← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 145

Sashe 28

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Misalin ƙarfe sha ɗaya na safe bayan ta gama ayyukan gida wanda duk tare suka yi da Salman, suna yi yana ba ta labarin yanda ya yi missing ɗinta jiya tare da yi mata mitar ta yi bacci ba ta jira ya dawo ba, haƙuri ta ba shi ta ce masa kanta ne yake mata ciwo a lokacin, shi ya saka ta sha magani ta yi bacci.

Suna zaune a parlour suna hira da tsokanar juna kamar yadda suka saba cikin nishaÉ—i Na'ima ta shigo parlour'n. Fuskarta É—auke da fara'a ta cewa Salaman. "Son yau na cika maka burinka na nacin son driving da kake yi, jiya na saka an yi maka bucking a wani guri da ake koyarwa, yau zaka fara zuwa, sai ka tashi ka shirya ka tafi, direbanku zai kai ka.

Salman ya fasa ihu ya ce. "Wow, thank you Mamina, na ji daÉ—i sosai."

"Sai ka tashi ka tafi, kar su yi ta jiran ka."

Cikin murnar Salman ya miƙe ya ce, "Amma har da Yaya ko Mami?"

"Sai dai Kakan Yaya ba Yaya ba, tana macen zan yi asarar kuÉ—ina in biya mata ta koyi wata Mota, sai dai ta mutu ba ta iya ba."

Ɓata fuska ya yi bai ce komai ba, sam ba ya jin daɗin abun da Mami take yiwa Yayarsa.

Murmurshi Abra ta yi ta ce, "Congratulations Bro, Allah ya bayar da sa'a ya taimaka."

Murmurshin ya mayar mata ya ce, "Ina ƙwarewa ke zan fara kaiwa unguwa Yayata."

"To Allah ya nuna mana lokacin."

Ya amsa da Amin sannan ya fice bayan ya yi musu sallama. A rayuwar Salman yana son ya ga yana driving, tun da ya so ya koya amma Mami ta hana ta ce Ya yi ƙanƙanta sai ya ƙara girma.

Na'ima tana jin Motar su Salaman ta fita ta wurgawa Abra wani wulaƙantaccen kallo, cikin tsawa ta ce. "Tashi ki je ɗakina zaki ga labulaye a ƙasa ki ɗauka ki je ki wanke, saura yau ma ki zauna laƙai_laƙai irin na jiya, wallahi idan baki wanke su ba tass sai na lahira ya fi ki jin daɗi."

Jikinta a matuƙar sanyaye ta miƙe ta je ta kwaso labulayen, hannunta har yau bai daina yi mata raɗaɗi ba na dirzar zanin gadon da ta dinga yi jiya, ga jikinta ba wani jin daɗinsa take yi ba.

Jiya ta yi fashin islamiyya yau baza ta so ta kuma yi ba, hakan yasa cikin sauri ta jiƙa kayan a cikin ƙaton baho ta zauna ta fara wankin zuciyarta babu daɗi.

Ko 5 minutes ba ta yi da zama ba ta ji alamun ana kallon ta, juyawa ta yi suka yi ido huɗu da wanda ba ta taɓa tunanin ganin shi a wannan lokacin ba, sai da ta juyo ɗin ne kuma ƙamshinsa ya cika mata hanci.

LITTAFIN DARE DA DUHU, ₦300 NE KACAL, ZA KU TURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0116886423 Sulaiman Na'ima s union Bank.
KU TUNTUƁI WANNAN LAMBAR DAN TURA KATIN WAYA NA NAIRA 500 TA WANNAN 09047871750
DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU AKAN WANNAN LAMBAR 07063065780\09047871750
MUNGODE.
[9/30, 8:55 PM] Abk: *DARE DA DUHU*

_Brigh pens✍️_
Nimcyluv
Ayushercool
Zee Kumurya

                               P12

Domin samun complete litattafanmu, ku yi following É—in wannan accounts É—inkin a Arewabooks

https://arewabooks.com/chapter?id=6316f4af434cfeb9e7fe2949

https://arewabooks.com/u/nimcyluv
https://arewabooks.com/book?id=

Elegant online writers

LITTAFIN DARE DA DUHU, ₦300 NE KACAL, ZA KU TURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0116886423 Sulaiman Na'ima s union Bank.
KU TUNTUƁI WANNAN LAMBAR DAN TURA KATIN WAYA NA NAIRA 500 TA WANNAN 09047871750
DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU AKAN WANNAN LAMBAR 07063065780\09047871750
MUNGODE.

