← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 145

Sashe 56

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"I miss your fume my cuty" tura baki tayi kamar tana gabansa tace "ba zan reply ba, bayan kayi mini tsawa É—azu".

General Ibrahim kuwa kamar jira akeyi, shedu suka dinga fitowa a kansa, a kan zagon ƙasar da ya dinga yiwa harkar tsaro lokacin yana bakin aiki.
Major Khamal Khamis, zai iya cewa ya fi kowa farincikin wannan kame da akayi, dan ya daɗe da sanin da hannun General Ibrahim a ayyukan ta'addanci, sai dai babu wata ƙwaƙƙwarar hujja da ze iya bayyanawa, wadda za ta sanya a kama General Ibrahim ɗin da laifi kai tsaye.
Aka same shi da badaƙalar kuɗin siyan makamai, a gwamnatin baya, tare da wasu manya -manyan ƙasa, da wasu ƙusoshin gwamnatin da ta gabata, abun takaici kuma sune da a cikin Gwamnatin da take mulki.
Abun takaici, Manyan mutane ne, da al'umma suke yiwa kallon jagorori, kuma madubi, wanda suka saka ran samun sassauci daga gare su, ashe sune suka maida harkar tsaro, harkar kasuwancinsu. Suka yi sanadiyar tarwatsewar al'umma da dama da aka daÉ—e ana ginawa.
Tofin Allah tsine da General Ibrahim da iyayen gidansa, da kuma yaransa suka dinga samu kuwa ba a Magana, tabbas ya ci amanar ƙasa, mussaman da a dalilinsa rayukan iya sojojin da suka salwanta ba adadi, ba'a ma kallon wancan laifin da ya aikata, ni lalalata da kuma kisan kai, tsabar Mamaki da takaicin taƙadirancinsa ya hana mutane magan, sai zuba ido domin suga, irin matakin da za'a ɗauka a kansu.

Sai magariba Salman ya dawo daga gurin ƙwallo, dan sai da yayi sallar magariba sannan ya dawo gida.

Sashen Mami ya wuce da kofin juice a hannunsa.

"Sai yanzu ka dawo?"

"Na tsaya nayi Salla ne Mami, baƙi mukayi a gidan ne? Naga guest room da kayan ciye-ciye, suwaye suka zo?".

"Abra ce tai baƙo".

Turus yayi yana kallon Mami yace "Wane irin baƙo kuma?".

Hajiya Na'ima tace "Ah, saurayi tayi, shine ya zo gurinta, kuma very soon zai zo yayi Maganar Aure".

"Impossible, akan me za'ai mata Aure? Idan har ina raye ba wanda zai auri Abra" yayi Maganar jijiyoyin kansa na miƙewa.

Na'ima ta ce "ba ka da hankali ne? Uban me za'ai da ita idan ba tayi Aure ba? Ai gara tai Auren ta bar mana gida, ko mahaifinka ya maida hankali sosai a kanka".

"Ba wanda zai Auri Abrah Mami? Abra tawa ce, Wallahi duk wanda ya kuma zuwa gidan nan da sunan yana sonta, sai na masa illa".

A fusace ta miƙe ta ce "Salman, ka san me kake faɗa kuwa? Me kake nufi da Abra taka ce?".

"Mami, let me voice out my secret to you, Wallahi Mami am in love with my sister, ina kishinta, Mami tun lokacin da kika gaya mini ba ke kika haifeta ba, na gane son da nake mata ba na 'yan uwanta bane kawai, Auren Abra nak.....  Marin da ta sauke masa ne, ya hana shi ƙarasa Maganar, ya dafe kuncinsa yana kallon Hajiya Na'ima.

