Sashe 136
Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Manyan kalaman da suke fita daga cikin bakin Salman sukai wa Afra nauyi a zuciya da sauri ta juya ta rungome Salmanun-faris a jikinta tana shassheƙar kuka wanda babu tantama na farin ciki ne.
"I love You Amore Mio, love you to the rest of my life"
"Amore Mio?" Salman ya tambaya yana ɗago ta daga jikinsa, taƙi yarda ta kalle shi sbd Kunya a hankali tana ɓoye kanta ta ce.
"My love" yana kashe mata ido ya ce "da wanne yare?" ta rufe idanu ta ce "French" ya É—ago ta zuwa jikinsa yana sauka kan bed É—in tare da nufar parlour da ita ya ce.
"Oh, ashe matar tawa ta iya speech shi ne take pretending" yana faÉ—in hakan yana kissing nata.
Abra dake zaune a parlour shigowar ta kenan tai gyaran murya kunya ta kama Salman da ita kanta Afra, Abra tai murmushi hannunta riƙe da Little ta ce.
"I'll pretend I didn't see anything".
Salman ya shafa kai yana sauke Afra data kasa kallon Abra ya ce "Yaya" ta watsa masa harara ba tare data ƙara kallon shi ba, ba sabon au bane gare ta ganin Salman ba riga shi ya sa ba taji komai ba.
Ya juya da sauri zuwa bedroom É—insa Afra kuma ta taka a hankali tana cije baki ta zauna tana faÉ—in.
"Daughter mai kama da Maman ta" Abra ta gyara zama domin Adnan ta guduwa tun É—azo yake gidan ya hanata sakat da naci.
Kuma ba tai niyyar zuwa gidan nasu ba kawai bata da zaɓi ne.
Abra na zaune bayan ta shirya cikin kayan barci ta ƙara fresh ƙirjinta ya cika sosai, tayi wani irin kyau kamar wacce batai jinya ba, fatar jikinta sai glowing take. A hankali ta zauna tana buɗe datar wayarta sbd littafin da take karantawa na IDAN BA KE ya gama tafiya da tunaninta, ita ba gwanar karatun hausa novels bace tafi ƙarfi a English. Kamar da wasa taga littafin a wattpad ta fara karantawa.
"Ikon Allah Surry muguwa ce, wannan ai muguwar shawara ce take bawa Zahrah, ta ya ya mijinta zai amshi budurcin wata a matsayin nata?" Tsaki taci gaba dayi ganin littafin yaje ending na free pages, kuma tana son taji ƙarshen labari ta ya ya Aljani zai auri mutum harda haihuwa a tsakani. Da sauri ta duba number da akai dropping 08119237616 tai adding number a WhatsApp tare da yin payment ganin marubuciyar bata Online yasa ta kashe network ɗin wayar.
A hankali idanunta ya sauka akan photon Sp Adnan Aliyu Matawalle ta sauke numfashi ta kasa tantance hukumcin da zuciyarta ke son ɗauka game da Adnan, duk da wulaƙancin da Adnan ya yi mata but till now yana da gurbi a zuciyarta tana jin tausayin shi.
Tana tuna makomar Aishatul-humaira. "You're the reason behind anything Adnan, ka rusa zuciyoyinmu"
"Uhm kafin ai É—aran akai kwanÉ—i, kafin kace uhm ake taÉ—i" Abra ta juya da sauri ta kalli Mami ta ce "Me nayi Mami?"
"Nace wani abu? Waƙa nayi, ZUCIYAR MUTUM, SIRRIN SA." Abra ta kwaɓe fuska ta ce "Kai Mami"
"Ba wani kai Mami, kije Abbinki na kira" zuciyar Abra ta buga ta miƙe da sauri kamar zatai kuka abinka da shagwaɓɓiyya ta ce.
"Mami me nayi, wayyo Allah" Mami ta saka hannu ta ɗauki Little tana faɗin "Zonan Mamana, wannan rigimar tafi ƙarfin ki muje ki yi barci" tana faɗin hakan tai waje domin ta lura da sauyawar Abra khamal Khamis ɗin.
Jiki a sanyaye ta saka hijabi tare da saka Hermes slippers a ƙafarta ta fita zuwa Main parlour. A zaune ta samu Abbi da Mami, Sai Ummi da Abdullah da kuma Salima. Tare da Adnan dake durƙushe ya saka dakakkiyar shadda amy colour wacce ta ƙara haska baƙar fatarsa, sai baza ƙamshin Pur oud yake,
Iya kyau ya zuba kyau sai ramar dake maƙale a jikinsa na azabtuwa da soyayyar Abra. Jikinta na rawa ta nemi waje ta zauna ta ce.
"Gani Abbi"
Ya gyara zama yana É—an sakin murmushi ya ce.
"Abra Daughter ga mijinki ada ya kawo abin da kike buƙata"
Ta É—aga kai da sauri ta kalli Abbi zuciyarta na harbawa tsoro da fargaba suka cika mata zuciya. Ta kasa magana sai sunkuyar da kai da tayi tana wasa da yatsun hannunta.
"Allahamdulillah Adnan ya yarda da ƙaddara ya amince da abin da kike buƙata, ya kawo takardar saki i mean divorce papers, kuma zai tafi da yarinyar shi kamar yadda kika ce,
dashi da ita bakya buƙatar su, ina miki addu'ar samun miji wanda ya fi shi, shi ma Allah ya bashi wacce ta fiki"
Bata san mai ya faru da ita ba, amma tuni hawaye ya gama wanke mata fuska ta shiga gogewa ba tare da kowa ya lura ba.
