← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 145

Sashe 65

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yarinyar da Adnan zai aura, Major Khamal ba shi ne ainihin Mahaifinta ba, tsinto ta ya yi a daji."

"Kai kuwa a ina ka jiyo wannan maganar mara daÉ—in ji?" Cewar Alhaji Mustapha cikin tsananin mamaki.

"Daga majiya mai ƙarfi, dan haka da sake wai an bai wa mai kaza kai da ƙafafuwa, tunda Allah ya sa kafin a ɗaura Aure muka samu wannan labarin dole a fasa abun nan, dan ba za mu haɗa iri da Yarinyar da ba a san asalinta ba!"

Littafin nan na kuɗi ne ₦300 NE
Via 0116886423  Sulaiman Na'ima s union Bank. Idan katin waya ne mtn na 500 idan transfer ta account ne ɗari uku kacal.

Evidence of payment 07063065680 ko 09047871750.
[10/7, 2:28 PM] Abk: "Sunan zuri'armu zai ɓaci muddin muka bari Adnan ya auri yarinyar nan wacce babu wanda ya san Asalinta balle iyayen da suka haife ta, We want a girl with originality and roots" Cewar Uncle Khabir ya faɗa yana mai girgiza kansa, alamar abinda ya ke faɗa tun da ga ƙasan zuciyarsa ya ke fitowa.
"this is not a problem, and Adnan must marry this girl as he intended, ni baga wani aibun Auren ta ba gaskiya, kowa akwai yadda Ubangiji ke tsara masa rayuwa" Kallon Alhj Mustapha Uncle Khabir ya yi fuska babu walwala ya ce.

"Yaya mara asalin kake so yaronmu ya aura? Kada ka manta yadda jama'a ke mutun ta familynmu, ta yaya zamu zuba idanu Adnan ya aure ta, bayan mun san abinda hakan ke nufi? Our dignity is seen, we have money, education. Mun fito daga cikin Ahhali mai kyau da nagarta, auren Adnan da wannan yarinyar na nufin zubewar Alhhalin Matawalle I don't want that to happen"
Da Mamaki Alhj Mustapha ke kallon Uncle Khabir, he just thinking ina ilimin Khabir ya tafi haka? numfashi ya sauke cikin tarin nutsuwa da nuni d cewa shi É—in he's educated ya ce.

"Idan Abra Khamal Khamis ta kasance Shegiya ko mara tushe da asali kamar yadda kake ta É—aga murya kana faÉ—a, ina tunanin cewa ba ita ta tsarawa kanta yadda za tazo duniya ba. Kuma bada yardar ta abinda ya kasance ya kasance É—in ba, God determines everything that happens, and He determines how a person will come to earth. Ka É—auka hakan zai iya kasancewa da wani namu, É—a kuma na kowa ne so please ka bar wannan maganar"
Jinjina kai Uncle Khabir ya yi cikin girmamawa kuma ya ce "Shi kenan yaya, Allah ya basu zama lafiya"
"Amin, Amin" Alhj Mustapha ya faÉ—a yana sakin Murmushin jin daÉ—i na amincewar É—an uwan nasa.

"Do me a favor, please."
Professor Aliyu Matawalle ya faÉ—a yana gyara zamansa kana kallon su kasan cewa, kuÉ—i ya gama yin kuka a jikinsu, ga tarin ilimi komai nasu a waye ya ke kuma cike da tsari.
"Muna jinka idan har bai gagara ba"
"Ba zai gagara ba Insha Allah" Abba ya faÉ—a idanunsa akan Uncle Khabir kafin ya ce.

