← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 145

Sashe 23

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kasancewar sun yi wanka kafin su tafi Tahfiz, kaya kawai ta sauya ta saka wata doguwar rigar abaya mai kyau da tsada purple colour, ta yi kyau sosai dan rigar ba ƙaramin haskakata ta yi ba. Ta fashe jikinta da turaruka masu sanyin ƙamshi sannan ta ɗauki handbag ɗinta ta fito parlour. Sallama ta yiwa iyayen nata ta fice bayan Abbi ya ba ta kuɗi ya ce su tsaya a hanya su siyawa su Fruits, tare da addu'ar Allah ya tsare. Na'ima ta bi ta da wani irin kallo tare da sakin wani munafukin murmushi.

Suna tafe Salman na yaba kyawun da ta yi kamar yadda ya saba yi mata kullum idan ta yi kwalliya, murmushin yaƙe kawai take yi masa amma ta gaza cewa komai, saboda tsoro da fargabar abun da za ta tarar a gidansu Mama na cin mutuncin kamar yadda suka yi mata kodayaushe. Duk yadda ta kai ga ɓoye damurta sai da Salman ya gane halin da take ciki, tausayin ƴar'uwar tasa ne ya cika masa zuciya. Ya rasa laifin da ta yi da ya saka Mami da danginta ba sa ƙaunar ta.

Mintuna goma sha biyar ne ya kai su Unguwarsu Mama, kasancewar ƙaramin gida ne a ƙofar gida Driver ya yi parking Motar. Salman dake gaba ne ya fara buɗe Motar ya fita, ya zagaya ya buɗewa Abra Motar wadda da zuciyarta ke bugawa da sauri da sauri, cikin matuƙar sanyin jiki ta fito, ledar fruits ɗin da suka siyo Salman ya ɗauka, ba tare da ɗayansu ya yi magana ba suka nufi cikin gidan.

LITTAFIN DARE DA DUHU, ₦300 NE KACAL, ZA KU TURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0116886423 Sulaiman Na'ima s union Bank.
KU TUNTUƁI WANNAN LAMBAR DAN TURA KATIN WAYA NA NAIRA 500 TA WANNAN 09047871750
DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU AKAN WANNAN LAMBAR 07063065780\09047871750
MUN GODE.
[9/30, 8:55 PM] Abk: *✷ DARE DA DUHU ✷*

Brigh pens✍🏾
Nimcyluv
Ayushercool
Zee kumurya

*P 10.......*
Elegant Online writer's

Akwai complete littatafanmu a Arewabooks, da wanda kuka karanta da wanda baku karanta ba, kuyi following wannan Acct ɗin domin sabbin littafai kamar *MIJIN MALAMA* da *RUƊIN ƘURUCIYA*

https://arewabooks.com/u/nimcyluv👇🏾

https://arewabooks.com/chapter?id=6316f4af434cfeb9e7fe2949.

_Littafin DARE DA DUHU na kuɗi ne akan ₦300 kacal, zaku tura kuɗin ta wannan acct ɗin 0116886423 Sulaiman Na'ima s union Bank. Ko kuma ku tuntuɓi wannan Numbers ɗin 09047871750.. idan katin waya zaka tura ₦500 ne. Transfer ne ₦300. Kuyi Mgn whatsapp kai tsaye 07063065780/09047871750. Bright pens na gdy😊_

Marairaice fuska Abra tayi, lokacin da suka isa ƙofar da zata kaisu zuwa parlourn gidan kakarsu wacce ta haifi Na'ima.

Salman ya kalli yayar ta sa kafin a hankali yace "Mene Yaya?" Muryar ta na rawa tace "Faris tsoro na keji"
Salam ya buÉ—e ido sai kuma ya yi dry yana faÉ—in "Yaya ba gani ba, ki daina tsoro idan ina tare dake"
Shiru tayi masa, gane cewa da gaske tsoran ta keji yasa Salman kama hannunta suka shiga cikin parlourn bakinsu É—auke da Sallama.

