← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 142 OF 145

Sashe 142

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajiya Mama ta ji daɗin ganin su cikin walwala da farinciki alamun sun daidaita kansu, Ta yi musu nasiha mai ratsa zuciya akan zamantakewar aure, Abba ma ya ɗora da tasa. Little ta maƙale wa iyayenta, duk inda Abra ta yi tana manne a jikinta. Haka Adnan da zai tafi masallaci ta dinga kuka sai ta bi shi, sai da Abra ta goya ta sannan ta yi shiru, daga nan ma bacci ya ɗauke ta, har suka baro daga gidan ba ta tashi ba. Daga gidan Mama ba direct gida Adnan ya yi da su ba, sai suka biya wani bakery suka yi siyayya sannan suka dawo gida. A parlour suka baje suka ci abubuwan da suka siyo cike da ƙauna da tattalin juna. Daren yau ma sun raya shi da nuna wa juna soyayya, sai a yanzu da suka kasance tare kowannen su ya gane ba ƙaramin kewar ɗan'uwansa ya yi ba. Washegari da safe Adnan yana gaban mirror yana shiryawa zai fita Abra ta fito daga toilet. Kallon ta ya yi yana murmushi ya ce. "Princess wai fushin ne bai ƙare ba?" Turo baki ta yi ta ce. "Ba na ce kar ka tafi ka bar ni ba ka ƙi, ni bana son ka yi nesa da ni ko na one second." Takowa ya yi ya zauna a bakin gado sannan ya ɗora ta a kan cinyarsa, yana shafa santala-santalan cinyoyinta ya ce. "Na ce fa ba daɗe zan yi ba, signing kawai zan je na yi na dawo."
"To zan bika." Ta faɗa a shagwaɓe." Gefen fuskarta ya shafa ya ce. "No prob Angel, shirya mu tafi." Cikin farinciki ta dinga kissing duk inda bakinta ya kai a fuskarsa tare yi masa godiya sannan ta tashi ta shirya. Shi ya zaɓar mata kayan da ta kasa a cikin waɗanda ya siyo mata. Ganin irin kyawun da ta yi ya ɓata fuska ya ce. "Gaskiya Angel a canza kayan nan." Marairaicewa ta yi ta ce. "Za mu ɓata lokaci fa, kuma ka ce jiran ka ake." Janyo ta ya yi jikinsa ya ce. "Kin yi kyau ne sosai my Queen, ba na son ai ta kalle mini ke."
"Babu wanda zai kalle ni fa."
"Ni dai ban yarda ba."
"Please Baby, kuma na san ko na saka wani kayan shi ma haka za ka ce ya yi mini kyau na cire." Ba don ya so ba ya kama hannunta suka fita. Shi kaɗai ya shiga headquarter ɗinsu ya yi abin da zai yi ya fito suka tafi, saboda wai kar a kalle masa ita. Ta ɗauka gida za su koma sai ta ga sun ɗauki wata hanyar daban. Sai da suka kusa zuwa ta gane prison zai kai ta gurin Daddaynta. Farinciki ya mamaye zuciyarta, ƙima da darajar Adnan suka ƙaro a idonta. Ba gurin da suka je ganin shi last time ta ga sun nufa, wani guri ne mai kamar Hospital suka shiga bisa jagorancin wani ganduroba. Suna shiga wani ɗaki ta hango Bulama kwance a gadon marasa lafiya. Da sauri ta ƙarasa ta kama hannunsa. A raunane ta ce. "Daddy ba ka da lafiya? Me