← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 145

Sashe 92

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wai kai ina ruwanka da Madam É—in nan da kullum sai ka tambaye ta?".

"To tambayar ma laifi ce kenan?"

Adnan ya ce "Eh kusan haka, dan da bata lafiya ba zaka ganni a kan kujerar nan ba".

Usman yayi murmushi ya ce "Yayi mijin balarabiya".

"A daina tanka mini mata dan Allah, duk bakinku ya sa ta fara duhu"

"Eh tunda gamu mayu ba".

"Ni dai bance ba" Adnan yayi Maganar yana murmushi.

Adnan ya ce "Wai ni ya batun Meenal ne, na jika shiru, ka rigani haÉ—uwa da ita fa kan in haÉ—u da Abra, amma haryanzu shiru, kar kayi wasa da hankalin 'yar mutane fa".

Usman ya ce "Hmm"

"Ban gane hmmm ba?"

"Sp zancen babu daÉ—i ne sam, ni na fasa Auren Meenal"

"Amma mai yasa?"

"Abubuwan babu daÉ—i ne sam, amma zan maka bayani".

"Allah ya sa ba daga gurinka aka samu matsalar ba Usman?"

"Ba daga gurina bane, amma nasan ko kaine, abin da nayi shi zaka yi".

"To shikenan Allah ya tabbatar da alkhairi" suka gama hirar aikinsu.

Suna magana amma hankalin Adnan yana kan Abra, haka ya lallaɓa ya kai azahar, yayi sallah ya tafi gida.

Yana zuwa gida ya nufi ɗakin Abra, amma ya tarar ba ta ciki, kayanta da ta cire a ƙasa a tsakar ɗakin.
Ya buɗe ƙofar banɗaki, amma bata ciki.
Ya shiga ƙwala mata kira "Abra! Abra!"

Ya duba kitchen amma ba ta nan, ya tafi É—akinsa amma nan ma ba ta nan.
Nan hankalin Adnan ya fara tashi, da ya tabbatar da Abra ba ta gidan gaba É—aya.
"Ina yarinyar nan ta shiga haka?" Ya tambayi kansa, gashi babu waya a hannunta balle ya kirata.

Waje ya fita yana lelleƙawa, amma layin nasu tsit yake, ba kowa balle ya tambayi wani.
Bai sare ba ya shiga bi gidajen dake kusa da nasu, yana ƙwanƙwasawa yana tambayar masu gadi, idan Abra taje amma ko ina sai suce su basu ganta ba, ba taje ba.

Abra kuwa bayan ta isa titi, mai napep ta samu ta gaya masa sunan unguwar su Adnan, da suka isa unguwar, tace mai napep É—in ya tambayi gidan Aliyu Matawalle.
Ya ce mata ai yasan gidan, ya kaita har ƙofar gidan.
Ta biya shi kuɗin motarsa, ta sauka ta shiga gidan tana bin bango, saboda tsananin ciwon da kanta yake mata, da kuma zazzaɓin da ya addabeta.

Mai aikin hajiya Mama ce ta buɗewa Abra ƙofar falon, tana ganin Abra ta fara murmushi tana mata sannu da zuwa, Abra ta jinjina mata kai kawai, ta wuce cikin falon ta zube a kan kujera tana maida numfashi. Mai aikin ce taje ta kirawo Mama, tana fitowa ta tarar da Abra a kwance a kan kujera, tana sauke numfashi da ƙyar.
Da sauri Mama ta ƙarasa in da Abra take tana faɗin "Abra lafiya kuwa?" Tayi maganar tana dafa kan Abra, jikin Abra zafi rau.
Mama ta kalli mai aikinta ta ce "ÆŠauko mini wayata in kira likita".

Ta kuma kallon Abra ta ce "Ina Adnan É—in yake?"

Cikin rawar murya Abra ta ce "Ya tafi gurin aiki, ni kuma naji zan mutu shine na taho nan"

"Amma wane irin rashin hankali ne Adnan yayi haka? Yaya za ayi matarka ba lafiya ka tafi aiki ka barta?"

Mama ta kira likita a waya, sannan ta sa aka haÉ—awa Abra Abinci, ba ta ci da yawa ba, ta dinga amai.

