← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 145

Sashe 81

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wannan takardar kuma ita ta ƙirƙiri kanta kenan?" Ya yi maganar cikin hucin ɓacin rai.

Rasa abin cewa ta yi sai matsanancin kuka da ta fashe da shi cikin nadamar faÉ—awa Salman ba su suka haifi Abra ba, da ta san haka al'amarin zai juye mata da ba za ta soma faÉ—a masa ba.

"Wannan takardar ta ƙara tabbatar mini da ke kika faɗa wa Abra ba mu muka haife ta ba kamar yadda kika faɗa wa Salman, tabbas biri ya yi kama da mutum, yanayin Salman kafin ya tafi china irin na wanda yake cikin tsantsar damuwa ne, na so na fahimci hakan, amma saboda kin san me kika shirya da na faɗa miki sai kika ce ba haka ba ne, miskilanci kawai ya koya. Kin cuce ni Nai'ma da kika bari yaran nan suka san su ba ƴan'uwan juna ba ne, kin kuma cuci kanki, domin ba zan ƙara zaman aure da ke ba har abada, I hate You!"

"Khamal ni ce fa, ni ce Na'imanka don Allah kar ka mini haka, na san na yi kuskure amma ka yafe mini, ka tsaya ka fahimce ni." Na'ima ta faɗi haka tare da riƙe ƙafafuwansa.

Hamɓare ta ya yi a zuciya ya ce. "Last maganata da ke, na ba ki 30 minutes ki tattara kayanki ki bar mini gidana."

Bai jira cewarta ba ya fice daga ɗakin, part ɗinsa ya nufa ya shiga bedroom ɗinsa ya kulle ƙofa. Innalillahi.... kawai yake maimaitawa a cikin ransa cikin tsantsar damuwa, sai taune lips ɗinsa yake tamkar zai tsinka shi, kyawawan fararen idanuwansa sun yi jajur saboda tsananin ɓacin rai. Ji yake kamar ya rufe Na'ima da duka saboda baƙin ciki, damuwarsa halin da Abra take ciki a yanzu, ya san ba ƙaramar damuwa za ta ɗora wa kanta ba. Tsaki ya ja cikin jin haushin kansa na amince wa Na'ima da ya yi akan Abra, gaskiya ne da aka ce bakin da ya furta ƙi ba zai taɓa furta so ba. Amma me ya sa ya kasa gane pretending kawai Na'ima take? Duk da kasancewar shi mai saurin fuskantar abu. _ƙaddara_ zuciyarsa ta ba shi amsa.

Hand bag kawai Na'ima ta É—auka ta saka hijabi tare da zira takalmi ta fice cikin tsananin tashin hankali. Domin ba ta ji a ranta ta bar gidan Khamal kenan, zuciyarta ba za ta iya É—aukar hakan ba, tana son Mijinta ba ta son rabuwa da shi.

Aunty Suwaiba ce ke kaikawo a parlour bayan Na'ima ta gama zayyane musu abun da yake faruwa. Cikin damuwa ta ce. "Wautarki ta yi yawa Na'ima, abun da nake jiye miki kenan tun farko, shi ya sa nake tausar ki akodayaushe akan ki dinga danne ƙiyayyar yarinyar nan da kishinki a kanta, amma ki ka ƙi ji, gashi nan ya sake ki." Cikin kuka Na'ima ta ce. "Wallahi Aunty ba ni da masaniyar abun da yake zargi na da shi, ni ban faɗa wa yarinyar cewa ba mu muka haife ta ba har yau."

"To waye ya faɗa mata? Ni dai a sani na ko Kaduna ba ku taɓa zuwa ba, balle a ce wani ya san ku a can ya faɗa mata. Kuma abubuwan da kike yi wa yarinyar ne ya saka ko da ba ke kika faɗa mata zai ce ke ce."

"Dan Allah Aunty ki bar ni da maganganun nan, in ji da abun da yake damu na mana, haba."

"Na bar ki Na'ima, amma ko kin ƙi ko kin so shegen kishin da ɗora wa kanki ne ya jawo miki."

A ƙufule Mama ta ce. "Wai wannan maganganun na mene ne? Abin da ya faru ya riga ya faru sai dai mu nemo hanyar da za a gyara shi, tunda kin ce saki ɗaya ne ko?" Ta ƙarashe maganar idanunta a kan Na'ima. Gyaɗa mata kai ta yi tana sharar hawaye. Duk wannan fafutukar da boloƙon da ta yi saboda Abra ta bar musu gida amma ƙarshe abin a kanta ya ƙare, tana murna shirinta ya tafi daidai ashe zai warware ne tas.

