← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 145

Sashe 63

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kai mijina ne, Faris kuma jinina ne, the only Brother i have, ni ji nake Kamar in fasa Auren nan".

ÆŠan shiru Adnan yayi ya ce "Baby kin dena sona kenan?".

"A'a ina sonka, amma bana son in rasa Faris É—ina".

"To shikenan, ki kwantar da hankalinki, kin ji Babyna ba in da Faris za shi ya barki, ai ni in cewa ki kai a gidana a ginawa Faris É—aki, ku tare a tare ba matsala" yayi Maganar cikin sigar rarrashi.

Adnan da shi aka wuni a Asibiti, Ana jinya, Su Ammi na ta yabawa kyawu da nutsuwar Adnan, a matsayin siriki.

Abra sai tambaya take ina Faris, amma ba wanda ya bata wata gamshashiyar amsa, ta kira wayarsa amma shiru ba ta shiga.

Bayan la'asar aka sallami Abra, Sai da Adnan ya rakasu har gida, wanda a nan ne Abbi ya sanar masa da larurar Abra, na rashin ji sosai sai da hearin aid, da kuma halin da take shiga idan ta shiga firgici da damuwa.
Adnan ya nunawa Abbi babu matsala, A nan Adnan ya sanarwa da Abbi Kaduna zai kai Abra, a nan Abbi ya ce bai amince ba, ba ta da kowa a Kaduna, kuma ga batun karatunta, kasancewar su Shureim ma suna gidan, su suka yi tausar Abbi, sun nuna masa aure ba in da baya kai mace, kuma sai a mata transfer, ko ta sake fresh tun da karatun ba nisa tayi ba.

Ƙarfe takwas na dare, Abra ta ɗaga hankalin kowa a gidan, a kan ina Faris ɗinta, ta je ɗakinsa baya nan.

Abba ya zaunar da Abra ya ce "Abra, ni mahaifinku ne, ba zamu taɓa zaɓa muku abunda zai cutar da ku ba, Faris jirginsa ya tashi ƙarfe sha biyu na rana, yanzu haka ya kusa China!!!

LITTAFIN RUƊI NE ₦300 NE
Via 0116886423 Sulaiman Na'ima s union Bank. Idan katin waya ne mtn na 500 idan transfer ne É—ari uku kacal.

Evidence of payment 07063065680 ko 09047871750
[10/6, 5:01 PM] Abk: Kallon Abbi kawai Abra take yi kamar ba ta fahimci me ya ce ba, idanunta duka a waje cikin kuka ta ce. "Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un, why Abbi, me ya sa za ku nesanta ni da jinin jikina, Abbi dan Allah ka dawo da shi, ba zan iya rayuwa babu Salman a kusa da ni ba." Cikin rarrashi Abbi ya ce. "I'm sorry Daughter, na san dole ki ji babu daɗi, amma haƙuri zaki yi, ni ma ba son raina ba ne hakan." Kuka ta fashe da shi tare da faɗin. "Amma Abbi me ya sa ya tafi ba mu yi sallama ba? Me ya sa bai zo na gan shi ba?"

"Ya zo da safe kina bacci." Abbi ya yi maganar tare da kamo hannunta, za ta kuma magana ya hana ta da faɗin. "Just pray for him Daughter, shi ne kawai soyayyar da zaki nuna masa, ki bar wannan koke-koken kin ga baki da lafiya, kar ki ƙarawa kanki wani ciwon." Numfashi ta sauke mai zafi tare da miƙewa ba tare da ta ce komai ba, ɗakinta ta shiga ta faɗa kan gado ta shiga raira kuka mai tsuma zuciya. 'Shikenan Salman ya tafi? Ya yi nesa da ganin ta? Anya za ta iya rayuwa mai tsayi ba tare da Salman ba? Faris ɗinta mai share mata hawaye akodayaushe, mai fifita farincikinta akan nasa. Wata irin kewar shi ta ji tana nuƙurƙusar zuciyarta.

