← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 145

Sashe 74

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Nayi kuskure, amma dan Allah kayi haƙuri kar ka kasheni" da Doctor ya ƙyale Meenal, bayan ta sha shaƙar da sai da ta kusa zuwa lahira.

Hall ya haɗu iya haɗuwa, Abra ta haɗe cikin wani danƙareren Material, kai da gani ka san ba duk jiki ba, sai jikin 'yar gata.
Adnan kuwa gaba ɗaya kishi ne ya mamaye masa zuciya, yadda kowa ke ɗaukar hoton matarsa a waya, shifa wannan taron bidi'ar dan anfi ƙarfinsa ne, amma da babu dalilin da zai sanya ayi wannan taron ana kallon matarsa.

MC ne ya kira Amarya, tare da umartar ta da taje ta taho da mamanta.
Cikin takun Abra na nutsuwa, taje gaban table ɗin da Hajiya Na'ima take, ta durƙusa ta kamo hannunta zuwa filin rawa.
MC ya ce "Ki kalli Mamanki, ki ce nata kin gode, kuma kina sonta"

Abra ta kama hannun Hajiya Na'ima, ta kalli idonta murya na rawa ta ce "Thank you very much Mamina, for all you did for me Bani da Abun da zance miki sai Allah ya baki Aljanna maɗaukaiya, and I love You Mamina" ta ƙarasa Maganar tana rungume Na'ima, tare da sakin wani irin kuka mai ban tausayi.
Nan dj ya saki waƙar Wayyo Allah mamana, Na'ima ma rungume Abran ta yi tana ɗan dukan bayanta alamar rarrashi. Yayin da ta ɓalle bakin jaka, ta dinga zubawa Abra kuɗi kamar ba gobe, ji take dama Abra 'yar ta ce ta halak, da shagalin da za tayi a bikin nan yafi haka.
Haka aka yi Dinner, 'yan uwa da abokan arziki, duk sun yi bajinta, ta hanyar liƙi da bada gudunmawa.

Abbi tuni ya sauka garin Kano tare da tasa tawagar, kasancewar bayan É—aurin Aure akwai reception na mussaman, da kuma parrate na sojoji, abunka da masu abu da abunsu.

A can birnin Sin kuwa, Salman ne zaune a wani katafaren ɗaki, a gaban madubi ya sanya hoton Abra a gaba, ya ƙura masa idanu, idan lissafinsa daidai ne, yau ne ake ɗaurawa Abra Aure, Abran da ya ƙallafa a rai, ya taso ya rayu da soyayyarta, a yau ta zama mallakin wani ba shi ba, ina ma Mami ba ta sanar masa Abra ba 'yar uwassa ba ce ta jini, da duk wannan al'amuran basu faru ba, gaba ɗaya tun da ya zo China ba ya jin daɗin garin, komai nasu daban kamar ba Normal Mutane ba, gashi ko turancin ma ba kowane ya iya ba a cikinsu, dan haka abubuwa suna masa wahala, duk da wai kafin su fara lectures, sai sunyi wata shida ana koya musu Yaren Chinese.

An ɗaura Auren Adnan da Abra, wanda dubban mutane suka sheda hakan, ɗaurin Auren da ya samu halartar manyan ƙasa daga ɓangarori daban-daban ciki har da Captain Faruk da aka tsinto Abra da shi.

Daidai gwargwado an yiwa Abra Nasiha mai ratsa zuciya game da rayuwar Aure, yayin da Granny ta ta Nasihar mai ɓaro_ɓaro ce ba rufi ba kunyar komai.

Da la'asar aka shirya Abra cikin wata dakakkiyar rantsatsiyar lafaya, Mami ta kaita gurin Abbi, yayi mata nasiha sosai tare da Adduoi da fatan shiga É—akin miji a sa'a.
Dangin Adnan sun zo da manyan motoci, domin É—aukar Amarayar su.

