Sashe 9
Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Murmurshi Lieutenant Faruk ya sakar masa tare da sake yin sallama. Amsa masa ya yi a can ƙasan maƙoshi. Faruk ya ƙaraso tare da janyo kujera da hannunsa mai lafiya ya zauna a gabansa.
"Good Morning Captain" Ya faÉ—a cikin respect.
ÆŠaga masa kai kawai Captain ya yi.
Cikin kulawa FaruÆ™ ya ce "Ya jikin naka?"
Cikin dakakkiyar muryarsa ya ce. "Alhamdulillah, and you?" Faruk ya ce. "Da sauƙi Alhamdulillah." Jinjina kai Captain ya yi tare da runtse idanunsa, lokaci ɗaya kuma ya buɗe idon kamar an tsikare shi ya ce.
"Faruk I want to ask you something?" Faruk ya ce. "Okay Sir."
Captain yana kallon cikin idonsa ya ce. "Akwai wata little Baby da na É—auko jiya tana ina, ance ba'a ganta ba?"
Faruk ya ce. "Tana cikin asibitin nan, ana bincikar lafiyar jikinta, Madam Halima ce tare da ita."
Ajiyar zuciya ya sauke mai ƙarfi ya ce. "Ina fatan dai babu wani abu da ya same ta ko?"
Lieutenant Faruk ya ce. "Babu Sir."
Ajiyar zuciya ya ƙara saukewa, yana jin yanda nutsuwa ta fara mamaye zuciyarsa.
Faruk ya cigaba da magana.
"Muna jiran a tabbatar tana cikin ƙoshin lafiya ne kafin mu fara cigiyar iyayenta, su sauran yaran ɗazu aka kaisu gidan gwamnati, za'a miƙa su ga iyayensu, ita kuma ba wanda ya san daga ina take, za'ai cigiyar iyayenta"
Da sauri Captain Khamal ya ce. "
No, not now."
Da mamaki Faruk yake kallon shi, da son jin dalilin da ya sa yace ba yanzu ba.
gyaÉ—a masa kai Khamal ya yi ya ce.
"A bar ta a hannun Madam Halima har zuwa lokacin da zan samu lafiya, da kaina nake son yin bincike a kanta."
"But Sir...."
Ɗaga masa hannu ya yi fuskarsa a haɗe, alamar ya ƙosa da maganganun Faruk, hakan yasa Faruk ya haɗiye maganarsa, amma cikin ransa fal mamaki ne akan abun da Captain ya faɗa.
A sanin da ya yi masa mutum ne wanda babu ruwansa da shiga shirgin da ba nasa ba, komai zaka yi sai dai ya bika da ido amma ba zai tanka ba. But bai san dalilinsa na yin hakan akan yarinyar ba. Ɗan taɓe baki ya yi ya miƙe ya yi masa sallama ya fita.
Ƙarfe ɗaya saura na rana tawagar su Chief of Army staff ta sauka a Kantagora Army barrack Naija state, direct inda Captain Khamal yake ya ce a fara kai su.
Su uku suka fara shiga ɗakin da yake, Chief da General Ibrahim sai wani Colonel, daga baya kuma Ministan tsaro da na sufuri da wasu jami'an tsaron suma suka shiga.
Yana kwance idanunsa a lumshe kamar mai bacci, amma ba baccin yake ba, wani likita na tsaye a kansa yana dudduba shi. Ƙamewa Likitan ya yi ya sarawa su Chief of Army staff tare da welcoming ɗinsu. Hakan ya saka ya buɗe idanunsa ya waiwaya ya kalle su.
Da sauri ya ɗago kansa tare da ƙoƙarin yin salute daga kwancen da yake. Chief ya ƙarasa kusa da shi ya kama hannunsa yana murmurshi ya ce. "No need, our Lion the king of the jungle, I salute you Captain Khamal Khamis"
Ƙasa ya yi da kansa cikin respect ya ce. "Welcome Sir."
Chief ya ce. "Thank you, How are you feeling now?"
Ya ce. "Better Alhamdulillah." Chief ya ce.
