Sashe 90
Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Hannu ya sa cikin sumarsa ya yamutsa ta, ya rintse idanunsa, a tunaninsa zuwan da yayi ya ga Abra, zai rage masa raɗaɗin da yake cikin zuciyarsa, da samun sassauci akan halin da yake ciki, duk da ya san hakan bai kyautu ba, kasancewar ita matar wani ce a yanzu, kuma ga alƙawarin da yayi, na ba zai sake zuwa Nigeria ba, amma ya kasa daurewa sai da yaje, amma zuwan nasa bai amfana masa Komai ba sai sake jefa shi cikin tarin damuwa da tambayoyi.
Abra tana auren wanda take so amma ta furta masa kalmar so, yayi shiru tare da tuna yadda Adnan ya mari Abra saboda kishi, da yadda ya kira shi da loser "No! Am not a loser" ya faÉ—a yana dukan kan mirror.
"Abra zata dawo gareni, amma ta yaya how? Wa zai bani goyon baya?"
Can kuma sai wata zuciyar ta gargaɗe shi 'Ina imaninka da iliminka na Addini, duk wani abu da zakai yinƙurin aikatawa, don mallakarta alhalin tana matar wani ya saɓawa Shari'a'
Rintse idanunsa yayi, tare da taune lips ɗinsa na ƙasa, da ya tuna yanzu Yaya ta san wacece ita, ta san matsayinta. Ko wani hali ta shiga lokacin da ta sani? Amma ya a kai ma ta sani, sam wannan bahagon mijin nata, ya hana shi ya samu ya sake da ita su yi hira. A hankali ya taka zuwa baki gado ya zauna, ya sunkuyar da kansa yana tunani.
Abbi ya rasa ta ina ya kamata ya fara binciken iyayen Abra, sai yanzu ya gane cewar yayi kuskure, tsananin son Abra da tausayin ta lokacin da ya tsince ta, ya rufe masa idanu, ya kasa tsayawa yayi bincike a kan su waye iyayen Abra, ba tare da tunanin akwai rana kamar irin ta yau da zata zo ba, wanda dole Abra zata buƙaci sanin haƙiƙanin suwaye iyayenta.
A hankali ya sauke ajiyar zuciya, ya fara laluben wayarsa, sai dai yana dubawa ya ga missed calls ciki har da na su Ammi.
Cikin hanzari ya shiga ƙoƙarin bin kiran Ammin. Ammi na ɗagawa cikin girmamawa suka gaisa. "Babana ina ka shiga ne haka? Ake ta kiranka baka ɗagawa?"
Major ya ce "Afuwan Ammi, wayarce a silent".
Ammi ta ce "Shikenan, kana gari ne?"
"A'a Ammi, ina wurin aiki".
"To duk abin da kake da ka shigo gari ka zo?".
"Lafiya kuwa Ammi?"
"Idan ka zo ka ji"
"Shikenan dama shari'ar nan ce ta sanya na taho wurin aiki, amma tunda an kammala insha Allah zan biyo jirgin dare in taho".
"To shikenan, Allah ya kawo ka lafiya"
Ya amsa da "Ameen"
Kamar yadda Abbi ya faÉ—a, a daren ya dawo gida, washegari da wuri ya shirya ya nufi gida, Mintuna kaÉ—an suka kai Abbi gidansu.
Tun da ya ga Baffa a gidan a daidai wannan lokacin kuma da alama duk shi suke jira, ya sha jinin jikinsa.
Ya gaishesu cikin girmamawa, sannan ya É—ora da Ammi "Gani, Allah yasa lafiya naji kin ce kuna nemana?"
Baffa ya ce "Au tambaya ka ke ko lafiya? Kai ba abin kunya ne ba abin da ka aikata Kamal, da ƙuruciyarka ba ka saki matarka ba sai yanzu, kuma ace ba wanda ka kira ka gayawa wannan maganar? Sai su daga can gidan nasu ne aka kiramu aka sanar mana, me ka aikata kenana Khama? Wane laifi zata aikata maka a yanzu, wanda ba kayi haƙuri a baya ba, da har za ta kai ku ga saki, bayan har 'ya kun kai ɗaki".
"Baffa dan Allah kuyi haƙuri, amma abin da Na'ima tayi mini bani da zaɓin da ya wuce aikata hakan".
"Ka kyauta ai, sai ka tashi mu tafi can gidan nasu, mu zauna mu tattauna, a gano bakin zaren".
Major ya ce "Baffa, zamu iya tattauna komai a nan, in gaya muku duk abin da ya faru".
"Ba shawarar ka muke nema ba, tashi koma menene muje can a tattauna" ba yadda Major ya iya, haka ya tashi suka tafi gidansu Na'ima.
Bacci ne mai nauyin gaske ya ɗauke Abra, sanyin tiles ɗin nan da ke ratsa ta ya sanya zazzaɓi ya ƙara rufeta sosai da sosai.
Sai can azahar sannan ta farka daga nannauyan baccin da ya É—auketa, har wani duhu take gani, saboda wata irin yunwa da take ji, ga jikinta babu daÉ—i. Ta kalli gurin da kayan Adnan suke a zube, kallon kayan kawai da tayi ta ji cikinta ya sake yamutsawa, zuciyarta ta fara tashi.
