← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 135 OF 145

Sashe 135

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Na son da kike mini ne da wanda nake miki."

Murmushi ta yi ta ce. "Da ni da Afra duk É—aya ne, tunda tana son ka kana son ta ku yi auran ku, kuma ina son sanar maka na fi kowa farinciki da hakan." Cikin É—aga gira ya ce. "Sure?"

"Of course ɗan ƙanina."

Ɓata fuska ya yi ya ce. "Yanzu ni ne babba ai, tunda zan auri yayarki." Cikin dariya ta ce. "Son girman naka har ya kai ka fitar da babba a cikinmu ba tare da an faɗa maka ba?"

"Na san ita ce ai, jikina ya ba ni."

"Shikenan na ɗauki ƙanƙantar Yaya Faris."

Murmushi suka yi a tare cikin ƙaunar junansu. Adnan dake kallon su ya ji zuciyarsa na wari irin tafarfasa saboda kishi, a fusace ya taho zai zare hannun Abra daga cikin na Salman tare da ja masa warning, taku ɗaya ya yi tari ya sarƙe shi. Da sauri Abbi ya kama shi suka fita ganin ya fara aman jini. Taɓe baki Abra ta yi tare da shigewa ciki, Salman ya bi ta da kallo.

Ya san Yayarsa tana son shi har yanzu shi ma kuma haka, amma shi ya fi son ta koma gidan Adnan ko dan little, ba ya son yarinyar ta taso ta ga iyayenta ba sa tare. Sannan Afra tana mugun son shi, a zaman da suka yi tare shaƙuwa mai ƙarfi ta shiga tsakanin su, idan ya ce Abra yake so ba ita ba za ta shiga mawuyacin hali.

ÆŠakinta ta shiga ta tarar da Ummi da Inna a zaune. Zama ta yi a kusa da Ummi dake sakar mata murmushi.
"Allah ya yi muku albarka." Ummi ta faɗa tana shafa kanta. Cikin jin daɗin kasancewa da mahaifiya Abra ta ce. "Amin." Kwantar da kanta ta yi akan kafaɗar Ummi ta ce. "A Ina ƴan'uwan mahaifinmu suke a ƙasar nan? Ina son mu haɗu da su." Ɓata fuska Ummi ta yi alamun ba ta san zancen Bulama, amma duk da ƙin shi da take ta san ba ta isa ta raba shi da Ƴaƴansa ba. Kamar an mata dole ta ce. "Suna Adamawa, amma iyayensa duk sun rasu, sai ƙanwarsa guda ɗaya Murja da sauran relatives ɗinsu." Kafin Abra ta kuma magana Afra ta shigo da Little a hannunta. Ba tare da yi magana ta ɗora ta a kan cinyar Abra. Kawar da kanta ta yi duk da cikin ranta cike take da zumuɗin ganin fuskar ƴar tata.

"Ki É—auki Æ´arki, wannan abin da kike yi ba daidai ba ne, tunda ba ta miki laifin komai ba, bai kamata kuma laifin mahaifinta ya shafe mata ba."
Afra ta faÉ—a cikin sigar nasiha.

Murmushi Inna ta yi a ranta tana mamakin hankalin da ƴar Baba ta yi a zamanta a gidan Abbi. Rungume little Abra ta yi tare da sakin ajiyar zuciya, ƙaunar yarinyar na ratsa ko wane saƙo na jikinta, ta ji duk duniya babu abin da ba za ta iya yi ba saboda ita. Haɗa su Ummi ta yi ta rungume gabaɗaya tana hawayen farinciki, Afra ta zo ta zauna a ɗaya b'arin ita ma ta rungume ta, ban da ajiyar zuciya da hawaye babu abin da suke.

Haka rayuwa ta cigaba da garawa cikin farinciki ga su Abra, duk da tunanin mahaifinsu da halin da yake ciki yana damun su. Sun samu labarin har yanzu ana shari'a akan asibinsa ba a ƙare ba, kuma kotu ta ƙi bayar da belin shi yana can a tsare. Shirye-shiryen bikin Salman da Afra ya kankama, Abbi ya sa an ƙara gyara wa Salman guest house ɗinsa, a can za su tare shi da amaryarsa da suke cin soyayyar su babu tsinke. Abra ta kwantar da hankalinta, ta cigaba da kallon Salman a matsayin blood brother ɗinta. Aunty Murja ta zo tun saura kwana uku biki, Ummi ta kira ta, ta sanar da ita duk abin da yake faruwa, da yake suna shiri sosai. Amma fa ta sha ciwon bakin ƙin sanar mata Bulama ya ƙara aure da ta yi. Adnan yana can jiki ya ƙara rincaɓewa, kuma ya ƙi yarda a fitar da shi waje, ya ce maganin ciwon shi kawai Abra ce. Abba kuma ya ƙyale shi ya ce ya je jikinsa ne, shi yake shan azabar ciwo ba wani ba. Kullum sai ya kira Abra ba adadi, ita kuma ba ta ɗaukar kiran, mamakin ma inda ya samu numbernta take, saboda sabon sim ta sake. An yi biki lafiya an gama lafiya, ba a wani ja abun sosai ba, dinner kawai aka yi da ɗaurin Aure aka kai amarya gidanta. Ranar Afra ta sha kuka, na barin su Inna da kewar Baba, ta so a ce ya ga ranar aurenta kamar yadda ya ci buri, amma Allah bai yi ba. Abra ma ta taya ta kukan, don duk da ba su jima da kasancewa da juna tare ba amma ta ji ba daɗi sosai a cikin ranta, a gefe kuma ta taya ta farinciki matuƙa na auren Namiji Jarumi, Yaro da halin manya Salmanul Farisi.

