← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 145

Sashe 27

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na'ima tana zaune a parlour ita da wata ƙawarta da ta kawo mata ziyara, suka yi sallama suka shigo, ta amsa musu tana bin Abra da wani wulaƙantaccen kallo, ƙasa ta yi da kanta gabanta na fad'uwa, ta san watan shan wahalarta ya kama tunda Abbi ba ya gari. Cikin girmamawa ta gaishe da baƙuwar tare da yiwa Nai'ma sannu da gida, sannan ta wuce ɗakinta. Salman kuwa zama ya yi ya gaishe da baƙuwar tare da faɗin. "Mami yau mun gama exam ɗinmu ta third semester Ss 1, ranar Saturday ɗin nan za mu yi speech in Allah ya kai mu. Na'ima ta ce. "Masha Allah, Allah ya nuna mana ya bayar da sa'a." Ya amsa da Amin sannan ya tashi ya nufi ɗakinsa.

Ƙawar Mami mai suna Maryam ta dube ta cike da munafurci ta ce. "Na'ima kar dai ki ce mun har yanzu kina riƙe da wannan Shegiyar yarinyar?"

"To ya zan yi, tunda mai gidan ya dage."

"Taɓ kin ga zaki iya ne, amma da ni ce da tuni ta bar mun gida wallahi, yanda take da kyan nan ai sai ta raba ki da mijin naki ma."

"Khamal ba zai taɓa son yarinyar nan ba na sani, dan a matsayin ƴa ya ɗauke ta, kuma ba ya son ta san ba shi ya haife ta ba, dan haka ki ma bar wannan zancen kar zuciyata ta buga, dan wallahi idan hakan ta kasance sai na kashe ta na kashe kaina na kashe khamal! Damuwata a yanzu yanda Khamal yake nuna mata ƙauna shi da ƴan'uwansa, dan a yanda suke nunuwa sun fi ƙaunar ta akan Salman, abun nan yana ci mini tuwo a ƙwarya ba kaɗan ba."

"To ai ke kika zauna komai yake faruwa, ta ƙarƙashin ƙasa zaki bi ki yi yanda dole ta bar gidan, azabtar da ita zaki na yi bana wasa ba idan baya nan."

"Hakan nake yi ai, dan kin ga bana komai a gidan nan ita take yi."

"Dan girki da su wanke_wanke ai mai sauƙi ne, aiki zaki na ba ta wanda sai ta kwanta ciwo dan wahala, idan wuya ta ishe ta da kanta za ta gudu."

Na'ima ta ɓata fuska ta ce, "To su girkin da nake ba ta ma cewa ya yi aikin ya yi mata yawa, a samo masu aiki suna yi, sai dabara na yi masa na ce ai ita ƴa mace dole sai an yi treating ɗinta a gidan iyayenta, kar ta je gidan Miji a ce ba ta iya komai ba, sannan fa ya hak'ura ya bari take yin aikin."

Maryam ta ce. "Ai idan baya nan zaki na ba ta ayyukan wahalar."

"Idan baya nan ai akwai mai yi masa c.i.d Salman, wannan yaron kamar cingum kullum yana naniƙe da ita, shaƙuwarsu da soyayyar junansu har tsoro take ba ni."

"Ke fa Na'ima idan kika yi wani abun kamar ba wayayyiya ba, yanzu komai sai an koya miki, ai da dabara zaki yi. Bari in faÉ—a miki yanda zaki na yi." Shawarwari kala_kala na mugunta da azabtarwa Maryam ta bawa Na'ima akan ta dinga yiwa Abra, ai kuwa ta ji daÉ—in su sosai ta ce a yau ba gobe ba za ta fara.

Fitowar ta kenan daga wanka ta zira riga mara nauyi da niyyar ta kwanta ta huta, saboda ciwon da kanta yake mata, dan jiya ba ta yi ishasshen bacci ba, ta tsaya karatun Nobels É—in da za'a yi musu question a exam É—insu ta Yau. Mami ce ta banko É—akin ta shigo ba tare da ta yi sallama.

"Ubanki kike yi a É—akin da ba za ki fito ki É—ora mana girki ba? Ba ki ga rana ta yi ba ne?"

Na'ima ta faÉ—i haka cikin masifa tana wurga mata uwar harara.

Ƙasa ta yi da kanta ta ce. "Ki yi hak'uri Mami, ban san baki girka ba."

"Tunda ga baiwar Ubanki ko? In girka miki ki zo ki ci?" Ta ja ƙwafa sannan ta juya ta bar ɗakin.

Ba ta ce komai ba, ta É—auki hijab É—inta ta zira ta bi bayan Na'ima, ta san da Abbi yana nan kafin su dawo daga school Mami ta yi girki, shi yasa yau ma ta É—auka ta yi.

"Salman! Salman!"

Firgigit ya farka daga baccin da ya fara É—aukar sa, Mami ya gani tsaye a kansa.

"Ka tashi zan aike ka?"

Idanunsa dake cike da bacci ya lumshe ya ce. "To Mami ina zuwa."

"Kamarya kana zuwa? Hajiya Maryam ce fa za ta tafi, zaku bi ta gidanta kai da driver za ta ba ka saƙo ka kawo mini, saƙon kuma na gaggawa ne ina buƙatar shi yanzu."

Duk da baccin dake cin shi haka ya tashi zaune ya amsa mata, bayan ta juya ta fita ya tashi ya shiga toilet dan wanke fuskarsa.

Ƙarfe uku da mintuna Abra ta gama lunch, tana ƙoƙarin shiga ɗakinta ta kwanta ta ɗan yi bacci kafin lokacin islamiyya ya yi, amma Na'ima ta hana ta, umarni ta ba ta akan ta biyo ta ɗakinta, babu musu ta bi ta.

