← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 145

Sashe 106

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Karɓar A'isha Humairah sai ya zamto fami a kan mikin dake kwance a zuciyar su Mami, tunda aka miƙo mata yarinyar take kuka, Hajiya Mama na taya ta da hawaye. Abbi kuwa ya yi shiru kawai sai numfashi yake saukewa. A haka Salman ya shiga inda suke ya same su, bai ce komai ba bayan sallamar da ya yi ya karɓi A'isha ya riƙe tare da zuba mata ido. Bacci take cikin kwanciyar hankali, ta ƙara girma da kyau da fari, a hankali ya kai hannu cikin ƙaunar ta ya shafa gashin girgarta zuwa kuncinta, idanunsa taf da hawaye ya ce. "Allah ya ji ƙan mahaifiyarki, ya raya mana ke, ya ba ki haƙuri da sanyin hali irin nata."

"Amin ya Allah." Abbi ya amsa idanunsa a kansu.

Kuka Nai'ma ta ƙara fashewa da shi tare da faɗin. "Da gaske dai ba zan farka daga wannan mummunan mafarkin da nake ba, ta tabbata Abra ta rasu, innalillahiwa'inna'ilaihirra'un, na kasa sabawa da rashin ki ƴata, kodayaushe kewar ki ƙaruwa take a cikin zuciyata."

"Sai haƙuri Hajiya, dukkan mai rai mamaci ne, mu ma duk zaman jiran ta muke, fatanmu kawai Allah ya sa mu cika da kyau da imani." Cewar Likitan da suka karɓi A'isha Humairah a hannunsa. Haka suka baro asibitin zuciyoyinsu babu daɗi, Salman dai na riƙe gam da Baby ya ƙi bawa kowa ita. A ranar suka juya Kano ba su kwana ba, duk kuwa da yadda Hajiya Mama ta so hakan, har suka taho ba su haɗu da Adnan ba, yana baccin allurar da aka yi masa.

Daf da Magriba ya farka daga baccin a firgice yana kiran sunan Abra. Aminu dake ɗakin ya yi hanzarin yin kansa ya riƙe shi.

"Abra! Tana Ina? Yanzu fa muke tare ta kawo mini ruwa mai sanyi ina sha tana ta mini murmushi, ashe ba ta mutu ba duk mafarki nake yi." Ya faɗa cikin son kwace jikinsa daga riƙon da Aminu yay masa tare da waige-waigen inda zai ga Abra."

Cikin son kwantar masa da hankali Aminu ya ce. "Ta fita ne, amma yanzu za ta dawo." Ajiyar zuciya ya sauke mai ƙarfi tare da yin murmurshi ya ce. "Ina ta je? Raka ni gurin ta, bana son tana yin nesa da ni, kar na je mummunan mafarkin da na yi ya tabbata."

"To zan raka ka, amma ka fara yin wanka ka ci abinci ka yi sallolin dake kanka?"

"Me ya sa?"

"Saboda ta ce idan ba ka yi ba kar na raka ka gurin ta."

Zabura ya yi cikin ƙoƙarin saukowa daga kan gadon yana faɗin. "Zan yi yanzu."

Taimaka masa Aminu ya yi ya raka shi toilet zuciyarsa cike da tausayin shi, idan ba dabara ake masa irin haka ba, ba za a samu kansa cikin sauƙi ba. Bayan ya fito ya yi Sallah ya fita parlour. Hajiya Mama da Abba ya tarar a parlour'n, cikin sauri ya ce. "Ina Abra? Where is my wife?" Dafe kai Hajiya Mama ta yi ta ce. "Oh My God! Adnan wai sai yaushe za ka yarda Abra ta rasu ne?"

"Ba zan taɓa yarda ba, saboda in dai hakan ya tabbata ni ma bin ta zan yi." Ya yi maganar cikin hawaye.

Kallon sama da ƙasa Abba ya yi masa, duk da yadda ya lalace ya yi baƙi amma bai ji tausayin shi ba ko kaɗan, taɓe baki ya yi tare da ɗauke kansa daga kallon shi. Kuka sosai Adnan ya saka tare da faɗin. "Abra me ya sa za ki tafi a lokacin da nake cikin tsananin ɓukatar ki a cikin rayuwata, ina son ki wallahi, na yi nadamar duk abubuwan da na aikata miki, don Allah ki dawo gare ni."

"Haba Adnan, yaushe za ka daina wannan kukan da surutun ne? Sai ka ce ba musulmi ba, Ubangijin da ya ba mu Abra ya fi mu son ta shi ya sa ya É—auke ta, addu'a kawai za ka yi mata, shi ne soyayyar da za ka nuna mata."

"Shikenan Mama, na yarda na haƙura, na rasa masoyiyata." Ya yi maganar cikin wani irin yanayi tare da kwanciya a ƙasa.

Girgiza kai Aminu da ya biyo bayan shi ya yi zuciyarsa cike da ɗimbin mamakin dama akwai abin da zai mayar da Adnan haka? Mutum mai tsananin zuciya da zafin rai gami da dakiya, lallai ya tabbatar ba ƙaramar k'auna yake yi wa matar nan tasa ba.

Hajiya Saudat ce zaune a bakin gado ta yi tagumi tana kallon Bulama dake kai kawo a É—akinsa kamar wani sabon soja.

"Wai don girman Allah Doctor me yake damun ka ne kwana biyu? Ka daina walwala, ka daina cin abinci, office ma an ce ka daina zuwa, ka faÉ—a mini me yake damun ka."