ya same ka?" Cikin ɗacin zuciya ya ce. "Daga cikin sharrukan da na aika da su gurare da dama ne suka fara dawowa kaina, wani aka kawo prison ɗin nan jiya, ashe ya sanni wai mahaifinsa ya rasu a asibitina bisa gangancinmu saboda ba su cika kuɗin da aka buƙata daga gare su ba." Cikin kuka Abra ta ce. "Waye ya yi maka wannan zaluncin haka? Daddy fuskarta duk ta kumbura fa ta yi taruwar jini." Murmushi Bulama ya yi mai ciwo ya ce. "Na tabbata zafi da raɗaɗin da ya ji a cikin zuciyarsa lokacin da mahaifinsa ya rasu sun fi wanda nake ji yanzu a jikina, don haka ban ga laifin shi ba ko kaɗan, hakan da ya yi idan har ya huce ya yafe mini to na yi farinciki, ko ba komai ya rage mini nauyin haƙƙin mutane da na ɗauka ranar gobe ƙiyama." Sun ɗan jima a prison ɗin Abra tana ta kuka, da ƙyar Adnan ya rarrashe ta, ta yi shiru. Ya so ɗaukar mataki a kan wanda ya daki Daddy amma Bulaman ya hana tare da faɗa musu hukumar gidan ta ɗauki matakinta da kanta. Sanadiyyar dukan aka yi masa ya sa aka ɗaga shari'arsa har sai ya samu lafiya sosai. Bayan sun baro prison ba su koma gida ba, wani haɗaɗɗen gurin shaƙatawa Adnan ya kai su, yanayin gurin ya burge Abra ba kaɗan ba. Sun daɗe a can cikin kulawa da ƙaunar juna, hakan ya rage mata kaso mafi yawa na damuwar halin da ta ga Bulama a ciki. Sai daf da Magriba suka dawo gida. Bayan ta yi Sallah ganin Adnan bai dawo ba ya sa ta kira Ummi a waya, ringing biyu ta ɗaga tare da yin sallama, ta amsa mata tare da gaishe ta. Gyara zama Abra ta yi cikin karyar da harshe ta ce. "Ummi don Allah ki yi haƙuri ki yafe wa Daddynmu, ki janye ƙarar da kike ƙoƙarin shigar da shi, yana cikin mawuyacin hali, ki taimaka masa Please ki taimake mu ma." Ajiyar zuciya Ummi ta sauke ta ce. "Nur mahaifinku ya ci amanata, ya cutar da ni ya cutar da ku, bana jin zan iya yafe masa har abada."
"Please Ummi, Ubangiji ma muna yi masa laifi ya yafe mana, kuma yana son bayinsa masu yafiya a tsakanin su, halin da Daddy yake ciki kaÉ—ai a yanzu ya ishe shi ishara da masu irin halinsa."
A sanyaye Ummi ta ce. "Shikenan na yafe masa saboda ku, amma aure tsakanina da shi ya ƙare." Ajiyar zuciya Abra ta sauke cikin maɗaukakin farinciki, ba ta yi zaton yadda Ummin ta ɗau al'amarin da zafi za ta sakko cikin sauƙi haka ba, godiya ta dinga yi mata kamar za ta ari baki. Tausayin su ita da ƴar'uwarta ne ya kama Ummi, duk lalacewar mahaifinsu a haka suke son shi da son ganin ya yi ingantacciyar rayuwa. Ita ma Afra bayan sun dawo ta kikkira ta tana cigaba da roƙon ta akan ta yafe wa Bulama. Sai da Adnan ya dawo ta ba shi suka gaisa da ummi sannan suka yi sallama ta katse wayar, dama a fitar da suka yi ɗazu Adnan ya loda mata kati a wayarta.

