← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 145

Sashe 12

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da azama ya tashi zaune, duk da haryanzu yana jin ciwo a in da aka harbe shi.
Abrar ta faɗa jikinsa ta ruƙunƙume shi, Captain ya rungumeta sosai a jikinsa yana faɗin "My daughter, i missed you" ta ɗago tana bin idon Khamal da kallo, tana murmushi.

Faruk ya sarawa Khamal sannan ya zauna yana faɗin "Yallaɓai ya jikin?"

Khamal yace "jiki Alhamdilillah"

Na'ima kuwa kallonsu take cike da rashin fahimta, ina Captain ya samo 'ya har ta ke kiransa da Abbi, ta daÉ—e da sanin sa kenan?.

Khamal ya kalli Na'ima yace "Madam, a kawo musu ɗan abun taɓawa"

Ta miƙe ta nufi hanyar kitchen, zuciyarta fal wasi wasi da tambayoyi.

Khamal ya kalli Faruk yace "ya akai aka ganta?"

Nan Faruk ya gayawa Khamal duk abunda ya faru, Captain Khamal yai shiru tare da jinjina kai yace "Salima again?"
Shiru ya ɗanyi yana nazari, sannan yai ƙwafa, yana sake rungume Abra a jikinsa.

Ya nisa yace "Faruk, ashe abunda ya kuma faruwa kenan, an kuma kwashe É—aliban jami'a?"

Faruk ya girgiza kai yace "bari kawai Captain, abun akwai tashin hankali, kullum abun ƙara worst yake, matsalar sake yawa take, kalli uban wanda muka kashe, da wanda muka kama, amma bayan ransom ɗin da suka buƙata har da se an sakar musu yaransu da muka kama, within seven days"

Khamal ya cije laɓɓansa na ƙasa, yana wani irin huci yace "Why? And When? Yaushe zamu samu 'yan ci, hankalinmu ya kwanta na 'yan ƙasa ya kwanta, har ɗan ta'adda yasan za'a bawa gwamnati tallafi, ya buƙaci wani abu a ciki, wannan wane irin abu ne, idan da gwamnati suke faɗa meye laifin innocent souls da suke sacewa suna cin zarafin su, yaushe hankalinmu ze kwanta? Gwamnatin mu na iya ƙoƙarin ta, mu kanmu jami'am tsaro muna namu ƙoƙarin, to a ina matsalar take? Waye me laifin?" Ya ƙarasa maganar yana huci.

Faruk yace "hakane, kowa yana ƙoƙari, amma akwai buƙatar mu gyara mu sake zage damtse gaba ɗayanmu, mutanen nan 'yan uwanmu ne, a cikin mu suke, meyasa za su zage su dinga kashe mu? Me mu kai musu? Akwai wani abu a ƙasa da yake buƙatar dogon Nazari".

Captain yai ajiyar zuciya yace "hakane, kuma idan aka tsaida hankali guri É—aya, za'a a iya samo bakin zaren"

Faruk yace "hakane, Allah ya iya mana"

"Ameen" Khamal ya amsa.

Na'ima ta dawo Falon ta kawowa su Faruk snacks, da ruwa da lemo me sanyi.

Abra tai ta bin abunda ta kawo ɗin da kallo, Captain ya ɗakko donut ya miƙa mata. Ta karɓa maimakon ta kai bakinta, se ta hau leƙa ɗan ramin nan na jikim donut ɗin tana dariya, a zatonta abun wasa ne.
Sai da Khamal, ya É—auka ya ci sannan ita ma ya nuna mata yadda za ta ci, sannan Abra ita ma ta fara ci.

Faruk da Khamal suka shiga hira abunsu, suna cigaba da tattaunawa akan matsalar tsaro, Abra na jikin Khamal tana ta kaɗa ƙafa tana ciye ciyenta.

Faruk ya miƙe tare da cewa "to Yallaɓai, ni zan tafi and Alhamdilillah na dawo da amanar da aka bani, ina fatan Ubangiji Allah ya taya riƙo, sannan ya ƙara maka lafiya"

Captain yace "Ameen ya hayyu ya ƙayyum, nagode ƙwarai Faruk, ka gaida gida".