Muryar Salman ita ta danne siririyar muryar Abra, hakan yasa Mama dake zaune, ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya zaton iya shi kaɗai ne yazo.
Cikin farin ciki ta É—aga Idanunta tana faÉ—in.
"Maraba, lale da Mai gidana"

Salman ya yi Murmushi yace.
"Ƴar Tsohuwa"
"Wace Tsohuwar Salmanun Faris? Kabar ganina a haka auren naka sai nayi niy....," Maganar Mama ta tsaya lokacin da Idanunta ya sauka akan Abra, wacce take ɓoyewa bayan Salman sai ka rantse shine gaba da ita.
Mama ta haɗe fuska, tare da ɗauke kanta gefe guda, sam bata ƙaunar ganin Abra da jikan nata Salman, tsoro da fargaba da tunanin wani abu, yana kawowa Zuciyarta farmaki.

Anuty Suwaiba tunda suka shigo take bin Abra da wani irin kallo, musamman ganin yadda lokaci guda Abra ta zama cikakkiyar budurwa kamar ita ta yi kanta sbd tsananin kyau, zubi, diri, na tsarin da Ubangiji ya yi wa jikin na ta.

Cikin sakin fuska, Salman ya ƙaraso cikin parlourn still holding her hands, Abra tayi saurin zame hannunta daga cikin na Salman, ta zauna ƙasan carpet muryarta na rawa tace.
"In...Ina...Inna...,"
Gaba ɗaya ta nemi gaisuwar ta rasa a cikin bakinta, Sbd Mama data murje mata yatsun hannunta da ƙafa.
Zafi da azaba yasa Abra sakin ajjiyar zcy, gomi na tsastsafo mata daga tsakiyar goshinta.

A fusace Mama ta juya inda Abra take zaune tace. "Kinga riƙe gaisuwar ki, munafukar yarinya mai mugun nufi a zuciya, ire-iren wannan baƙin halin naki yake sawa wani yayi zaton cutarki muke, ban taɓa yin jika mai mugun hali irin naki ba, KURMA kawai!"

"Wlh Mama mugun halin yarinyar nan yafi ƙarfin ta, na samu labarin ita take hana Salman zuwa gidan nan, Allah na tuba mene haɗin kashi da kiyashi ma? Shegiyar yarinya ke dai wlh Allah wadarai da halinki"

Anuty Suwaiba ta ƙarashe zan can tana Miƙewa tsaye, ita ta yadda ta tsani mutuwarta haka ta tsani ganin buɗe idanunta ta ga Abra a cikin gidan Na'ima, musamman yanzu yadda duniya ta lalace ka gama kiwata yarinya ka waye gari Uban riƙon ya aureta.

Abra tayi ƙasa da kanta, cikin damuwa Salman yace "haba Mama! haba Mama!! haba Mama!!!.. laluran nan fa Allah ne ya ɗorawa Yaya, babu wanda ya shige haka fa, kuma ni Anuty ki daina cewa yaya ta hanani zuwa gidan nan, ni yaro ne da za'a hanani abinda nai niyya? I don't want to go to your house since you don't like to see my sister"

Anuty Suwaiba ta saki baki kafin tace "your fifteenth year in the world, ban fa manta time É—in da akai maka kaciya ba, yanzu nan kai har jinka kake wani babba?"

Wani irin baƙin ciki ya ziyarci zuciyar Salman, babu abinda ya tsaya masa a rai irin maganar kaciyar da Anuty Suwaiba ta yi, idanunsa har wani ruwu ruwa ya tara sbd zafin zuciya.

Mama ta riƙe baki tace.
"Salmanu! Akan wannan mowar kake faÉ—a mana Mgn? Kalli yadda ta gagara gaishe ni balle ta gaida Suwaiba? is this is what Na'ima train to you?"

Mama tayi mganar tana bugawa Abra tsawa, wacce ta sanya tayi saurin fashewa da kuka muryarta na rawa tace.
"Kiyi hqr Mama"
Miƙewa Mama tayi, domin idan taci gaba da zama a nan, zata iya lakaɗawa Abra dokan mutuwa!.

Salman yabi Grandma ɗin su da kallo, zuciyarsa nayi masa wani irin zafi baya ƙaunar duk abinda zai sanya yayarsa kuka, duk abinda ake wa Abra shine ya kejin zafin abin a zuciyarsa (Heartache) yana tsanin so da ƙaunar farin cikinta He is jealous of his sister, he sympathizes with her.