"Masha Allah, Allah ya ƙara lafiya, rundunar soja tana matuƙar Alfahari da samun jajirtacce kamar ka, shugaban ƙasa ma ya yabawa ƙoƙarin da ku kai, duk da baya gari amma ya turo wakilansa, muna tare da ministan tsaro da na sufuri, duk muka zo duba ku."
Captain Khamal ya jinjina kai tare da faÉ—in "Thank you sir"
General Ibrahim ya ƙaraso cikin ƙoƙarin ɓoye halin da yake ciki ya yi masa sannu ba yabo ba fallasa, shi ma ya amsa masa a haka.
Minista kuwa cikin fara'a ya yi masa sannu tare da yi masa jinjina akan aikin da suka yi.
Ta gefen ido General ya dinga hararar Khamal cikin tsananin baƙin ciki. Chief ya zauna a kujerar da Likitan ya kawo masa, yana duban Captain Khamal cikin jinjina ya ce.
"Sannu da ƙoƙari Captain, tabbas kai ɗin na daban ne kuma mai sa'a ne ko a cikin sojoji. Irinku Jajirtattu masu aiki domin Allah ƙasar mu take buƙata, da ace ƙasar mu za ta samu kamar ka su fi rinjaye a cikin jami'an tsaro da ma mutane da an samu sauƙin ta'addanci da duk wani criminals acts a cikin ƙasar nan. An daɗe ba'a samu Nasara a fita operation kamar wannan da kuka fita ba, hakan ya ƙara nuna mana jajircewarka Hukumar sojojin ƙasa ta yaba muku kuma ta jinjina muku."
Captain ya ce. "Thank you Sir." Chief ya ce. "Allah ya ƙara lafiya, bari mu zagaya mu duba sauran soldiers ɗin daga nan zamu wuce government House na nan garin, dan miƙa yaran nan ga iyayensu.
" Captain ya ce. "Okay Sir, a fito lafiya."
Cikin yaƙe General Ibrahim ya ce masa. "Allah ya ƙara lafiya Captain" A ransa kuwa cewa ya yi. 'By the grace of God ba zaka tashi daga wannan ciwon ba sai dai a ɗauki gawarka daga gurin nan, ba dai ka taka da ƙafafuwanka ka bar shi ba.'
Da ƙyar Madam Halima ta saka yarinyar, ta sha tea ɗin kaɗan bayan ta saka mata Fo ta yi fitsarin a ciki.
Abun mamaki kuma mijin Madam Halima yana kawo Banana ta karɓa ta fara ci cikin sauri-sauri, hakan ya ƙara nuna tana jin yunwa sosai.
Cikin mamaki Madam Halima ta dubi Mijinta Captain Abdussamad ta ce. "Captain ka ga abun mamaki, yarinyar nan ɗazu daƙyar ta sha tea kamar zata yi kuka, amma ka ga yanzu yanda take cin Bananan."
Captain dake kallon Yarinyar ya ce. "May be tana son ta ne that is why." Madam Halima ta jinjina kai ta ce. "She is so cute, amma har yanzu a cikin firgici take, ta ƙi sakin ranta ta nutsu, kamar ma a firgice take da environment ɗin"
Captain ya ce. "Dole ai, tunda babu wanda ya san tsawon lokacin da ta É—auka a hannun azzaluman mutanen can, kuma a cikin dokar daji"
Numfashi Madam Halima ta sauke ta ce. "Allah Sarki, yanzu haka maybe iyayenta sun yi cigiyar ta har sun gaji."
Captain ya ce. "Wa ya faÉ—a miki iyaye suna gajiya da neman É—ansu? Ai sai dai masu bincika musun su gaji."
Madam Halima ta ce. "Haka ne, amma yarinyar nan ba ta mun kala da 'Æ´an Africa ba, ko shi yasa idan muka yi mata magana ba ta ganewa, ko ba bahushiya bace? amma kuma É—azu ta yi mun Hausa."
Captain ya ce "Komai ma zai iya kasancewa, may be ba ta jin hausan ne sosai."
Jinjina kai kawai Madam Halima ta yi Idanunta akan yarinyar, ita kam har cikin ranta take jin tausayi da k'aunar Yarinyar, ko dan ba ta Ƴaƴa ne ya saka?