Kuka sosai Abra ta yi akan tafiyar Salman, tunda ta shiga ɗaki ba ta fito ba har bayan isha'i, Sallah ce kawai take ɗaga ta, ita ma da ƙyar take iya tashi ta yi saboda wani azababben ciwon kai da yake damun ta, ji take kamar kan nata zai tsage gida biyu. Tana jin wayarta na ta vibrate amma ba ta kula ba, duk da ta san Adnan ne yake kiran ta.

Hajiya Na'ima ce zaune a gefen Khamal cikin farinciki, zuciyarta fess take jin ta yau, tamkar wadda aka yiwa bushara da wani babban albishir. Kallon ta Khamal ya yi na wasu sakanni cikin murmurshi ya ce. "Wai yau nishaɗin me kike yi ne Wifey? Na ga kamar ma ko kewar ɗan gaban goshin naki ba kya yi?" Yalwataccen murmushi ta saki ta ce. "Ai ko da bakina na faɗa maka ban yi kewar Salman ba na san ba za ka yarda ba My Man, kawai ina ɓoyewa ne saboda ban san na damu kaina akan abin da ya zama dole, nishaɗin da nake yi kuma na kasancewa tare da kai ne Mijina." Ta ƙarashe maganar tare da kashe masa ido. Murmushi Khamal ya yi ya ce. "Bayan wannan kamar akwai wani abun a ranki, ki faɗa mini mana sai na taya ki farincikin."

"Babu komai, idan ma da akwai bai wuce na zumuÉ—in ganin ranar Auren Daughter ba."

"Uhm, saboda kin kusa zama surika ko?"

"Suruka kuma ta nawa? sai dai ka ce saboda na kusa zama granny."

Murmurshi suka yi a tare, duban time Abbi ya yi ya ce. "Har 9 ta kusa amma Daughter ba ta fito ba? Allah ya sa ba jikin nata ba ne?" Taɓe baki Na'ima ta yi ta ce. "Ko dai sakarcin nata ne ya motsa ba, na san yanzu tana can tana ta aikin kuka saboda tafiyar Salman."

"Kin ga lefinta dan ta damu? Ni kaina sai bayan ya tafin kuma jikina ya yi sanyi, na san tsananin shaƙuwar yaran nan, ba ƙaramar damuwa za su shiga da rashin juna ba."

"Ai gara su saba, tunda ko ba su rabu ba yanzu za su rabu lokacin da za ta yi aure, bari na je na dubo ta." Na'ima ta faɗi haka tare da miƙewa.

"Abra! Abra."

A hankali ta buɗe idanunta da suka gaji da tsiyayar da hawaye tare da juya kanta da ƙyar ta dubi Nai'ma. Cikin raunin murya ta ce. "Mami Faris...."

"Shiiiii! kar ki ishe ni da wani zancen Faris, ki tashi ki ci abinci ki sha magungunanki."

"Bakina ɗaci Mami, ba zan iya cin komai ba, Faris kawai nake son gani, dan Allah Mami ki lallaɓa Abbi ya dawo mini da ɗan'uwana kusa da ni." Ta yi maganar wasu hawaye masu ɗumi na kwaranyo daga cikin idonta. Cikin takaici Mami ta ce. "Sai dai nai uban lallaɓa Abbi, yarinya sai masifar tsiya, ina murna hankalina ya fara kwanciya kina ƙoƙarin tayar mini da shi, saboda wannan damuwar da kika yi har ya fara cewa jikinsa ya yi sanyi da ma bai tura shi karatun ba, nan gaba kuma na san zai iya cewa zai dawo da shi, tunda ba ya son ganin ki cikin damuwa. Wallahi idan baki bar koke-koken banzan nan ba sai na saɓar miki, ki tashi ki je ki wanke fuskarki mu tafi parlour ki ci abinci, saura kuma idan kin je ki cigaba da nuna wannan damuwar, ni da ke ne."

Cikin dauriya Abra ta tashi ta shiga toilet, Na'ima ta bi ta da harara. Sai da ta sake yin wani kukan sannan wanke fuskarta ta fito.

