← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 145

Sashe 48

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wannan kallon fa? Mu je in ka gama shiryawa, dama kai nake jira."

"Kin yi kyau sosai kamar na sace ki." Ya faÉ—a cikin siririyar murya.

Tana murmurshi ta ce. "In ka sace ni Salman ka kai ni ina?"

"Gidana." Ya ba ta amsa cikin confidence.

Jinjina kai kawai ta yi ba tare da tunanin komai akan maganar tasa ba, ta É—auki jakarta tana shirin fita Salman ya ce. "Where is your facemask?"

"Yau ba zan saka ba gaskiya, damu na yake yi."

Dan haɗe rai ya yi ya ce. "Ki saka, yana ina in ɗauko miki." Cikin shagwaɓa ta ce. "Ka fiya takura Faris, don Allah ka ƙyale ni." Bai kula ta ba ya janyo drawer inda ya san tana ajiyewa ya ɗauko sabo ya miƙa mata. Da farko ƙin karɓa ta yi, sai da ta ga kamar ransa ya ɓaci sannan ta karɓa, cikin marairaicewa ta ce. "Ka yi haƙuri Bro zan saka." Ɗauke kai ya yi alamun he is angry with her.

"Zan saka fa, Please kar ka yi fushi, ka san bana iya jurar fushinka." Ta yi maganar kamar za ta yi kuka. Sakin fuskarsa ya yi ya ce. "Ya wuce cry cry Baby, kawo in saka miki ma da kaina, sai ya fi yin kyau." Ba ta yi musu ba ta miƙa masa. Idanunsa a cikin nata yana narkar da su ya saka mata, bayan ya gama ya kashe mata ido ɗaya tare da sakar mata wani tattausan murmushi. Turo baki ta yi ta ja karan hancinsa da ƙarfi, ta ce. "Gashi nan ka lalata mini rolling ɗina."

"I'm sorry the best among the best." Ya faÉ—a cikin kulawa.

Na'ima ce ta turo ƙofar ɗakin ta shigo, cikin faɗa ta ce. "Ba za ku makarantar ba ne? Kun tsaya kuna shiririta ko? Tun ɗazu driver yana jiran ku."

"Ga mu nan fa Mami." Cewar Salman.

Harararar shi ta yi ba ta ce komai ba ta juya ta fita.

Littafin nan na kuɗi ne ₦300 NE
Via 0116886423  Sulaiman Na'ima s union Bank. Idan katin waya ne mtn na 500 idan transfer ne ɗari uku kacal.

Evidence of payment 07063065680 ko 09047871750.

Kamar kowacce Monday yau ma around 12 su Abra suka tashi, ta zauna a inda ta saba jiran Salman tana tsimayin shi. Shiru-shiru har 1 ta wuce bai zo ba, wata irin yunwa Abra ta ji tana ƙwaƙular hanjin cikinta. Cikin ƙosawa da zaman gurin ta ɗauko wayarta ta kira shi, har 3 missed call ta yi masa amma bai ɗaga ba. Miƙewa ta yi dan a yanda take jin yunwa ba za ta iya jiran har ya zo ba tare da ta ci abinci ba, Cafeteria ta nufa direct cikin tafiyarta mai tattare da nutsuwa da ɗaukar hankali.

