Sashe 34
Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Driver na hango su ya fito daga mota da sauri, cikin al'ajabi ya fara tambayar Salman abun da ya faru.
"Please buÉ—e mun baya na saka ta mu tafi asibiti."
Salman ya faɗa masa haka cikin damuwa da ɓacin rai.
A hanzarce Driver'n ya buɗe masa Motar, kwantar da Abra dake sume tamkar babu numfashi a jikinta ya yi, sannan shi ma ya shiga bayan, akan cinyarsa ya ɗora kanta ya ƙurawa fuskarta ido cikin tsananin damuwa da fargabar kar ya rasa ta, a hankali ya ɗora hannunsa akan fuskarta yana shafawa cikin rashin sanin abun yi, addu'a kawai yake a cikin ransa akan Allah ya tashi ƙafaɗun Yayarsa.
Cikin mutunen da suka biyo su suna musu Allah ya kiyaye gaba, wani ya miƙa masa handbag ɗin Abra da ledar siyayyar da suka yi. Ko kallan shi bai yi ba dan ba ta su yake ba, sai driver ne ya karɓa ya saka a front seat.
Matashin saurayin nan kuwa (Abdallah) ya kasa É—auke idonsa daga kansu, sai da Motarsu ta bar gurin sannan ya sauke numfashi ya shiga tasa motar cikin sanyin jiki, zuciyarsa cike da tsananin mamakin wani al'amari.
Asibitin Isyaka Rabi'u nan Driver'n ya kai su, saboda yanda Salman yake azalzalar shi akan ya yi sauri, asibitin kuma shine asibiti mafi kusa daga nan Ado Bayero mall É—in.
Ko gama daidaita parking driver bai yi ba Salman ya buÉ—e Motar tare da fitowa ya nufi cikin asibitin cikin sassarfa. After some minutes suka fito tare da wasu Nurses dake É—auke da kujerar É—ora marasa lafiya.
Cikin sauri Salman ya fito da Abra daga cikin motar aka É—ora ta akan wheel chair, Nurses É—in suka tura ta zuwa ciki Salman na biye da su.
Emergency suka nufa da ita. Har É—akin da aka shigar da ita Salman ya so bin su, amma aka dakatar da shi aka ce ya jira waje.
Numfashi ya sauke mai zafin gaske saboda yanda zuciyarsa take yi masa ƙuna, hoton saurayin nan a lokacin da ya riƙe hannun Abra tare da ƙoƙarin kai hannunsa fuskarta ya kasa b'acewa daga cikin zuciyarsa, ganin abun yake tamkar yanzu yake faruwa. Ga kuma damuwar halin da Abra ta shiga lokaci ɗaya, zuciyarsa sai bugawa take saboda fargaba da tashin hankali.
Dafe kansa da gumi ke kwance akai ya yi, innalillahiwa'inna'ilaihirra'un kawai yake maimaitawa a cikin zuciyarsa.
"Allah ka tashi ƙafaɗun Yaya ka ba ta lafiya."
Ya faÉ—i hakan a fili cikin tsananin damuwa.
"Me ya same ta ne wai ƙaramin Alhaji?"
Driver da ya biyo bayansu ya tambaye shi a rud'e.
"I don't know, ƙara kawai na ji ta yi, shikenan sai ta faɗi."
"Subhanallahi, to Allah Ubangiji ya ba ta lafiya."
"Ameen."
Ya amsa a ƙasan maƙoshi.
Zarya ya shiga yi a reception ɗin cikin tashin hankali, dan ya rasa a ina ma zai saka ransa ya ji daɗi, sai kallon ɗakin da aka shigar da Abra yake, ji yake kamar ya tafi ya faɗa cikin ɗakin ya ga halin da take ciki, danne zuciyarsa kawai yake yi, tunda ya san dokar asibiti ne hakan. Daga baya sai ya koma bakin window'n ɗakin yana leƙawa, amma babu abun da ya iya gani saboda glass ɗin window'n a zuge yake, kuma da akwai labule ta ciki.
Sai a lokacin ya tuna da ya kamata ya kira gida ya sanar musu halin da ake ciki.
