Sashe 5
Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gaba É—aya ganinta take kamar a wata duniyar ta daban, Madam Halima taiwa yarinyar nan wanka tsaf, aka samo wata rigar aka saka mata, aka kwantar da ita akan gadon marasa lafiya, ba ta umm ba ta um'um, sai aukin rarraba idanu, babban burinta bai wuce ta ga wannan mutumin da ya É—akkota daga hannun wannan mutanen ba.
Sai dai ba ta san in da aka kai shi ba, wasu mutanen ne daban suke zuwa suna duba ta, suka dinga soka mata allura suna É—ibar mata jini, sai da suka saka ta kuka, dan haka gaba É—aya tsoron gurin take ji.
"Ashhadu alla ila ha illallah, Rabbana alaika tawakalna wa ilaika anabna wa ilaikal masir" shine abunda ya ke ta maimaitawa, tare da ƙoƙarin buɗe idanunsa a hankali.
Dumm yake ji a kansa, ga shi dishi dishi yake gani, a hankali ya cigaba da lumshe idonsa yana buÉ—ewa har Allah ya sa ya buÉ—e su yana ganin komai clearly.
"Congratulations Captain, you survive" wani matashin likita ya faÉ—a yana murmushi.
A hankali ya yunƙura zai tashi zaune, amma Likitan yai saurin cewa "No relax, ba'a daɗe da fitowa da kai daga tiyata ba, mun cire maka bullet a cikinka ne.
Ajiyar zuciya yai yace "Alhamdilillah, yaran fa suna ina?"
"Suna nan tare da mu a cikin Asibitin nan, ana musu gwaje gwaje kan a sada su da 'yan uwansu"
Kamar dirar mikiya, haka yarinyar da ya tsinta ta faÉ—o masa, da sauri ya ce "There was one little baby, da na samo a cikin dajin, tana ina?"
Likitan ya ɗan yi shiru sannan yace "kai gaskiya ni banga yarinya ƙarama a cikin yaran nan ba, duk 'yan makaranta ne"
Da sauri ya ce "No, their is one little girl, ba tafi 3 years ba, wata fara haka"
Doctor ya ce "Please calm down, kaga yanzu muka fito da kai, ka kwantar da hankalinka kar jininka ya hau".
Captain ya girgiza kai yace "dole a nemo ta, she's not among the students, ba a cikin su take ba".
"Shikenan is ok, za'a nemo ta insha Allah, bari inje in duba amma for now, dan Allah ka kwanta ka samu nustuwa"
"Nutsuwata É—aya, shine a ga yarinyar nan"
"Ok, bari inje a duba".
Captain ya koma ya gyara kwanciyar sa yana lumshe ido.
Doctor da yaiwa Captain aiki ya cire masa bullet ya fita, dan neman yarinyar da Captain ya saka shi.
Sai dai duk iya binciken da yai, babu wanda ya ga yarinyar, kowa ya tanbaya sai ya ce bai ganta ba, iya É—aliban nan suke nan babu wata yarinya 'yar shekaru uku a cikin su.
Har mutuary ya je, ya duba cikin gawarwakin yaran, amma babu wata yarinya ƙarama a cikin su.
Komawa É—akin da Captain yake yai, ya tarar an zaunar da shi, wani likitan ya kammala yi masa dressing É—in in da ya samu rauni a bayansa.
Ɗagowa Captain yai ya ɗan tsura masa idanu, yana jiran jin amsar da zai ba shi, duk da kasancewar likitan soja ne, amma sai da gabansa ya faɗi da irin kallon da Captain ke masa, saboda kasancewar sa mutum me matuƙar kwarjini.
"Am.. duk cikin yaran nan an duba ba ta ciki, kuma har gawarwaki na duba amma babu ita a ciki, kowa na tambaya sai ya ce babu wata yarinya ƙarama a cikin yaran da aka kuɓutar duk matasa ne 'yan makaranta.
"Impossible" Captain ya faɗa yana ƙoƙarin tashi.
Saurin riƙe shi su kai suna cewa yayi haƙuri.