Bayan ta zauna ta yi order'n abun da take so ta ɗauko wayarta ta fara latsawa kafin a kawo mata. Haka kawai ta ji ta a takure tunda ta zauna a gurin, gyara mask ɗin fuskarta ta yi, ya rufe mata har saman hancinta, kyawawan idanunta ne kawai a waje. Duk da haka ba ta ji ta daidai ba, ɗago kanta ta yi a hankali tana kallon mutanen gurin, Cafeterian da ɗan jama'a amma kowa sabgar gabansa yake yi. Duk yadda ta so daurewa amma ta kasa, wani irin ido mai kaifi ta ji yana yawo a cikin jikinta alamun akwai wanda yake kallon ta. Slowly ta juyar da kanta gefe, lokaci ɗaya wani irin daddaɗan ƙamshi mai saukar da nutsuwar zuci ya ziyarci hancinta, ba ta san lokacin da ta lumshe idonta ta buɗe ba, ƙamshin ya yi mata kamar ta taɓa jin shi. Wata irin faɗuwar gaba ce ta ziyarce ta, lokacin da ta tsinci idanunta a cikin mutumin da ba ta taɓa tunanin sake ganin shi ba, ta ma manta da shi gabaɗaya a cikin rayuwarta. Cikin sakanni ƙwaƙwalwarta ta tuno mata inda take jin ƙamshinsa, a jikin i.d card ɗinta ne, tun ranar da ya ba ta har yau ƙamshinsa yana nan manne a jikinsa. Sassanyar ajiyar zuciya ta sauke tare da saurin janye idanunta daga cikin nasa, wani irin abu ta ji yana yi mata yawo a jinin jikinta, gabaɗaya sai ta rasa nutsuwar zuciyarta ba tare da ta san dalili ba. Juyar da kanta ta yi daga ɓarin da yake, cikin ƙoƙarin daidaita nutsuwarta gudun kar a gane yanayin da take ciki. Wayarta dake hannunta ce ta fara vibrate, dubawa ta yi ta ga Salman ne yake kiran ta.

Jikinta ne ya hau rawa, ta kasa É—aukar wayar, saboda wanda ta gani ya ja kujerar gabanta ya zauna.

Kamar kullum, yau ma kasa ɗaga idanunta tayi ta kalleshi, sai wani irin bugu da zuciyarta keyi, tamkar zata tsaga ƙirjinta ta fito.

Dubansa ya kai kan screen É—in wayarta, yaga sunan Faris akan screen É—in.

Ɗan taɓe baki yayi, a daidai lokacin kuma aka kawo mata Abincin da tayi order, aka ajiye a gabanta.

Sai dai haryanzu ta kasa É—ago kanta, sai wasa da take da yatsun hannunta.

"Eat your food, i have something to discuss with you" yai Maganar yana tura mata plate É—in Abincin gabanta.

Kamar gunki haka Abra ta zama, gashi da ƙyar take numfashi, saboda tsoro ga uban facemask a fuskarta, gefe ga Salman na ta rangaɗa mata kira, ba ƙaƙƙautawa.

"I said you should eat your food, zamu yi magana sauri nake".

ÆŠago fararen idanunta tayi ta kalle shi, karaf ta sanya idanunta cikin nasa, saurin janye nata ta yi daga nasa.
Yayin da shi kuma ya cigaba da kallon ta yana nazartar ta.

Ya É—an fesar da iskar bakinsa ya ce "Well, tun da ba zaki ci Abincin ba, ni bari inyi abunda ya kawo ni, ina da abun yi."

Abra a ranta ta ce "Ikon Allah".

"I am Sp Adnan Aliyu Matawalle, so na san maybe na takura miki, saboda yawan bibiyar ki da nake yi. So ni ba yaro ne ƙarami, ba shiririta ce ta kawo ni gurinki ba. Amm ina tunanin ina son mu kasance ƙarƙashin inuwa guda dake, duk da bai kamata in tunkare ki kai tsaye in sanar da ke ba, sai na nemi iznin mahaifinki, ina son zan Aure ki ne, idan ba damuwa ina son ki bani Address ɗin gidanku, zan zo".

Zaro ido ta yi, tare da jin wata mummunar faÉ—uwar gaba, ta ina zata fara kai shi gidansu? Tukuna ma haka ake neman Aure ba soyayya ba komai, sai kace dole?".

"Kin yi shiru"

In a cracking voice ta ce "Ni karatu zan yi, Abbinmu zai mini faÉ—a".

"Kina nufin ba zaki yi Aure ba kenan?".

"Ni dai gaskiya Abbi zai mini faÉ—a".

"Ai Abbin naki zan fara samu, ni zan same shi".

Shiru Abra ta yi, ba ta sake cewa komai ba.

"Bana son ina magana ayi banza da ni, ki bani Address É—in, ina sauri zan koma Kaduna ne".

Shiru ta kuma yi, ba tace komai ba.

