Sashe 61
Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Salman ne zaune sanye da farar singlet ya rame sosai, abun duniya ya yi masa yawa, soyayyar Abra na addabar zuciyarsa, ga tsinewar da Mami ta ce za tai masa, ga lokacin bikin Abra na kusantowa, gaba É—aya baya hayyacinsa, ko Makaranta ya je, baya gane komai ba ya iya cin abinci sam.
Ga shi ita kanta Abra yanzu, tafi maida hankali akan wayarta, ta dena bashi attention ɗinta kamar da, kullum tana maƙale da waya tare da Adnan.
Gashi Adnan ya auri hanyar Kano, kullum yana hanyar zuwa gurin ganin Abra, hakan ya sa sukayi wani irin sabo da shaƙuwa, wanda yasa Abra sakewa da Adnan Sosai. Sai dai duk da haka, tana damuwa da halin da Salman ke ciki, wanda ba ta san asalin abun da yake damunsa ba, ta barshi a alhinin rabuwa da za su yi, wanda ita kanta tana tsintar kanta a irin wannan yanayin, ba ta jin ko Abbi za tayi missing Kamar yadda za tai missing Faris. Ta kan yi kuka sosai da sosai, idan ta tuna lokaci ƙalilan ya rage, su rabu da Faris ɗinta.
Salman ya lula a duniyar tunani, Kamar da ga sama yaga Abbi ya shigo bedroom ɗin nasa, hannunsa riƙe da tarin takardu. Miƙewa tsaye Salman ya yi yana faɗin "Wlcm back Abbi ya hanya? Ashe ka dawo?"
ba yabo ba fallasa ya ce "Yawwa, tun É—azu nake cigiyarka ai, naga ba ka da niyyar fitowa, ko ba ka ji dawowata ba ne oho"
Salman ya ce "Abbi na É—an yi bacci ne, shiyasa".
miƙawa Salman takardun ya yi Salman ya bisu da idanu kafin ya ce "Na mene wannan Abbi?" Abbi ya kalli Salman sosai ya ce "Na gama dukkanin shirye shiryen da ya dace, na biya maka Makaranta a China, a can zaka cigaba da karatunka, saboda karatu a wannan ƙasar sai a hankali, babu wani inganci, dan haka next week zaku fara lectures, jibi in Allah ya kaimu zaka tafi, dan haka ka shirya!!!
LITTAFIN RUƊI NE ₦300 NE
Via 0116886423 Sulaiman Na'ima s union Bank. Idan katin waya ne mtn na 500 idan transfer ne É—ari uku kacal.
Evidence of payment 07063065680 ko 09047871750
[10/5, 5:43 PM] Abk: Saroro Salman ya bi Abbi da kallo, kamar bai gane da yaren da Abbi yai Maganar ba.
Abba yace "Look Salman, mahaifiyarka ce ta zo mini da batun gara a kaika karatu China, kuma ba mun yanke wannan hukuncin ne dan ɓata maka bane, ka san karatun Nigeria sai a hankali".
Cikin rauni Salman ya ce "Abbi, exams É—in first semester fa zamu fara, you are planing to make me far away from my sister, ko Auren na ta ba zaku bari in gani ba Abbi?"
"My Son, ban amince da hakan dan nesan ta ka da Abra ba, ko ba daɗe ko a jima dole wataran zaku rabu, tafiyar ce ta zo daidai yanzu kayi haƙuri ka ji Salman, idan ka zo hutu sai kaje har gidanta, ai ba wanda ya isa ya raba hanta da jini"
Salman ya jinjina kai, Abbi kuma ya juya bar É—akin.
Abbi na fita Salman ya saki takardun a ƙasa, ya faɗa kan gadonsa ya lumshe idanunsa, hawaye na zuba daga idonsa a hankali ya ke furta 'Mami why? Har abun ya kai kisa a rabani da ƙasar, Mami why" haka ya dinga maimaitawa a hankali.
