← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 145

Sashe 14

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani salati Granny ta rafka tare da miƙewa tsaye tana gyara ɗaurin zaninta ta ce. "Huhuhu, mutanen duniya babu gaskiya da tsoron Allah, ban da tsabar sharri ina Khamalu zai haifi wannan kyakkyawar yarinyar mai zubi da turawa, yana ɗan baƙi da shi? A gaskiya wannan mata babu abun da za mu ce miki sai dai kawai Allah ya shiga tsakaninmu da ke, haka kawai kina daga kwance ki narkawa jikana sharri, bayan kuma kina zaune a cikin gidansa kin gama cin abincinsa kin yi ƙat dake, kin murmuro daga ramar da kika zo da ita." Ammi ta ce. "Hajiya wannan maganar fa an wuce ta, ɓacin rai ne ya saka Na'ima ta yi haka."

Baffa da ya kasa ɗauke idonsa daga kan Abra ya miƙa mata hannu, ba ta yi musu ba ta je gurinsa, ko dan ta ga suna kama da Abbinta ne. Baffa ya ce. "Allah Sarki, sannu yarinya, Allah ya bayyana iyayenki." Ammi ta amsa da Amin. Granny ta zo zata ɗauki Abra ta ƙi yarda da ita, da ta takura sai Yarinyar ta saka kuka ta koma gurin Abbinta ta lafe a jikinsa.

Riƙe haɓa Granny ta yi ta ce. "Yau na ga yarinya da jaraba, dan ma zan taimaka in ɗauke ki ba tare da na san daga inda kike ba shine zaki mun tijara, ban da ma zuciyar musulunci irin tawa mene haɗina dake? Aba jawur a koɗe kamar ƙosai" Ta taɓe baki tare da komawa ta zauna tana cigaba da mitocinta.

Baffa ya miƙe yana duban su Captain ya ce. "Mu za mu wuce, sai a daɗa hak'uri da juna, ɗa kuma na kowa ne, idan ka riƙe na wani kai baka san wa zai riƙe maka naka ba." Na'ima ta danne zuciyarta ta ce. "Insha Allahu Baffa, mun gode Allah ya ƙara girma."

"Baffa ba za ku jira a yi Sallah ba sai ku tafin, kuma ko ruwa fa ba ku sha ba." Cewar Captain.

Baffa ya ce. "Alhamdulillah, wucewa za mu yi, na ga sauran lokacin da ya rage a kira sallah zai kai mu gida insha Allahu."

Granny ta ce. "Dama ba'a yi niyyar ba mu ruwan ba, sai yanzu za'a wani ce mu zauna mu sha." Captain ya dube ta ya ce. "Kin taɓa zuwa gidan kafin yau an hana ki ruwan ne?"

Ɗaure fuska ta yi ta ce. "Ni dai ba zan biye ka mu yi tashin hankali ba tunda ba halina ba ne kowa ya shaida, ato." Sannan ta mayar da duban ta ga Baffa ta ce. "Sai dai in ce ku gaishe da gida, dan ni anan zan zauna in kula da wannan zabiyar yarinyar mai ƙwala ƙwalan idanuwa kamar na kakata haulatu, tunda ita wannan asararriyar ta yi nauyi ba iya kula da ita za ta yi ba, tana juyi da ƙyar tana mirgina uban ciki amma se jaraba, gobe idan Allah ya kai mu Shureim sai ya kawo mun kayan sakawata."

Baffa ya ce. "A'a tare za mu wuce da ke yanzu, Iman ta zo ta zauna a nan ɗin tunda sun kusa yin hutu a school." Bai jira cewarta ba ya yi gaba. Granny ta bi shi da wani irin kallo sannan ta miƙe ba tare da ta yi magana ba ta yi waje fuuu. Ɗan murmushi Captain ya yi ya bi bayansu.

