← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 145

Sashe 40

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin sauri Khamal ya ce. "Ki yi haƙuri abun bai kai haka ba." Sannan ya kalli Nai'ma ya ce. "Ki ba ta haƙuri." Kafin ya gama rufe baki Granny ta ce. "Kamalu mahaukaciya ka mayar da ni ko me? Uban haƙuri za ta ba ni ba haƙuri ba, to ba zan haƙuran ba, wallahi in dai ƴar halak ce ni sai wannan abar ta bar gidan nan a yanzun nan, munafuka ta san ba ta da gaskiya ai, sai fiƙi_fiƙi take da ido."

Marairaicewa Nai'ma ta yi ta ce. "Dan Allah Granny ki yi haƙuri, duk da ban san laifin da na aikata ba."

Mitsss, ta ja dogon tsaki tare da ƙanƙance ido tana jefawa Nai'ma wani irin kallo ta cikin glass, ba tare da ta yi magana ba ta fice daga parlour'n fuu tana faɗin. "Ka nuna mini ban isa da kai ba, bari na saka a kira mini wanda ya isa da kai, shi ai bai isa ya ƙetarewa umarnina ba."

"Oh My God, rigimar Granny ta yi yawa, mene fa'idar wannan abun da ta zo ta yi?"

Hawayen munafurci Na'ima ta fara ta ce. "Ban san me na yiwa Kakarka ba Khamal ba ta so na, kullum zancenta za ta ƙaro maka Aure, ko kuma ta ce ka rabu da ni." Cikin rarrashi Khamal ya ce. "Halin Granny ne ba ki sani ba Wifey ko me? Rikicinta ne kawai ba wani abu ba, idan ya tashi kowa ma yi masa take babu wanda ta ƙyale."

"Wannan ba rikici ba ne Khamal, tsana ce kawai."

Daidai nan Granny ta dawo hannunta riƙe da wayar Driver ta miƙawa Khamal. Ba tare da ya karɓa ba ya ce. "Me zan yi da ita?"

"Huhuhu, yau na ga jaraba, to wacce ta yi cikinka ta tsuguna ta haife ka ce take son magana da kai." Granny ta faÉ—i haka kamar za ta ki fa masa mari.

Karɓar wayar ya yi ya kara a kunnensa. Kafin ya yi magana muryar Ammi ta doki kunnensa a kausashe da faɗin. "Khamal ka yi abin da Granny ta ce."

"Amma Ammi..."

"Ba na son jin komai, ka yi ko mene ne, daga baya ma yi magana."

Jiki a sanyaye ya ce. "Shikenan." Tare da katse wayar. Kallon Nai'ma ya yi ya ce. "Ki je gidan, I will come tomorrow." Fashewa da kuka ta yi ta ce. "Yanzu Khamal yau ni kake kora daga gidanka? Ni Nai'ma uwar Ƴaƴanka kake cewa in bar maka gida?"

"Babu yadda zan yi ne Nai'ma, umarnin mahaifiyata na bi, but don't worry, everything will be okay insha Allahu." Daga haka ya miƙe ya nufi part dinsa.

"A tashi a tashi da Allah, gida ne tunda ba na Ubanki ba ne sai kin bar shi wallahi, kuma a cikin satin nan zan aurawa Kamalu zankaÉ—eÉ—iyar budurwa, kuma ta cikin gida ce ba bare ba, bari uban nasa ya dawo."

A zuciye Nai'ma ta goge hawayen fuskarta tare da miƙewa tsaye ta nufi ɗakinta kamar za ta tashi sama. Tafa hannuwa Granny ta yi ta ce. "Au da bangaje ni za ki yi? To Uwarki kika yi niyyar bangajewa ba ni ba, kuma gidan jikana yau dole a bar shi." Guri ta samu ta zauna ta kunto goro dake ɗaure a jikin zaninta ta basga tana karkaɗa ƙafa, idanunta akan ɗakin Na'ima."

Sai da Granny ta ga fitar Nai'ma daga gidan sannan ta tafi, zuciyarta fess yau ta kawo ƙarshen iskancin Na'ima.