Zannuwan gado farare tass wanda Na'ima ta wawwatsa musu manja da gayya ta nunawa Abra ta ce. "Kwashe waÉ—annan kayan ki je ki wanke su tass yanzun nan, akwai sabulu da omo a cikinsu."

Abra ta kalli kayan ta kalli mahaifiyarta, ta ce. "Mami ba zan iya ba wallahi, sun mini nauy..."

Ba ta ƙarasa Maganar ba Na'ima ta ɗauke ta da wani gigitaccen mari.

"Dan kaza_kazanki in ce ki yi abu ki ce mun a'a? Wato kin fara riƙa ko? ina magana kina musa mun saboda kin raina Ni, kina ganin kin girma yanzu kanmu ɗaya."

Abra dake dafe da kuncinta tana hawaye ta ce. "Ki yi haƙuri Mami, zan yi."

"Kar ma ki yi, yanzu in saka ki tsallen kwado a gidan nan, ba ke mayya ba, kin nace sai kin zauna, wahala yanzu kika fara shan ta a gidan nan, kaÉ—an ma kika gani." Abra da ba fahimtar abun da take cewa ta yi ba saboda gigitar marin da ta sha, ta sunkuci bedsheets É—in ta nufi bakin tap.

Tana kuka sosai ta tara ruwa a cikin bucket ta fara wankin. Har kusan Magriba ba ta gama ba, sai gurza su take yi da sabulu amma manjan ya ƙi fita, ga shi zanin gadon ya ƙara nauyi saboda ruwan da ya sha, ta rasa ma ta yaya za ta jujjuya shi ta wanke ko'ina, gashi abu ba guda ɗaya ba har uku. Hannayenta kamar ba'a jikinta suke ba saboda ciwon da suke mata, bayanta ya ƙame saboda sunkuyo, haka ma wuyanta, ga yunwa dake addabar cikinta. Matsalar kuma ita ba iya wanki sosai ta yi ba tunda ba sa yi, daga socks sai undies ɗinta kawai take wankewa, suna da masu yi musu wanki a gidan.

Bayan su Salman sun kai Hajiya Maryam gida ta dage sai ya shiga ciki ya karɓi saƙon, ba dan son ransa ba ya bi bayanta. Ta zaunar da shi a parlour ta ce bari ta shiga ɗaki ta ɗauko masa, ta yi kusan mintuna talatin sannan ta fito, Salman har ya gaji da jira.

Ta zauna akan kujera ta ce. "Salman na duba ban ga saƙon da zan baka ba, amma bari na yi waya yanzu a kawo wani sai na baka ka, ka kai mata." Cikin ƙosawa Salman ya ce. "Bari kawai mu koma Aunty, wani lokacin na zo na karɓar mata, yanzu lokacin islamiyya ya kusa." Hajiya Maryam ta ce. "Ka ɗan jira dai, yanzu fa za'a kawo, Mamanka tana buƙatar saƙon yanzu_yanzu shi yasa." Bai ƙara cewa komai ba, amma kallo ɗaya zaka yi masa ka san bai so hakan ba, Hajiya Maryam ta tashi ta kawo masa drinks da snaks.

Wasa_wasa har ƙarfe uku ba'a kawo saƙon ba, sai ƙarairayi Hajiya Maryam take yi masa, ta ce mai kawo saƙon ne Motarsa ta samu matsala, amma ya kusa ƙarasowa. Ganin la'asar ta kusa Salman ya ce zai tafi gida, sai Hajiya Maryam ta kira Na'ima ta sanar mata, Na'ima ta ce ta ba wa Salman wayar, yana karɓa ta balbale shi da faɗa, ta ce kuma ko dare zai kai ya jira ya karɓar matar saƙon. Sai shida na yamma saura aka kawo saƙon aka ba shi suka taho gida.

Sai da Na'ima ta ji shigowar Motar su Salman gidan sannan ta fito bakin tap É—in cikin sauri, tana zuwa ta hand'aka Abra gefe ta ce. "Makirar yarinya, tun É—azu Uwar me kika zauna baki gama ba? Sai ki wuce mu tafi ciki."

Ba ta ce komai ba, dan idan ta ce za ta yi magana kuka ne zai kufce mata. Mami ta tasa ta a gaba suka shiga ciki, saboda gudun kar Salman ya zo ya tarar da ita a gurin ya sanar da mahaifinsa.

Kamar za ta faɗi haka take jin kanta, daƙyar take iya taka ƙafuwanta, haka ta daure ta ƙarasa ta shige ɗakinta ta faɗa kan gado tare da sakin wani marayan kuka, ko'ina a jikinta ciwo yake mata, amma ita ba wannan ne ya fi damun ta ba, tsanar da mahaifiyarta take nuna mata ya fi komai damun ta, a kodayaushe cikin tambayar kanta dalilin da yasa take mata hakan take.

Bayan Salman ya shigo ya ba wa Nai'ma saƙon sai ya wuce kitchen ya ɗebi abinci ya ci, saboda yunwar da yake ji, dan ƙin cin komai ya yi a gidan Hajiya Maryam tsabar takaici. Yana Allah_Allah ya gama cin abincin ya je ya ga Yayarsa dan ba ƙaramin kewar ta ya yi ba yau, amma kafin ya gama aka kira Sallah, hakan ya sa yana gamawa ya wuce masallaci. Da ya dawo Na'ima ta tare shi a bakin ƙofa ta aike shi ya kai mata saƙo, bai dawo ba sai bayan isha'i, a lokacin kuma Abra ta gama cin kukanta bacci ɗauke ta, hakan ya sa ba su haɗu ba sai washegari.
Chapter 27 · 0% Book details