Na'ima kuwa ba ƙaramin farinciki ta yi ba, dan tun bayan da Anty Suwaiba ta rakata gurin malami, ta biya kuɗi dan a rufe bakin Abbi a kan tafiyar Salman ƙasar waje, kuma a cire Abra daga zuriyar Salman.
Bayaj sun dawo gida ne, ta kuma samun Abbi a kan tafiyar Salman, da fari yayi mata buyagin na sa, amma ta kwantar da kai, tare da nuna masa illar barin Salman a ƙasar nan yaga bikin Abra, Abra za ta iya tuburewa ta ce ta fasa Auren, ko kuma ya ce zai dinga zarya a gidan Abra, wanda ba kowane miji ne zai yadda ba, da haka ta lallaɓa Abbi ya amince, ya nemawa Salman Makaranta a China.
Sallama ya ke ta kwaÉ—awa a falon, kamar baza'a amsa ba, sai kuma can a kasa amsa cikin siririyar muryarta mai cike da iyayi.
Cikin Palourn ya shiga, Meenal ta kalli mutumin ta ce "ya dai?"
"Dama saƙo ne wani mutum ya kawo, ya ce a bawa doctor idan ya dawo".
Maman Meenal da ke zaune ba tace uffan ba, sai yanzu da ta ji ance saƙo za'a bawa Doctor sannan ta kalli mai gadin ta ce "Bani nan" ya ƙarasa ya miƙa mata envelope ɗin ya fice.
Meenal ta kalli Mummynta ta ce "Mummy, sai na dawo"
"Shikenan, ki kula da hanya, ayi tuƙi a hankali".
"Ok Mum" Meenal ta amsa tana ficewa daga falon.
Mummy ta fara buÉ—e envelope, dan ganin mai aka kawo a ajiyewa doctor.
A razane ta miƙe tsaye, a lokacin da ta yi tozali da abun da yake cikin envelope ɗin.
Jikinta ne ya hau rawa, ta fara waige-waige don tabattar da babu wanda ya ganta.
Da hanzari ta nufi ƙofar falon, ta fito harabar gidan tana ƙwalawa maigadi kira.
Ya ƙaraso cikin rawar jiki yana faɗin gani Hajiya.
"Waye ya baka wannan saƙon?".
"Wasu ne Hajiya"
"Ba ka san su ba?"
"Eh gaskiya ban san su ba, dan ban taɓa ganinsu ba"
Ta yi ajiyar zuciya ta ce "Shikenan koma bakin aikinka".
Cikin gida ta koma, kai tsaye ta wuce kitchen, ta rufe ƙofar kitchen ɗin da key, ta yayyaga saƙon nan, ta kunna masa ashana ta ƙone tsaf, ta tattare tokar ta bar kitchen ɗin.
Salman kam nan da nan yayi wata uwar rama, ko falo ba ya fitowa kullum yana É—aki, yana tunani tare da zullumin yadda zai tafi ya bar Abra ta auri wani.
Yana kwance a kan gadonsa, Mami tayi sallama ta shigo É—akin.
"Kai Salman" a hankali ya buÉ—e jajayen idanunsa yana kallon Mami.
"Babanka bai zo ya gaya maka cewar ya biya maka kuɗin Makaranta, zaka tafi China ba? Na zubamaka ido inga iya gudu ruwanka, ko zaka zo ka sameni da batun, a fara ƙoƙarin fara shirin tafiyarka, amma kullum kana ɗaki ka ƙi zancen ma gaba ɗaya"
Lumshe idanunsa ya kuma yi, saiga hawaye na zubowa ta gefen idonsa.
"Sakarcin meye haka kuma Salman, kuka kamar wani yaro ƙarami".
Salman ya tashi zaune ya kalli Mamai ya ce "Mami, bayan kandagarkin da kika mini akan soyayyar Abra, shine kuma kika sa a rabani da ƙasar ma? Mami kin san wannan abubuwan zasu biyo baya, mai yasa kika bari na san Abra ba 'yar uwata ba ce, Mami ko kin rabani da ƙasar nan zuciyata na Nigeria tare da Abra, ina sonta Mami, amma ai ko Auren na ta kya bari in gani".
