← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 145

Sashe 20

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani murmushi ne ya bayyana a fuskar Abra, tare da murna tace "Abba ya sauka a gids, se dai Wannan karon ban masa girki ba".

Kan su gama maganar Abbi ya shigo falon tare da sallama.

Yana ganin Abra a kwance a gigice ya ƙarasa yana faɗin "sweetheart what's wrong? Ya na ganki a kwance? Har da drip haka?"

Hajiya Na'ima ta hau yaƙe tace "Yallaɓai barka da sauka"

"Yawwa Madam, meya sami Abra na?"

Salman yace "Abbi ba ta da lafiya ne"

Hajiya Na'ima tace "yanzun nan doctor ya bar gidan nan, she start first period today, shine take ta shagwaɓa da koke koke"

Abbi yace "Eyya, sorry my dear, dole ta damu sosai, this is her first day is not easy for her, sannu Sweetheart".

Baƙin cikin yadda Salman da Khamal suka lalace akan Abra, kowa yana mata Sannu kamar za su maida ita ciki ya sa wani baƙin ciki ya turnuƙeta, gashi se wani shagwaɓa Abran take, har da hawaye, Hajiya Na'ima ji take Kamar ta ɗura musu Ashar su duka ta huta.

Haka Hajiya Na'ima ta shiga hidimar dole, da yaƙe ta samar musu da Abinci, kasancewar me girkin gata kwance ba lafiya.
Abba da kansa ya din ga bawa Abinci, Salman kuma yana ɓallo magani yana bata.

Hajiya Na'ima baƙin ciki ya sa ta koma ɗakinta tana huci, tana jin kamar ta ɗakko muciya ta saukewa Abra muƙamuƙi kowa ya huta.

Haka Abbi ya wuni ririta Abra, tare da yi mata nasiha akan yadda zata kula da kanta da Addinin ta.

Sakkowa take daga kan bene, hannunt a riƙe da waya ƙirar iPhone, se taune taune take.

"Meenal" ya kira sunanta.

Ƙarasa sakkowa tai daga kan benen, cikin siririyar muryarta tace "Daddy i miss You"

Yace "I miss You too, ya school É—in?"

"School Alhamdilillah, mun kusa gamawa, ya aiki ya fiÉ—a"

Yai murmushi yace "fiÉ—a sekace wani mahauci?"

Tai murmushi tace "Daddy ai banbancinku ku mutane kuke fiÉ—ewa"

Yace "Meenal kenan? Ina fatan zaki gajeni ai"

Cikin sauri Meenal tace "No, no, Daddy, ka manta Art class nake yi, ni bana son ganin jini, is so iiritating to me, ni masscom zanyi"

"Yanzu shikenan Daddy baze samu magajiya ba?"

Tai dariya tace "Daddy ba shi da magajiya"

Yai murmushi yace "To shikenan, Allah ya ida nufi".

"Aku me Magana, tun da kika dawo gidan nan kowa se yasan kin zo, se surutu kike masa ki bar shi ki huta mana" cewar matar da take sakkowa daga kan step me tsananin kama da Meenal.

Meenal tace "Mummy I have to show him how much I miss him"

Doctor yace "And i miss you too dear, yau tare ma zamu ci Abinci ma, banda ma ke kike son boarding É—in nan, ai da ni ba in da zaki matsa daga kusa da ni".

Abra ta ji sauƙi sosai, dan har ta koma makaranta, Salman se nan nan yake da ita yana bata kulawa, duk da ita tana art class shi kuma yana science, amma buni buni se yaje ajinsu ya ga ko tana Lafiya.

Kasancewar Khamal yana nan, hakan yasa Abra ta samu sauƙin hantara da zagi daga gurin Mami.