"Maganar nan ta tsaya iya mu, bana son Sp Adnan yaji wannan maganar, balle wata rana ya goranta mata, I know he loves her, but the heart can decide for him one day. Even Hajiya bana son ta san haka balle ya fita zuwa Matawalle Family please brother's"
Murmushi Alhj Mustapha ya ƙara saki ya ce.
"U don't have to be worried about, babu wanda zai ji haka Insha Allah. Adnan nada hankali da tausayi ba zai taɓa aikata hakan ba koda yaji haka, nasan kuma Barrister ba zata ce komai ba"

"Bar sha'anin mata yaya, bana son Hajiya ta san zan can wallahi kasan abin surutu da yayatawa baya yi musu yawa, zata iya hana auren wanda kan janyo matsala ga Adnan. Bana son komai ya samu Adnan"
Uncle Khabir ya ce.
"Extly. Mace taji zance ka tabbatar kowa ya sani more Especially irin wannan, Allah dai ya ki yaye"
Rufe zan can sukai tare da fara tattaunawa akan sabon Companyn da zasu buɗe ƙarƙashin Matawalle Family.

Bayan Magrib Sp Adnan ne zaune shi da Usman cikin wani ƙaramin garden dake gidan, ba zaka taɓa cewa duhun dare ya fara kawo kai ba, sbd yadda wajan ya ƙayatu haske ko ina.
A hankali Sp ke sipping tea É—in da ke kusa da shi, yana lumshe fararen idanunsa gaba É—aya gajiya ta saukar masa a karo na farko na rayuwarsa damuwa ta bayyana akan fuskarsa.
"Gaskiya gidan ka ya haÉ—u Sp duk wanda ya yi maka zanan gidan ya iya, anya ba za'ai min irinsa ba"
Harara Sp ya watsawa Usman ba tare da ya ce komai ba. Usman ya gyara zama ya ce "U looks so worried what's up?" Watsa hannun Sp ya yi a hankali ya ce.
"Time É—in bikina nake gani kamar baya zuwa"

"Are you serious? Maganar 3weeks ake shi ne baya sauri this is wonderful yau Sp ke son kasancewa da mace"
Idanunsa dake a rufe ya buÉ—e tare da kai hannunsa ya ja zip É—in gaban rigarsa surar jikinsa ta bayyana.

"Ina jinta a nan"
Ya faɗa yana nuna saitin zuciyarsa da hannunsa "komai ƙwace min ya ke idan naji muryar ta, i can't control myself idan nai tozali da Fuskar ta, kamar nai ta kasancewa da ita har gaban Abada"

"The day I've been waiting for has come. Allah ya nuna min Annabi kamar yadda naga wannan ranar, yau Adnan ke sambatu akan wata"

"Ba wata bace, she's my wife mother of my children my life partner"
Sai kuma ya gyara zamansa sosai jikinsa na fidda Ƙamshin Pur oud ya ce.

"My wife is different from other women, firstly sanyin halinta ke ƙara sawa na sota, uwa uba haƙuri da biyayya, she never lie to me" baya ya yi kaɗan yana lilo jikin Kujera da ya ke zaune tare da rufe idanunsa a hankali ya saki lallausan murmushi wanda ya sanya fararen haƙoransa bayyana cikin husky voice ya ce.

"A beautiful woman, with big white eyes and a small mouth with a sweet voice and a lot of religious knowledge. Wow Sp Adnan Aliyu Matawalle I'm lucky ni mai sa'a ne"

Dariya Usman ya yi sosai yana ɗaukan bottle of water tare da ɓalle murfin gorar ya tsiyaya wa Adnan ya ce.
"You have to drink this ko ka samu nutsuwa" tashi Adnan ya yi yana shafa kansa bai ƙara cewa komai ba ya nufi cikin gida saboda kiran sallar issha da ya ji.
Miƙewa Usman ya yi ya ce.

"Amma da ga É—an iska sai kai, ka kirani akan tsara Invitation na É—aurin aure, But you didn't tell me anything about it,We don't have time, we don't have anything planned for the ceremony"

"Karka min ihu akan I.v ko da shi ko babu dole a ɗaura min aure kuma a kawo min Angle gidana" dry kawai Usman ya yi yana ƙara mamakin yadda idanun Sp ya rufe akan Abra, ga shi ko a photo ya hana ya ganta Maybe shi da ganinta sai kuma biki idan Allah ya kaimu da rai da lafiya.