"Ki daina kuka Yaya"
Salman ya faÉ—i mganar a raunace, idanunsa ya kaÉ—a ya yi wani irin jaa na zafin zuciya, kallonsa kawai Abra take.

"Salman mene mowa? Ni na haifi kaina ko Mami ce ta haifan? Wanne laifi na aikata mai girma haka Faris? My mother's relatives do not love me at all, ina tsoran kada su rabani da kai Salman zan jure komai banda rabuwa dakai"

Kuka ta fashe da shi, jikinta na rawa da ɓari, gaba ɗaya tayi kan Salman sbd duhun da take gani a cikin idanunta.

Salman ya yi mata masauki a ƙirjinsa, ya riƙeta Tsam-tsam yana shafa kanta tare da jijjigata a jikinsa yana faɗin.
"Kin gani ko yaya? Kinga abinda zaki jawa kanki sbd damuwa? Idan kinga na rabu dake yaya Kice Ubangiji ne ya É—auki raina"

Muryarta na rawa tana riƙe Salman ta ce.
"Salman ka maye gurbin Mami don Allah,Ina jin zuciyata na yi min zafi Salman"
Kasa Mgn Salman ya yi, sun jima a haka kafin ta zame jikinta tana goge Hawayen idanunta zuwa Fuskarta. Shiru ya biyo baya babu wanda ya sake Mgn, Salman da ya tuna zan can kaciyar nan sai ransa ya ɓaci.

A hankali ya zauna gefenta cikin ƙasa da murya yace.
"Ina jin babu daÉ—i Angel.. bana son ganin Yayata cikin damuwa, please please ki daina Stop crying"

Ya faɗa yana sanya hannunsa saman Fuskarta, slowly ya shiga goge mata hawayen da yaƙi tsaya mata, yana jin yadda take sauke ajjiyar zuciya, da Idanu kawai yake binta sai kuma ya girgiza kai.

Gyara zamansa yyi very close to her yana É—aukan remote ya ce "Yaya na tambayeki?" A hankali Abra tace "Uhm"

Kansa ya shafa sbd Mganar da ta yi masa nauyi, Abra ta haÉ—e fuska tace "All ears, kasan ban son haka ko?"
Juyawa ya yi suka haÉ—a idanu yana sakin Murmushi yace "I knw, Yayata nada tsari" idanunta akan T.v tace "FaÉ—i?"

Salman idanunsa gaba É—aya akan Abra wacce ita kuma hankalinta yake kan T.v yace.
"The stomach ache you had a few days ago Yaya"
Shiru ya yi mata, ta juya tace. "To ina jinka ai, mene ya faru?"
Sumar kansa ya shafa, shifa tunda ya yi niyyar Mgn bai ga kuma abinda zai hanasa yin shiru ba, fisgewa ya yi yace.
"The blood, i mean shine al'adar da ake Mgn mata su nayi?"

Abra ta juyo da sauri tana buÉ—e daradaran Idanunta waje tace.
"Jini? Injiwa? Yaushe kuma?" Duk ta daburce da tambayar da ƙanin nata ya yi mata.

Murmushi ya yi ya ce
"Why are you answering my questions with a question Yaya..?"
Abra dai ta haÉ—e fuska tace "To ban gane ba ai"
Salman ya yi Murmushi kawai yana girgiza kai sai kuma yace.

"Our biology teacher told us" Attention É—in Abra yana wajan Salman, amma idanunta na kan t.v, kamar ba zatai Mgn sai kuma tace.
"Ya ce muku me?"
Salman yace.
"Adolescent period mana Yaya, and you know what Hadda wannan blood É—in acikin alamun fa" shiru kawai Abra tayi tana Mmkin yadda Salman baya jin kunyarta, ko dan su biyu suka taso a cikin gidan nasu?.

Bai damu da yin shirun nata ba yace.
"Kinga yace, idan maza suka balaga fa, muryarsu na zama ƙatuwa, Chest hair, armpit hair, and pubic hair suna fitowa maza sosai, da kuma gemu, Man's bottom is getting bigger....,"

"Faris...!!!"
Abra ta faɗa da ƙarfi tana rufe bakinta tare da zaro idanu waje, ita kanta Mgnar ƙanin nata Kunya yake bata.
Chapter 23 · 0% Book details