Ammi ta miƙe tana duban Na'ima ta ce. "Ki yi hak'uri, na san zaki ga kamar ba'a kyauta miki ba, amma ba rashin kyautawa ba ne, hakan shine dai-dai. Ɗa na kowa ne, sanadiyyar riƙon yarinyar sai ki ga Ubangiji ya baki wani abun da baki taɓa zo ba a cikin rayuwarki, dan Allah ki riƙe yarinyar nan saboda da Allah, kar ki cutar da ita. Kema ba ki san me gaba zata haifar ba"

Na'ima ta share hawayen fuskarta cikin dakiya ta ce. "Insha Allahu Ammi, ɗazun ma ɓacin rai ya saka na yi hakan, ku yi hak'uri, insha Allahu komai ya wuce. Ammi ta ce. "Yawwa, Allah ya yi albarka, ya sauke ki lafiya." Ta amsa da Amin tare da miƙewa ta raka Ammi bakin ƙofa.

A haukace ta dawo cikin parlour ta shiga bedroom É—inta ta kulle ta É—auki wayarta ta kira lambar Yayarta, tana jin ta É—aga ta fashe da kuka ta ce. "Na shiga uku Aunty, ina cikin damuwa, Khamal ya zo mun da wata masifa cikin gidana." A rud'e Aunty ta ce. "Subhanallahi! Mene ya faru?"

"Yarinya ya kawo mun cikin gidana wai za mu riƙe ta, a cewarsa wai a operation suka tsinto ta, ni kuma na san wallahi k'arya yake yi ƴarsa ce suka haifa da wata karuwar a waje."

"Ya aka yi kika san hakan? Ke da kullum cikin yabon Captain kike akan kamewarsa da rashin bin matan banza?"

"Aunty ba ki ga yanda suke yi da yarinyar ba ne, shak'uwarsu ta fi ƙarfin a ce a cikin abun da bai 1 month suka yi kamar ta ba, kuma baki ga shegiyar Yarinyar ba, kyau kamar ita ta yi kanta, irin kyawun nan dai na ƴaƴan shegu, dan dama a gurin aikin nan nasu akwai mata masu bibiyarsa. Na kira iyayensa kuma domin su zo a yiwa tufkar hanci amma sun goyi bayan ɗansu, ni na yi kara ban kira nawa iyayen ba dan kar ace sun zo sun goyi da bayana, ashe su ma son kai za su yi. Wallahi Aunty ba ki ji yanda zuciyata take mun zafi ba, ni dai ba zan zauna da wannan yarinyar a gidan nan ba, ki bani mafita Please."

Aunty ta ce. "Shi Captain ɗin ya kuka yi da shi?, ki nuna masa bakya san riƙon yarinyar mana."

Cikin sheshshek'a Na'ima ta ce. "Aunty cewa fa ya yi sai dai in zaɓa ko in riƙe ta ko in bar masa gidansa, ya zaɓe ta a kaina, duk irin tarin soyayyar da Khamal yake mun amma yau ni yake faɗawa haka? ba dole in ji na tsani Yarinyar ba tunda a kanta ya faɗa mun haka."

Cikin mamaki Aunty ta ce. "Shi Captain É—in ne ya faÉ—a miki haka?"

"Wallahi Aunty shine." Nan ta kwashe labarin duk abun da ya faru ta faɗawa Aunty. Cikin ɓacin rai Aunty ta ce. "Lallai ma Khamal, yanzu akan wata banza can shine zai nemi ya wulak'anta ki? Ya fifita ta a kanki? To amma idan ya san wata ai bai san wata ba, ki k'yale shi ki taushi zuciyarki, ki nuna masa kin amince zaki riƙe yarinyar, taa k'ark'ashin ƙasa za mu biyo masa, a gabansa ki dinga nuna duk duniya babu wanda ya kai ki k'aunar Yarinyar, a bayan idonsa kuma ki dinga cin ubanta son ranki kina gallaza mata, yanda komai ƙanƙantarta da kanta za ta nemi ta bar gidan, koma ta gudu da ƙafafuwanta."

