Sashe 83
Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Fitar mini daga office, wace irin masifa ce haka, shi kansa doctor Shamsu zan ja masa kunne, Asibitina ba na taimako bane, ya daina turo mini Mutanen da ya san they can not afford our services".
Jamila ta kuma komawa, Musa ya tare ta yana faɗin "Dan Allah ni ki nuna mini likitan in roƙe shi, kar mu rasa shi, yana da wata 'ya da idan muka rasa shi bamu san halin da zata shiga ba".
"Ɗan uwa kayi haƙuri, likita ba zai iya cire masa ciwon ba, sai dai ya taimaka masa, mu je in ga idan da Allurar da zan iya yi masa ko bacci ya samu".
"Suna shiga ta tarar Wannan dattijo ya kai gargara, sai numfarfashi yake yana kiran " 'Yar Baba, ki zo....ki zo. ...kusa da ni, abi....abin da.....zan faÉ—a mu.......muku.... 'yar Baba".
Jamila ta ce "wace wannan 'yar baban da yake ta faÉ—a?"
Musa ya ce " 'yar sa ce, ku taimaka mana, Wallahi zamu iya yin rashi biyu, mu rasashi mu rasata, a duniya soyayyar da yake mata ba kowa yakewa ba".
Cikin hanzari Nurse Jamila ta fara ƙoƙarin neman allurar da za ta yi wa dattijon, idan yaso ko me doctor zai yi ya yi. Sai dai kash tana dawowa ta tarar Dattijon ya yi kalmar shahada ya cika!!!.
A ɗaki Adnan ya samu Abra ya ce "Sai ki tashi, ga babanki na riƙo can ya zo" duk tsananin jiri da zafin zazzaɓin da ke jikin Abra, ba shiri ta miƙe ta sakko zata fita.
"Ke mahaukaciya, ba fa babanki ne mahaifi ba, babanki ne na riƙo haka zaki fita da wannan rigar? Wuce ki wanke fuskar ki, ki sanya kaya".
A gaggauce ta iya dafa bango ta zura doguwar riga tayi falo da sauri, tana zuwa ta zube a jikin Abbi tare da fashewa da wani irin matsanancin kuka.
Cikin jarumta Abbi ya ce "Haba Sweetheart, kinga yadda kika rame kuwa? Kin yi duhu haka meke damunki?".
Adnan da ya kamile a gefe ya ce "Ai Abbi tun da aka yi Auren nan a haka muke, ko Abincin kirki ba ta iya ci, ba bacci kullum cikin kuka, na rasa a ina ta ji wannan mummunar Maganar".
Abra har mamakin makircin Adnan take, kamar wani mace, amma dayake ba ta tashi take ba, cikin kuka ta ce "Abbi, tun da aka kawo ni, ba ka zo ka ganni ba, Mami ba ta zo ba, su Ammi ma haka, Faris É—ina ma.... Sai ta sake rushewa da kuka".
Abbi ya shiga goge mata hawaye yana faɗin "Am sorry daughter, kin san an naɗani a shugabancin kwamitin binciken General Ibrahim, ko weekends bana iya zuwa, kina raina, Ammi ce kuma ta hana kowa zuwa, ta ce bai kamata daga kawoki a dinga yi muku sintiri ba, amma kiyi haƙuri" ya ƙarasa Maganar yana sake gyara mata zaman hearing aid ɗinta.
"Abbi waye babana? Dagaske tsinto ni ka yi?"
Abbi yayi shiru sannan ya ce "Waye ya gaya miki wannan maganar ne?".
"Abbi ka daina binciken waye ya gaya mini, dan Allah Abbi ka gaya mini gaskiya" wata irin karaya da tausayin Abra ya kama Abbi.
Abra ta fara ƙoƙarin sanya idanunta a cikin na Abbi, amma ya ɗauke kasa ya ƙi kallon ta yana girgiza kai.
"Abbi kar kace mini zancen nan gaskiya ne? Abbi idan ba kaine babana ba waye?".
