← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 145

Sashe 93

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Insha Allah sai cikin nan ya zube, Allah sai ya saka mini Adnan, insha Allah sai cikin nan ya zube ba zan haihu da kai ba".

Jinin da take zubarwa a hannunta duk ya ɓata masa jiki, Nurses ne suka shigo dan bawa Abra magani, amma suka tarar da halin da take ciki, da ƙyar aka dannenta aka yi mata allurar bacci, duk ta galabaitar da kanta.

Gargaɗi sosai likitan da ta duba Abra ta yi wa Adnan a kan a guji abin da zai dinga jefa ta a cikin damuwa, gudun kar a rasa ta ita da abin da ke cikinta, sannan ta ba ta bedrest na sati biyu. Ya kira Mama ya sanar mata halin da ake ciki, ta aiko mai aikinta ta kawo musu kayan buƙata, saboda ita ta je unguwa kuma wurin da nisa.

Sai bayan Magriba Abra ta ƙara farkawa, har lokacin Adnan yana zaune a gaban gadon da take yana latsa waya. Duk da wata irin kasala da take ji amma haka ta daure ta tashi zaune. Cikin kulawa ya ce. "Kin tashi? Ya jikin naki?" Wata uwar harara ta wurga masa ba tare da ta ce komai ba, sai dafe kanta da ta yi. Miƙewa ya yi ya ce. "Ba dai kan ne ke ciwo ba? Sannu, How are you feeling now?" Tsaki ta ja cikin takaici ta ce. "Shut up Malam! Haba, tun ɗazu sai ihu kake mini a ka, Please ka bar gurin nan in daina ganin ka don bana ƙaunar ganin ka ko kaɗan wallahi." Murmushi ya yi ganin yadda ta yi maganar cikin tsiwa, wadda ba ta dace da ita ba sam. Bai ce komai ba ya juya don kiran Likita, ganin drip ɗin da aka saka mata ya ƙare.

Lumshe idonta ta yi bayan ya fita, kalamansa na ɗazu ne suka dawo mata cikin kunnenta da yake cewa tana da ƙaramin ciki. Wasu hawaye masu ɗumi ne suka fara zuba daga cikin idonta. A fili ta furta. "Allah na gode maka da duk Yadda ka tsara rayuwata ta kasance, Allah ka ba ni ikon cinye jarrabawar cikinta." Slowly ta kai hannunta kan cikin ta shafa cikin wani irin yanayi, wanda ta kasa tantance na farin ciki ne ko akasin haka. The thing is so amazing to her, wai yau ita ce ɗauke da juna biyu? Za ta haifi girl or boy nan da wasu watanni? Za ta zama uwa ita ma?

Dawowar Adnan tare da wata Nurse ya katse mata tunanin da take. Saurin share hawayen fuskarta ta yi ba tare da ta bari sun haÉ—a ido da É—ayansu ba.

"Patient, ya jikin naki?" Nurse din ta faÉ—a cikin murmurshi.

"Alhamdulillah." Ta amsa mata cikin sanyin murya.

Bayan ta cire mata drip ɗin Abra ta dube ta in serious talk ta ce. "Don Allah Nurse ki taimake ni ki cire mini cikin dake jikina, ko ki faɗa mini abin da zan sha ya ɓare." Cikin matuƙar mamaki Nurse ɗin take duban ta, kallon Adnan ta yi ta ce. "A'a ba mijinki ba ne wannan? Ke kuwa me zai saka ki so rabuwa da Ni'imar da Ubangiji ya yi miki? Abin da wasu suke ta fafutukar nema ba su samu ba."

"Ni dai in za ki taimaka mini ki taimaka mini kawai don Allah."

Nurse din za ta yi magana Adnan da ya kafe Abra da ido ya É—aga mata hannu tare da faÉ—in. "Don't worry, you can go idan kin gama yi mata abin da za ki mata, i will solve the problem."

"Okay, Allah ya ƙara lafiya."

"Amin, thank you."

Kuka Abra ta saka bayan Nurse din ta fice, cikin ɗaga murya ta ce. "Kome za ka yi ba zan bar cikin nan ya zauna ba, domin ba zan so na hahu tare da azzalumi mugu mara imani ba." Wani murmushi ya yi ya ce. "Tunda Mother ta haƙura ta haife ki da azzalumin mutum ke ma sai ki haƙura ki haifa, kin ga an yi 1/1 kenan." Ya ƙarashe maganar cikin ɗage gira. Saboda baƙin ciki kasa magana ta yi, sai kuka da ta kuma fashewa da shi. Still yana murmushi ya tashi ya koma gefen gadon tare da zama daf da ita, ƙoƙarin ja baya ta yi saboda ƙamshinsa da ba ta ƙaunar shaƙa ko kaɗan, amma ya hana ta aiwatar da hakan sakamakon hannunsa da ya sa ya zagaye bayanta da shi tare da ƙara matsawa jikinta. Yana bin ta da wani irin kallo ya ce. "Abra Mrs Adnan, yau babu faɗa da rigima a tsakaninmu, saboda farin cikin da nake ciki na samun new Unborn." Ya ƙarashe maganar tare da ɗora hannunsa a kan cikinta ya fara shafawa a hankali.

