Sashe 123
Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Abbi ya yi ajiyar zuciya ya ce "Ki zo muje falo, ki ga wani abu".
"Ba abin da zan gani, kaje ka ƙyaleni kawai"
Major ya ce "Abin yana da mahimmanci, ki zo muje".
"Kaje ka nunawa matarka bani ba, ita ya dace taga abu mai mahimmanci daga gareka bani ba".
"Ko da kuwa abin da ya shafi Salman ne ko Abra?"yai Maganar yana kallonta. Sai kuma jikinta ya yi sanyi, Abbi ya sanya hannu ya janyo hannun Mami zuwa falo.
Afra kuwa tun da ta shigo, tangamemen hoton Abra ne da Salman ya yi mata maraba, babu yadda za'ai ka kalli hoton kace ba ita bace a jiki.
Jikinta ne ya hau rawa tana nuna wa Salman hoton. Salman ya taka ya ciro hoton ya miƙawa Afra ya ce "This is your sister, we are really missing her" yayi maganar ba tare da ya iya tsayar da hawayen da suka taho masa ba.
Salima kuwa bin su ta dinga yi da ido, tana son tayi magana, amma ta kasa magana, saboda yadda Salman ke mata kwarjini, sam yaron baya sakar mata fuska a matsayinta na matar mahaifinsa.
"Yanzu ta mutu? Yayata ce ko ƙanwata ce, ko mu biyu ne? Babu wanda ya sani sai Allah, me yasa ban haɗu da ke kan ki mutu ba? 'yar uwata me yasa kika tafi ban ganki ba, a rayuwata ace ko sau ɗaya naga jinina, yanzu idan ba a gano iyayenmu ba fa, shikenan kin mutu kin barni ni ka ɗai haba 'yar uwata" tamkar mahaukaciya, haka Afra take gunjin kuka, Salman ya karɓe hoton yana share mata hawaye, ganinta yake ba ta da banbanci da Afransa.
Mami ce ta fito tana hura hanci, hannunta ɗaya riƙe da Little, ɗaya kuma yana cikin na Abbi. Wata irin mummunar faɗuwar gaba ce ta ziyarci Mami, jikinta ya hau rawa bakinta ma haka.
Nema take ta saki Little, Abbi yai sarin karɓeta daga hannunta.
"Major me nake gani? Abra ce fa? Abra ce ko baka ganinta ne?".
"Calm down please, ba Abra bace ba kalleta da kyau".
Cikin tsawa ta ce "Ta yaya zaka cemini ba Abra bace, kalleta fa a kusa da Faris, Abra ba ta mutu ba kenan, ko kuma fatalwa ce" Salman ya taso da sauri ya karɓi Little, Mami kuwa gaba ɗaya ta birkice, Abbi ya zaunar da ita, amma ta kasa nutsuwa, sai nuna masa Afra take tana cewa Abra take gani.
Abbi ya yiwa Afra nuni da ta zo, Afra ta taso ta ƙaraso gaban Mami, aikuwa ta rirriƙeta ta ce "Abrana, Wallahi Major Abra ce kalleta fa".
Abbi ya kalli Afra ya ce "Afra, ga maman 'yar uwakki, ita ce ta riƙe Abra, wannan jaririyar kuma, ita ce wadda ta rasu ta bari, ki gaya mata ke ba Abra ba ce".
Afra ta riƙo hannun Mami cikin nata, tana hawaye ta ce "Mamanmu, ba 'yar ki ba ce wadda ki ka rasa, amma zan iya cewa 'yar ki ce ta dawo gareki, kamar 'yar uwata nima tsinta ta aka yi, aka riƙeni a wani ƙauye har na girma, mijin 'yar uwata ne yaje ƙauyenmu ya ganni, shima da fari cewa ya yi, ni matarsa ce amma daga baya ya gano, ba ita bace, ni sunana Afra ana ce mini 'yar Baba a garinmu, ni a ƙauye na tashi, Abranki kuma a birni, mijin Abra ya ce ta fini hankali da nutsuwa, da rashin hayaniya, ni kuma... Sai kuma tai shiru tana murmushi, a lokacin da hawaye ke zuba daga idonta.
"Major yanzu kana nufin ba Abra na ba ce?".
"Ba Abranki ba ce, 'yar uwatta ce" Nan Abbi ya yiwa Mami bayanin komai.
Mami ta rungume Afra a jikinta tana wani irin kuka, tamkar zata shiÉ—e, Afra ma ta rungumeta tana kuka.
Salima ta ce "Sweetheart, nifa ban gane meke faruwa ba, wannan ba ita ce 'yarka ta hoton nan da aka ce ta mutu ba?"
Abbi ya ce "Ba ita bace, zan miki bayani".
Adnan kam ko da ya isa garin Kaduna, a Asibiti ya samu masauki, saboda yadda zazzaɓi da ciwon kai suka rufe shi, sai da aka sa masa ruwa sannan ya wuce gida.