Kallon wayarta dake sake vibrating ya yi, ya miƙe tsaye ya sa hannu ya ɗau wayar da ID card ɗinta, ya watsa su a aljihunsa yace "Idan kin shirya, kya iya nemana, sai ki karɓi wayarki"

"Dan Allah ka bani wayata" Banza yai mata ya nufi hanyar fita daga gurin.

Miƙewa ta yi domin ta bishi, tana bin shi tana masa magiya, amma ko waiwayowa bai yi ba, ya buɗe motarsa ya shige, ya ja ya bar gurin.

Abra ji tai kamar ta É—ora hannu a ka ta kurma ihu, ita yanzu ina zata sake ganinsa? Gashi ta ji yace Kaduna zai tafi.

A hankali tace "Wayyo Allah wayata, me zance a gida?".

Littafin nan na kuɗi ne ₦300 NE
Via 0116886423  Sulaiman Na'ima s union Bank. Idan katin waya ne mtn na 500 idan transfer ne ɗari uku kacal.

Evidence of payment 07063065680 ko 09047871750.
[10/1, 2:40 PM] Abk: A gigice Baby ta cillar da jakar hannunta, cikin waro ido ta kurma wani uban ihu tare da ficewa daga ɗakin hotel ɗin a ruɗe. Ƙarasawa Janna ta yi ta shiga girgiza ƙafar Ihsan cikin kuka da tsananin tashin hankali.

ÆŠaya daga cikin ma'aikatan hotel É—in ne ya hawo sama da sauri jin kururuwar Baby.

"Hey, Lafiya kike mana wannan kwakwazon?"

Kasa magana Baby ta yi, nuna masa ɗakin kawai take yi da hannu tare da toshe bakinta. Shiga ɗakin ya yi cikin sauri, cak ya tsaya tare da dafe ƙirjinsa cikin firgici.

"Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un!" Abun da ya furta kenan a fili idanunsa akan gawar Ihsan dake kwance cikin jini malel-male. Da sauri ya juya ya fita ya je ya sanar da Manager na hotel É—in abun da yake faruwa.

After some minutes
Su Janna ne zaune a police station mafi kusa da hotel É—in, idanuwansu sun yi luhu-luhu alamun sun ci kuka sun gode Allah, sai zazzare idanuwa suke yi cikin firgici.

D.p.o dake bin su da kallo ɗaya bayan ɗaya ya dubi wani jami'i ya ba shi  umarnin ya shigar da Janna cikin cell, kuka ta fara tare da yi masa magiya tana ba shi haƙuri, tsawa ya daka mata wanda ta sa su duka suka razana, ba shiri ta yi shiru ta shiga jujjuya kai. Tasa ƙeyarta jami'in ya yi har cikin cell.

"Ki nutsu, tambayoyi zan miki, kuma ki faɗa mini gaskiyar abin da kika sani, domin idan ma kin mini ƙarya zan gano daga baya, kuma hakan ba zai haifar miki da ɗa mai ido ba." Cewar D.p.o yana kallon Baby da jikinta ke tsuma.

"In...insha Allahu zan faɗa maka gaskiya yallaɓai."

"Good." Ya faÉ—a cikin gyaÉ—a kai.

"Mene ne alaƙarki da wacce aka kashe?"

"Ƙawata ce."

Jinjina kai ya yi ya ce. "Tsawon wane lokaci kuka É—auka tare? Kuma a ina kuka haÉ—u?"

"4 Years back, a makaranta muka haÉ—u, A.b.u Zaria, course É—inmu É—aya da ita."

"Okay, shi ne aka haÉ—a baki dake kenan aka kashe ta?"

Cikin kuka Baby ta ce. "Wallahi ba haka ba ne Yallaɓai, ba ni da masaniya akan kisan Ihsan, ta yaya ma za a haɗa baki da ni a kashe ta? Ƙawata ce fa." D.p.o ya ce. "Ku ƴan wanne gari ne?"

"Dukanmu Æ´an Kaduna state ne."

"Kaduna? Amma me ya kawo ku Abuja?"

Shiru Baby ta yi ta fara sosa kanta tana rarraba idanuwa.
Chapter 48 · 0% Book details