"Baka isa ba Salman, Wallahi kayi kaɗan, ni zaka tonawa asiri, yarinyar ta girmeka da shekaru uku, kace mini ita ka ke so, kwata kwata shekarunka nawa zaka yi wani zancen soyayya, ko dan kana ganin ka haka da girman jiki?, yarinyar da ta zame mana alaƙaƙai nake neman maraba da ita.
Wato so kake ka tona mini Asiri, mahaifinka ya san na gaya maka ba ni na haifeta ba ko? Wai kai banda hauka irin na ka ka manta ubanku É—aya da ita? Karuwar babanka ce ta haifeta ta yaya za kuyi Aure?".

Girgiza kai Salman yayi yace "A'a Mami, Abbi ba ze taɓa aikata abunda kika faɗa ba, ina nan akan bakana Mami, Abra nake so, Ina sonta Sosai".

"Shut up Salman! Wato ba zaka dena wannan banzar Maganar ba ko? Gara yayi ya dawo in sanar masa, ayi a aurara da ita in ga ta tsiya, idan kuma shirya tona mini Asiri ka yi a gurin mahaifinka ga fili ga mai doki. Amma duk jarabarka Wallahi ba zaka auri yarinyar nan ba, dole ta auri wani ta bar gidan nan".

"Am sorry Mami, amma babban kuskuren da za'a aikata shine a aurawa Angel wani ba ni ba, zan iya aikata duk abunda zuciyata ta raya mini, dan cinma burina, she's mine" ya faɗa tare da nuna ƙirjinsa da yatsa, daga nan ya fice daga ɗakin.

Wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke ta ce "tirƙashi, lallai Salman ba ka da hankali, ba za ka janyo mini sakiyar da babu ruwa ba, dole in maganinku gaba ɗaya.

Major Khamal kuwa, cike da farin ciki, gefe guda kuma baƙin ciki ya dawo Kaduna, dan ji yake ko ba duka, an samo lagon rashin tsaron da ya addabi ƙasar mu, daga gefe yana sake jinjina tare da baƙi cikin samun bara gurbi a cikin rundunar tsaro.

Bayan Adnan ya sauka a Kaduna, har dare Abra ba ta neme shi ba, sai shi ya nemeta duk da kuwa yadda tai kewarsa.

Ita Abra babban abun da ya dameta rashin ganin Faris, taje ɗakinsa ta tarar ya rufe ƙofa, dan haka ta haƙura ta koma ɗakinta.

Tana zuwa ta tarar da kiran Adnan na shigowa wayar ta ta, ta sa hannu ta É—au wayar, tare da kwanciya akan lafiyayyen gadonta.

"Angel shine ko ki neme ni, balle ki ji yana je gida ko?".

Tace "Na neme ka mana"

"A ina?".

"Addu'a na yi maka, Allah ya kaika lafiya".

"Na ji, na kuma gode, amma ai Yakamata ki kirani ki ji ko naje lafiya".

"Ba kai ne kai mini tsawa ba kafin ka tafi".

Adnan yayi dariya yace "Fushi kike kenan? Ai idan nace bana son abu, bana buƙatar sake maimaitawa, amma ke se kiyi biris, shiyasa nai miki tsawa, amma na dena kinji My wife".

Tayi ajiyar zuciya tace "to ya kaje gida?".

"Ba na so, tun da sai da na roƙa".

"To nima ban haƙura ba da kai mini tsawa".

Abra ba dai shiririta ba, ya faɗa a ransa, ya dinga janta da hira, har kusan ƙarfe goma na dare, sannan sukayi sallama.

Duk É—okin da Abra take idan Abbi zai dawo, a wannan karon sai ta shiga fargaba da zullumi, dan bata san ya zai É—auki Maganar Adnan ba idan Mami ta gaya masa.

Da daddare Hajiya Na'ima ta sami Major a É—akinsa, suna cikin hira ta ce "to kai fa 'yar ka magana ta É—akko".

"Wace Maganar kenan?".

"Ta zo ta sameni da wani batu, ta ce mini in sanar maka ita Aure ta ke so".