Ko da Adnan ya jewa Hajiya Mama da Abba abin da ya faru Abba ya ce "Lallai wannan lamari akwai ban mamaki a cikin sa, dan haka zuwa jibi insha Allah, zan shirya in je Kano da kai na".
Adnan ya ce "Dan Allah Abba idan ka je kace su bani Auren Afra, zan iya rasa raina idan ba sameta ba".
"In ka rasa ranka Allah ya jiƙanka, ai Nagode Allah da ya sanya yarinyar ta ce bata sonka, ni dai Adnan ba zan kuma yin jagoranci a nema maka Aure ba, da mahaifiyarka ma ta mutu dangana na yi, kaima in ka mutu Allah ya jiƙanka".
"Abba dan Allah, kai mini rai, na tuba nabi Allah na bika, ba zan sake maimaita kuskuren da nayi a baya ba"
"Sai kuma kayi Adnan, idan har ina raye babu mai aura maka 'yar uwar Abra, kaje can ka nemi wata 'yar ka aura, amma ba 'yar uwar Abra ba".
Mama ta ce "Dan Allah Yallaɓai ka sassautawa yaron nan, kalli yadda ya koma" Abba ya ɗaga mata hannu ya ce "Wannan yaron ba abin tausayi bane, kuma na gama Magana, kuma idan har ka takura sai sun baka yarinyar nan, zan tona maka Asirin irin riƙon da ka yiwa 'yar su" haka Adnan ya dinga kuka wiwi, kamar wanda uwarsa ta mutu.
"Ok Zuwa next week nake son Visa don Allah, abu ne na gaggawa ya taso mini, da yake buƙatar in je da kaina"
Hajiya Saudat ta zubawa doctor ido, tana saurarensa, sai da ya gama wayar sannan ta kalleshi ta ce "Wai ni don Allah doctor, sai yaushe zaka bawa iyayen yaron nan damar zuwa su ganka ne?"
"Sai na dawo daga tafiya"
"Ni ban ma tambayeka ba, ina zaka je naji kana maganar visa?".
Doctor ya gyara zamansa ya ce "Dubai zanje" hantar cikinta ce ta kaÉ—a, ta dube shi a firgice ta ce "Kaje Dubai kayi me?"
"Wurin wanda na ajiye zani, ai kin fi kowa sanin ina da ajiya a can".
"Me kake nufi? Me kake nema a can da babu a nan?".
Bulama ya ce "Abu mafi mahimmanci da kika sa na wofantar, dole in gano alaƙata da yarinyar da nake bincike a kai, dan haka dole in tafi Dubai"
Gaba daya ta rikice ta ce "Amma ka san zuwanka Dubai na nufin tonuwar Asirinka wataƙila ma da karayar arzikinka?"
"Ban damu ba, ida har abin da na rasa ne zai dawo gareni"
Wayar Hajiya Saudat ce ta fara ringing, jiki na rawa ganin lambar Meenal ce ta É—aga.
"Muna magana da mahaifiyar Meenal ne?".
"Eh nice"
"Ku zo nan Asibitin Health well, yarinyarki babu lafiya, ana buƙatar sa hannunku ku zo ku biya kuɗ ayi mata aikin gaggawa"
₦300 kacal, a biya kan a karanta dan Allah 08081012143
[11/17, 2:50 PM] Abk: A kiÉ—ime Hajiya Saudat ta ce. "Wacce Meenal É—in? Ban gane ba bawan Allah, me ya samu Æ´ata?"
"Idan kika zo za ki fahimta, amma fa ana buƙatar ku yi gaggawar zuwan, saboda gudun kar a rasa rayuwar ta."
Suɓucewa wayar ta yi daga hannunta ta faɗi ƙasa, cikin gigita ta ce. "Doctor wai Daughter ce babu lafiya, tana health well ana buƙatar mu je mu saka hannu za a yi mata aiki." Babu yabo ba fallasa ya ce. "Allah ya ba ta lafiya."
"Haba Doctor, ya na ga kamar ba ka damu ba, Æ´armu fa Meenal nake magana a kai."
"Damuwar da nake ciki ta fi ƙarfin wannan, ki ɗauki ATM ɗina ki je a yi duk abin da ya dace."
Bai jira amsar ta ba ya fice daga ɗakin, zuciyarsa cike da tunanin wanne abu ne yake damun Meenal da har ya kai sai an yi mata aiki ba tare da sun sani ba? Da kallo Hajiya Saudat ta bi shi cikin bugawar zuciya, mamaki da fargaba sun cika mata fal a cikin ranta, yau Bulama ne take masa maganar Meenal tana cikin mawuyacin hali na ciwo amma ya kaɗa ƙafarsa ya yi gaba? Shi da ko ciwon kai take kusan tare suke jinyar saboda yadda yake nuna damuwarsa tare da ba ta kulawa. Lallai dole ta miƙe ta nemi mafita gami da kawar da abin da ya ɗauke masa hankali daga gare su.
Cikin matuƙar tashin hankali ta zari gyalenta da handbag da wayarta dake yashe a ƙasa ta yi waje zuwa asibitin da aka ce mata Meenal tana can.