Abbi ya yi murmushi ya ce "ina tunanin ke kike son haka ko?baki da idda san haka na baki sati guda ki fito da miji ko na zaɓa miki wanda naga dama"
Mami ta ce
"Kayi mata haƙurin wata ina za taga wani saurayin yanzu?" Abbi ya ɗaga hannu ya ce. "Tunda ta ce mijinta ya saketa ai ta shirya fito da wani, ba wani wata da zan bata" ya juya kan Adnan ya ce "Allah ya yi maka Albarka Adnan da umarnin mahaifin ka da kabi, maza ɗauki Mamana Aishatul-humaira ku tafi"
Muryar Adnan a sarƙe ya ya miƙe tare da faɗin "Na gode Abbi, Allah ya ƙara girma" ya faɗa idanunsa akan Abra wacce ta kasa motsi.
Yana miƙawa Little hannu kamar mai jira ta ɗaga hannunta tana sakin dariya ya yi murmushi kaɗan tare da rungome ta.
Da sauri Abra ta miƙe ta ce.
"Ka bani Æ´ata ai ba kai ka haifar mini ita ba" Ummi dai kallon komai take hukuncin Abbi É—in ya yi mata daÉ—i domin yanzu tausayin zaryar da Adnan É—in yake take.
Adnan ya kalli Abra wani abu na fisgar shi yana jin kamar ya rungome ta ya yi ta kuka ko zata sassauta masa, zuciyarsa har wani dunƙule masa take.
"Ka bani Æ´ata Malam, ka fita daga cikin rayuwarmu, ka saki uwa me Æ´a zatai maka kuma?"
Mami zatai magana Abbi ya dakatar da ita, tare da nuna mata ta zuba idanu zuwa inda dramar zata ƙare. Adnan ya sassauta murya mai nuna ki tauyasa mini komai nayi kuskure ne ba son raina bane.
"Na rasa abin da kike nufi? Kince na sake ki? Kuma kince na ɗauki ƴata dani da ita bakya buƙatarmu, mene laifina saki ke kika nema fa? Ƴa kuma ta wace" a fusace Abra ta wani lailayo zagi zatai komai ta tuna kuma Ohu! Taja baki tare da yin shiru.
Idanunta ya yi jaa sosai ta juya wajen Abbi ta ce
"Abbi kace ya bani Æ´ata? Tunda ya yi abin da zuciyar shi take so nima zan yi abin da nai niyya"
"A'a ba ruwana Daughter,bana son rashin gaskiya ke kika bashi zaɓi kuma yabi, Son kada dare ya yi maka" Abra ta fashe da kuka sosai tare da shigewa part ɗin ta, ta shiga kiran number Abba da Hajiya Mama amma duk basu ɗauka ba kamar haɗin baki.
Ta shiga rera kuka a yanzu babu abin da zuciyarta ke muradi da son kasancewa da ita irin Aishatul-humaira gashi Adnan ya yi amfani da maganar da tayi wajan rabata da gudan jikinta. MAGANA ZARAR BUNU.
Tun daga lokacin Abra ta shiga gaba da kowa ta yini kuka ta kwana kuka, Salman da kansa ya bawa Abbi haƙuri akan a bawa Abra ƴarta. Amma Abbi ya yi masa korar kare.
Ummi taja Abra jikinta ta shiga yi mata nasiha akan ta koma gidan mijinta daga nan ta ƙwato ƴarta ko kuma ta koma sbd yarinyar badan halin Adnan ba.
Hajiya Mama ta ci-gaba da kula da Little yarinya mai shiga rai. Æangaren Salman da Afra soyayya mai zafi ake tun tana jin kunyar shi har ta daina ya shagwaÉ“ata da tarin soyayyar shi da kalar nasa salon mai mantar da duk wanda Æ´a mace duniyar da take ciki. Har ta kai idan ba shi sam ba zata iya bacci ba ta sama da rayuwar auren kamar yadda yake buri tattali take samu sosai cikin sati guda daga Salman har Afra suka Æ™ara wani haske da Æ™ima Masha Allah.
Ummi da Abdullah suka koma Dubai bayan an mata al'ƙawarin zuwan twins ɗin nata, burinta na son tafiya dasu bai cika ba, Dr Bulama har yanzu yana tsare domin an gano manya-manyan laifukan daya aikata a asibitin shi da ɗaukan ma'aikatan wanda sam basu dace ba, uwa uba kuma Ummi ta ƙara sawa akai masa sammacin cinye mata dukiya da ya yi, domin har yanzu wasu kuɗin basu fita ba, tare da cewa ya bata takardar sakin ta.
Wannan abu ya zaga ko'ina har kunan gwamna, aka shiga binciken ko wanne asibiti tare da tabbatar da ingancin ma'aikatan. Aka ƙi bada belin Dr Bulama yana tsare labarin ya ɗaga hankalin Abra da Afra duk da laifin na Mahaifinsu ne amma ta wani ɓangaren suna tausaya masa ainun.
A week later.
Tana durƙushe gaban Abbi tare da sauraran abin da zai faɗa mata, zuciyarta sai bugawa take..
Abbi ya gyara zama ya ce "kamar yadda na baki umarnin sati guda ki fito da miji, na zuba miki ido amma shiru, to a yau bayan sakkowa masallaci na ɗaura miki aure da wanda zuciyata ta amince da shi, ga sadakin" ya faɗa yana miƙa mata damin kuɗi a lokacin nan idanun zuciyarta yarinyarta Aishatul-humaira da tsohuwun mijinta Sp Adnan Aliyu Matawalle kawai suke hango mata, har bata gane mai Abbi yake ce mata.
"Daughter?" Ya kira sunanta da ƙarfi ta saurin cewa "Na'am Abbi" ya kalleta da kyau ya ce.