Sai dai Abra ta ƙanƙame Mami tana kuka, karo na farko a rayuwar Na'ima, tun da ta fara riƙon Abra, taji jikinta yayi sanyi, dan tun a gurin Dinner jiya Abran ta sa jikin Na'ima yin sanyi.
Abra ta ƙanƙame Na'ima tana faɗin "Mamina, a zaman mu idan na yi miki laifi ki yafe mini, Mami bana son barinki".

Anty Suwaiba ce cikin masifa ta ce "Wai ke bayinki ne mutanen da suka tsaya suna jiran ki, dalla ki fito ki wuce mu tafi"

A hankali Na'ima ta shafa bayan Abra ta ce "Na yafe miki Abra, Allah ya baku zaman lafiya, muje in rakaki bakin Mota".

"Mami to ke yaushe zaki zo?".

"Very soon" daga haka ta ja hannun Abra zuwa bakin mota. Da ƙyar Abra ta yadda ta shiga, tana kuka tana ɗagawa Mami hannu.

Anty Suwaiba ta ce "Ke Na'ima, wai me kike yi hakane kamar kin damu da tafiyar yarinyar nan? Allah ya raba ki da ƙwallon mangwaro kin huta da ƙuda, amma naga kamar kina cikin damuwa? Wai ni fa kamar ƙwalla nake gani a idanun ki".

Jiki a sanyaye Na'ima ta ce "Gaskiyar Husawa da suka ce, 'Sabo turken wawa' a zamana da yarinyar nan ban taɓa jin abunda na ji ba jiya da ta kalli idanuna tana mini Addu'a tare da jaddada soyayyarta a gareni, idanunta ɗauke da zallar soyayyar uwa da ɗa, duk da kwashe shekarun da nayi ina azabtar da ita, amma tana mini biyayya fiye da yadda ɗan da na durƙusa na haifa yake mini, ko ba komai da ina ganin gilmawar ta da ta Salman, amma Yanzu shi ya tafi, ita ma kuma haka".

"To shine me? Ke ba hutunki bane bama, ta je can ta ƙarata Allah ya tsare miki mijinki da ɗan ki".

Na'ima ta ce "Hakane, dama babban fatana kenan, ta bar mini gida, shekarun da mukayi Allah ya amfana, kawai dai kin san zuciya".

"Ke dalla can manta da ita".

Awanni uku cif, da magariba su Abra suka isa garin Kaduna, aka fara kaita gidan su Adnan, aka yi mata nasiha, suka bata kyaututtuka, sannan suka wuce da ita gidanta.

Tubarkallah Adnan ya ƙera mata gida na gani na faɗa, Abbi kuma da Hajiya Na'ima sun cika gidan da kaya na kerewa sa'a, Masha Allah gida yayi komai tsaf.

Wanda suka rako Abra daga Kano, suka koma gidansu Adnan su kwana a can, daga nan su koma Kano, Abra ji tayi Kamar ta tashi ta bisu, haka suka watse suka bar Abra.

Abra ta zauna jiran shigowar Ango, sai dai har ƙarfe goma sha ɗaya ba ango ba dalilinsa, tun Abra na jira har ta fara gajiya, tsoro ya fara kamata, ta takure a ƙuryar gado, gaba ɗaya tsoro ya baibayeta.
Abu kamar wasa har ƙarfe biyu na dare, Adnan be shigo ba, ta ɗauko wayarta domin ta kirashi amma wayarta ta ɗauke babu caji.
Rashin sanin abun yi ya sanya ta fara kuka.
Haka Abra ta kwana a zaune, sai É—an gyangyaÉ—i da ta dinga yi daga zaune a haka har Asuba tayi.

A tsorace ta lallaɓa ta shiga banɗakin da ke cikin ɗakin tayi alwala, ta gabatar da sallar Asubahi, ta koma gefe ta takure.