"Abra bani da amsar tambayar ki"
"Abbi ta tabbata tsinto ni kayi kenan?".
"A'a ba haka ba ne Abra"
"To Abbina yaya ne? Abbi baka yi mini ƙarya tun tasowata, hasali da kai nake koyi gurin gaskiya da riƙon amana, Abbi daga bakinka ne kawai zan iya jin abin da zai fidda zuciyata daga shakku komai ɗacinsa ka gaya mini zan dake".
Adnan ya ce "Kinga Abra, ki ƙyale Abbi, daga zuwansa ba gaisuwa baki bashi Abinci ba, amma kin cika shi da tambayoyi marasa ma'ana".
"Dalla ka rufe mini baki, kai mini shiru ba da kai nake ba, Abbi kayi Magana dan Allah". Ta yiwa Adnan Magana cikin tsawa.
Abbi ya ce "Ya na ji jikinki da zafi haka? bari temperature jikinki ta saki sai mu yi Magana".
"Abbi ta tabatta haka ne kenan? Zargina gaskiya ne? Abbi kar ƙwaƙwalwa ta ta juye in haukace, ka gaya mini dan Allah". Gaba ɗaya Abra ta fara fita hayyacinta, ga hawaye ga gumi ga majina, ga jikinta na rawar sanyi saboda zazzaɓi.
"Haka ne Abra haka ne, amma...." Toshe wa Abbi baki tayi, ta fara maimaita "Innalillahi wa Innalillahi raji'un" tare da miƙewa tsaye ta tsaya cak, can ta yi wata irin shaƙuwa tamkar fitar rai, ta faɗi a gurin!
Littafin kuɗi ne,biya ₦300 via 0116886423 Sulaiman Na'ima s union Bank... Idan katin waya ne zaka Turo 500 shaidar biya 08081012143 or 09047871750
[10/20, 12:46 PM] Abk: A kusan tare cikin gigita da firgici Abbi da Adnan suka fasa ƙara tare da faɗin "Abra!" Kafin Abbi ya Ƙarasa gareta Adnan ya rigasa gaba ɗaya ya sanya hannunsa tare da ɗagota zuwa jikinsa yana bubbuga ta tare da kiran sunanta.
"Angel.. Angel... Angel"
Ya faɗa yana girgiza ta da iya ƙarfinsa ganin ko motsi ba tayi sai ya kalli Abbi da Yake tsugune dab da su hannunsa riƙe dana Abra yana murzawa.
Cikin tashin hankali Adnan ya dubi Abra hannunsa na rawa ya kama nata hannun, jin babu alamar jijiyar hannun na harbawa ya sanya shi kara kunnensa a ƙirjinta nan ma bai ji bugawar zuciyar ta ba, hannunsa ya mayar kan hancin ta sai a lokacin ya ji kamar huci na fita. Muryarsa na rawa sosai ya dubi Abbi ya ce.
"Help me Abbi I don't want to lose my wife. Angel, open your eyes" Adnan ya faÉ—a a gigice,tare da nuna kulawarsa ga Abra wacce ke kwance kan cinyarsa. Seeing Abbi in front of him made him pretend to be worried about Abra's illness but in his mind it was all a plan.
"Adnan tunda ta zo gidan ka tayi Irin haka?" Girgiza kai Adnan yayi still holding onto her yana shafa kanta ya ce. "No, she didn't, Abbi. we are happy. Tunda ta samu wannan maganar komai ya lalace,she is not happy, she has stopped everything, eating, talking, she is always crying in her room. Ta rame tai baƙi ta damu kanta. Mahaifiyata har ganin laifina tayi"
Shiru Abbi yayi shi kansa, baya cikin hayyacinsa komai nasa ya tsaya dauriya kawai yake na ganin ya nuna babu komai, amma rashin iyaye a wannan rayuwa babbar illa ne ga mutum. Musamman ga Abra wacce ta ɗauki soyayya mai tarin yawa ta ɗora akan su, ba lallai ta jure zafin wannan ƙaddara ba, ya san tana da haƙuri da karɓar dukkan abin da ya zo mata da hannu bibbiyu. Amma wannan abu ne wanda kai tsaye ba zaka iya gane al'amarin sa ba, bayan tsintar ta da ya yi ita ɗin halattacciyar ƴa ce kamar ko wanne yaro? Ko kuma an sameta ne ta gurɓatacciyar hanya? Wannan abin shi ke kaiwa da dawowa cikin tunanin Major Khamal Khamis.
