← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 145

Sashe 104

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya karɓa ya fara dubawa, jifa yai da kwalin allurar ya shaƙo hijjabinta jikinsa yana rawa ya ce "Are You mad? Kin taɓa ganin an bawa mai ciki wannan allurar? Kin yi kisan kai ana nema a ɗora zargin a kaina a rufe mini Asbiti, kin yi hauka ne?" Nan take idanunta suka yo waje ta fara nishi da ƙyar, sai da ma'aikatan wurin suka haɗu da kyar suka ƙwaceta.

Yana wani irin huci, ya kwafe lambar wayar jikin mai file É—in nan ya fice, jikinsa na wani irin rawa, gaba É—aya ya rikice kalaman matashin nan da yayi masa, da hoton yarinyar da ya gani ya jefa shi. Ya shiga tsananin tunani, dan son gano dalilin da ya sanya wannan yarinya ta ke kama da shi, shi dai a rayuwarsa ya san 'yar sa guda É—aya ce tal, amma mai ya haÉ—ashi kamanni da wannan kyakywar balarabiyar yarinyar?.

"A wane hali take sanadin allurar da aka yi mata, an fita da ita daga Asibitin nan tana zubar da jini bana wasa ba, ko ta rayu? Ko kuma ta haÉ—u da wani ciwon sanadin allurar? Wane laifi na yiwa wannan matashin yaro?"

Dafe kansa yayi da yake jin tamkar barazanar tsagewa, wani irin ɗaci na tasowa daga ƙirjinsa zuwa maƙogwaronsa, ga wani irin jiri da yake ɗibarsa, tun da yake bai taɓa dana sanin wasa da lafiyar wani ba, irin yadda aka yi wasa da lafiyar yarinyar nan da bai da tabaccin yanzu tana raye ko ta mutu oho, sannan yana son gano alaƙar da ke tsakanin sa da yarinyar, da har wannan matashi yake danganta ta da zama 'yar sa, alhalin 'ya ɗaya gare shi.

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Mama wai ina Abba ne? Dan idan ke ba zaki gaya mini gaskia ba na san shi zai gaya mini, a nuna mini É—akin da mata ta ke dan Allah, na tashi daga baccin da nake haka dan Allah ku haÉ—ani da mata ta" Adnan ya cihaba da surutai tamkar mahaukaci.

Tsawa Mama tayi masa "Adnan meye haka kake ne kamar ba musulmi ba? Ƙarshe wanda muka fi ƙauna a duniya shi ne Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam, amma Allah ya karɓe shi baya duniya mun haƙura mun dangana, sai kace a kanka a fara yin rashi, duk kabi ka gallabi kan ka, ba zaka iya miƙa lamarinka ga Allah ba?".

Cikin kuka Adnan ya ce "Yanzu Mama ta tabbata Abrana ba ta raye, ta tafi ta barni kenan?".

"Zan maka ƙarya ne?".

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Innalillahi wa Innalillahi raji'un! Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Allah ka yafe mini. Allah Ina son matata, Allah.. Allah".

"Kai kar ka mana saɓo, Addu'a zaka yi mata kawai".

Miƙewa yayi ya sakko daga kan gadon, ya nufi hanyar fita, Mama ta ce "Ina zaka kuma?".

"Zanje in ga gawarta ne, in mata addu'a in mata kallon ƙarshe".

"To yau kwana uku da rasuwar Abra, kwananta uku a gidanta na gaskiya".

Zaro jajayen idanunsa yayi ya ce "Mama kwana uku fa kika ce? Akan me za'a rufeta ban gama ganinta ba? Mama meyasa?".

"To wa zai tsaya jiranka, ka fita hayyacinka kana ta sambatu, allurai aka yi ta yi maka, kwana uku kenan an binneta" ɗora hannu yayi a ka, ya zube ƙasa a gurin yana sake fashewa da kuka, just rembering the bad memories he makes with her, how bad he treated her, da sauran abubuwa marasa daɗi. Yayi kuka yayi kuka, sai da hawayensa suka bushe ya kalli Mama ya ce "Mama ina Abba ne?".

"Kakar mahaifin Abra, wadda suke cewa Granny ce ta rasu jiya, saboda rasuwar Abra, tun da ta faÉ—i shikenan, ita ma jiya ta rasu, suna wajen zaman makoki, amma Salman da sirikarka suna Asibitin nan muna tare da su, amma basu sani ba, dan kar a sake É—aga musu hankali, yanzu ka tashi kayi wanka da alwala, ka zo ka ci Abinci ka rama salloli duk na ji ance ruwan da aka dinga saka maka ba zai bari kaji yunwa ba".

Kallon Mama yake, ita a tunninta har wani Abinci zai iya ci?.
Har yaje yayi alwala ya tada salla, ya sanyawa ransa cewar mafarki yake yi, kuma zai farka.

Lokaci É—aya Salman yayi wata irin muguwar rama, yayi duhu fararen idanunsa sun yi jawur.
Mami na ta rarrashinsa ya ci Abinci, amma yaƙi sai zubar hawaye kawai yake yi.

Hajiya Mama ce tayi sallama a É—akin na su, Mami ta amsa, Mama ta zauna suka gaisa tare da sake yiwa juna gaisuwa da kuma tambayar masu jiki.

Mama ta ce "Salman ya dangana, Adnan kuwa sai fama nake da shi, haryanzu sai shirme yake yi, wai shi mafarki yake yi".

Mami ta girgiza kai ta ce "Dole ya shiga cikin ɗimuwa Allah ya basu lafiya gaba ɗaya, ya jiƙan Abra".