Faruk ya juya ze tafi, Na'ima tace "a'a ya na ga kuma ze tafi ya bar yarinyar?"

Khamal yace "karki damu zan miki bayani"

Faruk ya juya tare da É—agawa Abra hannu, itama É—aga masa hannu tai tana masa murmushi.

Na'ima ta dawo da dubanta kan Khamal tace "Nifa ban gane ba, bayanin me za kai min?"

Khamal yace "Calm down baby, ki zauna mana"

Zama tai tana tura baki tace "Gaya min, meye ma'anar wannan abun? Wacece wannan yarinyar?"

Khamal ya gyara zamansa, ya gayawa Na'ima komai, tun daga tsintar Abra da yai har zuwa yanzu, sannan ya ɗora da cewa "A hukumance ma, hukumar mu sun san da zaman Abra a hannu na, za'a cigaba da neman iyayenta, in Allah yasa an samesu shikenan, idan ba'a same su ba ina son Abra ta cigaba da zama tare da mu a nan, mu riƙe ta tamkar 'yar da mu ka haifa".

"Dan Allah ɗan saurara mana Khamal, wai shekaruna nawa ne yanzu a duniya da har kake tunanin zaka iya raina min hankali? Wato ka mai da ni ma wata nusarar mahaukaciya, wadda ba ta san me take ba, kaje karuwa ta haifa maka 'ya, kuma ka ɗakko kace in riƙe kana cikin hayyacinka kuwa? Kai ina zaton sautin ƙarar bom da ka saba ji a daji ya taɓa maka ƙwaƙwalwa ba ka sani ba.
To bari kaji in gaya maka, wannan 'ya Wallahi ba zan riƙeta ba, ka mayarwa da uwarta can da kuka haifeta tare ta riƙeta, dama aiku sojoji ba wanda za'a bawa amana bane, wato uwarta na gudun abun kunya ba zata riƙe ba se ni, karkatacciyar bishiyarka me daɗin hawa, ni zan riƙe 'yar karuwa to Wallahi da sake"

"Shut up Na'ima!" Tsawar da Khamal yai mata se da É—an cikinta ya juya, saboda tsabar razana da ta yi.

"Ni kike cewa na haifi 'ya da karuwa a waje? Na'ima yanzu shedar da zaki bayar a kaina kenan? Kin fi kowa sanik ni ba mutumin banza bane"

Cikin tsiwa tace "Abu na ɗan Adam kowane lokaci ai yana iya canzawa, kuma in da kake zuwan tunda ba wani ne yake binka ya ga me aikata ba, ai Allah kaɗai ya san me kake yi, dan haka Wallahi ba zan riƙe 'yar karuwa ba, ka maida ita gurin uwarta tun da wuri".

Khamal yace "Na'ima, nan gidana ne, kuma ko 'yar karuwa na kawo nace ta zauna, gida na ne ba naki ba, idan ba zaki iya riƙe Abra ba, zaki iya tattara kayanki ke ki koma in da kika fito".

A razane ta kalli Captain Khamal tace "yanzu zaka iya rabuwa da ni, da É—anka na sunna da zan haifa akan 'yar da karuwa ta haifa maka Khamal?"

Yace "yes of course, idan ba zaki zauna da Abra ba, ni zan iya rabuwa da ke, kuma ko ki yadda tsintar Abra nai, ko kar ki yadda ki cigaba da zama akan bakanki cewar 'ya ta ce da na haifa a waje, wannan ke ta shafa amma Abra a nan zata zauna tare da mu".

Fashewa Na'ima tai da kuka, ta wuce bedroom ɗinta, ta cire wayarta da ke caji, ta shiga neman lambar Ammi, wato mahaifiyar Khamal, Ammi na ɗagawa Na'ima ta sake fashewa da kuka tace "Ammi dan Allah ku zo gidanmu akwai matsala, Khamal yaiwa karuwa ciki a waje, ta haihu tace ba zata riƙe ba, shine ya kawomin ita wai in ban riƙe ba ze sakeni"

Ammi tace "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Khamal É—in?"