"Ya za'ai yarinyar da na saka a Mota, ace ba'a ganta ba, a gabana fa ta shiga Motar?"
"Ka yi haƙuri a sake dubawa za'a ganta".
"No, zan duba da kaina" yai maganar yana ƙoƙarin miƙewa, sai dai jiri ya kwashe shi, da tsananin azaba da cikinsa ke yi, hakan ya tilasta masa komawa ya zauna.
Comment and Share please
Nimcyluv
Ayshercool
Zee kumurya.
[9/30, 8:55 PM] Abk: *✷ DARE DA DUHU ✷*
_Bright pensâœðŸ¾_
Nimcyluv
Ayushercool
Zee kumurya
*4.....*
Elegant Online writer's
_Kuyi following wannan acct É—in a Arewabooks_
https://arewabooks.com/u/nimcyluv
Captain Khamal ya yi saurin zame kan matarsa dake kafaÉ—arsa, idanunsa ya ware tare da sakin kwantaccen Murmushi, saboda ganin waÉ—anda suka shigo Room É—in. Babbar mace ce, fara tas da ita zata iya yin shekaru hamsin a duniya.
"Finally, my son survived Alhamdilillah" Hajiya A'isha ta ce, tana ƙarasawa bakin gadon da Major Khamal yake kwance.
Lumshe idanunsa ya yi, He breathed slowly kafin ya ware idanunsa akan matar cikin ƙasa da murya yace.
"First love" Ya Faɗi maganar yana ƙara sakar mata Murmushi. hannunsa ta kama tare dayi masa ƙuri da Idanunta, she tries to understand, if there is something wrong with him.
A Hankali tace "Hankali na, ya tashi sosai Babana, na kasa samun nutsuwa bana son aikin nan naka, kullum cikin zullumi nake da tashin hankali" Captain Khamal ya kama hannun Hajiya A'isha wacce ta kasance Uwa a gare shi, ya É—an yi murmushi yace
"First love, ba gashi kinga lafiya nake ba? Zan warke insha Allah"
"Tsoro take kada a kashe mata Jaruminta" Da sauri Captain Khamal ya É—aga kansa, with so much surprise yake kallon mai maganar, Sai a lokacin ya kula dashi.
"Baffa" Captain ya ce, yana ware idanunsa akan mahaifinsa dake tsaye cikin shigar manyan kaya, kamarsa da Major Khamal ta bayyana sosai, hatta baƙar fatar Captain irinta Baffa ce.
Baffa ya harari Khamal, cikin wasa ya ce "An manta da Baffa saboda anga first love? Shine ni aka ƙi kulani"
"It's not like that, Baffa" waje Baffa ya nema tare da zama cikin tausayin É—an nasa ya ce "Ya jikin naka?" .
"Jiki Alhamdilillah Baffa"
Jinjina kai Baffa ya yi yana kallon wajan da aka harbi Khamal, cikin sanyin murya Baffa yace
"I received a call on phone, from the military command in Abuja, sun gaya min Wanda suka rasa rayukansu a dajin, hankali na ya tashi sosai, mun É—auka ko har da kai, Sai daga baya muka samu full information akan cewar kai raunuka ka samu"
Captain dai murmushi yake, yana son iyayensa bashi da kamar su.
"Yaya K, ya jiki?" Cewar wani matashin saurayi. Khamal ya kalli ƙaninsa Shureim yace "You?" Shureim ya kwaɓe fuska tare da faɗin "Duk na damu zan rasa Big bro, shine ya kula kowa banda ni"
"Sorry Shureim"
Shureim ya ce "Ya jikin Yaya K?" Captain ya rufe idanunsa A hankali ya ce "I'm good" surutun da yake yi, gaba É—aya ya fama masa ciwon, yana jin yadda gurin yake masa zafi sosai.
Na'ima dake gefensa, ji take kamar ta É—auke mijinta su tafi gida haka take ji. Tayi kewarsa sosai, har tsanar aikin take saboda tsayin lokacin da suke É—auka basa tare.