Fayyad na gaba Adnan yana bin shi a baya suka shiga parlour'n gidan, wata farar matashiyar matar dake zaune akan kujera ta amsa musu sallamar da suka yi cikin fara'a.

"Wow Masha Allah, yau ga Sp Adnan a gidana, kullum ana mini hirar ka, yau ma tun safe ake maimaita mini zaka zo, welcome." Ta faɗi haka tana miƙewa tsaye.

Murmurshi Adnan ya yi bai ce komai ba, gurin zama Fayyad ya nuna masa ya zauna. A hankali ya ce. "Yana yi miki gulmata kenan Maman Boy?" Still tana murmurshi ta ce. "Sosai ma, kai dai a yi shiru kawai." Fayyad ya zauna a gefensa ya ce. "Ai bana gulamar tuzurai sai ta Ma'aurata." Ko kallon shi Adnan bai yi ba. Dariya Maman Boy ta yi ta haye upstairs.

Tare suka dawo da wata budurwar yarinya, wadda da alama K'anwarta ce saboda kamar da suke. Tunda suka sauko ta zuba wa Adnan na mujiya, har plate ɗin da ta ɗoro drinks a kansa ya kusa suɓucewa daga hannunta, cikin son burge shi ta gaishe shi, ba tare da ya ɗago ba ya amsa mata. Maman Boy ta miƙa masa Boy sannan suka koma saman.

Suna shiga ɗaki K'anwar Maman Boy ta ce. "Wow amma Aunty guy ɗin nan ya haɗu, ga kyau ga aji, yanda kika san irin Black Americans ɗin nan, ni na taɓa ganin baƙin mutum mai kyan shi kuwa?"

"Kai Ramlah uwar zuzuta, daga ganin mutum sau ɗaya har kin ƙare masa kallo?"

"Aunty ba za ki gane ba ne, amma guy É—in ya haÉ—u over, Matarsa ta more."

Murmurshi Maman Boy ta yi ta ce. "Ko dai kin ƙyasa ne?"

"Rufa mun asiri, kar Matarsa ta ji ta mun duka, kawai dai na faÉ—i abun da yake da akwai ne, kin san ni ba na gani in yi shiru."

Maman Boy ba ta kuma cewa komai ba, Ramlah kuwa cigaba ta yi da yaba kyawu da zubin halitta irin na Adnan.

"Ka sha juice É—in mana, ka wani lumshe ido ina magana ka mun shiru, tunanin me kake?" Fayyad da ya gama zuba drinks a cikin glass cup ya faÉ—i haka.

Ba tare da ya buÉ—e idon ba ya ce. "I'm okay, thank you."

"Wannan ai wulaƙanci ne, Matata ta kawo maka abu amma ka ce ba za ka sha ba."

"I will drink, amma ba dan kai ba."

"Na ji É—in, Malam ka faÉ—i gaskiyar abin da yake damun ka, ka zo Æ´anmatan Kano sun ruÉ—a ka shine kake wani babbasarwa, wannan yanayin da kake daga gani na fall in love ne.

"Ka fi kowa sanin ba ni da time É—in shirme ko?" Ya yi maganar yana gyara kwanciyar Boy da ya yi bacci a jikinsa.

"Allah ya nuna mun ranar da ka zo kana cewa, dama Fayad haka so yake, lokacin zan ci dariyata in more, wai wa ya ga su Adnan ana Baby please sorry, you know I love you more." Ya ƙarashe maganar cikin dariya.

Taɓe baki kawai Adnan bai ƙara magana ba.

Abra ba ta nan Granny ta zo, kuma har ta tafi ba su dawo ba, saboda sun biya siyo school bag ita da Salman bayan sun baro gidan Aunty Iman, saboda normal handbag ba za ta É—auki tarkacen school ba. Ba su farga Nai'ma ba ta gidan ba sai da daddare lokacin dinner, saboda sun saba idan Khamal yana gari kodayaushe tana part É—insa.