"Ta yaya Aunty? Yarinya ce fa k'arama, ba tafi shekara uku ba, ni fa kawai damuwata yarinyar nan ta bar gidan nan a yau. Dan ba zan raini 'yar haram ba in ci kashinta in ci fitsarinta ba"

"DaÉ—ina dake gajen hak'uri, ki yi yanda na ce miki kawai, da kissa da makirci zaki kori yarinyar daga gidan ba tare an yi tunanin ke kika aikata hakan ba, amma fa dole sai kin danne zuciyarki kin ajiye wannan masiffaffen kishin naki a gefe, in kuma ki kayi dalilin kashe Auren naki ai kin huta." Haka Aunty ta dinga tausar Na'ima da koya mata irin abubuwan makircin da za ta yi, har aka yi Sallar Magriba suna wayar, sai da ta ji shigowar Captain gidan sannan ta yi mata sallama ta share hawayen fuskarta ta tashi ta fito parlour.

A tsugunne ta tarar da shi yana cirewa Abra takalmin ƙafarta wadda ke shan choculate hankali kwance. Wani abu ne ya soki zuciyarta, wato masallacin ma da yarinyar ya tafi saboda tsantsar k'aunar da yake yi mata. Danne baƙin cikin da ya taso mata ta yi ta kakalo murmushi ta ce. "Sannu da zuwa My Man." Ko d'agowa bai yi ba balle ya ba ta amsa. Ƙarasawa ta yi ta tsugunna a gabansa cikin kissa ta ce. "Magana nake maka fa." Nan ma banza ya yi da ita. A hankali ta kamo hannunsa cikin marairaicewa ta ce. "Dan Allah ka yi hak'uri My Man, na tuba na gane gaskiya, wallahi ɗazun ma sharrin shaidan ne." Ta ƙarashe zancen idanunta cike da ƙwalla.

Ba tare da ya kalle ta ba ya ce. "Ya wuce." Yana ƙoƙarin janye hannunsa daga nata ta riƙe shi gam tare da sakar masa kuka. Numfashi ya sauke ya ce. "Mene haka kuma? Ba na ce na hak'ura ba?"

"Ai na san ba ka hak'uran ba, Please My Man ka san ba zan juri fushinka ba." Sakin fuskarsa ya yi ya ce. "Komai ya wuce ki bar kukan nan haka." Sannan ya saka hannu ya shafi cikinta cikin k'aunar Unborn ɗinsa." Ajiyar zuciya ta sauke ganin da gaske ya hak'uran. Hannu Abra ta kama ta ce. "Zo nan Daughter." Ƙin zuwa ta yi ta lafe a jikin Major tare da kwab'e fuska za ta yi kuka. Duk da haka ba ta yi zuciya ba ta shafa fuskarta ta ce. "Ya sunanki?"

"Abra."

Captain ya ba ta amsa idanunsa akan Abra.

"Wow nice name, Allah ya raya mana ke"

"Amin"

"Bari na je na yi Sallah." Na'ima ta faɗa tana miƙewa, dan dauriyarta ta kusa ƙarewa akan pretending ɗin da take yi, ji take tamkar ta janyo Abra ta shaƙe ta ta mutu saboda tsanarta dake ƙara cika mata zuciya.

Bai ce komai ba sai bin ta da ya yi da wani irin kallo, darajar cikin cikinta ta ci, da kuma nasihar da Ammi ta yi masa bayan sun fita, akan ya yi hak'uri ya mayar da komai ba komai ba tun da Na'iman ta yi nadamar abun da ta aikata, shi yasa kawai ya haƙura, amma da ya yi niyyar sai ya hukunta ta akan hauka da ƙazafin da ta yi masa.

LITTAFIN DARE DA DUHU, ₦300 NE KACAL, ZA KU TURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0116886423 Sulaiman Na'ima s union Bank.
KU TUNTUƁI WANNAN LAMBAR DAN TURA KATIN WAYA NA NAIRA 500 TA WANNAN 09047871750
DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU AKAN WANNAN LAMBAR 07063065780\09047871750
MUNGODE.
Chapter 14 · 0% Book details