← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 145

Sashe 73

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Mami Wallahi ban sani ba, ba guri É—aya muka je kwalliyar da ita ba, ni gurin da naje daban".

Mami ta ajiye waya tana faÉ—in "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, yarinyar nan gidan ubanwa ta tafi ne? Ace an gama kwalliya tun uku amma har haÉ—u da rabi ba ta iso gida ba, ga mutane sun fara taruwa".

Anty suwaiba ta ce"Allah yasa ba guduwa ta yi ba".

Mami ta zare ido ta ce "Ta gudu ta je gidan uban wa? Lallai ma yarinyar nan".

Abu kamar wasa, ba Abra babu dalilinta, tun ana maganar ƙasa_ƙasa, har mutane suka fara jin halin da ake ciki.

Abokan aikin Adnan ne, suke ta shiri cikin shigarsu ta police, domin dai za'a yi parrate na ban girma ga Adnan da amarayarsa.
Usman ne ya kalli Adnan da ke ta haÉ—e rai ya ce "Wai haÉ—e ran me kake ne?".

Adnan ya ce "Am jealous ne, duk wannan garadan sai kun je kun kalle mini mata".

Aminu ya ce "Kai dalla ware, ai kaima gardin ne, sai kace a kanka aka fara Aure, ko da yake tsiyar mutum ya zama tuzuru kenan, duk sai ya fara behaving abnormal".

"Meye banbancina da kai? Har gara ma ni yanzu zan shige daga ciki, kai kana waje".

"Nima ina hanya ne" Usman yayi Maganar yana murmushi.

Daga haka suka kammala shirinsu, suka fara haramar tafiya gidansu Abra.

Granny ce ta shiga sashin Na'ima tana faɗin "Ke Na'ima, wai wace Maganar banza nake ji ne? Wai kamar Ana Abra ta ɓata, gidan ubanwa ki kai ta?"

"Haba granny, Ina kuwa zan Kai ta, daga zuwa kwalliya ba ta dawo ba".

"Ƙarya ki keyi, ana Magana kina wani ƙifta ido kamar ta Allah, ki fito da yarinyar nan duk in da ki ka kaita, kan in samo madoki in shemeki a gurin nan".

Ammi ce ta ce "Granny ki yi haƙuri, ya za'ayi ta aikata haka ga 'yar ta, Yanzu dai muyi ta addu'a, kuma a kira shi angon a sanar masa dan a san abun yi".

Granny ta ce "Wai ke Yaushe zaki gane kan makircin wannan yarinyar ne? Ai duk abun da akace tayi babu mamaki, yau duk abun da za'ayi sai an nemo mini jikata. Amm ke nace ina tabarau na ne? in ƙarewa wannan mara Kunyar kallo, in kalli idanunta sosai, dan ni idan na kalli idon mara gaskiya ina gane shi".

Ammi ta ce "Glass É—inki yana in da ki ka yi salla, amma dan Allah ki dena wannan maganganun, bari a san abunyi, ko a tura wasu gurin mai kwalliyar".

Na'ima kuwa iya ƙuluwa ta ƙulu, ji take kamar ta rufe Granny da duka, shegiyar tsohuwa hayyataciya, sai tsawon rai kamar dabino, ta ƙi mutuwa kuma kullum cikin rikici take, tsawon shekarun da Na'ima tayi tare da Khamal Granny ba ta ƙaunarta sam.

Gida ya rikice ana neman Abra, ita kuma Granny ta rikice tana neman tabarau, ta ɗora da masifar cewa bayan sace Abra da Na'ima tayi, ta kuma sace mata glashinta, saboda baƙin hali.

Anty Suwaiba ta ce "Wai ke Na'ima ba wani mataki da zaki É—auka a kan wannan sokuwar tsohuwar, shegen surutun tsiya kamar an jefeta a ka?".

"To ni ya zan yi da ita? Wannan kaidinta ya fi yadda kike tunani, yanzun nan za ta ƙullawa mutum sharri.

ÆŠakin Salman Granny ta nufa, tana cigaba da zage Na'ima, Ammi ta ce "Granny me zaki yi a nan kuma?".

