aurena, bana son shirman banza kada ka sake yi min magana akan Abra,banda masifa me zakai da ita?" Mami ta ƙare zan can cikin ɓacin rai da kuma damuwa.

A fusace shima Uncle Faisal ya ce.
"Igiyar auren ki bata gabana, kuma aure ne anyi mugani sai dai idan bana raye wallahi, Abra mallakina ce tun tana ƙarama nake fama da son ta a zuciyata to ayi mu gani idan tusa zata hura wuta"
Yana faÉ—in hakan ya fice da ga cikin gidan baki É—aya, Anuty Suwaiba ta ce.

"Kan uba me Faisal ke nufi? Me zai aikata Na'ima ba kiga ta zama ba, idan baki son ki dawo gida mu jere matsayin zawarawa sai ki san
abinyi"
Dafe kai Mami ta yi cikin rashin sanin Abinyi ta ce "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un"

A hankali motar Fayyad ta shigo cikin Railway quarters ɗin yana zaune ɓangaren mai zaman banza sai Fayyad da ke driving yana tsokanar Sp Adnan.

"Da safe munyi waya baka ce min zaka zo ba, sai yanzu naji kira da ga sama wai kana airport"
Idanunsa akan gate É—in gidan su Abra ya ce.
"To Ubana ne kai da zan faÉ—a maka? Ko shi bai san zan zo kano ba"
Parking Fayyad ya yi yana faÉ—in.
"Fitar min a mota to mara mutunci" kafaɗa ya ɗaga irin ko a jikinsa ɗin nan. Fita ya yi a motar Fayyad na faɗin "babu ko godiya?" Banza ya yi masa. Walking slowly ya nufi gate ɗin, yana zuwa gatekeeper ya buɗe masa ƙofar cikin girmamawa, gaba ɗaya sojojin da suke wajan suka gaishe sa dake duk sun san shi.

Wayarta ya fara kira amma bata É—auka ba, ga shi ba abin ya shiga gidan kai tsaye ba, kuma ba zai iya komawa bai ganta ba, tafiya ce da shi zuwa Egypt. A hankali ya kalli É—aya da ga cikin sojojin kafin ya yi magana wani ya ce.

"She's in the garden"
Hanyar Garden ɗin aka nuna masa, a hankali cikin nutsuwa da kamala ya nufi ciki, tun daga nesa ya hango ta ƙasan wata bishiya ta ɗora kanta akan wani ƙaramin dining dake wajan sai bottle water da ke kusa da ita, ta ɓoye kanta a hannayenta. Kamar mai bacci a hakan, har ya Ƙarasa inda take ya ja Kujera ya zauna bata sani ba.
Hannunsa ya sa baki ɗaya ya ɗagota, ganin bacci ta ke a hakan ya sa ya ɗan tsora mata shanyayyun idanunsa, yana ƙara yaba kyan da Ubangiji ya yi mata. Kumatun ta ya shiga bubbugawa daidai kunnen ta ya ce.

"Open your eyes Wife ga mijinki ya amsa kira"
Turo baki tayi ta ce
"Faris i knw one day zaka dawo gareni please kada ka sake barina" ta faɗa tana ƙanƙame jikin Sp Adnan Aliyu Matawalle tare da ɓoye fuskarta a ƙirjin sa a tunaninta Faris ne, domin bacci ta ke amma mafarkin sa ta ke.

Bakin ta Sp ya kama ya murza yana faɗin "Ohh Wannan Faris anya ba zan tayaki biko ba?" jin yadda ake murza bakinta ga Ƙamshin Pur oud da ke ratsa hancinta ya sanya tayi saurin buɗe idanunta da ke cike da bacci.
Haɗa idanu sukai ta ganta male-male a jikin mutum, jikinta na rawa ta fara ƙoƙarin sauka amma ya riƙeta sosai.

"Ba inda zaki, tunda a nan kike bacci gwamma kiyi a jikin mijinki" ya faɗa yana ƙara riƙe ta. turo baki tayi ta ce "ka cikani ba ruwana da kai" ganin abinda ya ke ƙoƙarin yi tayi saurin ɗauke fuskarta ta shiga dokan ƙirjinsa tana sakin kuka..
"Ba ruwana Allah ba kace ba zaka zo ba?kayi tafiyarka ni ban son auren na fasa"

"Baki son auren ko baki sona" kuka kawai ta ke sakar masa hadda shassheƙa, shiru ya yi mata yana ƙara riƙeta a jikinsa.

Washe gari bayan taiwa Sp rigima sosai a makaranta da ke a Kano ya kwana da ƙyar ya rarrashe ta, ta ce Faris ya tafi shima zai ta fi ya barta a haka suka rabo da al'ƙawarin zai dawo Soon. Har yamma tana shcl karatu ya fara ɗaukan zafi, da ƙyar ta ke yaƙi da zuciyarta wajan ganin tai karatu amma tunanin Faris da Unknown Kullum da su take kwana ta ke ta shi, wanne hali Faris ke ciki? Fushi ya ke da ita ko mene?. Waye Unknown mene ya sa kalamansa suke da tasiri a Zuciyarta yaushe zai bayyana gareta mene ya sa ya daina yi mata messages yanzu?.

Meenal ce tsaye a gaban makeken Bulama hospital, cikin nutsuwa ta shigo reception ɗin tana bin mutunan wajan da kallo. Wata mata dake riƙe da yarinya mai Sikila ta kalla kafin ta ce.
"Ya kike zaune da ita tana soma? Ko ba soma bane?" Kafin tai magana da ga bayanta akace "ku kaita Emergency room yanzu, ai mata duk abinda ya dace ban san mene ya sa kuke barin patient ba kulawa haka ba"

"Daddy"
Meenal ta faÉ—a daidai kunan Bulama, hannunta ya kama yana nufar office É—insa da ita ya ce.
"My dear zuwan ba zata?" Fari tai da idanu ta ce.
"Wallahi Daddy kawai naji ina son zuwa hospital naka, amma banji daÉ—in yadda naga marasa lafiya haka ba"

"Shi yasa na so ki karanci Ɓangaren lafiya amma kika watsa min ƙasa a idanu, gaba ɗaya basu da serious akan aikin su, banda muna da tsananin kulawa ban san zai dinga faruwa ba, wasu da ga cikin Likitocin kuma idan ba kuɗi basa duba mara lafiya"
Chapter 66 · 0% Book details