Likita ya ƙaraso gidan Hajiya Mama, ya yiwa Abra tambayoyi, ya yi mata allurai ya samata ruwa sannan yace da Mama "Idan jikin nata yayi sauƙi zuwa yamma shikenan, idan Allah ya kaimu gobe zan dawo in kuma duba jikin nata, sai ku taho da ita Asibiti for further investigation".

Mama tace "to shikenan"

Abra taji daÉ—in jikinta sosai, har sakwara Mama ta sa aka yi mata, ta samu ta É—an ci.

Abra ta ce "Mama dan Allah ki bani aron waya in kira su Mami".

"A'a Abra, ba zaki kirasu ki É—aga musu hankali ba"

Abra ta marairaice ta ce "Mama tunda nayi Aure fa ya ƙwace mini waya, bana waya da kowa a gida, ba ɗaga musu hankali zan yi ba".

'mai yasa ya ƙwace miki wayar?"

Abra ta ce "Nima ban sani ba"

Mama ta girgiza kai ta bata wayarta.

Wayar Abbi ta fara sanyawa ta kirashi, bugu biyu ya É—aga "Hello Abbina".

"Daughter na, ya kike ya jikin naki?"

"Da sauƙi Abbi, ina Mami?"

"Mami tana bacci".

"Abbi ka tasheta ka bata muyi magana, tunda na bar gidan fa banyi waya da ita ba".

Duk da Abbi baya shiga sabgar Mami, amma saboda farincikin Abra ya tafi ɗakin Na'ima, ya miƙa mata waya. Ta kalleshi da mamaki ta ce "waye?".

"Ki karɓa kiji".

Ta karɓa ta kara wayar a kunnenta.

'Hello Mami"

"Na'am Abra"

"Mami ba kya nemana ko? Kin ƙi zuwa gidana"

Na'ima ta ce "Na nemi wayarki na ta shiga, kuma mijinki idan aka kira shi kullum baya nan".

"Mami to ba zaki zo ba?"

"Zan zo mana, amma jira muke a gama haÉ—a kayan garar ki, sai mu taho gaba É—aya".

"Haba Mami, ni dai kawai ki zo dan Allah, in ba haka ba ni zan dawo gida".

"A ina kika taɓa ganin an yi haka? Ki kwantar da hankalinki zan zo insha Allah".

"To Mami yaushe?".

"Ba zan sa miki rana ba, amma zan zo insha Allah"

Bayan waya da Mami, Abra har su Ammi ta dinga kira a waya, tana musu koke koke, sukai mata alƙawarin za so zo.

Adnan fa hankalinsa yayi ƙololuwar tashi, ya rasa abin da yake masa daɗi, dan ya fara tunanin sanar da hukuma.
Kafin yayi hakan, ya É—au motarsa ya nufi gidansu, cike da zullumi da tunani.
A falo ya tarar da Hajiya Mama, tana ganinsa ta ce "Yawwa dama kai nake nema".

"Lafiya kuwa Mama?".

"Dole ka tambayeni lafiya mana, ka fita ka bar Yarinya a gida babu lafiya, Allah yasa tayi kyan kai ta fito ta taho nan, a galabaice ta ƙaraso gidan nan".

Adnan ya ce "Alhamdilillah, dama nan ta taho?".

"Ban sani ba" Mama ta bashi amsa, Adnan ya sunkuyar da kai yana sosa ƙeya.

"Tana É—akina, likita ya bata magunguna ya sa mata ruwa, yace gobe in Allah ya kaimu kuje Asibiti ai mata teses".

Adnan ya jinjina kai ya miƙe, ya nufi ɗakin Mama ya tarar da, Abra a kwance a kan katifa da ruwa a jikinta, hannunta ɗaya riƙe da wayar Mama.

"Da iznin wa kika fita ki ka bar gida? Kika bar mini gida a buÉ—e ba kowa?"

A hankali ta É—aga idanunta ta kalleshi, ta É—auke kanta ta mayar kan waya.

"Ba Magana nake miki ba".

"Dan Allah ni ka ƙyaleni in ji da kaina, idan ba haka ba Wallahi saina faɗi irin zaman da muke kowama yaji gayyar ta watse in huta da bala'inka da zaluncinka".