Washegari da safe Afra tana baccin gajiyar da Salman ya tara mata a daren jiya ta ji ana yi mata tafiyar tsutsa a ƙafa. A hankali ta buɗe kumburarrun idonta da suka ci kuka ta sauke a kan fuskarsa. Murmushinsa mai kyau ya sakar mata tare da ranƙwafowa cikin sanyin murya ya ce. "Morning princess." Juyar da kanta ta yi gefe tare da turo baki. Kissing lips ɗinta ya yi tare da faɗin. "Tun ɗazu nake jiran ki tashi ki yi breakfast kar yunwa ta illata mini ke, kuma bana son na tashe ki kanki ya yi ciwo." Cikin shagwaɓa ta ce. "Ai dama ciwon yake." Marairaice fuska ya yi ya ce. "I'm sorry dear, mu je ki wanka sai ki sha magani, idan bai daina ciwon ba sai mu je asibiti." Riƙe duvet ɗin da yake ƙoƙarin yayewa ta yi ta ce. "To ka bar ni zan tashi da kaina." Murmushi ya yi cikin ransa yana faɗin. "Wanne dare ne jemege bai gani ba." Ƙarar da ta saka ya sa shi saurin ɗago ta yana tambayar ta lafiya? Hawaye ta fara ta ce. "Na kasa tashi, ko'ina a jikina duk ciwo yake mini, ƙafafuwana kamar ba a jikina suke ba. Cikin tausayawa ya shafa kanta tare da faɗin. "Sorry, har yanzu jikin bai bar ciwo ba?" Gyaɗa masa kai tare da taune lips ɗinta saboda zugin da take ji a ƙasanta.

"Okay bari na ga gurin ko da rauni."

Kuka ta saka masa tare da ƙanƙame jikinta ta hana shi ganin abin da yake son ganin. Numfashi ya sauke a hankali tare da saka hannu ya fara goge mata hawayen fuskarta, ture hannun ta yi tare da ƙoƙarin tashi daga jikinsa. Riƙe ta ya yi sosai cikin rarrashi ya ce. "Har yanzu fushin bai ƙare ba? Na ce fa ba zan kuma fa, jiyan ma duk ke kika ruɗani da kyawun da kika yi da daddaɗan ƙamshin da kike." Ya ƙarasa maganar tare da tusa kansa a wuyanta yana shaƙar ƙamshinta dake saukar masa da kasala. Ajiyar zuciya suka sauke a tare da lumshe ido. Jin ya fara sassauke numfashi tare da yawo da hannunsa a jikinta ya sa ta buɗe ido da sauri tare da ture kansa, don ba ta manta bak'ar azabar da ta sha ba a hannunsa jiya. Bai ce komai ba ya ɗauke ta cak ya kai ta toilet.

Littafin dare da duhu na kuÉ—i ne, mai so ya tuntube mu a wannan numbern. 09047871750
[11/30, 9:12 PM] Abk: Da yamma Salman na zaune a parlourn gidansa ya yi wani fresh alamar tun a daren jiya angwancin ya amshe shi, shi kaɗai sai murmushi yake lokaci zuwa lokaci yana ɗaga kansa tare da kallon ƙofar bedroom ɗin ta.
A hankali ya miƙe tare da ajjiye remote ɗin hannunsa kai tsaye bedroom ɗin ya nufa daga shi sai trousers iya giwwa jikinsa ko riga babu. Kwance ya sameta har yanzu saman gado ta rufe jikinta da duvet barci take a wahale har yanzu.

"Oh sweetheart barci har yanzu?" Ya faɗa yana saka hannu tare da zame duvet ɗin, firgigit ta farka tana buɗe idanunta wanda hawaye ya gama cika su. Hucin zazzaɓi na fita a jikinta Salman ya haura gadon baki ɗaya suna haɗa ido ta fashe da kuka sosai, domin gani take kamar yana sane yake mata komai haushin shi duk ya kamata.
Cikin rarrashi yana jawota jikinsa baki É—aya tare da shafa kanta ya ce.

"Sorry wife double sorry ni ne ko?" Kai ta ɗaga masa alamar "eh" tana ƙara shigewa jikinsa saboda daɗi ɗumin jikin da take ji. Ya ya yi kissing lips ɗinta yana zame mata hannun duguwar jikinta a ƙoƙarin shi na son sake haɗa jikin nasu waje guda da kyau! Yadda za tafi jin daɗi domin ya lura da yanayin nata..
Gaba ɗaya ta juya tare da rungome shi sosai sbd bayyanar jikinta hannunta a ƙirji shi tana duka tare da ƙananun kuke ta ce.

"Uhm Uhm zan faÉ—awa Abbi da Mami mugunta kake mini"
Ya kwaikwayi muryarta yana sake riƙeta a jikin nashi tare da ƙoƙarin lalubar bakin da ya yi maganar ya ce.

"Uhm to ai haka shi ne auren sweetheart wife"

"Sure?" Ta tambaye shi tana kafe shi da maraitattun idanunta wanda suke ƙara kashewa Salman jiki da zuciya. Ya tarairayota baki ɗaya saman sa sun jima suna kallon juna cikin ƙasa da murya ya ce.

"I love You Afra Yusuf Garba Bulama, ban san adadin son da nake miki ba, bani kuma da bakin yi miki godiya a bisa kyautar da kika bani,
I am immensely thankful to you for deciding to marry such a stubborn person like me and for going forth numerous times just to assure I was happy. Wallahi Afra ina son ki so mai yawa, son da baki ba zai taɓa iya faɗa ba sai dai gangar jikina tayi aikin ta,
The best part of my day is your smile. Being with you is the easiest choice I have ever made, and I'm so lucky I get to make it every day. I love you more every day. I love your honesty, your passion, your resilience, your courage, your partnership, and your smile"
Chapter 135 · 0% Book details