Mama ta amsa da Ameen, sannan ta ce "Amm na e Yakamata muje a duba jaririyar can ta cikin kwalba".

Mami ta ce "Ni Wallahi tun da na rasa 'ya ta na manta da ita, shikenan bari muje, ni Major tunda yace mini zasu je Kano su dawo haryanzu shiru, na kirashi a waya sai yace mini zasu dawo, ina son in koma gida saboda masu gaisuwa".

Mama ta ce "Eh ina ga ya bari ne ku ƙara samun sauƙi".

Mami tace "Sauƙi kuma ai sai a hankali, amma har mu koma ga Allah ba zamu warke daga wannan rashin ba" tayi maganar tana share hawaye.

Mama ta ce "Kiyi haƙuri, duk zaman jiranta muke yi".

Haka suka tafi Nursery, wurin da aka sanya Aishatul Humaira a kwalba, ake cigaba da rainonta kasancewar ta bakwaini.

Mami ta ƙurawa yarinyar ido, gata 'yar mistula sai uwar suma cunkus a kanta, ga dogon hanci kamar na babanta, sai farar fatar Abra da ta ɗakko, take ta hasko Abra lokacin da aka kawo mata ita tana yarinya, da yadda ta fara azabtar da ita, kawai ta fashe da wani irin kuka ta ce "Ni dama wannan 'yar ce ta mutu, aka bar mini tawa 'yar, wayyo Allah na Abrata, har Abada ba zan manta zaman da muka yi ba, kuma ba zan daina kewarki ba 'ya ta, ki yafe mini".

Hajiya Mama tace "Kiyi haƙuri, shi Allah ba a tsara masa yadda zai yi, shi ya san hikimar karɓe uwar ya bar 'yar"

Haka tayi ta rarrashin Na'ima, suka biya ta duba Adnan, shima duk ya ƙara rama, sai uban dogon hanci irin na 'yar sa. An kuma yi masa allurar bacci, amma yana yi yana surutai.

Kwanakin Abra shida da rasuwa, sannan Abbi ya aiko da mota, Ya ce a tafi da su Salman, Hajiya Mama ta ce zata yi musu rakiya, suje ta ƙara musu gaisuwa.
Adnan kuwa ko gaisuwa an hana ayi masa, saboda likitoci sun kafa doka sosai a kansa, idan ba abi an kiyaye ba ƙwaƙwalwarsa zata iya samun matsala.

Kafin su Mami su tafi, ta tambayi yadda za ayi da Aisha, ko zasu tafi da ita, amma likitoci suka ce haryanzu ba ta yi ƙwari ba, sai an sake barinta.

Gaba ɗaya hankalin Mami yayi gida, dan haka tace su bar Aisha, a dawo daga baya a ɗauketa, dan ta ita bata ƙi Aishan ta mutu ba, a dawo mata da Abra, ta nuna mata soyayyar 'ya da uwar da Abran tai ta roƙa a baya ba ta samu ba.

Ga Mamakin Naima, maimakon ta ga an yi hanyar gida, amma sai taga an yi hanyar gidansu Ammi, ba ta yi mamaki ba a zatonta a can ake zaman makokin Abra, tun da gidansu ba kowa ba ta nan, sai dai bayan zuwansu suka riski labarin cewar makoki biyu ake yi, dana Abra da na Granny Innalillahi wa Innalillahi raji'un, tashin hankali ba a sa masa rana, da mutane da 'yan uwa sun dangana, amma zuwan Naima da Salman ya sanya mutuwar ta dawo sabuwa aka dinga koke_koke.
Kwanan hajiya Mama É—aya a Kaduna, tare da su Mami, sannan ta koma Kaduna, saboda hankalinta yana kan Adnan da ta baro shi a Asibiti.

Zaune yake a falonsa, ya ɗora ƙafarsa ɗaya kan ɗaya, yayi shiru ya ƙurawa saman roofing, kusan kwanaki bakwan nan, baya iya bacci, hoton yarinyar nan fes ya ƙi barin idanunsa, zuciyarsa na cike da zullumi da son sanin tana raye ko kuwa? Sannan zuciyarsa ta kwaɗaitu da son sanin sahihiyar alaƙar da ke tsakanin ta da shi. Ya koma Asibitin da matashin yaron nan ya shiga babu adadi, amma bai ga ko alamar zai ga mai kama da Adnan ba.
"Doctor wai meke faruwa ne, gaba É—aya ka canza mai ya faru?" Ta faÉ—a tana zama a kusa da shi.

"Bakomai" ya bata amsa a taƙaice.

"Kamar yaya bakomai? Ba ka ko cin Abinci, ka daina zuwa wurin aiki, kuma kace mini bakoma".

"Nace miki bakomai, ki ƙyaleni Please".

"To naji zan ƙyaleka, magana ce dama nake son mu yi, Yaron nan da yake zuwa wurin Meenal ne yake son ya turo iyayensa, da tun wancan satin ma ya so ya turo, amma an musu rasuwa wai matar abokinsa ce ta rasu, kuma abokin nasa na Asibiti babu lafiya, amma yaushe za su sameka ko zuwa sati na gaba ne sai su zo ku yi magana".

"Ke ki ƙyaleni na ce, ba wannan ne a gabana ba yanzu!" Yayi Maganar cikin tsawa.

"To ko ma meye a gaban naka Allah yayi maka magani, amma dole ayi maganar auren 'yarka, koma menen tun da ba zaka faÉ—a ba kai ya dama, amma dole a san abin yi a kan Auren 'ya ta".
Chapter 104 · 0% Book details