"Tabarau na nake nema".

"To mai ze kai glass É—inki nan kuma? Na ga tunda muka zo baki je nan ba".

"A'a, ance idan raƙuminka ya ɓata ka neme shi har kura tandu, yo na sani ko wannan algungumar ta yi garkuwa shi ta kai ta ɓoye" ta ƙarasa Maganar, tana nufar ɗakin Salman.

Sai dai tana shiga ɗakin, ta ƙwala uban ihun da ya janyo hankalin 'yan biki.

"Gata nan ku zo gata!" Ta yi maganar cikin ihu.

Su Ammi na zuwa, suka tarar da Abra a zaune, fuskarta sharkaf hawaye.

Ashe tun bai fi uku da rabi ta dawo gida ba, ta shiga ta ƙofar baya, tabi ta kitchen ta shige ɗakin Salman abunta, kuma ta kashe wayoyinta.

Ammi ta ce "Abra, dama kina nan ki ka ɗagawa mutane hankali? Kuma kalli duk kin fara ɓata kwalliyar".

Cikin kuka Abra ta ce "Ammi Faris É—ina, zan yi Aure baya nan, dan Allah Ammi kice musu na fasa Auren nan a dawo mini da Faris É—ina".

N'a'ima a fusace ta ce "wannan wane irin sakarci ne haka Abra? Mun tara mutane kina neman ki bamu Kunya? Kawai kin É—agawa mutane hankali".

"Mami ni bana son Auren nan na fasa, dan girman Allah Ku dawo mini da ɗan uwana" tayi maganar tana ƙoƙarin cire ɗaurin kanta, ga numfashinta da ya fara sama.

Ammi ta girgiza wa Na'ima kai, alamar ta dena yiwa Abra faÉ—a.

Granny ta ce "Ji min 'ya da wauta, ke yanzu sai ki fasa Auren, aikuwa da kin yiwa kanki kutunguilar tsiya, hmm jiya ba yau ba tsohuwa ta tuna kwanan turaka, yarinya karki cuci kanki" Granny ta yi maganar tana watsa guntun goronta a baki, ta bar É—akin, murmushi Ammi ta yi, Granny ba ruwanta haka take sakin 'yan maganganunta idan ta raya mata".

Ammi ta maida hankalinta kan Abra, ta din ga yi mata Nasiha tana rarrashinta, ƙarshe sai da aka kira Abbi video call, shima yayi ta rarrashinta, Sannan ta haƙura.
Aka samo wata mai kwalliyar ta gyara mata kwalliyar da ta fara ɓatawa da hawaye.
Na'ima ma haÉ—awa tayi cikin wani rantsatsten leshi fari da golden, tun daga wuyanta zuwa yatsunta gwal ne.

Hakan yayi daidai da ƙarasowar Adnan da da abokansa, haka zalika mota mota na 'yan uwan Adnan ɗin suka hallara a ƙatuwar harabar gidan Major Khamal Khamis, wadda akai matuƙar ƙawatawa.

Mami ce da kanta ta kamo hannun Abra ta fito da ita daga cikin gida, duk da kanta a sunkuye yake, ta rufe jikinta da mayafi, amma hakan be hana Adnan tsinkayen farar fatarta da ta sha gyara ba.
Nan masu police band suka sauke gangunan su, suka fara bugawa domin gabatar da parrate na ban girma ga Ango sha guɗa Sp Adnan Aliyu Matawalle, da matarsa gimbiya Abra Khamal Khamis, abun na masu ɗamara ne, dan haka parrate ɗin ya ƙayatar matuƙa, tare da crossing sword da aka gabatar duk dan murna ga amarya da ango.
A ka zo ɓangaren kamu, a kama amarya ta buɗe fuskarta, ƙanwar Hajiyar Adnan, ta ce sun biya dubu ɗari biyar a buɗe musu fuskar Amarya.
Nan wasu suka shiga tafi, yayin da Mami ta ce "ita dubu ɗari biyar yayi kaɗan". Ammi ce tsawatar dan kar ayi halin ƙaranta.
Nan aka shiga gudanar da shagali, bayan Abra ta buÉ—e fuskarta, wanda ba su santa ba, suka dinga jinjina kyawunta, wasu kuma suna gulmar ya za tayi da Adnan, dan da kaÉ—an ta wuce cikinsa.