Bayan sallar issha Sp da Abba da Hajiya Mama duk suna zaune a dining area suna yin dinner, rabin cin abincin Abba ne da Hajiya, Sp tea kawai ya ke sha a hankali, sai fried indomie wacce akai masa ta sha hanta sai Ƙamshin ta ke, bayan sun kammala ne Hajiya ta kalli Sp ta ce.
"Ya kamata a kawo min Daughter-in-law" É—ago kansa ya yi a hankali ya zubawa mahaifiyar tasa ba tare da ya ce komai ba.

"Ka tsare ni da idanunka ko baka gane bane?"
ÆŠan marairaicewa ya yi ya ce "Haba Hajiyata idan ban gane ba to maganar wa zan gane?" Abba ya kalli Adnan ya ce.
"Rigima ce kawai ta Barrister amma tun daga Kano ya É—akko Æ´ar mutane har Kaduna, ai iyayen ta ba zasu amince ba"
Jinjina Kai Sp ya yi kafin ya É—auki wayarsa ya ce "Ina laifi a haÉ—aku V.c amma is too par from kano to Kaduna"

"I knw, na matso naga Daughter-in-law É—ita nima kafin Allah ya kawo mana Grandchildren"
Shafa kansa ya yi zuwa Fuskarsa yana sakin Murmushi "I'm so anger to see my wife kusa dani"

"Me kace?"
Hajiya Mama ta watso masa tambayar domin kusan a fili ya yi maganar bawai a zuciya ba kamar yadda yai niyya. Miƙewa ya yi idanunsa akan wayarsa ganin notification.

"Abba, Hajiyata good night" da idanu suka bisa sai da ya ɓacewa idanunsa Hajiya Mama ta ce "A wanne part zai saka Amaryar ne naga baya magana hakan?"

"A gidan sa zai sakata" nan da nan Mama ta ɓata fuska domin har zuciyata ta ke son zaman Abra kusa da ita, ko Adnan baya nan sai su zauna tare. Haƙuri Abba ya bata akan ta rabo da shi yanzu yana kan giyyar soyayya ba zai fahimta ba.

Misalin 11:00 na dare bayan ya kammala shirin kwanciya bacci sbd gobe tafiya ce da shi mai muhimmanci, a hankali ya gama saka rigar pyjamas É—in kana ya zauna gefen gado yana kwanciya tare da sakin ajjiyar zuciya.
Wayarsa mai ƙirar iphone 13max pro ya ɗauka a nutse ya lalubi number ta tare da danna call ba tai wani rigging da yawa ba akai picking call ɗin.

"Bebbbb"
Ta faÉ—a cikin siririyar muryarta wacce bata fita sosai, saurare É—aya kuma zakai mata kasan cewa mamallakiyyar muryar tana cikin damuwa.
"What happened to your voice?" A shagwaɓe ta ce masa "Nothing, how are you?"

"Good and you?"
Cikin salon taɓara ta ƙara narkar da muryarta ta ce "not good" a hankali Sp Adnan Aliyu Matawalle ya mirgina kaɗan yana jan pillow zuwa jikinsa.

"Lafiya? Jikin ne?"
Kamar tana gaban sa ta girgiza masa kai low É—in voice É—inta tasa keyi "No lafiya nake, I'm just wanted to see you please" wani kalar murmushi ya saki ya ce.

"Cewa zaki kina son ganin mijinki right?" Turo masa baki tayi ba tare da ta ce komai ba, kamar wanda ya ke Kallon ta ya ce.
"Allah ya baki sa'a a turo bakin nan a gabana yarinya"
Chapter 65 · 0% Book details