Wayar driver ya karɓa da niyyar kiran Abbi, sai kuma ya tuna baya nan, hakan yasa ya kira number Na'ima.
Tana zaune a parlour tana karkaɗa ƙafa, idanunta akan ƙofa tana jiran shigowar su Abra ta ji dalilin da yasa su ka je suka zauna, alhalin Abran ta san za ta yi girki.
Wayarta dake kan cinyarta ce ta fara ringing, É—an tsaki ta yi sannan ta É—auki wayar ta duba, ganin Number Driver ya saka gabanta fad'uwa. A fili ta ce. "Wayyo, Allah yasa ba wani abun ne ya samu My Son ba." Ta É—aga wayar cikin sauri tare da karawa a kunne, a hanzarce ta ce. "Hello, driv...."
"Ni ne Mami"
Salman ya katse ta da faÉ—in haka.
Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi ta ce. "Salman a ina kuka tsaya ne har yanzu ba ku dawo ba?"
"Mami Yaya ce ta faÉ—i a cikin mall É—in, yanzu haka muna asibiti."
"Kamar ya ta faÉ—i? Aljanu ne da ita ko me?"
Ta yi maganar cikin yamutsa fuska.
"I don't know, ban san me ya same ta ba Mami, dan Allah ki zo asibitin yanzu."
Ya yi maganar cikin tsantsar damuwa.
"In zo in mata me?"
"Haba Mami, ki ga jikin nata mana, Æ´arki ba lafiya amma ki ce me zaki zo ki mata."
Cikin tsawa ta ce, "Ƴar karuwa dai, kar ka ƙara danganta ni da ita, na faɗa maka."
"Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un, Mami dan Allah ki daina wannan maganar, ba ki san yanda nake jin ba daÉ—i ba a cikin raina idan kika faÉ—a."
"Tunda na taɓa Uwarka ba? Ka kiyaye ni fa Salman! Ka fita daga cikin idona in rufe."
"Shikenan ki yi haƙuri, yanzu dai Please ki daure ki zo, wallahi Yaya tana cikin mawuyacin hali, numfashinta fa gaba-d'aya ya ɗauke."
"Ta mutu ma ina ruwana? Idan na zo shi ne zai saka ta warke ko me?"
"Amma zuwanki yana da muhimmanci, kin ga Abbi ba ya nan."
"To ba zan zo ba É—in, Salman ka kiyaye ni fa!" Mtss, ta ja tsaki tare da kashe wayarta.
Bin wayar da kallo kawai Salman ya yi cikin matuƙar sanyin jiki, damuwar dake cikin ransa na ƙara yawaita, ya rasa wanne irin hali ne da mahaifiyarsa, ya rasa waccen irin ƙiyayya take yiwa Abra, har yanzu jin al'amarin yake kamar a mafarki, Yayarsa a bar soyuwa a gare shi ba ƴar'uwarsa ba ce ta jini! Zuciyarsa ta kasa ɗaukar wannan al'amarin, don ya yi mata girma da nauyi.
Numfashi ya sauke mai zafi, wani irin sarawa kansa yake yi masa, tunanin kiran wayar Ammi ya yi, sai dai ya san Driver ba shi da Numbern ta, shi kuma ba shi da ita a kansa, kuma ba ya son ya kira Abbi ya sanar masa ya tayar masa da hankali. Wani tunani ne ya faɗo masa, hakan yasa shi fita waje da sauri, driver ya bi shi da ido. Motarsu ya buɗe ya ɗauko handbag ɗin Abra, cikin sa'a ya ga abun da yake nema. Numbers ɗin relatives ɗinsu ne Abra ta rubuta a cikin wata ƴar ƙaramar jotter, duk inda za su da ita take tafiya a cikin jakarta, saboda rana irin wannan, tunda su har yanzu Abbi bai ba su damar riƙe waya ba.
Ajiyar zuciya mai ƙarfi ya sauke, Numbern Aunty Iman ƴar Autarsu Abbi ya yi copy a wayar Driver sannan ya yi dialling, ringing kaɗan ta ɗaga tare da yin sallama. Bayan ya amsa ya ɗora da faɗin. "Aunty muna Hospital Yaya Abra ba ta da lafiya, na kira wayar Mami tun ɗazu ba ta ɗauka ba."
