Sashe 82
Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ɗaga kai ta yi da ƙyar ta dube shi amma ta kasa magana, hawaye ne kawai yake zuba daga cikin idonta. Ƙoƙarin jan bargon da ya yaye mata ta yi amma ya riƙe bargon tare da buga mata tsawa da faɗin. "Tashin ne ba za ki yi ba ko me da kike ƙoƙarin jan bargo? Wato ga mahaukaci yana magana ba za ki tashi ki yi abin da na saka k....." Ƙarar doorbell ta hana shi ƙarasa faɗar zancensa. Ƙwafa ya yi tare da nuna ta da hannu ya ce. "Na dawo na tarar ba ki tashi ba, wallahi na lahira sai ya fi ki jin daɗi." Ya ƙarashe maganar tare da yarɓar mata da bargon a fuska. Lumshe idonta kawai ta yi tana jin yanda zuciyarta ke bugawa da sauri da sauri. Adnan da matsalarsa ba su ne damuwarta ba a yanzu, damuwarta kawai sanin gaskiyar abin da Adnan ya faɗa mata na cewa ita TSINTACCIYA ce, Abbinta mafi soyuwa a gare ta ba shi ya haife ta ba, ba ta fatan hakan ya kasance, domin ta san zuciyarta ba za ta iya ɗauka ba bugawa za ta yi. Addu'a take Allah ya sa Abbinta ya musan mata ya ce ba haka ba ne, domin ta ƙudurce a ranta duk wanda zai faɗa mata ba za ta taɓa yarda ba, ko da Mami ne da Salman kuwa, Abbi kawai zai tabbatar mata da gaskiya ne ba shi ya haife ta ba ta yarda.
Adnan yana buɗe ƙofa kamar a mafarki ya ga Abbi tsaye cikin wani irin yanayi, sai da gabansa ya faɗi amma bai nuna hakan ba, murmushi ya yi tare da yi masa iso zuwa cikin parlour'n cike da girmamawa.
Sai ƙarfe tara da rabi wani likita ya zo ya ƙara dudduba jikin malam, bayan ya gama ya ce su Inna su same shi a office. Bayanin ciwon dake damun Malam ɗin ya yi musu wato ciwon zuciya wanda already sun san da shi.
Ya ƙara da faɗin, "Ciwon nasa ya yi tsanani sosai, don haka ana buƙatar yi masa aiki cikin gaggawa. Amma gaskiya wannan Asibitin ba mu da kayan aikin, sannan likitan da yake aikin bai ƙaraso ba"
A ruÉ—e Inna ta ce. "Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un! To likita ku yi masa aikin mana, don Allah ka taimake mu ka ceto mana rayuwarsa, idan muka rasa shi za mu shiga cikin wani hali, shi ne bangon rayuwarmu."
Cikin son kwantar mata da hankali likitan ya ce. "Kar ki damu Hajiya, zai samu lafiya insha Allahu, sannan kuma a nan asibitin ba mu da kayan aiki masu kyan da za mu yi masa aiki, amma zan tura ku wani babban Private Hospital wanda da yardar Allah za a yi aikin successfully."
"Likita ina ne firaben honfital kuma?" Inna ta tambaye cikin damuwa.
"Asibitin kuɗi kenan, sunansa G.Y BULAMA, suna da ƙwararrun likitoci gami da kayan aiki masu inganci."
"Asibitin kuɗi fa ka ce ɗana, ai ba mu da kuɗin da za mu biya, na gwamnatin ma da ƙyar muke iyawa."
"To Hajiya, in dai kuna son samun lafiyar shi gaskiya ku je can É—in."
Inna za ta kuma magana Musa ya hana ta da faÉ—in. "Shikenan likita, mun gode sosai." Sannan ya dubi Inna ya ce. "Mu je Inna."
Bayan sun fita Inna ta saka kuka ta ce. "Allah ka fitar da mu daga cikin wannan tashin hankalin, yanzu Musa ya za mu yi?"