Ajiyar zuciya Mami ta yi, ta zauna kusa da Salman ta ce "Salman, kai baka tunanin halin da zata shiga idan har ta san cewa bamu muka haifeta ba, kai kanka kawai ka sani, baka tunanin abunda kake shirin yi mai zai haifar, barinka ƙasar nan shine samun nutsuwarka kuma ka manta da ita, haba Faris ɗina da kaina zan samo maka tsaleliyar yarinha da ta fita komai in aura maka, ka fara shirin tafiyarka ka ji Salman" tayi maganar tana share masa hawaye, daga haka kuma ta fice daga ɗakin.
Bin ta yayi da kallo, Maminsu a komai son kanta kawai take dubawa.
Abra kuwa yanzu kusan kullum tana kan wayarta, tare da Adnan hakan yasa ba ta iya maida hankali akan komai, sai dai ta lura tunda aka kawo kuÉ—in Auren nan, Salman ba shi da walwala, kuma a 'yan kwanakin nan kamar wani abu yana faruwa a gidan, wanda ba ta gane ko menene ba.
Lokaci lokaci, ta kan shiga cikin matsananciyar damuwa, idan ta tuna idan tayi Aure, zata rabu da Faris É—inta, ba ta jin za tayi Missing É—in wani kamar Salman É—in ta.
Yanzu ma ɗakinsa ta nufa, tana shiga ta tarar yayi rigingine ya ƙurawa roofing ɗin ɗakin ido.
Sai dai yayi rama matuƙa, ga ɗan siririn saje da ya fara fito masa da gashin baki na girma.
"Bloody what's wrong with you ne? Gaba ɗaya gidan nan yayi duhu saboda baka walwala, meyafaru da ne?" Tayi maganar tana ƙarasawa kan gadon.
Juya mata baya yayi, yaƙi ko kallon in da take.
Zagayawa tayi ta hau gadon tana kuma cewa "Faris wai menene?"
Miƙewa yayi, ya sauka daga kan gadon, ya janyo Akwati ya fara ƙoƙarin zuba kayansa.
Cikin fushi ta ce "Faris wai meye haka ne? Wannan kayan na menene ina maka Magana ka mini shiru".
"Leave me alone Abra!" Ya faÉ—a cikin tsawa, wanda saida ta firgita.
"Abra dama Akwai lokacin da zai zo ki manta dani? Kwana biyu ina cikin yanayi na damuwa, amma wands zai aureki ya É—auke miki hankali ko nemana ba kya yi, ba ki san halin da nake ciki ba? Abra China zan tafi ina fatan Allah ya sa haka shine mafi Alkhairi".
"Faris, ka yi mini uzuri mana, muna cikin weekends ne, kuma ga shirin exams muna yi, don't judge me wrongly please, but ban gane China ba ina ne China?".
"Ohh baki ma san meke faruwa ba, Abbi ya biya mini Makaranta a China, jibi in Allah ya kaimu zan tafi, bana nan za'ayi Aurenki, ina fatan Allah ya baku zaman lafiya, ya dawwamar da farinciki a rayuwar Aurenki da wanda kike so".
"Impossible" Abra ta faÉ—a tana wani haÉ—e rai.
"Meye ma'anar tafiyarka China? Saboda me?"
"Bani zaki yiwa wannan tambayar ba, kamar yadda kika ji maganar sama ta ka, nima haka na ji ta".
Da gudu Abra ta juya, ba ta tsaya ko ina ba sai sashen Abbi.
"Abbi, Abbi! Abbi".
Abbi ya ce "Na'am Sweetheart ya akayi?".
Na'ima ta ce 'Wannan wane irin rashin hankali ne?"
Abra ba ta kula Na'ima ba ta ce "Abbi, mai yasa za'a kai Faris China? Laifin me yayi? Mai yasa za'a rabani da shi tun Yanzu, har ace zai tafi jibi ban sani ba, amma dai Abbi Faris da wasa yake mini ko?"