← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 124 OF 145

Sashe 124

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ɗakin Abra Abbi ya sa Salima ta gyara wa Afrah, bayan ta gama ta dawo parlour inda duk suke ta ce. "Our new daughter na kammala miki gyaran dakin, sai ki shiga ki kwanta ki huta." Murmushi Afra dake riƙe da Little ta yi, ba tare da ta ɗago kanta ba ta ce. "Na gode sosai Aunty." Cikin son cusa kai Salima ta ce. "Haba mene abun godiya don Uwa ta yi wa ƴarta abu?" Murmushi kawai Afra ta yi ba ta ce komai ba, sai shafa fuskar little take cikin ƙaunar ta da ta mamaye zuciyarta lokaci ɗaya, farinciki mara iyaka take ji a cikin ranta, yau ta ga jininta a duniya, Allah Sarki Baba, dama yana nan ya ga wannan ranar mai cike da tarin farinciki a gare su. Mami kuwa taɓe baki ta yi jin abin da Salima ta faɗa, Abbi kuwa murmurshi ya yi cikin jin daɗi ya ce. "Daughter, tashi ki je Antinki ta nuna miki ɗakinki." Cikin girmamawa ta ce. "Toh." Salman dake ta kallon ta ya miƙe tare da ɗauke little daga cinyarta, cikin murmurshi ya ce mu je na raka ki yayata." Da sauri ta kalle shi cikin mamakin jin ƙato da shi ya ce mata Yaya, shi ma kallon ta yake, hakan ya sa idanuwansu suka sarƙe cikin na juna, da sauri ta janye nata saboda wani irin abu da ta ji ya daki zuciyarta, bayan ya kai ta ɗakin yana ƙoƙarin fita ta ce. "Ka bar mini ita a nan." Fahimtar da ya yi little take nufi ya sa ya ce. "Kina buƙatar ki yi wanka a yanzu, ita kuma rigima ne da ita, kina ajiye ta za ta iya farkawa tay ta kuka, idan kin yin wankan sai Mami ta kawo miki ita." Gyaɗa masa kai ta yi ba tare da ta bari sun haɗa ido ba har ya fice, haka kawai ta ji suna mata kwarjini shi da Abbi, shi ya sa ta nutsu kamar ba ita ce Ƴar Baba gagarau ba. Bin ɗakin ta shiga yi da kallo, ƙawatuwar shi da yadda ya tsaru ba ƙaramin burge ta ya yi ba, sai tambayar kanta take yi wai wannan haɗaɗɗen ɗakin duk nata ne? Yau ita ce za ta kwana a birni gidan ƴan gayu mai kyau irin wannan, ba don halin kewar su Inna da take ba da sai ta raba dare tana tsallen murna a kan wannan luntsumemen gadon.

"Allah Sarki Innata, na san yanzu suna can suna kuka da alhinin tafiyata ita da Yaya Musana." Ta faɗi haka a fili ƙwalla na cika mata ido. A hankali ta zauna a bakin gado tana ƙara bin ɗakin da kallo, Adnan ne ya faɗo mata a rai, turo baki ta yi kamar yana gabanta, lokacin da ta tuno yadda yake yi mata magiya akan ta so shi.

Salima ce ta shigo É—akin bakinta É—auke da sallama, bayan ta amsa mata ta ajiye wata leda mai É—auke da kayan bacci a kusa da Afra tare da faÉ—in. "Ga kayan bacci nan idan kika yi wankan sai ki saka." A hankali Afra ta ce. "Toh na gode, amma na taho da kayana ma suna cikin Mota ba a shigo da su ba ne."

"Okay, bara zan yiwa Honey magana sai a shigo miki da su yanzu, ki saki jikinki kin ji, nan ma gidanku ne, bari na kawo miki abinci.'

Gyaɗa mata kai ta yi ta ce. "Ina zan ɗebo ruwan da zan yi wanka da alwala?" Murmushi Salima ta yi ta ce. "Duk akwai a cikin toilet, mu je na raka ki, ki gani." Miƙewa ta yi ba tare da ta ce komai ba, duk wannan kanbanbar da Salima take ba ta wani yi mata ba, sai ta ji ta fi son farar matar nan mai kama da Salman. A toilet ɗin ma lalacewa ta yi wajen kallon yadda aka ƙawata shi, kasa ɗaurewa ta yi ta ce. "Yanzu nan ne bayin gida kamar wani ɗaki? Taɓ, ai da ni kaɗai na shigo fita zan yi na ce ban ga bayan gidan ba, na saba da namu na ƙauye ko rufi babu balle siminti." Murmushi Salima ta yi ta nunnuna mata duk abin da ta san zai mata wahalar ganewa da yadda za ta yi amfani da shi. Bayan ta fita ta ce. "Wai aljannar duniya, har da wani fanfon ruwan zafi? To shi daga ina yake zuwa kuma? Ko ta cikin ƙasa ake dafa shi?"

"Khamal wai me kake nufi da ni a gidan nan ne? Ina cikin damuwar rashin Abra amma mai kama da ita ta zo sai kaita tura waccan matar tana yi mata abubuwa? Alhalin gani a zaune."

"Na sani ko ita ma za ki ce Æ´ata ce karuwa ta haifa mini? Ki azabtar da ita kamar yadda kika yi wa Abra."