Ganin Khamal ya fito shi kaÉ—ai yasa Salman ya ce. "Abbi Mami fa? Tunda muka dawo ban gan ta ba, na je É—akinta ba ta nan."

"Ta je gidan Mama." Ya ba shi amsa

"Mama kuma? Lafiya?" Ya tambaya cikin mamaki.

"Lafiya ƙalau."

"Yaushe za ta dawo?"

"Gobe."

"Me ake yi a can Abbi?"

"I don't know, Mama ce ta kira ne za su tattauna akan something important."

"Me ne abun?"

"Na ce maka ban sani ba, Family issue ne, ka zama É—an jarida ne Salman da za ka titsiye ni da tambayoyi haka? ka ci abinka, kar na kuma jin bakinka." Khamal ya faÉ—i haka cikin faÉ—a.

Ƙasa Abra ta yi da kanta tana wasa da cokali a cikin abincinta, amma ta kasa ɗiba ta kai bakinta.

"Ki ci abinci Malama, ba wasa za ki tsaya ba." Khamal ya faÉ—a mata haka ba yabo ba fallasa.

Gyaɗa masa kai ta yi a hankali ta fara cin abinci. Kaɗan Khama ya tsakuri abincin ya ci ya miƙe, shi ma dan kada yaran nasa su yi tunanin da wata matsalar ne, musamman Salman da yake da saurin fahimtar abu. Daga dinning area ɗin ɗakinsa ya wuce ya dauko car key ya fice zuwa gidan Ammi.

"Yaya, ba ki yi tunanin wani abu ya faru ba da bama nan?" Salman ya tambayi Abra cikin nazari.

Ajiyar zuciya ta sauke ta ce. "Like what?"

"Ko Mami sun samu matsala ne da Abbi shi yasa ta tafi gida? dan yanayinsa ya nuna yana cikin damuwa."

"I don't think that gaskiya Faris, kuma insha Allah ba haka ba ne."

"To Allah yasa." Ya yi maganar tare da cigaba da cin abincinsa.

ita kuwa kasa cigaba da cin abincin ta yi, don tana cikin damuwa, ɓoyewa kawai take dan kar Salman ya fuskanta. Ta damu sosai akan fushin da Abbinta yake da ita, na makircin da Nai'ma ta shirya mata, ta ba shi haƙuri ya ce ya haƙura amma ya ƙi sakar mata kamar da.

Khamal ne zaune a ɗakin Ammi yana zayyane mata abun da ya faru, bayan ya gama ta ce. "Yanzu ya kake so ayi?" Ya ce. "Toh Ammi, na rasa ma me zance, rigimar Granny ta yi yawa, haka kawai ta zo ta kora yar mutane gidansu, babu wani dalili." Ammi ta ce. "Ka kira Baffa ka sanar masa, zai yi mata magana kuma na san za ta haƙura." Numfashi ya sauke cikin damuwa ya ce. "Zan kira shi insha Allahu, amma ni Ammi ban so kika biyewa Granny ba, yanzu Nai'ma sai ta ga kamar na wulaƙantata ne."

"Hakan shi ne solution da kwanciyar hankali, ko so kake yau Granny ta hana ni bacci da mitar na ƙi bin umarninta, saboda ba ita haife ni ba?"

Girgiza kai kawai Khamal ya yi, zuciyarsa cike da takaicin halin Granny, amma abu ɗaya da ya daure masa kai shi ne, ya san duk jarabar Granny ba ta yin ta ba tare da dalili ba ko an taɓo ta, idan haka ne kenan Na'ima ta yi mata laifin da gaske, amma wanne irin laifi ne? Ko dai rikicin tsufan nata ne ya ƙaro?

Hankali a tashe Nai'ma ta ƙarasa gidansu, Mama tana ganin ta, ta san ba ƙalau ba.

"Ke lafiyarki kika faÉ—o mana gida babu ko sallama?"

"Ina fa lafiya Mama? Allah ya haɗa ni da matsiyaciyar ƙaddararriyar kakar miji, ƴar kaza_kaza." Nai'ma ta faɗi haka tana hawaye.
Chapter 40 · 0% Book details