Salman ta gani a tsaye yana bin ta da kallon mamaki, cikin hanzari ya ƙara so in da take durƙushe, yana faɗin "Yaya, me kike haka a durƙushe?" Yana ƙarasowa ya kalli tulin labulayen da ke gabanta tana murzasu da ƙyar.

Salman yace "Yaya? Waye ya sa ki Wannan aikin haka?" A wannan karon kasa jurewa ta yi, ta fashe da kuka.

ÆŠagota Salman yai yana cewa "Am sorry, de na kukan gayamin waye ya saki Wannan aikin haka?".

Ta share hawayenta tace "labulayen É—akin Mami ne, da na guest room"

"To waye yace ki wanke?"

"Mami ce"

Salman yace "What? Mami kuma, duk almajiran da ke gidan nan, a rasa wanda za'a saka wannan aikin se ke? Ba ta ganin ko ƙwarin kirki ba ki da shi, kalle ki fa, ajiye kayan nan muje ciki" yai maganar yana jan hannunta.

Riƙe shi tai ta girgiza masa kai tace "No Faris, please ka zo ka tayani mu wanke, saboda ina son zuwa Islamiyya, kaga jiya ban je ba, kuma ana screening na saukar Alqur'ani".

"What, jiyan ma ba ki je Islamiyya ba, why?"

Abra tace "a'a mantawa nai, naje ai ya nake nufi"

Salman yace "kin ga wuce muje".

"Faris please, Mami ce fa ta sani, ni dai kawai ka tayani mu gama".

Banza yai mata ya cigaba da jan ta zuwa cikin Falo, Mami na zaune tana kallo tana kaɗa ƙafa, ta tsikaro ɗauri gaban goshi, tana danna remote.

Babu tsammani Hajiya Na'ima ta ɗaga kai, ta ga Salman riƙe da hannun Abra, sai da ta sha jinin jikinta amma ta maze tace "Ya na ga ka dawo?"

Salman be amsa mata Maganar ba yace "Mami, wai ke kika saka Yaya wankin wannan manyan labulayen?"

"Eh, ni ma sata ko ban isa bane?"

"Mami kin isa mana, amma kina ganin yana yinta ba ta da ƙwarin kirki, ni Yakamata ki saka in ma wankewar ne, ga lokacin islamiyya yayi".

"Sannu ubana ka gama? Nace ka gama?, Ba mace bace? Idan ban sata aiki ba sai yaushe gidan wani fa zata, tana da tabbacin in da zata zata samu masu wanke mata ne, shine ki ka kai masa ƙarata?, algunguma kin wuce kin ƙarasa wankin nan ko sai na zo na kakkarya ki a gurin nan, shegen ido Kamar Magen mayu" Jikin Abra a matuƙar sanyaye ta zare hannunta daga ma Salman tai waje.

"Haba Mami, dan Allah meyasa kikewa Yaya Abra haka?, a duniya ban taɓa ganin uwar da takewa ɗanta haka ba, kinga ba ta da cikakkiyar lafiya, dan Allah Mami kar abunda kike mata ya kuma illata lafiyarta"

A hasale tace "Ka rufen baki ko se na ta so kanka, uban me ma ya dawo da kai gidan nan, bayan ga in da na turaka?"

Ransa haÉ—e yace "lokacin Islamiyya ne yayi" yana gama faÉ—in haka ya bar Falon, in da Abra take ya koma, ya tarar da ita a zaune akan labulayen, tana ta uban kuka, farar fatar fuskarta tai jawur.