"Ba zan faɗa ba Saudat, na ce ki ƙyale ni ki daina biyo ni kina mini waɗannan tambayoyin amma ƙin ki ko? Wallahi zan saɓar miki!" Ya yi maganar cikin ɗaga murya.

Cikin tsantsar mamaki ta ce. "Ni ce fa Saudat matarka Doctor kake mini magana cikin tsawa? Ko ka manta ne?"

"Get out from My room, kafin na wurga ki ta window!"

Jijjiga kai ta yi ba ta ce komai ba ta tashi ta fice. Da wani mugun kallo ya raka ta, bayan ta fice ya rufe ƙofarsa tare da faɗin. "Idiot, abu yana damun mutum za ta ishe shi da wasu mahaukatan tambayoyinta."

"Me ya faru Mom na gan ki a haka?" Meenal ta tambayi Hajiya Saudat.

"Akwai matsala Daughter, mahaifinki ya burkice gabaÉ—aya, har da yi mini tsawa yau."

"Ni dai ba wannan ne damuwata ba, kin ƙara masa maganar Usman?"

"Ki shiga ki yi masa da kanki." Hajiya Saudat ta faÉ—a cikin harararar Meenal.

Baki ta tura gaba ta fara ƙunƙuni tare da magana ƙasa-ƙasa, ƙwafa Hajiya Saudat ta yi ta shige ɗakinta.

"Maman Rahama har yanzu kin kasa cire damuwar mutuwar yarinyar nan daga ranki, ta riga ta tafi fa, ba za ta dawo ba."

Tagumin da ta yi ta sauke ta ce. "Dole na damu Baban Rahama, ranar da muka kai ta asibiti kawai nake tunawa, ashe mutuwa za ta yi ma, Allah Sarki baiwar Allah."

"Addu'armu kawai take buƙata a halin yanzu."

"To Allah ya ji ƙan ta, ya gafar ta mata, amma mutuwar ta ta duke ni ba kaɗan ba."

"Haka rayuwar take, ni sai damu na da kira Doctor Bulama yake, wai dole sai na haÉ—a shi da mijinta."

Tsaki Maman Rahama ta yi ta ce. "Rabu da shi, bayan wulaƙancin da suka yi mana a asibitinsa, ana ta fadar rashin mutuncin mutumin nan, amma ban zata ya kai haka ba."

"Shi ya sa na ce masa ban san inda zai same shi ba, don ni ma ranar ya ɓata mini rai."

"Allah ya kyauta."

Hajiya Nai'ma na zaune a main parlour tana jijjiga A'isha Humairah dake kuka. Abbi dake parlour'n yana karatun Alqur'ani ya ce. "Kukan little Abra ya yi yawa yau, ko wani abun ke damun ta?" Cikin damuwa Nai'ma ta ce. "Ban sani ba ni ma, amma ina jin ko cikinta ne ya ɗan kumbura, don kafin ka ji kukanta ana daɗewa, na ba ta abincinta ma ta ƙi shan na kirki."

"To, ko sai mun ga likita ne?"

Kafin Nai'ma ta yi magana Salman ya shigo parlour'n, bin shi suka yi da kallo ganin yanayin shi, kullum Salman ƙara lalacewa yake saboda damuwar rashin Abra. Jiki a sanyaye ya zauna a kan carpet bayan ya karɓi A'isha tare da gaishe da iyayensa. Jijjiga ta ya shiga yi a hankali, babu jimawa ta yi shiru bacci ya ɗauke ta.

"Lalle ma yarinyar nan, saboda kina hannun Ubanki sai kika yi shiru ko?"

Murmushi ya yi a saman leɓɓensa bai ce komai ba, karɓar ta Mami ta yi ta kwantar a kan kujera tare da faɗin. "Ga abinci can a dinning ka je ka ci."

"Na ƙoshi Mami."

Gyara zama Abbi ya yi ya ce. "Rayuwa ba za ta yiyu babu cin abinci ba Salman, ina lura da kai tunda Abra ta rasu ba ka wani cin abincin kirki. Haƙuri za ka yi ka daure, mu ma duk ƙarfin hali kawai muke."

Cikin hawaye Salman ya ce. "Na kasa Abbi, na kasa daurewa, lokaci É—aya a ce babu Yaya babu Granny."

"Haƙuri za mu yi Salman, haka Ubangiji ya ƙadarto mana, Please my son ka rage wannan damuwar, We are all Muslim, yarda da ƙaddara mai kyau da mara kyau ya zama dole a gare mu, Abra ta tafi, amma ta bar mana wata, wadda muke fatan ta samu zuri'a daga gurin ta."

Share hawaye Nai'ma ta yi ta ɗauki A'isha ta bar parlour'n, cikin ƙoƙarin mayar da kukan da ya taho mata.

"Insha Allahu Abbi zan rage, sannan dama na zo ne in maka maganar komawa ta China a cikin week É—in nan insha Allahu."

"A yadda kake za ka fahimci wani karatu kuwa Salman?"

"Zan fahimta Abbi, kar ka damu."

"Tom shikenan, Allah ya kai mu ya ba da sa'a."

Nasiha Abbi ya cigaba da yi wa Salman, wanda ya zaɓi komawa China ne ba don karatu ba kamar yadda ya ce wa Abbi, don shi a karan kansa ya san babu abin da zai fahimta, ya yi hakan ne kawai don ya nesanta kansa da duk wani abu da zai dinga tuna masa da Abra, saboda a kodayaushe gani yake kamar za ta dawo su cigaba da rayuwa, zuciyarsa ta kasa ɗaukar dangana da rashin Abra, ta kasa haƙurin rashin ta. Shi ya sa yanke wannan shawarar ko zai samu salama.
Chapter 106 · 0% Book details