Cikin hawaye Mami ta ce. "Me ya sa kake son dawo da abin da ya wuce ne? Ai babu wanda ba ya yin kuskure a rayuwarsa." Wani kallo ya watsa mata ya fice ba tare da ya kuma magana ba. A zuciye Mami ta ce. "Kuma yarinya a gurina za ta zauna ba a gurin wata baƙar yarinya ba, sai dai a yi duk abin da za a yi. Ban da neman fitina yarinyar kusan sa'ar ta amma ita za ta riƙe ta, ita ma shegiyar da neman gindin zama har da wani ce mata ƴarta, ko a gidan uwar wa ta haifi kamar ta oho?" Ta ƙarashe maganar tare da jan tsaki.

"Doctor me yake damun Æ´ata da har ya kai a yi mata surgery without knowing us?" Hajiya Saudat ta tambaya a gigice.

"Mu ƙarasa office mana sai mu yi maganar."

"Ba ni da nutsuwar ƙara taku ko nan da can? Please tell me what happened to my daughter?" Ta yi maganar cikin kuka.

Cikin tausawa likitan ya ce. "Ki dai daure mu ƙarasa office ɗin, kin ga nan reception ne, bai dace mu yi magana ba."

Ba ta kuma magana ba ta bi shi suka tafi. Bayan sun shiga sun zauna ya ce mata. "An yi mata abortion ne, sai kuma aka samu matsala ta samu raptured utherus, mahaifarta ta ragargaje gabaÉ—aya, yanzu za a yi mata aikin gaggawa a cire t....."

"Innalillahiwa'inna'ilaihirrajj'un, na shiga uku! Meenal É—in za a cirewa mahaifa? Mahaifa fa ka ce Doctor?"

"Eh, ta sha maganin abortion ne wanda ya wuce ƙa'ida, hakan ne ya janyo mata wannan matsalar, ba don da wata Nurse da take aiki a nan asibitin suka zo ba ma da ba za mu karɓe ta ba."

Gumi ne ya shiga yankowa Hajiya Saudat ta ko'ina a jikinta, cikin rawar murya ta ce. "Doctor, kuma babu wani abu da za a iya yi dole sai dai a cire mahaifar?"

"Babu." Ya faɗa a taƙaice.

A dole ba bisa son rai ba Hajiya Saudat ta saka hannu aka yi wa Meenal aiki, wadda ke cikin mawuyacin halin ciwo.

Ba ƙaramin tashi hankalin Hajiya Saudat ya yi ba da ta ga Meenal, Saboda yadda ta ɗashe ta yi fari fat alamun babu jini a jikinta, ga wata rama da ta yi kamar wadda ta daɗe tana jinya, tsabar galabaita ko magana ba ta iya yi, sai hawaye kawai take.

Washegari bayan Salima ta gama haɗa breakfast ta shiga ɗakin Afra don ta taso ta. Tarar da ita ta yi har lokacin tana kwance tana bacci, saboda jiya ba ta yi bacci da wuri ba, kewar Inna da baƙunta sun hana ta. A hankali ta tashe ta, bayan ta shiga toilet ta fice ta ɗauko mata sabuwar abaya da undies a cikin kayan lefenta, ta haɗo da su lotion da powder ta kawo mata. Cikin mintuna ƙalilan Afra ta shirya, kasancewar ta mai kazar-kazar ba kamar Abra ba. Sosai ta yi kyau cikin bak'ar abayar da ta haska farar fatarta. Kallon kanta ta tsaya yi a mirror cikin murmurshi, gani take ba kamar ba ita ba saboda kyawun da ta ga ta yi. Sai da Salima ta ƙara dawowa ta kira ta sannan suka fita tare.

Abbi na zaune a dinning suka shiga parlour'n, É—agowa ya yi yana kallon su tare da amsa sallamar, cikin girmamawa Afra ta tsugunna ta ce. "Ina kwana?"

"Lafiya ƙalau, ya kwanan baƙunta?" Ya amsa cikin fara'a.

"Alhamdulillah." Ta faÉ—a cikin sanyin muryar da ta ara daga jiya, don sosai ta ji jikinta ya yi mata wani irin sanyi ba tare da ta san dalili ba.

"Ƙaraso mu karya." Cewar Salima tana nufar dinning area.

"Bari na fara gaishe da Mami idan ta tashi."

Cikin jin haushin abin da ta faɗa Salima ta ce. "Ai ko da ƙyar in ta tashi."

"Ta tashi, mu je na raka ki." Abbi ya faÉ—a cikin jin daÉ—in yadda ta nuna girmamawa ga Mami.

Da kallo Salima ta bi su zuciyarta cike da baƙin ciki, ta gama yi wa yarinya hidima sannan tana fitowa ta ce wani za ta gaishe da Mami? Lallai dole ta tashi tsaye don ganin ta ja Afra jikinta sosai, ta san hakan zai ƙara ninka ƙaunar da Abbi yake mata.

Mami tana shirya little suka shigo É—akin, da fara'a ta É—ago tana duban Afra, Abbi kuwa juyawa ya yi ya koma parlour.

"Daughter har kin tashi?"

Gyaɗa mata kai ta yi tare da gaishe ta, rungume ta Nai'ma ta yi hawaye na cika mata ido saboda tuno Abra da ta yi, don ganin Afra cikin abaya ba ƙaramin ƙara kamar su da Abra ya yi ba, kasancewar ta ma'abociyar saka ta.

"Lafiya ƙalau daughter, dafatan kin tashi lafiya?"
Chapter 124 · 0% Book details