"What? Abran ce ta gaya miki haka?"

"Ƙwarai kuwa, tace mini Aure take so, dan ta kawon wanda take so ɗin har gidan nan ya zo jiya".

"Dan meyasa kika bari wani yazo mini gurin 'ya ta ba da izinina ba?".

Hajiya Na'ima tace 'ban gane ba, ta zo ta sameni da Magana, kuma sa ince mata a'a".

"Tambayar ki nake dan me wani zai zo mini gida gurin 'yata ba da izini na ba? Kuma ita Abran zan sameta, karatu za tayi ba Aure ba".

"Wai me kake nufi ne da yarinyar nan? Idan ba ai mata Aure yanzu ba sai Yaushe, kai da É—anka kun hana kowa ya zo gurinta da sunan yana son ta, wai ni ko kai ke son yarinyar nan ne?".

Major yayi murmushi yace "Ina son 'ya ta mana, amma kin manta ni ne ubanta, ko har kin manta 'yar da karuwa ta haifa mini ce?"

Hajiya Na'ima ta kwantar da murya, ganin yana nema ya maida Maganar wani na daban.

"Major dan Allah ka duba lamarin nan, yarinyar nan tum da har ta riga ta furta tana son Auren nan, ni banga dalilin da zai sa ka ce saita gama karatu ba sannan za'ai mata Aure, yarinyar nan Allah yayi mata kyau me É—aukar hankali, baka tunanin abunda ka iya faruwa a jami'ar da ka tuarata.
Shi kuwa Aure garkuwa ne ga 'ya mace, idan akai mata Aure zata samu wata kariya daga sharrin mazan jami'a da lalacewa".

"In kinga ɗa ya lalace a makaranta, to dama can lalataccen ne, amma ni 'ya ta ba lallatacciya bace, kuma ba gazawa nai da ɗaukar ɗawainiyarta ba, dan haka a ƙyalemini 'ya ta".

"Yanzu kana ganin lamarin nan ba abun dubawa ba ne? Ita fa da bakinta ta ce mini Auren ta ke so".

"Na'ima, ba zanwa Abra Aure yanzu ba, na gama Magana" yana faÉ—in haka, ya tashi ya bar mata É—akin.

Shiru ta yi tana tunanin, meye mafita al'amura na neman su kwaɓe mata, ga Salman na neman bijiro da wata Magana, ga mahaifinsa ya dage baze aurara da Abra yanzu ba, dole ta yi wani abu a kai, dan kar abunda ta ke gudu ya faru, wato Salman ya auri Abra.

Littafin nan na kuɗi ne ₦300 NE
Via 0116886423  Sulaiman Na'ima s union Bank. Idan katin waya ne mtn na 500 idan transfer ne ɗari uku kacal.

Evidence of payment 07063065680 ko 09047871750
[10/3, 2:40 PM] Abk: Miƙewa Na'ima ta yi ta nufi ɗakin Abra.

Tana kwance idanunta a lumshe cikin damuwa da fargabar yadda Abbinta zai karɓi maganar Adnan, saboda Adnan ya takura mata akan maganar Aure daga daren jiya zuwa safiyar yau, ya sanar mata har ya faɗa wa Abbansa ya ce Next week za su zo tambayar Auranta, ga rashin saka Salman a idonta, tun jiya kafin ya tafi Ball ba su ƙara haɗuwa ba, ta kikkira wayarsa kuma ba ya ɗauka, ga Mr unknown sai Text yake mata na magiyar yana son duk rintsi duk wuya kar ta rabu da shi, soon zai bayyana a gare ta.

"Abra! Abra! Abra!"

Ta tsinkayi muryar Mami a cikin kanta, a hankali ta buÉ—e idonta tare da tashi zaune cikin sanyin jiki. Zama Na'ima ta yi a gefenta ta ce. "Ke lafiya kike kuwa?"
Chapter 56 · 0% Book details