Tana ji Adnan ya shiga toilet ya yi wanka ya fito amma ita ta kasa ko da ɗaga ɗan'yatsanta ne, wani irin nauyi take jin kanta ya yi mata, ga duk jikinta dake mata ciwo saboda gajiyar da Adnan ya tara mata. Ita kaɗai ta san me take ji a cikin ranta na tsantsar damuwa, addu'a take yi Ubangiji ya sa mafarki take ba gaske ba ne ABBI BA SHI NE YA HAIFE TA BA. Zuciyarta ta kasa yarda da hakan duk kuwa da yanda Adnan yake ta nanata mata, tabbas a yau ta yarda Adnan ba ya ƙaunarta kamar yadda yake furtawa, tunda har iya faɗa mata abin da zai tarwatsa mata zuciya. Idanunta a kansa yana shiryawa cikin kwanciyar hankali da nishaɗi, alamun rayuwar tana yi masa daɗi. Wasu hawaye masu ɗumi ne suka shiga kwaranya daga cikin idanunta. Cikin dauriya ta tashi zaune da ƙyar ta ja rigarta ta saka, hannunta dafe da ƙirjinta saboda nauyin da ta ji ya yi mata, cikin haki ta ce. "Adnan! Don girman Allah dan darajar iyayenka ka taimake ni ka sauwaƙe mini aurenka, ba don ni ba." Sai ta fashe da kuka mai tsuma zuciya da karyar da zuciyar duk wani mai imani. Wani mugun kallo ya wurga mata cikin tsawa ya ce. "In kin ga kin bar gidan nan to gawarki a ka fitar." Kallon shi ta yi tana son ta yi magana amma ta kasa. A tsawace ya ce. "Malama ki tasar mini daga kan gado da najasa a jikinki, ki kuma gyara mini shi kafin warin abin da kika fitar ya hautsina mini ciki." Duk da yanayin da take ciki amma sai da ta yi wani murmushi da ya fi kuka ciwo sannan ta yunƙura ta sauka daga kan gadon. Kamar yadda ya umurce ta, ta kama zanin gadon da nufin cire shi amma sai ya bar hannun nata saboda rawar da jikinta yake yi kamar ana kaɗa mata gangi. Dafe kanta ta yi da sauri saboda juyawar da ta ji yana mata, ƙofa ta nufa don ta fice zuwa ɗakinta, kafin ta kai ga yin hakan ta faɗi a ƙasa sumammiya. Adnan dake kallon ta ya ja tsaki cikin takaici ya ce. "Yarinya sai ka ce mai farfaɗiya, abu kaɗan sai ki zube salon ki janyo wa mutane masifa." Kamar wata Dabba haka ya ja ta ya fitar da ita parlour ya juya ya koma ɗakinsa ba tare da ya ƙara bi ta kanta ba.

Sai wajen ƙarfe ɗaya na dare Adnan ya fita dan da ya haɗa coffee, a inda ya bar ta ya tarar da ita kwance tamkar gawa, tsaki ya ja ya ƙarasa ya buɗe fridge ya ɗauko ruwa mai sanyi ya shiga sheƙa mata daga tsaye, kusan 3 minutes sannan ya ji ta ja dogon numfashi tare da motsawa. Taɓe baki ya yi ya tafi ya bar ta. A hankali ta buɗe idonta da suka yi mata nauyi ta bi bayansa da kallo, ta daɗe a haka sannan ta miƙe da ƙyar ko gani ba ta yi sosai ta shiga ɗakinta ta faɗa kan gado.

Rabi da rabi baccin Abbi ya kasance a yau saboda tunanin halin da Abra take ciki. Washegari da sassafe ya shirya direbansa ya kai shi airport ya bi Flight ɗin ƙarfe takwas zuwa Kaduna.

Wata dattijuwar mata ce zaune a gaban gadon marasa lafiya da wani tsoho yake kwance, ta yi tagumi tana kallon yanda numfashisa yake fita da wani irin sauti gami da ɗagawar da ƙirjinsa yake yi, lokaci zuwa lokaci tana share hawayen dake fita daga cikin idonta. A hankali ta ɗaga kanta tare da amsa sallamar da wani matashi yake yi a kusa da ita. Cikin damuwa ta ce. "Ba su zo ba ko Musa?"

Numfashi ya sauke cikin damuwa ya ce. "Ba su zo ba Inna, sai waÉ—annan masu fararen kayan ne kawai."

"Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un, kalli yanda numfashin Malam yake fita fa musa, wallahi gabana sai faÉ—uwa yake, ina tsoron kar mu rasa shi." Inna ta faÉ—i haka cikin kuka.

"Ki yi haƙuri Inna, insha Allahu Malam zai samu lafiya, cuta ai ba mutuwa ba ce.

"Ba za ka gane ba Musa, ka kira masu fararen kayan don Allah su zo ko za su iya yi masa wani taimakon."

Wata mata dake zaune a kusa da gadonsu tana jinyar nata mai gidan ta ce, "Sai haƙuri Baba, haka muke fama da likitocin nan, ba sa son zuwa da wuri, Nurses ɗin nan kuma ba wani abu za su iya ba, sai dai kawai su ta ƙara wa mutum ruwa da ɗan abun da ba za a rasa ba."

"To me ya sa su likitocin ba sa zuwa da wuri? tun cikin dare Malam yake wannan abun, waɗanda suka yi aikin kwana sun yi masa gwaje-gwaje sun ce mu jira sakamakon idan likitan da zai karɓi aikin safe ya zo zai ba mu, muna ta jira har ƙarfe tara amma babu wanda ya zo."

"Hmm, asibitin gwamnati kenan, sai haƙuri, ku yi ta addu'a kawai. Dan shi wannan likitan ma da zai duba shi sau ɗaya yake zuwa a sati"

Girgiza kai Inna ta yi ta ce. "Allah Sarki takaka, shikenan bari mu jira."

Sai Asuba sannan Abra ta iya tashi ta shiga toilet ta yi wanka tare da ɗauro alwala ta fito ta yi sallolin dake kanta a zaune. Sosai ciwon da kanta yake mata ya tsananta, tamkar zai tarwatse haka take ji. Ga wani irin zafi da raɗaɗi da zuciyarta ke mata. Tana idar da Sallar ta koma kan gado ta ƙudundu ne a cikin bargo saboda sanyin da ta ji yana ratsa ta, wani irin zazzaɓi mai zafin gaske ne ya rufe ta wanda ya haifar mata da rawar ɗari. A haka Adnan ya shigo ɗakin ya tarar da ita tana numfarfashi. Cikin nuna ko in kula da halin da ya gan ta a ciki ya watsa mata singlets and boxes ɗinsa a jikinta tare da ba ta umarnin tashi ta wanke masa a lokacin.
Chapter 81 · 0% Book details