Cikin tsananin baƙin ciki Abra ta fizge jikinta, ji take kamar ta kikkifawa fuskarsa mari. Saurin riƙo ta ya kuma yi tare da faɗin. "Ki yi a hankali, kar ki illata mini gudan jinina." Tsaki ta ja ta juya masa baya ta kwanta, zuciyarta na mata tuƙiƙin baƙin ciki, ita kaɗai ta san abin da take ji a cikin ranta, Allah ya sani ba ta so haɗa zuri'a da Adnan ba, amma babu yadda za ta yi da ƙaddara.

"Me za ki ci?"

Ta tsinkayi muryarsa yana tambayar ta, banza ta bawa ajiyar shi. Shi kam ko a jikinsa, da gaske yake har cikin ransa yana ƙaunar abin da ke cikin Abra sosai, shi kansa ya yi mamakin faruwar hakan. Lumshe idonsa ya yi yana imagining ranar da Abra za ta haifa masa Baby, bai san irin farincikin da zai yi ba a lokacin.

Bai haƙura ba ya cigaba da tambayar Abra abin da take son ci cikin lallaɓawa, ita kuma ta ƙi kula shi ta bar shi yana ɓaɓatu shi kaɗai. A haka Hajiya Mama ta zo ta same su, ba ƙaramin farinciki ta yi ba da jin Abra na da juna biyu. Ta dinga nan-nan da ita tare da ba ta kulawa. Ita ta kwana tare da Abra, ta ce Adnan ya koma gida.

Washegari aka sallami Abra, Gidansu Adnan Hajiya Mama ta wuce da ita sai dare sannan Adnan ya zo ya ɗauke ta suka koma gidansu, tare suka tafi da mai aikin Hajiya Mama za ta zauna a gidan har zuwa lokacin da Abra za ta samu lafiya. Cikin ƴan kwanakin nan ta samu sauƙin tijara da takurar Adnan, don sosai yake nuna k'aunar cikin jikinta, amma in abin ya motso masa yana taɓawa. Ba ta kula shi saboda ba ta shi take ba, ta jinyar kanta take. Ga mai aikin Hajiya Mama tana ɗebe kewa sosai, don matar babu ruwanta tana da kirki.

Yau kwana biyar da sallamo ta daga asibiti, da daddare tana kwance a É—akinta suna chatting da Abbi yake mata zancen karatunta.

"Daughter tunda an gama cin amarcin ya kamata a koma school kuma."

Murmushi ta yi cikin jin kunya ta tura masa emojin rufe fuska. A hankali ta kai hannu ta shafa cikinta, tana jin yadda wata zazzafar soyayyar shi take zagaye ko wani gurbi na zuciyarta. Abbi bai san tana da ciki ba, shi ya sa yake mata zancen karatu, ta sanar masa dai ta yi ciwo, amma ba za ta iya faɗa masa tana da ciki ba. Sai dai ita ma tana son ta cigaba da karatun, damuwar da take ciki ne ya sa ta manta da babun shi, tunin Abbinta kuma a yanzu ya dawo mata da son karatun, ko ba komai idan tana zuwa school ɗin zai rage mata damuwa tare da ɗebe mata kewar kaɗaici. Sallama suka yi da Abbi ta miƙe ta nufi ɗakin Adnan.

Tana shiga ta tarar da shi yana shiryawa, alamun bai jima da fitowa daga wanka ba. Kallo ɗaya ta yi masa ta ɗauke kanta, saɓanin shi da ya ƙura mata ido. Cikin haɗe rai ta ce. "Magana na zo mu yi Adnan."

"Ba ni da lokaci." Ya faÉ—a tare da É—auke idonsa daga kanta.

"Kamar ya ba ka da lokaci? Maganar karatuna ce to ba wani abu ba, Abbi ya mini magana ya ce ya kamata zuwa yanzu na koma school, kar a mini nisa da yawa.

Kallon sama da ƙasa ya yi mata ya ce, "Lallai wuyanki ya isa yanka, wato kwana biyu na sake miki shi ya sa har kika samu damar faɗa mini magana son ranki, saboda ba ki jibgu ba ko? To darajar cikin jikinki kike ci, domin duk ranar da ya bar jikinki sai na fanshe duk bashin da kika ɗauka."

"Is not my concern, ka yi ko ma mene ne, ni yanzu maganar karatuna nake maka, ya ake ciki?"

"To ba za ki cigaba ba, ke da karatu har abada in dai a gidan Adnan Aliyu Matawalle ne, saboda karatu na masu asali, gata da Æ´anci ne, ba na TSINTATTU irin ki ba."

Littafin kuɗi ne, ki/ka biya kafin ku karanta. Don neman ƙarin bayani 09047871750
[10/27, 11:38 AM] Abk: Kallonsa take cike da takaicin yadda gaba É—aya yake son É—auke mata dukkan wani farin ciki na rayuwarta.
"I am your husband and I have control over you, karatu ne ke dashi har abada sai a lahira idan anayi, Everything I know will make you happy so I prevent it from happening.. Ki daina wahalar da kanki kina wahalar min da unborn okey"

"Zaka iya hanani farin ciki, amma baka isa ka É—auke mini raina ba, duk wahala duk tsananin nasan Ubangiji yana tare dani kuma shi ne zai saka mini akan cutar da kake aikatawa a gareni,
I'm your wife amma na zama jaka a wajanka mara Æ´an ci, ka sani ko Ubangiji baya kama bawa da laifin da bai san ya aikata ba,
balle Mutum akwai haƙƙina a rataye a wuyanka"
Chapter 93 · 0% Book details