Cikin damuwa Musa ya ce. "Inna mu je can inda ya ce manan kawai, don gaskiya likitan nan ya faÉ—a mana a asibitin nan ba yi masa aikin za su yi ba, kin manta yanda aka yi ne wancan karon, kullum cikin saka mana ranar aikin suke amma ba su yi ba har Allah ya ba shi lafiya muka koma gida."
GyaÉ—a kai Inna ta yi ta ce. "Haka ne, to amma Musa kuÉ—in nake ji, ba mu san nawa za su ce mana ba."
"Allah ba zai hana mu yanda za mu yi ba, mu je ya yi mana kwatancen asibitin."
Jiki a sanyaye Inna ta ce. "Toh, addu'ata kullum kar Allah ya karɓi ran malam ba tare da ya sanar da mu aihinin gaskiyar al'amarin nan ba, domin mu san ta inda za mu fara bincikawa, tunda komai daren daɗewa sai gaskiya ta yi halinta."
"Insha Allahu Malam zai samu lafiya har ya warware komai da kansa kamar yadda yake da buri, ki kwantar da hankalinki Inna, mu dai mu yi ta addu'a Allah ya ba shi lafiya kawai."
"To amin amin .Amma naji ance shi likitan da zamu je gurin nasa yana zuwa nan duba marasa lafiya, ba za mu jira shi ba?"
Musa ya ce "Inna ance yau babu lallai ya shigo, kawai gara mu bishi can É—in, bari in je sun ce zasu bamu wata takarda mu tafi da ita".
Inna ta ce "Shikenan, je ka dawo mu tafi". Musa ya juya ya fice, yayin da mara lafiyan ke ta cigaba da kakari.
Kamar yadda aka yi musu kwatance haka suka isa GY BULAMA HOSPITAL AND MATERNITY.
A gaggauce Musa ya shiga cikin Asibitin, ya fito da Wheel chair, suka É—ora Malam a kai, ya tura shi zuwa cikin Asibitin.
Gaba É—aya Musa a rikice yake, bai tsaya saurarar kowa ba ya fara bulayin in da zai kai Malam ya kwantar.
Wata Nurse ce tayi masa tsawa ta ce "Malam lafiya, ya zaka zo da mara lafiya kawai ka wuce mu?"
Musa ya ce "Yi haƙuri, wallahi duk a gigice nake ne, shiyasa daga Asibitin cikin gari aka turo mu nan, aka ce mu zo muga likita nan".
"To ai ba Chemist bane nan, ba haka kai tsaye aka ganin likitan ba, zaku fara buÉ—e file dubu goma".
Musa yayi turus, ya ce "bakomai a buÉ—e masa".
Inna cikin damuwa ta ce "Musa idan ka biya dubu goma, abun da zai yi saura a hannunmu ba shi da yawa".
"Bakomai Inna, Allah zai bada yadda za'a yi".
Ya cire kuɗi ya miƙa, ya biya aka buɗe File ɗin.
Nurse Jamila ce ta taho, hannunta riƙe da wasu files, ta kalli Musa ta ce "Bawan Allah, tura dattijon nan daga gefe mana, ka bar shi yana ta haki haka, tallafo kansa ka maida shi gefe".
Musa yaji daÉ—in yadda Nurse Jamila ta kula su da nuna wa mahaifinsu kulawa.
Ya ce "Wallahi hajiya a rikice muke ne, mun kai shi babban Asibitin birni, aka ce mana likitan da yake zuwa duba masu irin rashin lafiyarsa sau É—aya yake zuwa a sati, kuma yau ba zai zo ba, shine suka turo mu nan da wannan takardar".
Nurse Jamila ta karɓi referral later, sannan ta kalli su Musa, wani irin tausayinsu ya kamata, ta ce "Kaga, ga Emergency room can, ku shiga da shi ku kwantar, bari na je na kai wa likitan".