"Wallahi Ammi da gaske nake, dan Allah kuzo, kar baƙi ciki ya kasheni, dan Wallahi se da ya zaɓa ko ni ko ita, ba zan zauna da 'yar zina in raineta ba!".

COMMENT AND SHARE

BRIGHT PENS
NIMCYLUV
AYSHECOOL
ZEE KUMURYA

Domin ƙarin bayani, ku tuntuɓe mu akan
07063065680
09047871750

m selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*[9/30, 8:55 PM] Abk: *✷ DARE DA DUHU ✷*

Brigh pens✍️
Nimcyluv
Ayushercool
Zee Kumurya

*6.....*
Elegant online writers

LITTAFIN DARE DA DUHU, ₦300 NE KACAL, ZA KU TURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0116886423 Sulaiman Na'ima s union Bank. IDAN KATIN WAYA NE #500 NE.
KU TUNTUƁI WANNAN LAMBAR DAN TURA KATIN 09047871750
DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU AKAN WANNAN LAMBAR 07063065780\09047871750
MUNGODE.

*_Masu son Littafin MIJIN MALAMA... Kuyi following Acct ɗin nan a Arewabooks👇🏾_*
https://arewabooks.com/u/nimcyluv

Cikin kaÉ—uwa Ammi ta ce. "Subhanallahi, Na'ima kin san me kike cewa kuwa? Baban nawa ne zai aikata wannan mummunan aikin?"

"Wallahi Ammi dagaske nake, kin san dai ba zan yi masa k'arya ba, ki zo ki ga yanda suke yi da Yarinyar, zaki tabbatar ÆŠa da Mahaifi ne."

Jiki a sanyaye Ammi ta ce. "Wannan maganar ba ta waya ba ce, bari na kira Alhaji, za mu zo yanzun nan insha Allahu, amma dan Allah kar ki tayar da hankalinki da yawa, kin san a yanayin da kike ciki ba'a buƙatar ki saka damuwa a cikin ranki."

"Toh Ammi sai kin zo" Ta faɗi haka cikin kuka, zuciyarta na yi mata wani irin suya saboda tsananin kishi. Khamal ya shayar da ita ruwan mamaki, ba ta taɓa zaton haka daga gare shi ba, she trusted him over, ashe ya ce zai nuna mata halinsu na sojoji.

Cillar da wayar ta yi ta fito daga ɗakin kamar mahaukaciya, ko nauyin cikin jikinta ba ta ji. Zaune ta tarar da Captain a parlour kan kujera two seater, Abra na jikinsa ta yi bacci abinta. Kallon Television yake yi hankalinsa kwance tamkar babu wani abu na ɓacin rai da yake damun shi. Hakan ya ƙara k'ular da Na'ima, ta tsani wannan maziyar tasa, abu ya faru ya mayar da kai mahaukaci shi kuma ya dinga pretending like everything is okay.

Kamar zautacciya ta fara cillar da pillows ɗin kujera cikin kuka tana faɗin. "Wallahi Khamal ba ka isa ka tozarta ni ba, sai na kashe ka na kashe yarinyar in yaso nima a kashe ni!" Khamal dake bin ta da wani irin kallo cikin tsawa ya ce mata. "Na'ima! Wallahi kika sake wani abun ya samu Yarona da ke cikinki garin haukanki sai na nuna miki ɓacin raina, wanda baki taɓa ganin irinsa ba."

"Ya mutu ma ina ruwana Ni, kuma ɓacin rai ka daɗe baka nuna mun shi ba, ƙarƙari dai ka ce ka sake ni in tafi in bar maka gidanka, to idan ka sake nin sai me? Na ce sai me?" Tai maganar tana zazzare idanunta da sukai jawur, saboda azabar kishi da kuma kukan da tai.

A firgice Abra ta farka daga baccin saboda hargagin Na'ima, fashewa ta yi kuka tare da ƙanƙame Captain tana kiran sunan "Abbi".
Chapter 12 · 0% Book details