← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 145

Sashe 96

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abra na zaune a Parlour kamar daga sama taji ana faɗin "Huhuhu azaba ita daman kadunan haka take bani da labari? Wallahi kamar dai tafi Saudia nisa, wannan azababbiyar tafiya kamar za'a sai da mutum" Granny ta faɗa tana turo ƙofar. Murmushi kawai Adnan ya yi, Ammi ta ce "haka fa" a haka suka ƙarasa shiga Parlour, wayyooo Allah daɗi duk irin ciwon da Abra take ji haka ta miƙe jiki na rawa kai tsaye wajan Mami ta nufa tana zuwa ta faɗa jikinta tana sakin wani irin kuka kamar ranta zai fita.
"Oh! Wannan kukan har yanzu yana nan ni Na'ima yaushe zaki girma" kuka kawai Abra take har da shassheƙa. "Ji Algunguma bafa kukan take ba sai yanzu data ganmu to kukan na menene ma ai babu kyau" Adnan dake tsaye ya ce "haka take Granny, kullum wai akaita wajanku shi ne nace bari ta haihu to" zare ido Granny tai ta ce "Ciki ne da ita? Oh na shiga uku abin babu wahala to wata nawa kuma?" Shafa kai Adnan ya yi ba tare da yace komai ba.
Farin cikin da Abra tai ba zai misaltu ba, ta rasa inda zata saka kanta, Adnan komai Angel har kunya yake bawa su Ammi, Abra ko inda yake bata kallo. Sai da ya kirata tare da KaÉ—a mata warning na zamantakewarsu. Da zasu tafi kuka tayi kamar ranta zai fita, a haka suka rakasu zuwa airport dake jirgi zasu shiga.

Washegari ya kama Monday tana zaune a ɗaki Adnan ya shigo kallo ɗaya ya yi mata ya ce "12 jirginmu zai tashi zuwa Dubai sai ki shirya" da sauri ta kallesa ta ce "Dubai? Akan mene ko sbd ka samu damar wulaƙantani?" Kafaɗa ya ɗaga ya ce "Duk yadda kika ce, amma bana mgn biyu ki tabbatar kin shirya" yana faɗin hakan yai waje. Babu yadda ta iya bisa dole ta shirya kamar yadda ya ce 12:3 jirginsu ya tashi zuwa Dubai.

*DUBAI*
Dubai, da Larabci دبي‎, birni ne dake a masarautar Dubai, A ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa. Shi ne babban birnin masarautar Dubai, kuma da babban birnin tattalin arziƙin Hadaddiyar Daular Larabawa. Bisa ga ƙidayar jama'a a shekarar 2018, akwai jimillar mutane 3,137,463.An gina birnin Dubai a ƙarni na sha takwas bayan haihuwar annabi Isah.