A kiÉ—ime ta ce, "Subhanallahi, me ya same ta? Kuna ina yanzu? Wanne asibitin ne?"
"Ban san me ya same ta ba, mun fita shopping ne kawai ta faÉ—i."
"Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un, ka tura mun address É—in asibitin, yanzu zan biya na É—auki Ammi sai mu taho tare, bari na kira baban Nu'aim na sanar masa."
"Toh Aunty sai kun ƙaraso."
Juyawa ya yi ya koma ciki, daidai lokacin Doctor's ɗin da suka rufu akan Abra suka fito daga ɗakin da take. Kamar zai tashi sama ya ƙarasa gare su yana faɗin. "Doctor ya jikin nata? Me ya same ta? Ta farfaɗo? Tana numfashi yanzu?"
"Ka kwantar da hankalinka, ba wata matsala ba ce, mun samu numfashinta ya daidaita, yanzu haka ta samu bacci ne sakamakon allurar da muka yi mata."
Cewar É—aya daga cikin likitocin cikin son kwantar wa da Salman hankali.
"Doctor me ya same ta to? Please ka mun bayani."
Ya yi maganar a rikice.
"Ina Mahaifiyarku ko wani babba?"
"Suna hanya sun kusa ƙarasowa."
"Ok, idan sun ƙaraso ka ce musu ina neman su a office ɗina."
Ya ƙarashe zancen tare da nuna masa inda office ɗin nasa yake da hannunsa."
Da to kawai ya amsa masa, dan ba ma wani fahimtar shi yake sosai ba, dan zuciyarsa na gurin Yayarsa cike da son ganin ta da halin da take ciki. Ko jiran a ba shi umarni bai yi ba ya tura ƙofar ɗakin ya shiga.
Ita kaÉ—ai ce a É—akin mai É—auke gadajen marasa lafiya biyu, tana kwance akan É—aya idanunta a rufe numfashinta na fita a hankali a hankali, an É—aura mata drip a hannun hagunta.
Tsayawa ya yi a kanta cikin dokawar zuciya, after some seconds ya tsugunna tare da kama hannun damanta ya ɗora shi akan kirjinsa, idanunsa a kanta cikin tsananin tausayi da ƙaunarta. A hankali ya saka ɗayan hannunsa ya shiga shafa fuskarta yana faɗin. "Alhamdulillah, zuciyata ta fara samun nutsuwa daga fargabar rasa ki, Allah ya baki lafiya My Angel!"
Kamar ta ji me ya ce sai ta ɗan motsa hannunta dake kan ƙirjinsa, ƙara ƙanƙame hannun nata ya yi cikin irin wani yanayi, a hankali ya kifa kansa a kan cikinta ya lumshe idonsa tare da sakin ajiyar zuciya, sassayan ƙamshinta mai daɗi yana ratsa ƙofofin hancinsa.
A haka su Ammi suka shigo ɗakin hankali a tashe suka tarar da su. Aunty Iman da ta yi tunanin kuka Salman yake ta ƙaraso ta dafa kafaɗarsa cikin lallami ta ce. "Salman ga mu mun ƙaraso, ka kwantar da hankalinka, Insha Allahu za ta samu lafiya, cuta ai ba mutuwa ba ce."
ÆŠago kansa ya yi ya dubi Aunty Iman da idanunsa da suka rine zuwa launin ja, cikin damuwa ya ce. "Aunty me yasa Mami ta tsani Yaya tsana mai tsanani? Ko da ba ita ta haife ta ba bai kamata ba, wannan tsanar ta yi yawa, me ta yi mata? Me ne laifin ta? Ko da abun da take tunani haka ne ai ba ita aikata ba, me yasa take huce haushinta a kanta?"
Kallon shi kawai su Ammi suke yi ba su ce komai ba, cikin ƙarfin hali Aunty Iman ta ce. "Ka yi haƙuri Salman, yanzu ba lokacin yin wannan maganar ba ne, ta lafiyar ƴar'uwarka muke yi, me ya same ta har ta faɗi ta suma?"