Army Doctor ɗin daya shigo ne, ya kalli su Baffa cikin sakin fuska ya ce "Ana buƙatar ya samu nutsuwa, wajan harsashin bai warke ba haryanzu"
Baffa ya miƙe tsaye, Yana faɗin "Daman da yaya aka barmu muka shigo ganinsa, tafiya za mu yi tunda kun mana fin ƙarfi" Dr ɗin dai murmushi ya yi, Baffa ya yi waje. Hajiya A'isha ta kalli Captain ta ce "Allah ya ƙara sauƙi Babana, Zuwa yaushe zaka dawo gida ka huta?".
"First love ban sani ba, but Soon in sha Allah"
ta ce "To, Allah ya tsare min kai"
yunƙurawa ya yi zai tashi da sauri Na'ima ta kamashi tana faɗin "Be careful"
Duk yadda yaso miƙewa kasawa ya yi, Dole ya koma tare da zama ya ce "Allah ya kiyaye hanya first love" fita duk sukai hadda Shureim.
Na'ima ta kalleshi tace "My man, ni ina nan tare da kai ko?"
Ya ware Idanu ya ce "Are You sure?" Kai ta É—aga masa tana kama hannunsa tace "I really really miss you Man, Over eight months banji É—umin ka ba"
hancinta ya ja "I miss you both, i mean you and my unborn child" Lamo tai a kafaÉ—ar sa, kewarsa na fisgarta, She misses every single thing about him, she wants to be with her husband.
Madam Halima kuwa ta rasa ya ya zatai da Yarinyar kuka kawai take tana kiran "Abbi" cikin damuwa da kuma son rarrashin Yarinyar Madam Halima tace
"Me kike so?" Yarinyar
Taƙi cewa komai, domin bama ta gane me Madam Halima ta ce ba.
Madam Halima tace "Jama'a na shiga Uku, wacce irin yarinya ce wannan?"
Miƙewa ta yi tare da zama kusa da yarinyar cikin rarrashi tace.
"Kin ga stop crying, A good child never cry."
Ƙanƙame jikinta tayi, bata so ko taɓa ta ayi, She's afraid of everything. Babu wanda take son gani sai Mutumin daya ɗakko ta, Idanunta na hango mata shi cikin jini.
Da hannu Madam Halima tai mata nuni irin Sign language É—in nan tace.
"Ke, kuka ki daina babu kyau".
"Abbi..."
Yarinyar Ta faɗa da ɗan ƙarfi, shiru Madam Halima tai, ko mahaifinta ne Abbi?.
Kallon yarinyar tayi, fara ce sosai, irin farin nan ƙal, But she looks very similar to Arabs, her eyes, hair, almost everything.
"ماذا تريد اين والدك"
Ma'ana "me kike so, ina mahaifin ki yake?" Madam Halima ta tambayeta da larabci, a tunaninta tunda tayi mata kala da Larabawa, may be tana jin larabci, bata san cewa gaba É—aya maganar ce ba sosai take jinta ba.
Cikin rarrashi ta ce
"Kee, yanzu zan kira Abbinki.. kina so?" Da sauri ta ɗaga mata kai tana mata ƙuri da Idanunta, ta fuskanci hakan ne saboda bakin Madam da ta kalla, Madam Halima tai Murmushi tana bata Teddy tace "sai Kinyi bacci Abbi zai zo, kwanta" tai mata alama da data kwanta, ganin ta sake ambatar Abbi yasa Yarinyar kwanciya ta sakin ajjiyar zuciya, kana ganinta kasan akwai ɓoyayyan abu a tattare da ita.
Sai da Madam Halima taga tayi bacci, ta zare mata yatsarta dake baki, a firgice ta farka tana shirin sakin kuka Madam Halima ta mayar mata da yatsar bakinta.
Duk a wahale take, ta jima Idanunta bai ga bacci ba, ihun dabbobin jeji, da kuma tsoro yasa bata wani baccin kirki. Girgiza kai Madam Halima tayi Ubangiji kaÉ—ai yasan halin da Yarinyar ta shiga, ko Æ´ar ina ce? Su waye iyayenta, they are alive or dead, Ohho!?. Wayarta ta É—auka tare da kiran Lieutanant Faruk, ta faÉ—a masa She wants to see him immediately.