Wani mummunan labari ne ya iske Major, kasancewar an kama manya manyan 'yan ta'adda, al'umma na ta murna, cewar ko ba komai an rage mugun iri, ku ma za'a samu sassauci dan za su bada wasu bayanan, idan aka hukunta su ko ba komai, wasu za su É—an rage raÉ—aÉ—in rashin 'yan uwansu da 'yan ta'addan su ka kashe, da wanda aka raba da mahallansu, da wanda aka sace musu 'yan uwa, da kisan da aka din ga yiwa mutane ba dalili.
Se dai bayan zama da shugaban ƙasa yai da manyan jami'an tsaro, labari ya cika gari cewa, gwamnati za tai afuwa ga waɗan nan 'yan ta'adda, za ta mai da wasu Makaranta wasu kuma a ba su aikin yi.
  Hakan ba ƙaramin cece kuce ya janyow ba, mutane na ganin ya za'ai wanda ya kashe mutum ɗaya an kama shi an ɗaure an yanke masa hukunci, amma wanda suka kashe dubban mutane, suka girgiza tattalin arzikin ƙasa, su za'ai musu afuwa har da ma samun wani tagomashi da ga gwamnati, nan mutane suka dinga sukar wannan hukunci na gwamnati.
Labari ya iske Major Khamal, shi kansa ya sa rai tare da zuba ido akan matakin da gwamnati za ta ɗauka, dan sun sha baƙar wahala tare da tsananta bincike, kan su samu nasarar kamo wasu daga cikin manya manyan mutane da ke cikin ƙungiyar ta'addanci, amma katsam ya samu labarin matakin gwamnati akan lamarin.

A hankali ya miƙe tsaye yana zagayawa yace "lokaci ya yi, da zan yi wasan kura da duk wanda suke da hannu cikin lalacewar tsaro a ƙasar nan! Sedai hakan ba ze yuwu ba se da goyom bayan manya, amma suwaye manyan? Su ne dai wanda sukewa harkar zagon ƙasa.
  A hankali ya nemi guri ya zauna tare da dafe kansa, da yai masa wani irin nauyi.

Hajiya Na'ima na ta shiri da daddare, zata tafi ɗakin Yallaɓai Khamal, sai dai wayarta ta fara ringing, ta amsa wayar tare da sata a kunnenta.

"Barka da dare Hajiya Na'ima, mrs Khamal"

Cike da rashin fahimta ta amsa da "yawwa barka wake magana?"

"Garajen me kike? Zaki ji ne, ya 'yata take ina fatan tana lafiya?"

"Wace 'yar kenan?"

"Abra Khamal Khamis, na kiraki ne dan jin ya 'yata take, fatan kina riƙemin ita da amana, sannan ina miki albishir da cewa daga yanzu zuwa kowane lokaci zan iya shigowa gidanki, domin cigaba da rainon 'ya ta da kaina!.

LITTAFIN DARE DA DUHU, ₦300 NE KACAL, ZA KU TURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0116886423 Sulaiman Na'ima s union Bank.
KU TUNTUƁI WANNAN LAMBAR DAN TURA KATIN WAYA NA NAIRA 500 TA WANNAN 09047871750
DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU AKAN WANNAN LAMBAR 07063065780\09047871750
MUNGODE.
[9/30, 8:55 PM] Abk: *DARE DA DUHU*

_Brigh pens✍️_
Nimcyluv
Ayushercool
Zee Kumurya

                               P9

Domin samun complete litattafanmu, ku yi following É—in wannan accounts É—in a Arewabooks

https://arewabooks.com/chapter?id=6316f4af434cfeb9e7fe2949

https://arewabooks.com/u/nimcyluv

Elegant online writers

LITTAFIN DARE DA DUHU, ₦300 NE KACAL, ZA KU TURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0116886423 Sulaiman Na'ima s union Bank.
KU TUNTUƁI WANNAN LAMBAR DAN TURA KATIN WAYA NA NAIRA 500 TA WANNAN 09047871750
DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU AKAN WANNAN LAMBAR 07063065780\09047871750
MUNGODE.

Wata irin bugawa zuciyar Na'ima ta yi, cikin ƙaraji ta ce. "What? Wacece ke?"

Dariyar rainin hankali wadda ta kira wayar ta yi ta ce. "Ko ba ki ji abun da na faɗa dai-dai ba ne in ƙara maimaita miki?"