"take her to the car"
Abbi ya faɗa yana mai ɗauke kansa cike da kamewa ganin yadda Adnan ko kunya babu yake ta rungome ta a jikinsa. Kamar wanda yake jira haka ya sunkuceta zuwa mota. Abbi yabi bayan su, Adnan na baya da Abra, Abbi na gaba sai driver a haka suka nufi asibiti har lokacin babu inda yake motsi a jikinta tamkar gawa haka ta kasance kwance jikin Adnan. Shi kuma ya tsura mata shanyayyun idanunsa yana ƙare fuskarta kallo ganin yadda tai duhu sai dugun hanci, da wuyanta da ya ƙara tsayi. Abin mamaki kuma ƙirjinta Ma sha Allah a cike yake kamar ana ƙara masa girma kullum!.
Har suka isa Asibiti Adnan yana riƙe da Abra a jikinsa,He shows his compassion and care for her. Da sauri Nurses suka amshi Abra daga hannun Adnan wanda da ƙyar ya amince ya bada ita, sai da Abbi ya bashi haƙuri tare da rarrashin sa, sannan ya bawa Nurse's ɗin ita. Kai tsaye Emergency suka shiga da ita, Oxcgyen aka sanya mata bayan sun kammala bincikar abin da ya ke damunta, kafin suka sanya mata drip tare da injection.
Abbi na tsaye ya goya hannunsa a bayansa, tare da ƙorawa ƙofar Room da aka kwantar da Abra ido. Tunanin yadda zata iya fuskanta rayuwar ta a nan gaba yake, ba zata taɓa jurewa ba, zuciyar ta, ta raunata ainun.
Yana tsaye wani Doctor ya fito yana goge zufa, da sauri Adnan ya miƙe yana kallon likitan baki na rawa ya ce.
"Ya matata likita? she recovered from her coma,Don't say anything happened to my wife"
KafaÉ—ar Adnan Likitan ya É—an buga idanunsa akan Abbi ganin yadda shi kaÉ—ai yake girgiza kai kafin ya maida ganinsa zuwa ga Adnan wanda yake da tabbacin shi ne mijin yarinyar da aka kawo,
ganin kamar yafi Abbi ruɗewa da shiga tashin hankali kallo ɗaya zakai masa ka fahimci hakan a kwance saman baƙar fuskarsa.
"pray for her, she will get relief from the pain that is bothering her". Ya ƙare maganar yana ƙara bubbuga kafaɗar Adnan can kuma ya ce.
"Who is the husband of Abra Khamal Khamis?"
Abbi dake tsaye ganin Adnan ya kasa magana sai ya kalli Likitan tare da nuna Adnan ya ce.
"Gashi nan" Kallon Adnan Dr ya yi kafin ya É—an yi tako É—aya zuwa biyu yana faÉ—in "Oh! I see."
"Follow me to my office" ya ƙara cewa yana yin gaba. Sai a lokacin Adnan ya buɗe baki da ƙyar ya ce "Ni? Ko Abbi?"
Likitan ya tsaya yana duban Abbi kafin ya ce "Who is he to her?"
"Her father"
Cewar Adnan yana kallon ƙofar Room da Abran ke ciki, a zuciyarsa yana tunanin wani abu nada ban.
"Oops. Both of you follow me" yana faɗin hakan ya shige Office nasa, Adnan ne ya fara yin gaba dai Abbi yabi bayan sa jiki a sanyaye, tare da tsoran abin da likitan zai faɗa masa wanda yake damun Abra a wannan karon duk da ya san larurar Abran amma yanzu tunaninsa ya saɓa zatonsa.