Tsaki tayi ta É—au kayan, tana toshe hanci, ga jiri na É—ibar ta ta tafi É—akinsa, tana zuwa ta shiga toilet É—insa, ta zuba kayan a bucket ta fice.
Ta nufi kitchen ta shiga buÉ—e buÉ—en kwanuka, ba abinda ta girka balle ta ci.
Bredi ta tarar a kan dining, wanda Adnan ya karya ya fita, ta zauna ta dinga ci kamar mayunwaciya, sai da ta ci ta ƙoshi sosai, ta koma fridge ta ɗauko lemo mai sanyi ta sha sai da ta ji babu gurin zubawa komai sannan ta haƙura.
A haka ta É—ora ruwa dan tayi wanka ta É—ora girkin rana, ta É—an fara gyara gidan, duk da gidan ba wani datti yayi ba, tana yi tana kwanciya saboda gaba É—aya jikinta babu daÉ—i. Cikinta ne ya fara juyawa kamar É—azu da safe, nan ta dinga kwara amai, sai da ta amayar da duk abin da ta ci, ta dawo falo ta kwanta gaba É—aya ta galabaita.
Tun tana jin aman ta tashi ta tafi banɗaki, har ta koma toilet ta zauna gaba ɗaya, kan kace kwabo, Abra ta fita hayyacinta. Da ƙyar ta iya lallaɓawa ta yi wanka, shima ba sabulu iya ruwa ta watsa, ta dawo tai salla a zaune, ta kwanta. Amma amai bai tsaya ba dan ba ta fasa yinsa ba.
"Kai muke saurara, kayi wa mutane bayani ya aka yi ka aikata wannan É—anyen aikin, bamu sani ba laifin me tayi maka?".
Major yayi ajiyar zuciya ya ce "Tun da na auri Na'ima, muka yi auren soyayya muke zane lafiya da ni da ita, har zuwa lokacin da na tsinci Abra, wanda tun daga wannan lokacin ta dinga bijiro mini da wasu irin halaye akan yarinyar, tana iƙrarin ni na haifi yarinyar da karuwa a waje, kuma ba zata riƙe ta ba. Idan ban manta ba a wancan lokacin na yi mata wani furuci na cewa, idan har ta bari wani yasan ba ni na haifi Abra ba daga gareta a bakin Aurenta. Sai ta dinga nuna mini bakomai, a gabana ta kula da Abra a bayan idona ta cutar da ita, wanda na daɗe da fukantar hakan amma nayi shiru na ƙyle. Ashe matar nan ta riga ta sanar da ɗanta cewar bamu muka haifi Abra ba, ina wurin aiki, na samu wayar mijin Abra ya haɗani da ita, yarinyar tana kuka ta sanar mini da cewa wai ashe bamu muka haifeta ba? Wanda na san ba mai gayamata sai Na'ima, kuma na dawo gida na tarar da wasiƙar da Salman ya bari a kan cewar ba zai sake dawowa Nigeria ba, ashe ya san Abra ba 'yar uwassa bace, ya fara sonta kuma ta sani duk ta munafunce ni, Wallahi Ammi bakiga a mawuyacin halin da na baro Abra ba, dan haka taje tayi rayuwarta nima in yi tawa, zan tabattar da samun farincikin yarana".
Na'ima ta fashe da kuka tana faÉ—in "Wallahi ni ban gaya mata ba"
Ammi ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, yanzu kana nufin Abra ta san ba kai ka haifeta ba?".
"Ta sani Ammi, ba kiga a yadda na baro ta ba, cikin matsanancin tashin hankali da damuwa, yanzu irin tsananin soyayya da shaƙuwar da ke tsakaninta da Salman da wani abu da ba a so ya shiga tsakaninsu fa a dalilin sanin su ba 'yan uwa bane? Duk bata kalli wannan ba amma ta sanar musu, ba yadda ban da Abra ba a kan ta gaya mini wanda ya gaya mata amma taƙi, wanda nasan dama ba zata gaya mini ba, saboda ba ta san ace ga laifin Na'ima dan ita uwa ta ɗauketa".
"Wallahi ni bani na gaya mata". Ta sake Maganar cikin raunin murya.
Baffa ya ce "Kuskure ne dai an riga an yi shi, amma kayi haƙuri ka maida yarinyar nan ɗakinta, ba shawara ba ce umarni ne".
Abbi yayi jimm, yayin da ƙanin mahaifin Na'ima shima haƙurin yake bayarwa.
Khamal ya ce "Shikenan, batun ɗan ta da ta sa na tura China kuma, sai taje ta nemo shi da kanta, dan dama ita tace a kai shi can, tun da yace ba zai dawo ba shikenan, dama mugunta ai fitsarin faƙo ce".
Ammi ta ce "A'a ai duk ba za'ai haka ba, haƙurin dai shi zaka yi" aka haɗu akai ta bawa Abbi haƙuri, ya amince Mami ta koma ɗakinta.