Sosai Abbi ya dinga lallaɓa Abra tare da ba ta baki, dan duk da ta ɓoye damurta amma kallo ɗaya ya yi mata ya san tana cikin damuwa. Ya sanar mata Salman ya kira ya ce ya sauka lafiya, lokacin tana ɗaki. Da sauri ta ce. "Abbi ba ni numbern da ya kira in kira shi."

"Ba numbernsa ba ce ara ya yi, sai gobe idan Allah ya kai mu zai siya nasa sim É—in, na san kuma ke zai fara kira da shi." Abbi ya ba ta amsa cikin murmurshi.

Murmushin yaƙe ta yi ba ta ce komai ba ta cigaba da cin abincin dake gabanta, wanda take jin shi tamkar maɗaciya a bakinta, da ƙyar take iya taunawa ta haɗiye. Kallon seat ɗin da Salman yake yawan zama ta yi idan za su ci abinci, ƙwalla ce ta tarar mata a ido, ƙoƙarin mayar da ita ta yi tare da lumshe idanunta, can ƙasan mak'oshi ta ce. "I'm missing you Bloody, yaushe zaka dawo gare ni?"

Adnan ne zaune akan two seater a guest parlour'n gidan Fayyad, hankalinsa gabaÉ—aya yana kan wayarsa yana tura wa Abra text, na k'auna da irin missing É—inta da ya yi daga yamma zuwa dare da bai ji muryarta ba, sai tarin addu'oi da fatan samun lafiya. Fayyad dake kallon shi ya yi murmurshi ya ce. "Thank God, yau Allah ya nuna mini wannan ranar, kamar a mafarki sai ga Adnan a cikin soyayya dumu-dumu." Murmurshi Adnan ya yi bai ce komai ba.

Gyara zama Fayyad ya yi ya ce. "Ya kamata zuwa yanzu a ce mun fara shirye-shiryen abubuwan da za a yi a bikin nan fa, na ga kai ta soyayyar ka kawai kake, kuma ga lokaci yana ta motsowa."

"Shirye-shirye like how?"

"Su dinner da sauransu."

"No need, É—aurin Aure kawai za a yi a kawo mini matata."

Hararar shi Fayyad ya yi ya ce. "Wallahi ba ka isa ba, dole mu warwasa." With serious Adnan ya ce. "Sai dai ku warwasa ku kaɗai, amma babu wani abu da zan yi, kawai matata ta yi kwalliya a gama kalle mini ita, a yi ta mata pictures ana ɗorawa a media kowane kare da biri ya gani, ba zai yiyu ba gaskiya." Murmurshi Fayyad ya yi ya ce. "Mayar da wuƙar Baban kishi, mu duk da aka kalle namu matan ai ba ma son su." Ɗage kafaɗa Adnan ya yi bai kuma magana ba.

Sai after 10 na dare sannan Abra ta kira Adnan, time ɗin ya koma masaukinsa fitowar shi kenan daga wanka ya ji wayarsa na ƙara, with special sound ɗin da ya saka wa Numbern Abra. Cike da zaƙuwa da son jin muryarta ya ɗaga kiran.

"Matata!" Ya faÉ—a cikin tsantsar k'auna.

A hankali ta ce. "Na'am." Ajiyar zuciya ya sauke ya ce. "I missed you Baby, ya jikin naki?"

"Alhamdulillah, na ji sauƙi."

"Are You sure?"

Gyaɗa masa kai kawai ta yi, saboda da ƙyar take iya magana.

"Ya na ji muryarki haka kuma? Ko dai jikin ne Sweetheart?" Ya yi maganar cikin kulawa.

Ya sosa mata inda yake mata ƙaiƙayi, hakan ya sa ta fashe masa da kuka. A rud'e ya ce. "Subhanallahi, Angel what happened? Are you okay?" Cikin kuka ta ce. "Faris ya tafi China."
Chapter 63 · 0% Book details