Be ce mata uffan ba, ya matsar da ita gefe, ya tattara labulayen wankesu tsaf, har ya kammala kuka take ba ta dena ba.
Se da ya gama wankin sannan yace "tashi muje ki ci Abinci ki shirya mu tafi Islamiyya". Jiki ba ƙwari ta bi bayan Salman, se dai a wannan karon Mami ta bar Falon.

Ɗakinta ta wuce, Salman kuma ya wuce ɗakinsa, dan ya yi shirin islamiyya, sai dai gaba ɗaya ransa babu daɗi, sai ƙoƙari yake ya gano dalilin da yasa Maminsu ba ta son Abra, Abunda take mata ya yi yawa, ya wuce ace kara ce ta ɗan fari, ƙiyayya ce kawai, to amma ya za'ai mutum ya haifi ɗa kuma ya dinga ƙin sa.

Haka ya dinga tunani daban daban a ransa, har ya kammala shirin makarantar.
Dining ya tafi dan cin Abincin rana, sedai Abra ta faɗo masa a ransa, ya san babu tabbacin ta ci Abincin, wata ƙila tana can tana laƙai laƙai koma kukan ta cigaba.

Ya miƙe da plate ɗin Abinci a hannunsa, ya nufi ɗakinta da sallama a bakinsa ya shiga, ya tarar da ita a zaune a gefen gado, ta saka uniform ɗin Islamiyya, se dai ta takure tana ta uban kuka.

Cikin damuwa Salman ya ajiye Plate ɗin Abincin akan dressing mirror, ya ƙarasa kusa da ita ya zauna, yace "Haba Abbis Fav, why? Dan Allah ki dena kukan nan haka ya isa".

"Faris, Meyasa Mami ba ta sona ne?" Tai maganar kamar za ta shiÉ—e.

Salman yace "tana sonki mana, kema ba kiga Abbi yafi sonki ba, nima tafi sona ne amma tana sonki kema"

Abra ta girgiza kai tace "No, she hates me, kai meyasa Abbi ba ya maka abunda take min? I so much Love my Mum, i have no one like her, ina son Mamina Faris, but why is she treating me like this? Ni aikin da take sani baya damuna, ta isa ta sani ne, amma meyasa take kyarata, ba ta son inje in da take? I so much Love her, dan Allah in laifi nai mata ka tayani bata haƙuri, amma dan Allah ta din ga sona nima"

Jikin Salman yai sanyi ƙalau, ji yai kamar ya taya Abran kuka, tabbas abunda Mami ke nuna mata ƙiyayya ce, amma shima ya rasa dalilin hakan.

Cikin hikima Salmn ya fara Magana "Haba Yaya, ke fa jaruma ce, kamar yau kika fara jin faɗan Mami, ai idan da sabo ya ci ace mun saba da wannan faɗan nata, watarn ma fa ba mu mu kai laifin ba, amma seta huce a kanmu, Yanzu ma karki raba ɗayan biyu, wani ne ya ɓata mata rai, let's forget about it, muci Abincin nan and hope kin yi shirin screening ɗin nan, dan shi ne na ƙarshe, ko ai sauka da kai ko kuma ka faɗi, ko kuma ai be kamata ma in tambaye ki ba, ku da kuke 'yan gaban goshin sheik Nurain, ai dole kiyi sauka" yai maganar ƙoƙarin basar da waccan Maganar.

Murmushi ta yi lokaci É—aya fuskarta É—auke da hawaye tace "Alhamdilillah, ai ni na kammala shiri, se addu'a Allah ya sa muyi nasara, dan Allah Faris kaima ka dage gobe in Allah ya kaimu ku za'ai wa screening É—in".

Yace "yanzu in ban ci ba ya zaki?" Yai maganar yana kallonta.

Tace "zama ka ci, in baka ci ba haƙura zan da saukar nima" murmushi yai yana jin son yayar ta sa a ransa, tana matuƙar son sa da son ganin cigabansa, shiyasa shima baya son ganin hawayenta.
Chapter 28 · 0% Book details