Wata Uwar ashariya Na'ima ta ƙunduma ta ce. "Wallahi k'arya kike matsiya, Shegiya karuwa, Khamal nawa ne ni kaɗai babu wacce ta isa ko da rab'ar shi ne ta yi balle har ta aure shi, ba'a halicci mace ba wallahi."

Cikin murmurshi ta ce. "Za kuwa ki gani, ganin idonki, ki cigaba da kular mun da my Daughter yanda ya kamata." Sannan ta ja tsaki ta kashe wayar.

A haukace Na'ima ta sauke wayar daga kunnenta ta shiga bin screen ɗin wayar da kallo, tamkar za ta ga matar da ta kira ta a cikinsa, babban baƙin cikinta sai da aka b'oye numbern sannan a kira ta.

Wani irin tuƙuƙwin baƙin ciki zuciyarta take mata, cikin takaici ta cillar da wayar, Allah ya taimaka ta faɗa kan gado. Hannunta ta ɗora akan goshinta tana bubbuga kanta ta fara magana ita kaɗai.

"Impossible! Wallahi ba zai yiwu ba, sai na gano ko wace ce ke na kashe ki, sai dai ki auri Khamal a lahira ba dai a duniya ba, matuƙar ina numfashi babu macen da ta isa ta shigo cikin gidana a matsayin matar Mijina.

Wayarta da ta cillar ta ɗauka ta fice daga ɗakin a matuƙar fusace ta nufi part ɗin Khamal.

Salman dake zaune a parlour yana kallon Ball ya bi ta da kallo cikin mamakin ganin yanayin da ta fito kamar wadda ba ta cikin hayyacinta.

"To Macuci, mayaudari, azzalumi, mugu, yau Allah ya toni asinka, dama an ce rana dubu ta ɓarawo rana ɗaya tal ta mai kaya."

Abun da Na'ima ta faɗa kenan bayan ta tura ƙofar ɗakin Khamal da ƙarfi ta shiga.

Da mugun mamaki Khamal dake zaune yana operating system yake kallon ta, kasa cewa komai ya yi saboda tsananin mamaki.

Cikin kuka ta ce. "Ka cuce ni, na yarda da kai Khamal, amma ban san me ya rud'e ka, ka ci amanata ba."

"Na'ima, wannan maganar banzan da kike yi duk na mene ne?"

"Na cikin shegen da kika yi aka haifi waccan shegiyar yarinyar ne."

Fauu! Fauu!

Khamal da ya miƙe cikin sauri kamar wanda aka hankad'a ya saukewa Na'ima tagwayen maruka a fuska.

Cikin tsananin ɓacin rai ya fara magana.

"I told you Na'ima, duk abun da zaki yi ki yi amma kar ki ƙara danganta mun ƴa da Shegiya, na faɗa miki ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba."

Na'ima dake riƙe da kuncinta wanda take jin kamar ba ya jikinta saboda tsananin azaba, idanunta na zubar da hawaye ta ce. "Ni ka mara Khamal akan waccan yarinyar mara asali?"

"Yes, kuma idan kika ƙara maimaita abun da kika faɗa, abun da ya fi mari ma zan miki wallahi!"

Yana gama faɗar haka ya fice ya bar mata ɗakin ya tafi other room dake part ɗin ransa a matuƙar b'ace.

Da wani irin kallo ta bi shi har ya fice, wani irin É—aci take ji tun daga zuciyarta har zuwa bakinta.

Zama ta yi a bakin gado tare da fashewa da kuka, a ranta tana faÉ—in, 'Komai zai faru sai dai ya faru, amma wannan karon ba za ta hak'ura ba, ba za ta cigaba da zama da Shegiya a gidanta ba, sai a yi duk wacce za'a yi.'

Sai da ta ci kukanta ta ƙoshi sannan ta lalubo wayarta dake gefenta, dan ko gani ba ta yi sosai saboda masifar ciwon da kanta yake mata. Numbern Aunty Suwaiba ta kira, ringing biyu ta ɗaga tare da ambatar sunanta.

Kuka Na'ima ta sakar mata cikin rashin abun yi.
Chapter 20 · 0% Book details