Kai tsaye wata unguwa mai suna Madinat Jumeirah. Motarsu ta nufa, cikin wani haɗaɗɗan gida mai kyau da tsari wanda ya kasance mallakin Aliyu Matawalle. Gaba ɗaya a gajiye suke musamman Abra wacce bata saba tafiya haka ba, ɗaki ya nuna mata ta kwanta shima ya nufi wani ɗakin. Bayan sallar issha tana tsaye a gaban mirror ta gama shiryawa cikin wata abaya mai kyau, Adnan da tun ɗazo yake tsaye yana kallon ta ya ce "Bani da time Malama" bayansa tabi har zuwa mota, shine da kansa yake driving dare ne amma sai ka rantse rana ce haske kamar zai illata ido sbd yawan da yayi. Wani mall suka shiga yace ta ɗauki abin da take so, yana faɗin hakan ya shige ciki. Juyawa Abra tayi a hankali ta rasa me zata ɗauka sai kawai ta nufi wani waje ta da nufin zama, kamar daga sama taga mutum a tsaye a gabanta, da sauri tai baya tana girgiza kanta mutumin data gani yasa hankalinta ta shi. Abdullah ya gyara tsaiwa tare da faɗin "You? Nasan dole zan sake ganinki" jiki na rawa ta juya zata bar wajan ya yi saurin kama hannunta yana faɗin "No please, may i have your number?" Shiru tai masa ya sunkuyar da kansa yana zaro Wayarsa tare da faɗin "Jikina yana bani daman zan sake ganinki please samin number ki" wayam babu Abra babu mai kama da ita, neman duniya babu ita a haka ya koma gida rai ɓace.
Yanayin Yadda ya shiga ya sanya ƙyakkyawar matar dake zaune saman Kujera hannunta riƙe da littafi tana dubawa ɗago kanta cikin kulawa ta ce "Lafiya dai Abdullah?" Girgiza kai yai ya ce "Ummi kai na ke ciwo" da ido ta kallesa haka nan taji bata yarda ba, a nutse ta ce "Ciwon kai?" "E, Ummi maybe gajiya ne" numfashi ta sauke ta ce "Allah ya sawwaƙe, kasha magani ina son muyi magana akan Sabon Companyn da aka buɗe last year,bana gane kan komai na Companyn Abdullah na zuba biliyoyin kuɗi amma yanzu duk babu su, hankalina ya fara tashi" Abdullah ya ce "Waye manager na Companyn ma Ummi?" Girgiza kai tayi tana ɗaukan Jarida ta ce "Jeka huta, we'll talk later" "Ok Ummi" part ɗinsa ya shige Ummi ta bisa da kallo.

Cike da tsoro Abra ta kwanta amma tana Mmkin gani na biyu da idanunta suka sake yiwa Abdullah waye shi? Mene yasa yake bibiyarta har haka? Da wannan tunani bacci ya ɗauke ta, cikin dare ta farka da matsanancin zazzaɓi hannunta ta miƙe da nufin riƙe kanta amma sai taji gashin kanta yana marmasuwa, da sauri ta saka hannunta duk biyu ai kam nan gaba ɗaya gashin ya shiga cirewa gefe guda na kanta tamkar wacce akai wa aski.....

Littafin kuɗi ne, mai buƙata ya yi magana ta wannan number 09047871750
[10/27, 3:04 PM] Abk: Gabanta ne yayi mummunar faɗuwa, wane irin abu ne haka gashin kanta zai dinga zuba? Shiru ta yi tana tunani, a iya saninta bata taɓa abu makamancin haka ba. 'may be sauyin weather ne' wata zuciyar ta bata amsa, haka ta yi shiru tana Adduointa, har bacci ɓarawo ya saceta.
Bayan sallar Asubahi ma, gado ta koma ta cigaba da bacci, tana cikin baccin taji an É—agota daga kwanciyar da take gaba É—aya.
BuÉ—e ido ta yi tana tura baki, ta kalli fuskar Adnan ta ce "Meye haka? Bacci fa nake yi".

"Ai na san baccin ki ke yi, ke baki san Yakamata ba ko? Kina da juna biyu amma har wannan lokacin kina bacci, ba zaki tashi ki nemi abin da zaki ci ba, baki san sai kin ci shima abin da ke cikin ki zai ci ba?".

"Au haba? Ya daÉ—e bai ci ba, ba zan ci Abincin ba, sai dai wahala ta kashe shi na huta nima".

"Aikuwa sai dai ku mutu tare, da in rasa abun cikinki gara ke in rasa ki, dama can ba ta taki nake ba, ki yi ƙoƙari mu rabu lafiya, ki haife mini yarona salin alin".

"Mu rabu ka ce?" Tayi maganar tana kallon fuskarsa.

"Eh mu rabu, ko da yake fa ashe ba zaki iya rayuwa babu ni ba ko?".

Abra tayi wani murmushi mai ciwo ta ce "Ai ko kashin awaki muka zo duniya da kai, na tsaneka ko sunan ka bana ƙaunar ji, idan har zamu rabu ka yiwa Allah da ma'aikinsa mu rabu yanzu kan mu koma Nigeria, daga nan in wuce gidan ubana".

