← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 131 OF 145

Sashe 131

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Masha Allah, Allahamdulillah ta'al ya ɗiyata" Ummi ta faɗa a bayyane farin ciki ya sanya Afra kasa motsa wa ta durƙushe a wajan ta shiga rusa kuka da dukkan ƙarfinta. Ummi da kanta ta kama Afra ta rungome itama hawayen take sosai. Bulama ya kasa koda motsi sbd matsanancin kunya da kuma tsoron matakin da Ummi zata ɗauka. Shi kansa kallon Afra yake yana ji tamkar ya rungume ta.
Murmushin fuskar Abdullah ya kasa ɓoyewa kusan yafi kowa jin daɗi a yadda fuskarsa ta nuna, at least Yayar tasa zata samu nutsuwar zuciya.
Bayan komai ya lafa Abbi ya kalli Afra ya ce "Daughter inama kika ce an tsinceki" tana jikin Ummi muryar ta har lokacin rawa take ta ce

"Baba ya ce wai ko wata rana yaje daji neman wani magani aka fara harbe harbe ya labe wani waje ya daɗe a wajan kafin ya fito daga inda ya ɓoye, yana fitowa idanunsa ya sauka akan wani mafarauci wanda yake kwance anyi masa harbi wajan huɗu, daga gefen shi kuma yaga wata jaririya kwance tana kuka, hakan yasa ya ɗauki Jaririyar taho hanyar gida shi ne yaje wajan ƴan sanda amma ya ɓoye labarin kisan yace kawai tsinta ta ya yi"
Adnan ya kalleta domin ba haka ta faɗa masa ba, kamar mai karantar zuciyarsa ta ce "Wannan shi ne gaskiyar maganar Baba ya ce na ɓoye duk wanda ya tambaya na dinga faɗar abin da ya faɗa mini, sai na samu iyaye na gsky zan faɗi gaskiyar Abin"
Cike da gamsuwa Abbi ya jinjina kai ya ce.
"Babu mal wanda suke kashe mafaraucin nan sune kidnappers ɗin da muka kama cikin daji a can muka samu Abra, har wani yace mini wancan tasu ce kada na taɓa ta babu ko shakka a wajansu ta rayuwa tsayin shekaru uku har ta samu matsalar kunne, Allah mai iko Al-hakkumu bowayi gagara misali Allah mai yin Yadda ya su, ina ganin matsalar mu ta zo kusan ƙarshe"

"Gaskiya kam abin da yake ɓoye ya fito, saura nemawa Salmanun-faris auren Afra yanzu a gaban iyayenta" Abbi ya yi saurin cewa.
"A'a ba za a yi haka ba, ina da wacce zan bawa Salman Please Alhaji Aliyu"

"Shi Salman É—in ya ce baya son Afra? Kai Salman kana son ta ko ya ya?" Ya faÉ—a yana kallon Salman wanda zuciyar shi ta fara harbawa da jin maganar ta Abbinsa.
Kasa cewa komai ya yi sbd Kunya kansa a ƙasa.
"Kaga ni ma kamar uba nake wajanka kada kaji komai yanzu zan amsar maka auren Afra da izinin Ubangiji"
Salman ya É—ago kai suka haÉ—a idanu da Afra tayi saurin rufe fuskarta a jikin Ummi. Ya ce "E, Abba ina son ta and I want marry her"

"Masha Allah Ubangiji ya sanya albarka" ya juya kan Dr Bulama wanda ya kasa cewa komai ya ce "Dr muna neman alfarmar wajanka, idan babu damuwa muna buƙatar ka yarje mana akan nemawa Salman auren Afra" kafin Dr Bulama ya yi magana Ummi ta ce.
"Sannu Alhaji, yanzu É—iyata bata da wani Uba wanda ya shige ni, ni ce uwarta ni ce uban ta, Abdullah zai zama waliyi a gare ta"

"Kada ki yi making decision cikin fushi uba, Uba ne komai lalacewar shi"

"Don Allah kayi mini wannan alfarmar zuciyata a kusa take"
Abba ya ce "To shikenan Allah ya yi mana maganin komai sai haƙuri"
Ummi tai murmushin baƙin ciki ta ce "Afra daman taku ce ni kawai ƴar kallo ce an baku ita halak malak"
Da sauri Adnan ya miƙe tsaye tare da Aishatul-humaira da sauri Mami ta ce.
"Adnan son Ina zaka da Mamana?" Kasa yi mata magana ya yi, ya nufi ƙofar fita tari na sarƙe shi ya fara yi babu ƙaƙƙautawa jini na zuba, Little ta fara kuka tana ƙanƙame mahaifin nata da sauri Abbi ya miƙe shi da Hajiya Mama.
Mami ta karɓi Little tana faɗin "Subuhanallah sannu Son" Abba ya kasa motsa wa tausayin tilon ɗanshi ya mamaye zuciyarshi amma duk abin da ya same shi, shi ne ya kawa kansa.

"Ya Salam sannu Adnan, Salman get the car immediately, zamu koma hospital" hankalin Hajiya Mama ya tashi suka nufi asibiti da Adnan Little na ihu tana buga ƙafa zata bi ubanta sbd ta fara gane shi.