Yau jikin Meenal ya yi tsanani fiye da koyaushe, tun cikin dare take bleeding, gabaɗaya ta fita daga hayyacinta ba ta san ma waye a kanta ba. Hankali a tashe Hajiya Saudat da ƙawarta suka ɗauki Meenal zuwa asibiti. Taimakon gaggawa doctor's suka shiga ba ta, bayan wani lokaci wani likita ya fito yana share gumin fuskarsa da alamun damuwa ya dubi Saudat dake gunjin kuka ya ce. "Ke ce mahaifiyar ta?" Ɗaga masa kai ta yi da sauri tare da matsawa kusa da shi ta ce. "Doctor ya jikin nata? Kun tsayar da jinin da take zubarwa, don Allah ku taimaka mini ta samu lafiya, ita kaɗai ce ƴata a duniya."
"Sai haƙuri Hajiya, Ubangiji ya karɓi ranta." A gigice Saudat ta ce. "Ban gane ba wanne ran? Me kake nufi?"
"Ina nufin ta rasu, Allah ya karɓi abarsa."

*Littafin dare da duhu na kuɗi ne, mai so ya tuntuɓe mu a 09047871750*
[12/7, 8:27 PM] Abk: Cikin tashin hankali Saudat ta ce "Meenal ta rasu? Wacce Meenal kuma ba dai tawa Meenal É—in ba?" Dr ya girgiza kai alamar alhini ya ce.
"Ki yi haƙuri Madam, yarinyar dai da kuka kawo Ubangiji ya amshi abar shi" Saudat ta ce.
"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un, na shiga uku wayyo Allah na, yarinyar dana haifa ɗaya ta barni don Allah Dr kace ba Meenal ba ce" kuka sosai take tana ihu kamar zautacciyya. Mutuwar ya sanya mata tsoro da ladama mara adadi, yarinyar data haifa ta mutu cikin mugun hali tana mai aikata alfasha, bata tabbacin Ubangiji ya yafewa Meenal ko a a'a. laifi zina abu ne mafi muni, amma ita nata laifin fa? Data raba zuƙata biyu, ta raba uwa da yaranta sbd son zuciya.
Da ƙyar ta samawa kanta nutsuwa aka amshi gawar Meenal tare da yi mata suttura. Saudat bata cin abinci ta lalace tunanin yadda rayuwar yarinyarta ya ƙare ya damu ranta, tazo duniya cikin kamala ta koma cikin tuzarci me yafi haka muni a rayuwa?. mafitar yadda haɗu da Ubangiji lafiya take a yanzu da kuma addu'ar samawa Meenal sassauci wajan Ubangiji.

Kwana uku da rasuwar data zaune Halima ta kalleta ta ce "Saudat mai zai hana ki faÉ—awa mahaifin yarinyar cewa yarinyar ta rasu?" Ta sauke numfashi kafin ta ce. "Ni ma nayi tunanin haka, amma ban san yadda zai É—auki abin ba, duba da yadda mukai uwar watsi da shi ba mu yi rabuwa mai kyau bane"

"Duk da haka, ƴar sa ce kuma yana da hakƙi akanta, ya cancanci yasan halin da ake ciki gudun abin da zai je ya dawo"
Ta ce "Shi ke nan bari na ɗauki wayar na manta rabon dana kunnata ma" ta faɗa tana miƙewa tsaye tare da barin wajan, bayan ta kunna wayar ta lalubi number Dr Bulama ta kira sau biyu not answering. A kira na uku ne aka ɗauka.

"Hello" ta faɗa a sanyaye akai mata shiru ta ƙara cewa "Assalamu alaika" sai a lokacin aka amsa tare da faɗin.
"Wslm waye?" Tai shiru alamar tunani can ta ce.
"Sorry Saudat my name, Bulama's wife, who am I speaking with?"

"Hello" ta furta jin anyi shiru can aka ce "Oh Saudat ya É—an ajjiye wayar ne, yanzu lafiya?" Ta ce "Idan babu damuwa ina son magana dashi urgent ne".

"Kiyi haƙuri, kina iya faɗar komai sai a faɗa mishi idan ya zo ko?" Rashin sani yafi dare duhu, Saudat na waya bata san cewa tracking number ta ake ba.

"Shikenan ka faÉ—a masa, Allah ya yi wa yarinyar shi Meenal rasuwa yau kwana uku, idan ya zo ya kirani" mai maganar ta waya ya ce.
"May her soul rest in peace"
Chapter 142 · 0% Book details