"Ni kike gayawa haka?".

"Na faÉ—a, idan kana da wuta ko Aljanna ka sani a ciki".

Ƙwafa yayi, ya fisge wayar hannun Abra ta Mama, ya fito falo.

Ya miƙawa Mama wayarta, Mama ta ce "Yauwa, maiyasa ka ƙwace mata waya ne? Ko waya bata yi da mutan gidan su".

"Wallahi Mama takura musu da koke koke take tana É—aga musu hankali, a kan bata da lafiya".

Mama ta ce "ba hujja ba ce, ka bata wayarta, umarni nake baka, wannan ai mugunta ce, ka hanata waya da mutan gidansu akan me?".

"Shikenan zan bata, bari ruwan ya ƙare in ɗauketa mu tafi".

"A'a ka bari sai Allah ya kaimu dare"

Cikin ikon Allah zuwa daren, Abra ta ɗan watstsake sai rashin ƙwarin jiki.

Ji take kamar tace ba zata bin Adnan ba, amma ta dake ta tashi suka tafi. Suna tafe ba wanda yake tankawa wani har suka isa gida, kusan ƙarfe sha ɗaya na dare.

Ba ta saurari Adnan ba ta wuce É—akinta, ta gyara ta kwanta.

Da safe kafin ya fita aiki ya shigo É—akin, ya tarar da ita a zaune a kan gado, dan fitowarta kenan daga wannan aman da take.

Ya cillo mata wayarta ya ce "gata nan, kin haɗani da mahaifiyata ta sa na baki wayarki, amma Wallahi muddin kika kuskura naga kina waya da wancan sakaran yaron ko makamancin haka Wallahi sai na ƙwace".

"Wallahi ba sakarai bane, Faris ba sakarai bane dan ya fiye mini kai".

Da wani irin mugun kallo ya bi Abra "Ni kike gayawa wancan shashashan ya fini?".

"Eh, ya fiye mini kai, dan tsawon tasowata ya bani kariya da kulawa, kai kuma a zamana da kai ba abin da na tsinta banda ɓacin rai da tashin hankali a kan abinda ban san tushensa ba, wanda yayi maka laifin ma ban sanshi ba balle in san laifin da aka yi maka, dan haka na faɗa Faris ya fiye mini kai"

Janyota yayi daga kan gadon, ya tsaida ita a kan ƙafafuwata, "Wallahi Abra idan kika kuma Magana a kan wannan banzan Salman ɗin saina casa ki".

"Wallahi Salman ba banza bane, kar ka sake ce masa banza"

Sauke mata wani lafiyayyen mari yayi ya ce "Nine banzan kenan?".

"Wallahi Adnan kaci amanata, ba zan yafe maka ba, kai da Allah" hankaɗeta yayi a gurin ta zube, ya dinga wani irin huci, dan ya tsani yaji tana ambatar sunan Salman, sai dai ya ga Abra bata motsi, ga jini ya fara bin ƙafarta.
Sai kuma ya nutsu, ya sunkuya ya ɗagota, amma bata motsi sai jini da yake bin ƙafarta.

Sai kuma ya gigice, ya ɗagota jikinsa amma yaga jikinta ya saki, ba shiri ya miƙe ya gyara mata jikinta, ya sata a mota sai Asibiti.

6hrs later
Abra ta buɗe idanunta, dishi-dishi take gani, a hankali ta gama buɗe idonta, ta kalli ruwan da ke shiga jikinta, da ƙyar ta tashi zaune, Adnan ya taso daga in da yake, kan ya ƙaraso Abra ta fizge ruwan nan daga jikinta.

"Ke meye haka?" Ai bai rufe baki ba ta fara ƙoƙarin dirowa daga kan gadon.

Aikuwa jini ya ɓalle ta jikin cannula hannunta, Adnan ya ƙaraso ya riƙeta yana faɗin "Abra kin yi hauka ne?"

Duka ta dinga kaiwa Adnan a ƙirjinsa, tana ƙoƙarin fizgewa daga jikinsa.

"Abra ki nutsu meye haka? Akwai ƙaramin ciki a jikinki, da yake barazanar zubewa ki nutsu".
Chapter 92 · 0% Book details