Gaba ɗaya ransa a dagule yake, yana cigaba da lissafin ta ina ze sake ɓullowa lamarin, dan wannan galabar da aka samu akan 'yan ta'adda kamar koma baya ne a gare shi, da samun raunin yadda a tsakanin sa da su Gwaska.
Wayarsa ce ta fara ringing, kamar ba ze ɗauka ba, se kuma ya miƙa hannu ya ɗauka, cikin hamzari ya miƙe tsaye yana sarawa wanda yake Maganar da shi a waya, kamar yana gabansa.
Daga cikin wayar aka ce "Mr. President ya dawo gari, ze yi zaman gaggawa da mu yau da daddare, akan harkar tsaro"
General Ibrahim yace "ok Sir" ya sake ƙamewa, sannan ya ajiye wayar.
Yana ajiyewa ya wani sake haɗe rai, tare da yin ƙwafa, ya daki tebur yai waje cikin sauri.
Manya manyan masu ruwa da tsaki a harkar al'amuran tsaro duk sun hallara, kama daga Chief of Army staff, AVM General General na sojoji, babba da ƙaramin ministan tsaro, masu bawa shugaban ƙasa shawara akan harkar tsaro, da sauran manya masu bada shawara akan harkar tsaro, da shi kansa shugaban ƙasan, sun hallara a cikin katafaren ofishin da shugaban ƙasa ke ganawar sirri, babu ɗan Jarida babu masu saka ido, babu duk wata Camera ta ɗauka, saboda ganawa ce ta sirri.
Shugaban ƙasa yai gyaran murya cikin harshen turanci yace "To nayi farin ciki matuƙa da irin nasarar da jami'an tsaron mu suka samu, akan ceto yaran nan da aka sace, dama gaba ɗaya idon duniya a kanmu yake, dan ganin ƙoƙarin da za muyi, to Alhamdilillah yaran sun kuɓuta kamar yadda na samu labari, duk da wasu sun rasa rayukansu, mun bada sanarwar jaje ga ahalin wannan yara.
Yanzu abu na gaba shine, wane mataki zamu ɗauka akan kawo ƙarshen sace mana ɗalibai da ake a makarantun kwana da ma na jeka ka dawo?
Ƙaramin ministan tsaro yace "Ai your Excellency, a nawa ganin a rufe Dukkanin makarantun sakandare da na primary na yankin gabashin ƙasar nan, tun da a nan rashin tsaron yake, zuwa a ga yadda hali ze yi"
Baban ministan tsaro yace "A' wannan ba shawara bace ai, shikenan se mu ajiye yaranmu a gida ba makaranta? Wanan ai kawo koma baya ne da naƙasu ga ilimin al'ummar yankin"
Ƙaramin ministan tsaro a ransa yace "wannan shine baban burinmu, al'ummar yankin suyi ta saun koma baya"
Haka akai ta tattaunawa, har aka samu matsaya akan cewar, dole a rufe makarantun a dakatar da ilimin wannan yankin, har se zuwa lokacin da za'a samar da tsaro.
Magana ta gaba kuma, shugaban ƙasa yai bayanin cewa, akwai ƙasashen da sukai alƙawarin tallafawa ƙasa da maƙudan kuɗaɗe dan siyo makamai da za'a bawa Sojoji dan cigaba da yaƙi.
Nan suma sojojin suka faɗi ƙorafe ƙorafensu, abubuwan da suke buƙata, da yadda kuɗaɗen da ake warewa harkar tsaro ba sa isa yadda Yakamata.
Shugaban ƙasa yai alƙawarin kafa kwamitin bibiya, akan yadda ake amfani da kuɗaɗen da ake warewa harkar tsaron.
Aka tattauna batutuwa masu mahimmanci, da shawarwari akan yadda za'a shawo kan matsalolin tsaro.
General Ibrahim yana komawa gida, ya samu wani keɓaɓɓen guri, ya fara kiran waya.
Dashshiyar muryar Gwaska ta bayyana a cikin wayar "ya, dama kai muke dako, kunyi zama da shugaban ƙasa, me ake ciki?"