"Gidan riƙo dai, a zatonki zan rabu da ke ne ki tafi da cikina gidan riƙo ya zama ɗan riƙo kamar yadda kika zama, no iya wuya banga wanda ya isa rabani da ke da cikin nan a jikinki ba".

Abra ta ce"Wanda yayi ni yaui cikin fa?" Kallonta yayi amma bai ce komai ba, ya basar ya ce "Malama ki tashi kije ki karya".

"Idan ka damu ɗanka ya ci Abinci, zaka iya zuwa ka haɗo Abincin ka kawo mini nan in ci, idan kuma ba ka matsu ba, kana iya ƙyaleni in cigaba da abin da yake gabana"

Tana rufe baki ya wani irin fizgota daga kan gadon, Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Abra ji tayi tamkar an haɗa ilahirin ƙasusuwan jikinta ana ƙoƙarin kakkaryawa saboda azabar ciwon da ya ratsata tun daga kwanyarta zuwa yatsun ƙafarta.

"Na shiga uku Adnan, kasheni zaka yi ne? Ka san yadda nake jin jikina kuwa?".

"Ban damu da duk abin da kike ji ba, wannan ke ta shafa ba ni ba, burina ɗana ya rayu, ki lafiya ko kar kiyi matsalar ki ce, akan ina Magana kina mini gaddama, mussaman a kan abin da ya shafi cikin nan, sai na ɓata miki rai" yana gama maganar ya shiga janta, wanda jan nan da yake mata ji take tamkar yana ƙoƙarin rabata da ƙasusuwan hannunta.

"Adnan Allah yana kallonka fa" ta faÉ—a cikin tsananin rauni.

"Kar ki sake gatsa mini sunana haka kamar ke kika raɗa mini, mara tarbiyya shi ma uban riƙon naki baki samu tarbiyya a hannunsa ba kenan, da har kike iya kallon tsabar idona ki kirani da sunana".

Ja tayi ta tsaya tare da riƙe ƙofa ta ce "Zan iya haƙuri idan ka zagi mahaifina, saboda ban san shi ba ban san mai ya haɗaku ba, amma ba zan juri ka zagi Abbina ba duk wani rashin mutunci da zaka yi mini ya ƙare a kaina ban da Abbi, kuma da ka auroni ai ina ɓoye sunan naka, amma na ga lamarinka babu mutunci dan haka na faɗa ADNAN ALIYU MATAWALLE, aka faɗi sunan Annabi ma balle sunan Azzalimin mutum irinka" rigarta ya sa ya shaƙo wuyanta yana huci, idanun Abra suka yo waje tana wani irin kakari, ya ƙarasa janyota cikin falon, ya jefata kan kujera. Ya ɗauko Abinci ya dinga ɗura mata tana kuka tana kakarin amai, amma babu tausayi ko imani a zuciyar Adnan.

Zaune take a kan wasu irin katafaren kujeru, tana zaune hannunta riƙe da waya, tana jujjuya wayar fuskarta ɗauke da damuwa, a hankali ta fara daddanna wayar, sannan ta kara a kunnenta, sai da wayar ta kusa katsewa sannan aka ɗauka, sallama tayi tare da yin ajiyar zuciya.

Daga can ɓangaren cikin wayar aka amsa mata.

"Kana ina ne Yanzu?".

"Ina nan lafiya, akwai damuwa ne?".

"Ina son in ji Yaushe zaka zo ne, saboda akwai damuwa, ina son mu tattauna wata magana da kai"

"Wace irin damuwa ce haka wadda har kike son in zo?".

Ta sake sauke ajiyar zuciya, fuskarta na bayyanar da tsantsar damuwa ta ce "Nifa gaba ɗaya na kasa gane kan kasuwancin nan, shekara da shekaru abu yaƙi gaba yaƙi baya, akwai buƙatar mu dakatar da deal ɗin nan, zan tsayar da duk wasu harkokina na nan ƙasar, in sako jami'an tsaro da manyan accontants a gudanar da bincike, a gano a ina matsalar take"
Chapter 96 · 0% Book details