Abba ya dafe kansa da hannu bibbiyu fargaba da tsoro ya cika masa zuciya. "Daman bashi da lafiya ne? Allahu ya sauwaƙe" Mami ta cewa Ummi "Amin ga grandchild ɗin naki nata rigima" Ummi tai murmushi ko inda Dr Bulama yake bata kallo yana son cewa zai duba Adnan amma babu mai yarda da shi. Jiki a saɓole ya miƙe tare da yin waje ko zai samu peace of mind

Yana fita wayar shi tai ƙara ganin number Saudat ya sanya ya yi tsaki jin kiran ya yi yawa ya ɗauka cikin faɗa ya ce "Wai ya akai ne?" Ta cikin wayar tayi dry sosai ta ce .
"Oh calm down Dr Yusuf Garba Bulama" ya buɗe baki da kyau ya ce "Ni kike kiran sunana haka?" Ta ce "Daga lokacin dana san ka san su waye yaranka, ni ma na shiga nutsuwata kafin dani dakai duk mu rasa mu fara yawo a titi ya sanya na nemawa kai na mafita, while before i say anything zan fara da wanda zai girgiza maka lissafi, ni ce na sanya a kwashe Mini yaran da Matarka Rumaisa ta haifa, aka maye gurbin su da matattun yaran dana bada kwangila aka sato suma a ranar aka haife su, na shirya wannan plan ɗin da P.a ɗin Hajiya Rumaisa tare da alkawarin zan bashi miliyoyin kuɗi, dana tabbatar ya ɗakko yaran kuma bana da kuɗin nasa aka buge motar ɗaya ɗakko yaran babbar mota tabi da kansu, nayi mamakin yadda yaran suka kuɓuta domin an tabbatar da P.a da motar ƙonewa sukai, abu na farko daya bani tabbacin jininka na raye saƙon da aka bani na baka, ina buɗewa naga photon wata budurwa mai kama dakai, tare da wasiƙar cewa jininka ce"

Tai dariya sosai kafin ta ce "Wannan ke nan, abu na biyu tunda yaranka sun dawo nasan kawo yanzu Matarka Rumaisa ta samu labarin aurena da kai da kuma Æ´ata Meenal, so dole zata É—auki matakin cin amanar da kayi mata, kafin haihuwar guzuma É—a kwance uwa kwance na kwashi rabona dana Meenal, duk wasu file na filayenka suna wajena wanda ka saka hannu da sunan Meenal kai da duk wani abu daka san ka mallaka, dan haka kayi ta kanka ina jiran takardar saki saduwar alheri"

Kusan mutuwar tsaye Dr Bulama ya yi "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un" ya shiga faÉ—a tare da faÉ—in "Na shiga uku" yana tsaye aka fara masa messages an rufe dukkan wani acct bank É—insa, daga na gida zuwa na company har na asibitin wanda kuma aikin Abdullah ne ko Ummi bata sani ba ya fita zuwa baya ya shiga kiran ma'aikata.

Dr ya fito da sauri daga room Abba ya kasa haƙuri ya ce "Dr ya jikan son me ya sa me shi ina ɗana" ya buga ƙafaɗar Abba ya ce "just pray for him Ita yake buƙata" Hajiya Mama ta saki kuka ta ce "Kaga abin da kake shirin jawa Adnan? Me ya sa ba zaka taya shi neman abin da yake so ba? Gashi nan zai rasa rayuwar shi yabi matar tasa" Abba dai ya kasa magana Abbi ya ce.
"Insha Allah za a ba shi auren Afra indai a kanta ne" cikin sauri Abba ya ce.
"Kasan Allah idan har ina raye Adnan ba zai taɓa Auren Afra ba" yana faɗin haka ya nufi office ɗin Dr ya same shi zaune bayan sun gaida Dr ya ce.
"Adnan ya samu ciwon zuciya wani gefe har ya fara kumbura ayi ƙoƙarin nema masa abin da zuciyarshi ke buƙata kafin mu samu ya farfaɗo daga dugun suman da ya yi"
Abba ya ce "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un yanzu sai yaushe zai farka?" Dr ya ce "for now ba zan iya cewa komai ba, sbd jikinsa ya yi tsanani da yawa anyi wasa da zuciyarshi" da sauri Abba ya fita waya kare a kunnenshi.

Daƙiƙo na juyawa zuwa sekonni, sekonni na juyawa mintuna, mintuna na juyawa zuwa awanni, a hankali suke sauyawa zuwa yini daga yini zuwa kwana. Adnan ya ɗauki wasu kwanaki kusan arba'in a gadon asibiti ba tare daya farfaɗo ba. Har lokacin Ummi na ƙasar gidan Abbi, Bulama kullum sai ya zo Ummi bata kula shi bata nuna masa ta san Abdullah ya rufe komai nasa ba, shi ma Bulama ya kasa cewa komai. Saudat ya yi neman duniya ya rasa inda zai sameta daga ƙarshe ma wayarta baya shiga.

A hankali ya shiga buɗe idanunshi wanda sukai masa sosai da sauri ya mayar da idanun ya rufe sbd hasken da ya yi masa yawa. Slowly slowly ya ƙara trying na buɗe idanun, har ganinsa ya sauka akan drip dake maƙale a jikinsa.
Hannu ɗaya ya sanya ya dafe kansa dake masa ciwo a hankali ya zame hannun zuwa saitin zuciyarshi dake bugawa da ƙarfi yana jin ciwo sosai ta cikinta.
"Allahamdulillah son ka farka?" Hajiya Mama ta faɗa tana yin waje kiran Dr da kuma Abba da Abbi da suke waje suna tattaunawa akan a fitar da Adnan ɗin ƙasar waje.
Salman ya gyara tsaiwa ba tare da ya kalli Adnan É—in ba, duk da cewa yana jin tausayi shi. Fararen idanunta ta É—aga kaÉ—an tana kallon inda yake kwance da sauri ta É—auke sbd wani abu mai kama da tausayi da taji..
Dr dasu Abbi suka shigo bayan Dr ya gama duba jikin ya ce.
"Allahamdulillah yanzu saura a É—ora shi akan magani" Abba ya yi murmushi yana faÉ—in "thank you Dr"
Chapter 131 · 0% Book details