Musa kamar zai durƙusa wa Jamila abinka da mutumin ƙauye "Mun gode hajiya, Allah ya saka da alkhairi".
"Ba komai ku je, ina zuwa".
GY BULAMA ne ya gifta ta can gefensu, yana cikin rigarsa fara ƙal ta aiki, sai zuba ƙamshi yake yi, yana takunsa cike da ƙasaita, kyawunsa ya ɓoye tsufansa ma'aikatan suna masa sannu da zuwa, yana ɗaga musu hannu tare da yi musu sannu da aiki".
Musa bai lura da abin da Malam ya ƙurawa idanu ba, sai ji ya yi Inna tana cewa Alhamdilillah, Malam ya buɗe ido.
Suna masa sannu haka suka kai shi Emergency suka kwantar.
A Office Jamila ta samu MD, ta yi masa bayanin Komai.
Ya karɓi takardar ya duba, ya ajiye takardar ya ce "Kije ki gaya musu, yana buƙatar ayi masa aiki da gaggawa, kuma kin san da likitoci turawa muke aikin nan, dan haka zasu biya 2.5millon, wani rami ne a zuciyar tasa.
Nurse Jamila jiki a sanyaye ta ce "Doctor, Ba su da wannan ƙarfin, dan da alama daga karkara suka zo".
"Well sai ku sallame su".
"Amma da mun je ka gan shi, ko wani taimakon gaggawa ne sai ka rubuta a yi masa, ba ma sallame su haka ba, yana cikin mawuyacin hali".
"Mai kike so in yi musu? Kin san muddin ba aikin nan aka yi ba mutuwa zai yi, dan haka ku sallame su, kar ya mace mana a nan a zo ana yadda za ai a fita da gawar".
"Please doctor, ko yaya idan suka ga an basu kulawa ko mutuwa ya yi, ba za su ce an wulaƙanta su ba, ko oxygen a sa masa a bashi wani abin da zai samu releif".
"Idan za su biya sai a sanya masa, in kuma ba haka ba maza ku sallame su".
"Please doctor...."
"Jamila out of my office, Asibiti na ba na taimako ba ne, na neman kuÉ—i ne".
"Amma....
"Ohhh my God, Jamila kina daf da kai ni bango a Asibitin nan, get out".
Jamila ta fita jiki a sanyaye, Musa na ganin ta ya ce "'yar uwa zo kiga abin da yake yi, dan Allah ki kira mana likitan ya duba shi" Musa ya yi Maganar kamar zai fashe da kuka.
Jiki a sanyaye Jamila ta ƙarasa, ta tarar da dattijuwar matar ta riƙe hannun dattijon da yake ta kokawa da numfashi. Wani irin tausayinsu ya sake kama ta.
Duk da wannan hali da dattijon ke ciki, nuna musu wani guri yake yana faÉ—in "'yar Baba"
"Me 'yar Baban tayi Malam, ka kwantar da hankalinka, in Allah ya yarda lafiya za mu koma gida, ka ga 'yar Baba".
Jamila ta ce "Ku yi haƙuri, yana duba wani mara lafiyan ne, idan ya gama zai zo".
"Ba wani likitan da zai zo kansa ne?" Dattijiwar tayi maganar tana share hawaye.
"ShikaÉ—ai ne likitan zuciya, bari in koma in gani ko ya gama".
Jamila ba ta karaya ba, ta koma gurin Bulama, amma ya balbaleta da masifa, ya ce "Ba zan je kansa ba, ko naje ba zan hana shi mutuwa ba, dan haka ki je ki yi abin da na ce ki sallame su, su je su kai shi wani wurin".
"Doctor ba zan iya faÉ—a musu haka ba, dan Allah ko ganin ka ne ka je su yi a kan mara lafiyan su, sai ka gaya musu da bakinka".