Mami 'yan biki sun watse, sai wanda ba'a rasa ba.
Tayi wanka tana ƙoƙarin shiryawa, ta ga wata takarda ta faɗo daga cikin wardrobe ɗin ta.
Ta sunkuya ta É—au takardar ta buÉ—e, rubutun Salman ta gani a jiki, hakan ya sanya ta sake gyara tsayuwarta ta fara karantawa.
*Assalamu alaikum warahmtullah. Ina fatan lokacin da saƙon nan zai riskeki kina cikin ƙoshin lafiya Mamina. Na san zakiyi mamakin ajiye miki wannan takarda da nayi, amma ba abun mamaki bane, duk da ba zan kira hukuncin da kika yanke a kaina kuskure ba, amma zan iya kiransa da shamaki da farinciki na, ta hanyar nisata ni da abu mai daraja da nake matuƙar ƙauna. Domin sake nesanta kaina da Abra kasancewar na san mallakin wani zata zama, ina mai sanar miki da cewa daga ranar da na bar Nigeria ba zan sake dawowa ba har Abad, dan muddin ina Nigeria, ruhina yana tare da Soyayar Abra, dan tabbatar da samun farincikinki da nutsuwar ki, ba zan sake dawowa Nigeria ba. Idan kuma kika yi ƙoƙarin tursasa sai na dawo, zan bar China in koma ba im da ba wanda ya sani. Ki huta lafiya Mamina, ki gaishe mini da Abra tare da yi mata fatan Alkhairi a rayuwar Aurenta. Salman Khamal Khamis*.

Littafin kuɗi ne,biya ₦300 via 0116886423 Sulaiman Na'ima s union Bank... Idan katin waya ne zaka Turo 500 shaidar biya 08081012143
[10/13, 11:29 AM] Abk: Mugun ganin da Abra ta yi, ya sanya ƙirjinta fara ɗa gawa zuciyarta tai mata nauyi. Rutse idanunta ta sakeyi tana ganin abin kamar almara, amma ta hana Zuciyarta gasgata abin da ta ke raya mata.

A hankali ta yi ƙasa da kanta ta shiga wasa da yatsun hannunta, jikinta duk rawa ya ke, ji ta ke kamar zuciyarta tai bindiga sbd fargaba. Juyawa Adnan ya yi tare da kallon budurwar ta ke tsaye a gefensa, cikin nutsuwa ya sakar mata wani kwantaccen Murmushi mai nakar da zuciyar ko wacce ƴar mace.
Fari ta yi masa da idanu tana girgiza ƙirji ganin hakan ya sanya Adnan, janye nasa idon ya lumshe kafin a hankali ya ce "My Surry" kashe murya wacce aka kira da Surry ta yi ta na shafa fuskar Adnan ta ce.

"Darling bee"
Hannunsa ya watsa yana ƙare mata kallo tare da ɗan matsawa kusa da ita he's trying to kiss her cheeks sai kuma ya ɗaga mata gira ya ce.
"Finally Bibina this is my house" "It's beautiful I like it but" hannunta ya kama ya ce "but what? Say it" rungomesa ta yi sosai ta ce "isn't ur house is our house okay" holding nata back yai ya ce "Oh! I almost frgt sbd ke ma na gina gidan".

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" sune kalaman da suka fita da ga cikin bakin Abra a wahale. Ta kasa fahimta, ta kuma kasa gane inda kalaman mijin nata ya dosa "My Surry? Bibina? Our house? What does that means?" Idanunta da suka sauya kala da ga farin da suke da shi zuwa launin jaa ta buɗe da ƙyar tare da zuba musu idanu.
Frm Head to toe ta ke kallon wacce aka kira da Surry, a ƙalla zasu iya age mate da Adnan idan ma zai girmeta sai da shekara ɗaya ko watanni, daurewa ta yi cikin sassauta muryarta tare da ɗauke damuwar da ke zuciyarta, but under her heart sunan Allah kawai ta ke kira, wasu har ƙwace mata suke.
Chapter 74 · 0% Book details