"Sweetheart,yau ranar farinciki ce, amma ya naga kamar za kiyi kuka?" Adnan ya faÉ—a a saitin kunnenta.

"Wani farinciki bai taɓa riskata, Faris baya kusa da ni ba, sai a wannan lokacin, wannan ne karo na farko, ban taɓa tunanin Faris ba zai kasance da ni ba, Ranar Aurena akan high table, ana mana hotuna da ni da shi da angona ba, sai dai....." Hawaye ne suka fara saukowa da ga idanunta.

Da sauri Adnan ya ciro hanky yana share mata ya ce "dan Allah kar ki ɓata mana Wannan Farincikin, ba kowane buri namu ne yake zuwa ya cika a yadda muke so ba, kiyi haƙuri" haka ya rarrasheta, aka kammala event ɗin wannan ranar.

Daren ranar, haka Adnan ya kasance da ita a waya, yana cigba da aikin rarrashi.

Zuba mata idanunsa yayi yana kallonta, yadda take maye, cike da rashin Sabo, sai tamɓele take ya sakata a gaba kawai yana murmushi, yana zuƙar shisha yana fesar da hayaƙin a cikin iska.
Ganin tana ƙoƙarin faɗuwa ne ya sanya shi tashi da sauri ya riƙota yana murmushi "Sweetheart, it seems like you are enjoying the moment" yayi Maganar tare da kissing ɗin goshinta.

Kan makeken gadon dake tsakiyar É—akin ya kaita, ya kwantar da ita, yana shafa dogon gashinta. Gaba É—aya Meenal ba ta hayyacinta, ba ta tashi farkawa daga mayen da take yi ba, sai bayan magariba.
A hankali ta buÉ—e idanunta ta kalli in da ya idar da salla, ta tashi da sauri ta kalli agogo, a gigice ta ce "Ya a kai na kai wannan lokacin? Me ka bani haka na sha?".

"Calm down Baby, kayan caji ne fa kawai"

"Kamar yaya kayan caji, lokacin komawata gida tuni ya ƙure, me zanje in ce a gida?"

"Haba ke kuwa, kamar ba babbar yarinya ba, da alama fa kin ji daÉ—in cajin nan da kika yi"

Wani gululun baƙin ciki ne ya cunkushe mata zuciya, a gurguje ta tattara kayanta da mukullin motarta, tai waje.

Gudu take tamkar zata tashi sama, saboda tsananin tashin hankali, cike da fargaba da zullumi ta shiga cikin gidan, a Falo ta tarar da Mummy tana kaiwa tana komowa, tana ganin Meenal a rikice ta ce "Ke daga gidan ubanwa kike Yanzu?".

"Amm...mm..... Mummy da..dama".

"Dama me? Gidan ubanwa kika tafi? Ƙarfe nawa yanzu? Kin sanya ya tayar mini da hankali, yanzu haka ya tafi kai report gurin hukuma, akan cewar kin ɓata, ina ki ka je?".

Kan Meenal ta bata amsa, sai ga Doctor Bulama ya shigo, yana ganin Meenal rai a ɓace ya ce "Ke! Daga ina kike?"

"Ba ko ina".

"Daga ina kike?!" Ya sake tambayar cikin tsawa.

Rawar baki ta fara yi, amma ta kasa Magana, aikuwa yayi kanta ya shaƙota yana zazzare ido tare da maimaita tambayar daga ina take?"

"Haba doctor,ka bita a hankali mana, idan ka illata ta fa, ko ka manta uta kaÉ—aice da mu?".

"Dan ita kaÉ—aice da mu ba shi ya bata lasisin yin iskancin da ta ga dama ba, gidan wa kika je?".

A shaƙe Meenal ta ce "Dan Allah Daddy ka yi haƙuri, ƙawata na bi gidansu, muka tafi gurin biki daga school".

"Meyasa baki kira kin gaya mini ba, aka dinga kiran wayarki amma a kashe?".
Chapter 73 · 0% Book details